Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Daga Lokacin Halitta Zuwa Ruwan Tufana

Daga Lokacin Halitta Zuwa Ruwan Tufana

Sashe na 1

Daga Lokacin Halitta Zuwa Ruwan Tufana

Daga ina ne sammai da duniya suka fito? Ta yaya ne rana, wata, da taurari da kuma abubuwa masu yawa na duniya suka kasance? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa na gaskiya sa’ad da ya ce Allah ne ya halicce su. Saboda haka, littafin mu ya fara da labarun halitta da suke cikin Littafi Mai Tsarki.

Mun fahimci cewa Allah ya halicci ruhohi kamarsa da farko. Mala’iku ne. Amma an halicci duniya ne domin mutane kamarmu. Saboda haka, Allah ya yi mata da miji na farko masu suna Adamu da Hauwa’u ya kuma sa su a lambu mai kyau. Amma sai suka yi wa Allah rashin biyayya suka kuma yi hasarar damar ci gaba da rayuwa.

Duka duka, daga halittar Adamu har zuwa Tufana mai girma, an yi shekara 1,656 ne. A cikin waɗannan shekaru kuma an sami miyagun mutane da yawa. A sama da akwai halittu marasa ganuwa, Shaiɗan da aljanunsa. A duniya kuma da akwai Kayinu da kuma miyagun mutane da yawa, da wasu mutane kuma masu bala’in ƙarfi. Amma da akwai mutanen kirki a duniya, Habila, Ahnuhu da kuma Nuhu. A wannan Sashe na Ɗaya za mu karanta game da waɗannan mutane da kuma abubuwan da suka faru.