LABARI NA 17
Tagwaye Da Suka Bambanta
YARAN nan biyu sun bambanta ƙwarai, ko ba haka ba? Ka san sunayensu? Mafaraucin sunansa Isuwa, wanda yake kula da tumaki kuma sunansa Yakubu.
Isuwa da Yakubu tagwaye ne ’ya’yan Ishaku da Rifkatu. Babansu Ishaku yana ƙaunar Isuwa ƙwarai, domin ya iya farauta ƙwarai, yana kawo abinci wa iyalinsa. Amma Rifkatu tana ƙaunar Ishaku sosai, domin yaro ne mai sauƙin kai, mai lumana.
Kakansu Ibrahim har ila yana da rai, za mu iya tunanin yadda Yakubu yake saurarar Ibrahim sa’ad da yake magana game da Jehobah. A ƙarshe Ibrahim ya mutu yana da shekara 175, sa’an nan tagwayen suna da shekara 15.
Sa’ad da Isuwa yana ɗan shekara 40 ya auri mata biyu daga ƙasar Kan’ana. Hakan ya ɓata wa Ishaku da Rifkatu rai, domin waɗannan mata ba sa bauta wa Jehobah.
Wata rana wani abin da ya faru ya sa Isuwa ya yi fushi ƙwarai da ɗan’uwansa Yakubu. Lokaci ya yi da Ishaku zai ba da albarkarsa ga ɗan farinsa. Tun da Isuwa ya girmi Yakubu, Isuwa yana saurarar ya sami albarka. Amma Isuwa ya riga ya sayar dama ga Yakubu da farko. Ban da haka, sa’ad da aka haife su Allah ya ce Yakubu ne zai karɓi albarkar. Kuma abin da ya faru ke nan. Ishaku ya yi wa ɗansa Yakubu albarka.
Daga baya da Isuwa ya sami labarin haka sai ya yi fushi ƙwarai da Yakubu. Ya yi fushi ƙwarai har ya ce zai kashe Yakubu. Sa’ad da Rifkatu ta sami labarin haka, sai ta damu ƙwarai. Saboda haka ta gaya wa mijinta Ishaku: ‘Ba zai yi daɗi ba idan Yakubu ma ya auri ɗaya daga cikin waɗannan matan Kan’ana.’
Saboda haka Ishaku ya kira ɗansa Yakubu ya ce masa: ‘Kada ka auri mace daga Kan’ana. Maimakon haka ka tafi gidansu kakanka Bethuel a Haran. Ka auri ɗaya daga cikin ’ya’yan ɗansa Laban.’
Yakubu ya saurari abin da babansa ya ce, ba tare da ɓata lokaci ba ya fara doguwar tafiya zuwa inda ’yan’uwansa suke a Haran.
Farawa 25:5-11, 20-34; 26:34, 35; 27:1-46; 28:1-5; Ibraniyawa 12:16, 17.