Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 104

Yesu Ya Koma Sama

Yesu Ya Koma Sama

SA’AD da kwanaki suka shige, Yesu ya nuna kansa ga mabiyansa sau da yawa. Sau ɗaya har wajen almajiransa 500 suka gan shi. Sa’ad da ya bayyana musu, ka san abin da Yesu ya yi musu magana a kai? Mulkin Allah. Jehobah ya aiko Yesu duniya ne domin ya koyar da mutane game da Mulkin. Kuma ya ci gaba da yin haka har bayan an tashe shi daga matattu.

Ka tuna abin da mulkin Allah yake nufi? Hakika, Mulkin gwamnati ne na Allah a sama, kuma Yesu ne Allah ya zaɓa ya zama sarki. Kamar yadda muka koya, Yesu ya nuna cewa zai zama sarkin kirki ta wajen ciyar da mutanen da suke jin yunwa, ya warkar da marasa lafiya, kuma ya ta da matattu zuwa rai!

To, idan Yesu ya yi sarauta daga sama na shekara dubu, yaya kake tsammanin duniya za ta zama? Hakika, za a mai da dukan duniya ta zama aljanna kyakkyawa. Yaƙe-yaƙe da yin laifi da cututtuka, da mutuwa duka za su shuɗe. Mun san cewa wannan gaskiya ne domin Allah ya yi duniya ta zama aljanna domin mutane su more. Abin da ya sa ke nan ya yi lambu na Adnin da farko. Kuma Yesu zai tabbata cewa abin da Allah yake so ya kasance haka.

Lokaci ya yi da Yesu zai koma sama. Yesu ya yi kwana arba’in yana nuna kansa ga almajiransa. Saboda haka sun tabbata cewa yana da rai. Amma kafin ya bar almajiransa ya gaya masu: ‘Ku zauna a Urushalima ku jira har sai kun sami ruhu mai tsarki.’ Ruhu mai tsarki shi ne ƙarfin aiki na Allah, kamar iska mai hurawa, kuma zai taimaki mabiyansa su yi nufin Allah. A ƙarshe, Yesu ya ce: ‘Ku yi wa’azi game da ni zuwa iyakan duniya.’

Bayan Yesu ya faɗi haka, sai abin mamaki ya faru. Ya fara tashi zuwa sama, kamar yadda kake gani a nan. Sai gajimare ya rufe shi, almajiransa ba su iya ganinsa ba kuma. Yesu ya tafi sama, ya fara sarauta bisa mabiyansa a duniya.

1 Korinthiyawa 15:3-8; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4; Ayukan Manzanni 1:1-11.