LABARI NA 52
Gideon Da Mutanensa 300
KA GA abin da yake faruwa a nan? Waɗannan sune mayaƙan Isra’ila. Mutanen da suka durƙusa suna shan ruwa ne. Alƙali Gideon ne yake tsaye kusa da su. Yana kallon yadda suke shan ruwa.
Ka kalli hanyoyin da mutanen suke shan ruwa da kyau. Wasu suna saka bakinsu cikin ruwan. Amma ɗayan yana ɗiban ruwan da hannunsa, saboda ya riƙa lura da abin da yake faruwa a gefensa. Wannan yana da muhimmanci, domin Jehobah ya gaya wa Gideon ya zaɓi mutanen da suke lura da abin da yake faruwa ne sa’ad da suke shan ruwa. Allah ya ce sauran su koma gida. Bari mu ga abin da ya sa.
Isra’ilawa sun sake faɗawa cikin babban masifa kuma. Dalili kuma shi ne sun ki su yi wa Jehobah biyayya. Mutanen Midiya suka fi ƙarfin su kuma suna cin zalinsu. Saboda haka Isra’ilawa suka yi wa Jehobah kuka suna neman taimako, kuma Jehobah ya saurari kukansu.
Jehobah ya gaya wa Gideon ya tara sojoji, saboda haka Gideon ya tara mayaƙa 32,000. Amma sojojin abokan gaban Isra’ila su 135,000 ne. Duk da haka Jehobah ya gaya wa Gideon: ‘Kun yi yawa sosai.’ Me ya sa Jehobah ya faɗi haka?
Domin idan Isra’ilawa suka yi nasara a yankin, za su yi tunanin cewa su suka yi nasara da kansu. Za su kuma yi tunanin cewa ba sa bukatar taimakon Jehobah domin su yi nasara. Saboda haka Jehobah ya gaya wa Gideon: ‘Ka gaya wa dukan mutanen da suke jin tsoro su koma gida.’ Sa’ad da Gideon ya faɗi haka, mayaƙa 22,000 suka koma gida. Waɗanda suka rage mayaƙa 10,000 ne kuma suna fuskantar sojoji 135,000.
Amma ka saurara! Jehobah ya ce: ‘Har yanzu mutanenka sun yi yawa.’ Saboda haka ya gaya wa Gideon ya kai mutanen su sha ruwa a rafi kuma ya mai da dukan waɗanda suka durƙusa suka sa bakinsu cikin ruwa. ‘Zan ba ka nasara da mutane 300 da suka kasance suna lura da abin da yake faruwa a gefensu sa’ad da suke shan ruwa,’ Jehobah ya yi alkawari.
Lokacin yaƙi ya yi. Gideon ya raba mutane 300 gida uku. Ya ba kowane mutum ƙaho, da gora, da kuma tocilan. Sa’ad da dare ya yi tsaka, dukan su suka zagaya sansanin abokan gaba. Sai a lokaci ɗaya, suka busa ƙahoni, suka farfasa goruna, suka yi kururuwa: ‘Takobin Jehobah da na Gideon! Sa’ad da sojoji abokan gaba suka farka, suka rikice suka tsorata. Dukansu suka fara gudu, Isra’ilawan suka ci yaƙin.
Alƙalawa sura 6 zuwa 8.