Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 60

Abigail Da Dauda

Abigail Da Dauda

KA SAN wannan kyakkyawar mace da take zuwa wurin Dauda? Sunanta Abigail. Tana da hankali, kuma ta hana Dauda yin mugun abu. Amma kafin mu koyi game da wannan bari mu ga abin da ya faru da Dauda.

Bayan Dauda ya gudu daga wurin Saul, ya ɓuya cikin kogon dutse. ’Yan’uwansa da kuma sauran iyalinsa suka koma wurinsa. Wajen mutane 400 suka je wurinsa, kuma Dauda ya zama shugabansu. Dauda ya je wurin sarkin Mowab ya ce: ‘Ina roƙonka, bari babana da matata su zauna a wurinka har in ga abin da ya faru da ni.’ Daga baya Dauda da mutanensa suka fara ɓuya cikin duwatsu.

Bayan wannan ne Dauda ya sadu da Abigail. Mijinta Nabal mutum ne mai arziki. Yana da tumaki 3,000 da awaki 1,000. Nabal marowaci ne. Amma matarsa Abigail kyakkyawa ce. Kuma tana da sanin ya kamata. Ta taɓa ceton iyalinta. Bari mu gani yadda hakan ya faru.

Dauda da mutanensa sun yi wa Nabal kirki. Sun taimaka wajen kiyaye tumakinsa. Wata rana Dauda ya aiki mutanensa su nemi abinci wajen Nabal. Mutanen Dauda sun isa wajen Nabal sa’ad da shi da mutanensa suna yi wa tumakin aski. Kuma ranar biki ne, Nabal yana da abinci mai yawa. Sai mutanen Dauda suka ce: ‘Mu yi maka kirki. Ba mu saci tumakinka ba, amma mun taimaka wajen kula da su. Yanzu, muna roƙonka, ka ba mu ɗan abinci.’

Nabal ya ce: ‘Ba zan ba da abinci ga mutane irin ku ba. ’Ya yi musu baƙar magana, kuma ya zazzagi Dauda. Sa’ad da mutane suka koma suka gaya wa Dauda abin da ya faru, Dauda ya yi fushi sosai. ‘Ku ɗauki takubbanku!’ ya gaya wa mutanensa. Suka kama hanyar zuwa kashe Nabal da mutanensa.

Ɗaya daga cikin mutanen Nabal, da ya ji abin da Nabal ya faɗa, ya gaya wa Abigail abin da ya faru. Ba tare da ɓata lokaci ba, Abigail ta shirya abinci. Ta ɗora su a kan jakuna ta kama hanya zuwa wurin Dauda. Sa’ad da ta sadu da Dauda, ta sauka a kan jakinta, ta durƙusa ta ce: ‘Ina roƙonka, maigida, kada ka kula da mijina Nabal. Wawa ne, kuma ya cika yin wauta. Ga kyauta nan na kawo. Don Allah ka karɓa, kuma ka gafarta mana.’

‘Ke mace ce mai hikima,’ Dauda ya amsa mata. ‘Kin tsare ni yau daga kashe Nabal domin in rama masa rowarsa. Ki koma gidanki cikin salama.’ Daga baya da Nabal ya mutu, Abigail ta zama ɗaya cikin matan Dauda.

1 Samuila 22:1-4; 25:1-43.