Tambayoyi don Nazarin Littafina Na Labarun Littafi Mai Tsarki
Labari na 1
Allah Ya Fara Halittar Abubuwa
Daga ina dukan abubuwa masu kyau suka fito, kuma za ka iya ba da misali?
Menene Allah ya halitta da farko?
Me ya sa mala’ika da Allah ya halitta da farko mala’ika ne na musamman?
Ka kwatanta yadda duniya take da farko. (Dubi hoto.)
Ta yaya Allah ya fara shirya duniya domin dabbobi da kuma mutane?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Irmiya 10:12.
Waɗanne halayen Allah ne suka bayyana ta wajen abubuwan da ya halitta? (Ish. 40:26; Rom. 11:33)
Ka karanta Kolossiyawa 1:15-17.
Wane abu Yesu ya yi a lokacin halitta, kuma ta yaya wannan ya kamata ya shafi yadda muka ɗauka shi? (Kol. 1:15-17)
Ka karanta Farawa 1:1-10.
Wanene ya halicci duniya? (Far. 1:1)
Menene ya faru a ranar farko ta halitta? (Far. 1:3-5)
Ka kwatanta abin da ya faru a rana ta biyu ta halitta. (Far. 1:7, 8)
Lambu Mai Kyau
Ta yaya Allah ya shirya duniya domin ta zama gidanmu?
Ka kwatanta ire-iren dabbobin da Allah ya halitta. (Dubi hoto.)
Me ya sa lambun Adnin wuri ne na musamman?
Menene Allah yake so dukan duniya ta zama?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 1:11-25.
Menene Allah ya halitta a rana ta uku ta halitta? (Far. 1:12)
Menene ya faru a rana ta huɗu ta halitta? (Far. 1:16)
Waɗanne irin dabbobi ne Allah ya halitta a rana ta biyar da ta shida? (Far. 1:20, 21, 25)
Ka karanta Farawa 2:8, 9.
Waɗanne itatuwa ne biyu na musamman Allah ya saka a lambun, kuma alamar menene ne su?
Namiji da Ta Mace na Farko
Ta yaya hoton da yake Labari na 3 ya bambanta da wanda yake Labari na 2?
Wanene ya halicci mutum na farko, kuma menene sunan mutumin?
Wane aiki ne Allah ya ba Adamu ya yi?
Me ya sa Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zurfi?
Shekara nawa ne Adamu da Hauwa’u za su rayu, kuma wane aiki ne Jehobah yake so su yi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Zabura 83:18.
Menene sunan Allah, kuma wane matsayi ne shi kaɗai yake da shi bisa duniya? (Irm. 16:21; Dan. 4:17)
Ka karanta Farawa 1:26-31.
Menene Allah ya halitta a ƙarshe a rana ta shida, kuma ta yaya wannan halittar ya bambanta da dabbobi? (Far. 1:26)
Wane tanadi ne Jehobah ya yi wa mutane da kuma dabbobi? (Far. 1:30)
Ka karanta Farawa 2:7-25.
Menene aikin Adamu na raɗa wa dabbobi suna ya ƙunsa? (Far. 2:19)
Ta yaya Farawa 2:24 ta taimake mu mu fahimci yadda Allah yake ɗaukan aure, yaji, da kuma kisan aure? (Far. 2:24; Mat. 19:4-6, 9)
Abin da Ya Sa Suka Yi Rashin Gidansu
A hoton, menene yake faruwa da Adamu da Hauwa’u?
Me ya sa Jehobah ya yi musu horo?
Menene maciji ya gaya wa Hauwa’u?
Wanene ya sa macijin ya yi wa Hauwa’u magana?
Me ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi rashin gidansu na Aljanna?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 2:16, 17 da kuma 3:1-13, 24.
Ta yaya ne tambayar da macijin ya yi wa Hauwa’u ta murguɗa manufar Jehobah? (Far. 3:1-5; 1 Yoh. 5:3)
Ta yaya Hauwa’u ta kasance misalin gargaɗi a gare mu? (Filib. 4:8; Yaƙ. 1:14, 15; 1 Yoh. 2:16)
A waɗanne hanyoyi ne Adamu da Hauwa’u suka ƙi su ɗauki hakkinsu? (Far. 3:12, 13)
Ta yaya mala’iku da suke gadi a gabashin gonar Adnin suka ɗaukaka ikon mallaka na Jehobah? (Far. 3:24)
Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Yaya yawan nasarar da Shaiɗan ya samu wajen juya ’yan Adam daga mulkin Allah? (1 Yoh. 5:19)
An Fara Rayuwa Mai Wuya
Yaya rayuwa ta kasance ga Adamu da Hauwa’u da aka kore su daga lambun Adnin?
Menene ya fara faruwa da Adamu da Hauwa’u, kuma me ya sa?
Me ya sa ’ya’yan Adamu da Hauwa’u za su tsufa kuma su mutu?
Da a ce Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah biyayya, da yaya rayuwa za ta kasance wa su da ’ya’yansu?
Ta yaya rashin biyayya na Hauwa’u ya jawo mata azaba?
Menene sunayen ’ya’yan Adamu da Hauwa’u biyu na farko?
Su wanene ne waɗannan sauran yara a hoto?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 3:16-23 da Kuma 4:1, 2.
Yaya la’anta ƙasa ta shafi rayuwar Adamu? (Far. 3:17-19; Rom. 8:20, 22)
Me ya sa sunan Hauwa’u, mai nufin ‘mai rai,’ ya dace? (Far. 3:20)
Ta yaya Jehobah ya nuna sanin ya kamata ga Adamu da Hauwa’u har bayan sun yi zunubi? (Far. 3:7, 21)
Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
Waɗanne “al’amura na fari” ne ka ke so ka ga sun shuɗe?
Ɗan Kirki, da Kuma Mugun Ɗa
Wace sana’a ce Kayinu da Habila suka shiga?
Wane baiko Kayinu da Habila suka bai wa Jehobah?
Me ya sa Jehobah ya yi farin ciki da baikon Habila, kuma me ya sa bai yi farin ciki ba da na Kayinu ba?
Wane irin mutumi ne Kayinu, kuma ta yaya Jehobah ya so ya yi masa gyara?
Menene Kayinu ya yi sa’ad shi da ƙaninsa kaɗai suke daji?
Ka bayyana abin da ya faru da Kayinu bayan ya kashe ɗan’uwansa.
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 4:2-26.
Ta yaya Jehobah ya kwatanta mugun yanayin da Kayinu ya shiga? (Far. 4:7)
Ta yaya Kayinu ya nuna abin da ke cikin zuciyarsa? (Far. 4:9)
Menene ra’ayin Jehobah game da zubar da jinin marar laifi? (Far. 4:10; Ish. 26:21)
Ka karanta Farawa 1 Yohanna 3:11, 12.
Me ya sa Kayinu ya yi fushi ƙwarai, kuma ta yaya wannan ya kasance gargaɗi a gare mu a yau? (Far. 4:4, 5; Mis. 14:30; 28:22)
Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ko idan dukan iyalanmu suka yi hamayya da Jehobah, mu za mu iya kasancewa da aminci? (Zab. 27:10; Mat.10:21, 22)
Ka karanta Yohanna 11:25.
Wane tabbaci ne Jehobah ya bayar game da dukan waɗanda suka mutu domin adalci? (Yoh. 5:24)
Gwarzon Mutum
Ta yaya Ahnuhu ya bambanta?
Me ya sa mutane a zamanin Ahnuhu suke ta yin miyagun abubuwa?
Waɗanne miyagun abubuwa ne mutane suke yi? (Dubi hoto.)
Me ya sa Ahnuhu yake bukatar ya kasance da ƙarfin zuciya?
Shekara nawa ne mutane suke yi a wancan zamanin, kuma shekara nawa Ahnuhu ya yi?
Menene ya faru bayan Ahnuhu ya mutu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 5:24, 27.
Wane irin dangantaka ce Ahnuhu ya yi da Jehobah? (Far. 5:24)
In ji Littafi Mai Tsarki, wane mutum ne ya fi kowa tsufa a duniya, kuma shekarunsa nawa ne sa’ad da ya mutu? (Far. 5:27)
Ka karanta Farawa 6:5.
Yaya yanayi ya zama a duniya bayan mutuwar Ahnuhu, kuma yaya wannan ya yi kama da zamaninmu? (2 Tim. 3:13)
Ka karanta Ibraniyawa 11:5.
Wane halin Ahnuhu ne ya ‘game Allah sarai’ kuma menene sakamakon haka? (Far. 5:22)
Ka karanta Yahuda 14, 15.
Ta yaya Kiristoci a yau za su yi koyi da ƙarfin zuciyar Ahnuhu, sa’ad da suke yi wa mutane gargaɗi game da yaƙin Armagedon mai zuwa? (2 Tim. 4:2; Ibra. 13:6)
Ƙattai a Duniya
Menene ya faru sa’ad da wasu mala’ikun Allah suka saurari Shaiɗan?
Me ya sa wasu mala’iku suka bar aikinsu a sama suka sauko duniya?
Me ya sa ba daidai ba ne mala’iku su sauko duniya su ɗauki jiki na mutane?
Ta yaya ’ya’yan mala’ikun suka bambanta?
Kamar yadda kake gani a wannan hoton, menene ’ya’yan mala’ikun suka yi sa’ad da suka zama ƙattai?
Bayan Ahnuhu, wane mutumin kirki ne kuma ya rayu a duniya kuma me ya sa Allah yake sonsa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 6:1-8.
Menene Farawa 6:6 ta nuna game da yadda halinmu zai shafi Jehobah? (Za. 78:40, 41; Mis. 27:11)
Ka karanta Yahuda 6.
Ta yaya ne mala’ikun “da ba su riƙe matsayi nasu ba” a zamanin Nuhu suka kasance abin tuni a gare mu a yau? (1 Kor. 3:5-9; 2 Bit. 2:4, 9, 10)
Nuhu Ya Gina Jirgi
Mutane nawa ne suke cikin iyalin Nuhu, kuma menene sunayen ’ya’yansa uku?
Wane abin mamaki ne Allah ya ce wa Nuhu ya yi, kuma me ya sa?
Menene maƙwabtan Nuhu suka yi sa’ad da ya gaya musu game da jirgin?
Menene Allah ya gaya wa Nuhu ya yi da dabbobi?
Bayan da Allah ya rufe ƙofar jirgin, menene Nuhu da iyalinsa suka yi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 6:9-22.
Menene ya sa Nuhu ya kasance fitaccen bawan Jehobah? (Far. 6:9, 22)
Yaya Jehobah ya ji game da muguntar da ake yi, kuma ta yaya wannan ya kamata ya shafi irin nishaɗi da muke so? (Far. 6:11, 12; Zab. 11:5)
Ta yaya za mu yi koyi da Nuhu sa’ad da muka sami ja-gora ta wurin ƙungiyar Jehobah? (Far. 6:22; 1 Yoh. 5:3)
Ka karanta Farawa 7:1-9.
Ta yaya ne yadda Jehobah ya ɗauki Nuhu mutum ajizai mai adalci zai ƙarfafa mu a yau? (Far. 7:1; Mis. 10:16; Isha. 26:7)
Ruwan Tufana Mai Yawa
Me ya sa babu wanda zai iya shiga cikin jirgin da zarar an fara ruwa?
Jehobah ya sa an yi ruwa na kwana nawa, kuma yaya zurfin ruwan ya zama?
Menene ya sami jirgin sa’ad da ruwan ya fara rufe duniya?
Ƙattan su tsira ne daga Tufana, kuma menene ya faru da iyayen ƙattan?
Menene ya faru da jirgin bayan watanni biyar?
Me ya sa Nuhu ya saki hankaka daga cikin jirgin?
Ta yaya Nuhu ya sani cewa ruwa ya ragu daga duniya?
Menene Allah ya gaya wa Nuhu bayan shi da iyalinsa sun yi fiye da shekara guda cikin jirgin?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 7:10-24.
Dukan abubuwa masu rai ne aka halaka daga duniya? (Far. 7:23)
Kwanaki nawa aka yi kafin ruwan Tufana ya ragu? (Far. 7:24)
Ka karanta Farawa 8:1-17.
Ta yaya Farawa 8:17 ta nuna cewa ainihin nufin Jehobah ga duniya bai canja ba? (Far. 8:17; 1:22)
Ka karanta 1 Bitrus 3:19, 20.
Sa’ad da mala’iku da suka yi tawaye suka koma sama wane hukunci aka yi musu? (Yahuda 6)
Ta yaya labarin Nuhu da iyalinsa ya ƙarfafa dogararmu ga iyawar Jehobah ya ceci mutanensa? (2 Bit. 2:9)
Bakan Gizo na Farko
Kamar yadda aka nuna a wannan hoton, menene Nuhu ya yi da farko bayan ya fita daga cikin jirgi?
Wace doka Allah ya bai wa Nuhu da iyalinsa bayan Tufana?
Wane alkawari ne Allah ya yi?
Sa’ad da muka ga bakan gizo, menene ya kamata ya tuna mana?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 8:18-22.
Ta yaya za mu iya ba Jehobah “ƙanshi mai daɗi” a yau? (Farawa 8:21; Ibraniyawa 13:15, 16)
Menene Jehobah ya lura da shi game da yanayin zuciyar mutum, kuma yaya ya kamata mu mai da hankali? (Far. 8:21; Mat. 15:18, 19)
Ka karanta Farawa 9:9-17.
Wane alkawari ne Jehobah ya yi da dukan halittun da ke duniya? (Far. 9:10, 11)
Yaya tsawon lokacin alkawarin na bakan gizon zai kasance? (Far. 9:16)
Mutane Sun Gina Babbar Hasumiya
Wanene Nim’rod, kuma yaya Allah ya ji game da shi?
A wannan hoton, me ya sa mutane suke yin tubali?
Me ya sa Jehobah bai yi farin ciki da ginin da suke yi ba?
Ta yaya Allah ya sa suka daina gina hasumiyar?
Menene sunan birnin, kuma menene ma’anar sunan?
Menene ya faru da mutanen bayan da Allah ya rikita yarensu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 10:1, 8-10.
Waɗanne halaye ne Nimrod ya nuna, kuma wane gargaɗi ne wannan ya yi mana? (Mis. 3:31)
Ka karanta Farawa 11:1-9.
Menene dalilin gina wannan hasumiya, kuma me ya sa ginin bai yi nasara ba? (Far. 11:4; Mis. 16:18; Yoh. 5:44)
Ibrahim, Abokin Allah
Waɗanne irin mutane ne suke zaune a birnin Ur?
Wanene a wannan hoton, yaushe aka haife shi, kuma a ina yake da zama?
Menene Allah ya gaya wa Ibrahim ya yi?
Me ya sa aka kira Ibrahim abokin Allah?
Su waye suka bi Ibrahim sa’ad da ya bar birnin Ur?
Menene Allah ya gaya wa Ibrahim sa’ad da ya isa ƙasar Kan’ana?
Menene Allah ya yi wa Ibrahim alkawari sa’ad da yake shekara 99 da haihuwa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 11:27-32.
Menene dangantakar Ibrahim da Lutu? (Far. 11:27)
Ko da yake an ce Terah ya ƙaura da iyalinsa zuwa Kan’ana, ta yaya muka sani cewa ainihi Ibrahim ne ya sa aka ƙaura, kuma me ya sa ya ƙaura? (Far. 11:31; A. M. 7:2-4)
Ka karanta Farawa 12:1-7.
Ta yaya Jehobah ya faɗaɗa alkawarinsa ga Ibrahim bayan Ibrahim ya isa ƙasar Kan’ana? (Far. 12:7)
Ka karanta Farawa 17:1-8, 15-17.
Wane suna aka bai wa Abram sa’ad da yake da shekara 99, kuma me ya sa? (Far. 17:5)
Wace albarka ce Jehobah ya yi alkawari zai yi wa Saratu a nan gaba? (Far. 17:15, 16)
Ka karanta Farawa 18:9-19.
Wane hakki ne aka bai wa Ubanni a Farawa 18:19? (K. Sha 6:6, 7; Afis. 6:4)
Wane abu ne da Saratu ta yi ya nuna cewa babu abin da za mu iya ɓoye wa Jehobah? (Far. 18:12, 15; Zab. 44:21)
Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim
Wane alkawari ne Allah ya yi wa Ibrahim, kuma ta yaya Allah ya cika alkawarinsa?
Kamar yadda aka nuna a cikin hoton nan, ta yaya Allah ya gwada bangaskiyar Ibrahim?
Menene Ibrahim ya yi ko da yake bai fahimci dalilin wannan umurni daga Allah ba?
Menene ya faru sa’ad da Ibrahim ya zaro wuƙa zai yanka ɗansa?
Yaya ƙarfin bangaskiyar Ibrahim ga Allah?
Menene Allah ya bai wa Ibrahim ya yi hadaya da shi, kuma ta yaya ya ba shi ragon?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 21:1-7.
Me ya sa Ibrahim ya yi wa ɗansa kaciya a rana ta takwas? (Far. 17:10-12; 21:4)
Ka karanta 22:1-18.
Ta yaya Ishaku ya miƙa wa babansa Ibrahim kai, kuma ta yaya wannan ya nuna abu mafi muhimmanci da zai faru a nan gaba? (Far. 22:7-9; 1 Kor. 5:7; Filib. 2:8, 9)
Matar Lutu Ta Dubi Baya
Me ya sa Ibrahim da Lutu suka rabu?
Me ya sa Lutu ya zaɓi ya zauna a Saduma?
Yaya halin mutanen Saduma yake?
Wane gargaɗi mala’iku biyu suka yi wa Lutu?
Me ya sa matar Lutu ta zama gishiri?
Wane darassi ne za mu iya koya daga abin da ya sami matar Lutu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 13:5-13.
Game da sasanta matsala tsakanin mutane, wane darassi za mu koya daga Ibrahim? (Far. 13:8, 9; Rom. 12:10; Filib. 2:3, 4)
Ka karanta Farawa 18:20-33.
Ta yaya yadda Jehobah ya yi sha’ani da Ibrahim ya ba mu tabbaci cewa Jehobah da Yesu za su yi shari’a da adalci? (Far. 18:25, 26; Mat. 25:31-33)
Ka karanta Farawa 19:1-29.
Menene labarin Littafi Mai Tsarki ya nuna game da yadda Allah yake ganin luwaɗi? (Far. 19:5, 13; Lev. 20:13)
Wane bambanci muka gani tsakanin yadda Lutu da Ibrahim suka bi ja-gorar Allah, kuma menene za mu koya daga wannan? (Far. 19:15, 16, 19, 20; 22:3)
Ka karanta Luka 17:28-32.
Yaya matar Lutu ta ɗauki abin duniya a zuciyarta, kuma ta yaya wannan zai kasance gargaɗi a gare mu? (Luk. 12:15; 17:31, 32; Mat. 6:19-21, 25)
Ka karanta 2 Bitrus 2:6-8.
Wajen koyi da Lutu, yaya ya kamata mu kasance a wannan duniya marar ibada? (Ezek. 9:4; 1 Yoh. 2:15-17)
Ishaku Ya Auri Matar Kirki
Su wanene ne mace da namiji da suke wannan hoton?
Menene Ibrahim ya yi domin ya samo mata ga ɗan, kuma me ya sa?
Ta yaya aka amsa addu’ar bawan Ibrahim?
Wace amsa Rifkatu ta bayar sa’ad da aka tambaye ta ko tana son ta auri Ishaku?
Menene ya sa Ishaku ya sake farin ciki kuma?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 24:1-67.
Wane halin kirki ne Rifkatu ta nuna sa’ad da ta sadu da bawan Ibrahim a bakin rijiya? (Far. 24:17-20; Mis. 31:17, 31)
Shirin da Ibrahim ya yi domin Ishaku ya ba da wane kyakkyawan misali ga Kiristoci a yau? (Far. 24:37, 38; 1 Kor. 7:39; 2 Kor. 6:14)
Me ya sa ya kamata mu nemi lokacin yin bimbini kamar yadda Ishaku ya yi? (Far. 24:63; Zab. 77:12; Filib. 4:8)
Tagwaye da Suka Bambanta
Su waye ne Isuwa da Yakubu, kuma ta yaya suka bambanta?
Isuwa da Yakubu suna ’yan shekara nawa ne sa’ad da kakansu Ibrahim ya rasu?
Menene Isuwa ya yi da ya sa mamarsa da babansa baƙin ciki?
Me ya sa Isuwa ya yi fushi da ɗan’uwansa Yakubu?
Wane umurni Ishaku ya bai wa ɗansa Yakubu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 25:5-11, 20-34.
Menene Jehobah ya annabta game da tagwayen Rifkatu? (Far. 25:23)
Wane bambanci ne ke tsakanin halin Isuwa da na Yakubu game da zama ɗan fari? (Far. 25:31-34)
Ka karanta Farawa 26:34, 35; 27:1-46; da kuma 28:1-5.
Ta yaya rashin ƙaunar abubuwa na ruhaniya na Isuwa ya bayyana? (Far. 26:34, 35; 27:46)
Domin Yakubu ya sami albarkar Allah, menene Ishaku ya ce masa ya yi? (Far. 28:1-4)
Ka karanta 12:16, 17.
Menene misalin Isuwa ya nuna game da ƙarshen waɗanda suke marasa ibada?
Yakubu Ya Tafi Haran
Wace budurwa ce a wannan hoton, kuma menene Yakubu ya yi mata?
Menene Yakubu yake shirye ya yi domin ya auri Rahila?
Menene Laban ya yi sa’ad da lokaci ya yi Yakubu ya auri Rahila?
Menene Yakubu ya yarda zai yi domin ya auri Rahila?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 29:1-30.
Ko da yake Laban ya yaudare shi, ta yaya Yakubu ya nuna cewa yana da daraja, kuma menene za mu koya daga wannan? (Far. 25:27; 29:26-28; Mat. 5:37)
Ta yaya misalin Yakubu ya nuna bambancin da ke tsakanin ƙauna da sha’awa? (Far. 29:18, 20, 30; W. Waƙ. 8:6)
Waɗanne mata huɗu ne suka zama matan Yakubu kuma suka haifa masa yara? (Far. 29:23, 24, 28, 29)
Yakubu Yana da Babban Iyali
Menene sunayen ’ya’ya maza shida na Yakubu da matarsa ta fari Lai’atu ta haifa masa?
Waɗanne yara maza biyu ne baiwar Lai’atu Zilpah ta haifa wa Yakubu?
Menene sunayen ’ya’ya maza biyu da baiwar Rahila Bilhah ta haifa wa Yakubu?
Waɗanne ’ya’ya maza biyu ne Rahila ta haifa, kuma menene ya faru sa’ad da ta haifi na biyun?
A wannan hoton, ’ya’ya maza nawa ne Yakubu yake da su, kuma me ya zo daga gare su?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 29:32-35; 30:1-26; sai kuma 35:16-19.
Kamar yadda ya bayyana a ’ya’ya 12 na Yakubu, ta yaya Ibraniyawa na dā suke ba wa ’ya’yansu suna?
Ka karanta Farawa 37:35.
Ko da yake Dinah kaɗai ce aka ambata sunanta cikin Littafi Mai Tsarki, ta yaya muka sani cewa Yakubu yana da fiye da ’ya mace guda? (Far. 37:34, 35)
Dinah Ta Shiga Masifa
Me ya sa Ibrahim da Ishaku ba su so ’ya’yansu su yi aure daga ƙasar Kan’ana ba?
Shin Yakubu ya yarda ne ’yarsa ta yi kawance da ’ya’yan Kan’ana?
Wanene ne wannan da yake kallon Dinah a wannan hoton, kuma wane mugun abu ya yi?
Menene yayun Dinah Simeon da Lawi suka yi da suka sami labarin abin da ya faru?
Shin Yakubu ya yarda ne da abin da Simeon da Lawi suka yi?
Ta yaya ne dukan wannan matsalar ta iyalin ta fara?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 34:1-31.
Shin kawance da Dinah ta yi da ’ya’yan Kan’ana sau ɗaya ne kawai? Ka yi bayani. (Far. 34:1)
Me ya sa Dinah ma tana da ɗan laifi wajen abin da ya same ta? (Gal. 6:7)
Ta yaya matasa a yau za su nuna cewa sun riƙe misalin gargaɗi na Dinah a zukatansu? (Mis. 13:20; 1 Kor. 15:33; 1 Yoh. 5:19)
’Yan’uwan Yusufu Ba Sa Son Shi
Me ya sa ’yan’uwan Yusufu suka yi kishinsa, kuma menene suka yi?
Menene ’yan’uwan Yusufu suke so su yi masa, amma menene Reuben ya ce?
Menene ya faru sa’ad da Isma’ilawa ’yan kasuwa suka zo wucewa?
Menene ’yan’uwan Yusufu suka yi domin babansu ya yi tunanin cewa Yusufu ya mutu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 37:1-35.
Ta yaya Kiristoci za su bi misalin Yusufu ta wajen sanar da laifi a cikin ikilisiya? (Far. 37:2; Lev. 5:1; 1 Kor. 1:11)
Menene ya sa ’yan’uwan Yusufu suka yi masa mugunta? (Far. 37:11, 18; Mis. 27:4; Yaƙ. 3:14-16)
Menene Yakubu ya yi da daidai ne ga mutumin da yake makoki? (Far. 37:35)
An Jefa Yusufu a Kurkuku
Shekarar Yusufu nawa ne sa’ad da aka kai shi ƙasar Masar, kuma menene ya faru sa’ad da ya isa can?
Me ya sa aka jefa Yusufu a kurkuku?
Wane aiki aka ba wa Yusufu a kurkukun?
Menene Yusufu ya yi a kurkuku ga mai shayarwa da mai tuya?
Menene ya faru bayan da aka sallami mai shayarwa daga kurkuku?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 39:1-23.
Tun da babu rubutacciyar doka daga Allah da ta hana zina a zamanin Yusufu, menene ya sa shi ya guje wa matar Fotifa? (Far. 2:24; 20:3; 39:9)
Ka karanta Farawa 40:1-23.
Ka kwatanta a taƙaice mafarkin mai shayarwa da kuma fassarar da Jehobah ya bai wa Yusufu. (Far. 40:9-13)
Wane mafarki mai tuya ya yi, kuma menene ma’anarsa? (Far. 40:16-19)
Ta yaya bawa mai-aminci, mai-hikima a yau yake koyi da halin Yusufu? (Far. 40:8; Zab. 36:9; Yoh. 17:17; A. M. 17:2, 3)
Ta yaya Farawa 40:20 ta ba da haske game da ra’ayin Kiristoci game da batun bikin ranar haihuwa? (M. Wa. 7:1; Mar. 6:21-28)
Mafarkan Fir’auna
Menene Fir’una ya yi cikin wani dare?
Me ya sa a ƙarshe mai shayarwa ya tuna da Yusufu?
Kamar yadda aka nuna a wannan hoton, waɗanne mafarkai biyu ne Fir’auna ya yi?
Menene Yusufu ya ce shi ne ma’anar mafarkan?
Ta yaya Yusufu ya zama na biyun Fir’auna wajen martaba a dukan ƙasar Masar?
Me ya sa ’yan’uwan Yusufu suka je ƙasar Masar, kuma me ya sa ba su gane shi ba?
Wane mafarki ne Yusufu ya tuna, kuma menene ya taimake shi ya fahimta?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 41:1-57.
Ta yaya Yusufu ya mai da hankali ga Jehobah, kuma ta wace hanya ce Kiristoci a yau za su bi misalinsa? (Far. 41:16, 25, 28; Mat. 5:16; 1 Bit. 2:12)
Ta yaya shekarun ƙaranci da suka bi bayan shekarun yalwa a ƙasar Masar suka kwatanta daidai yanayi na ruhaniya na mutanen Jehobah a yau da na Kiristendam? (Far. 41:29, 30; Amos 8:11, 12)
Ka karanta Farawa 42:1-8 da 50:20.
Laifi ne bayin Jehobah su durƙusa a gaban mutum domin daraja matsayinsa idan al’adar ƙasar ce? (Far. 42:6)
Yusufu Ya Gwada ’Yan’uwansa
Me ya sa Yusufu ya ce wa ’yan’uwansa su ’yan leƙen asiri ne?
Me ya sa Yakubu ya ƙyale ɗan autansa ya je ƙasar Masar?
Ta yaya kofin azurfa na Yusufu ya shiga jakar Biliyaminu?
Menene Yahuda ya ce zai yi domin a ƙyale Biliyaminu?
Ta yaya ’yan’uwan Yusufu suka gyara halinsu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 42:9-38.
Ta yaya furcin Yusufu a Farawa 42:18 abin tunawa ne mai kyau ga waɗanda suke da hakki cikin ƙungiyar Jehobah a yau? (Neh. 5:15; 2 Kor. 7:1, 2)
Ka karanta Farawa 43:1-34.
Ko da yake Reuben ne ɗan farin, ta yaya ya bayyana cewa Yahuda ne kakakin ’yan’uwansa? (Far. 43:3, 8, 9; 44:14, 18; 1 Laba. 5:2)
Ta yaya Yusufu ya gwada ’yan’uwansa, kuma me ya sa? (Far. 43:33, 34)
Ka karanta Farawa 44:1-34.
Ta yaya Yusufu ya gabatar da kansa domin kada ’yan’uwansa su gane shi? (Far. 44:5, 15; Lev. 19:26)
Ta yaya ’yan’uwan Yusufu suka nuna cewa sun daina yin irin kishin da suka yi wa ɗan’uwansu a da? (Far. 44:13, 33, 34)
Iyalin Ta Ƙaura Zuwa Ƙasar Masar
Menene ya faru sa’ad da Yusufu ya gaya wa ’yan’uwansa shi Yusufu ne?
Wane bayani Yusufu ya yi wa ’yan’uwansa?
Menene Fir’auna ya ce sa’ad da ya sami labarin ’yan’uwan Yusufu?
Yaya girman iyalin Yakubu sa’ad da suka ƙaura zuwa ƙasar Masar?
Me aka koma kiran iyalin Yakubu kuma me ya sa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Farawa 45:1-28.
Ta yaya labarin Yusufu a cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah zai iya canja niyyar cutar da bayinsa zuwa albarka? (Far. 45:5-8; Isha. 8:10; Filib. 1:12-14)
Ka karanta Farawa 46:1-27.
Wane tabbaci Jehobah ya bai wa Yakubu a hanyarsa ta zuwa ƙasar Masar? (Far. 46:1-4)
Ayuba Mai Aminci ne ga Allah
Wanene Ayuba?
Menene Shaiɗan ya yi ƙoƙarin yi, ya yi nasara ne?
Menene Jehobah ya ba wa Shaiɗan izinin ya yi, kuma me ya sa?
Me ya sa matar Ayuba ta ce masa “la’anci Allah ka mutu”? (Dubi hoto.)
Kamar yadda ka gani a hoto na biyu, ta yaya Jehobah ya albarkaci Ayuba, kuma me ya sa?
Idan kamar Ayuba muka kasance da aminci ga Jehobah, wace albarka ce za mu samu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayuba 1:1-22.
Ta yaya Kiristoci a yau za su yi koyi da Ayuba? (Filib. 2:15; 2 Bit. 3:14)
Ka karanta Ayuba 2:1-13.
A waɗanne hanyoyi biyu ne dabam dabam Ayuba da matarsa suka amsa tsanantawa na Shaiɗan? (Ayu. 2:9, 10; Mis. 19:3; Mik. 7:7; Mal. 3:14)
Ka karanta Ayuba 42:10-17.
Waɗanne kamanni ne ke tsakanin albarkatai da Ayuba da kuma Yesu suka samu domin rayuwarsu ta aminci? (Ayu. 42:12; Filib. 2:9-11)
Ta yaya albarkar da Ayuba ya samu domin kasancewarsa da aminci ga Allah ya ƙarfafa mu? (Ayu. 42:10, 12; Ibran. 6:10; Yaƙ. 1:2-4, 12; 5:11)
Mugun Sarki Yana Sarauta a Masar
A wannan hoton wanene wannan mutumin da yake riƙe da bulala, kuma waye yake bugu da bulalar?
Bayan mutuwar Yusufu me ya sami Isra’ilawa?
Me ya sa Masarawa suka ji tsoron Isra’ilawa?
Wace doka Fir’auna ya ba wa matan da suke taimakon Isra’ilawa mata su haihu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 1:6-22.
A wace hanya ce Jehobah ya fara cika alkawarinsa ga Ibrahim? (Fit. 1:7; Far. 12:2; A. M. 7:17)
Ta yaya ungozomai Ibraniyawa suka nuna daraja da tsarkakar rai? (Fit. 1:17; Far. 9:6)
Ta yaya aka albarkaci ungozomai domin amincinsu ga Jehobah? (Fit. 1:20, 21; Mis. 19:17)
Ta yaya Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya lalata nufin Allah game da zuriya da aka yi wa Ibrahim alkawari? (Fit. 1:22; Mat. 2:16))
Yadda Aka Ceci Musa Yana Jariri
Wane jariri ne ke wannan hoton, kuma yatsar waye ya riƙe?
Menene mamar Musa ta yi domin kada a kashe shi?
Wace yarinya ce a wannan hoton, kuma menene ta yi?
Sa’ad da ’yar Fir’auna ta sami jaririn, wace shawara ce Maryamu ta bayar?
Menene gimbiyar ta ce wa mamar Musa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 2:1-10.
Wane zarafi mamar Musa ta samu na koyar da Musa sa’ad da yake yaro, kuma wane misali wannan ya kafa wa iyaye a yau? (Fit. 2:9, 10; K. Sha 6:6-9; Mis. 22:6; Afis. 6:4; 2 Tim. 3:15)
Dalilin da Ya Sa Musa Ya Gudu
A ina Musa ya girma, kuma menene ya sani game da iyayensa?
Menene Musa ya yi sa’ad da yake ɗan shekara 40 da haihuwa?
Menene Musa ya gaya wa wani Ba’isra’ile da yake faɗa, kuma yaya mutumin ya amsa masa?
Me ya sa Musa ya gudu daga ƙasar Masar?
Ina ne Musa ya gudu ya tafi, kuma wa ya sadu a can?
Menene Musa ya yi a cikin shekaru 40 da ya gudu daga ƙasar Masar?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 2:11-25.
Duk da shekaru masu yawa da ya yi yana koyon hikimar Masarawa, ta yaya Musa ya nuna amincinsa ga Jehobah da kuma mutanensa? (Fit. 2:11, 12; Ibran. 11:24)
Ka karanta Ayukan Manzani 7:22-29.
Wane darasi za mu koya daga ƙoƙarin Musa ya ceci Isra’ilawa daga bauta da ikonsa? (A. M. 7:23-25; 1 Bit. 5:6, 10)
Kurmi Mai Cin Wuta
Menene sunan wannan dutse da ke hoton nan?
Ka kwatanta abin mamakin da Musa ya gani sa’ad da ya je wannan dutsen da tumakinsa.
Menene murya ta ce daga kurmi mai cin wuta, kuma muryar wanene?
Yaya Musa ya amsa sa’ad da Allah ya ce masa zai ceci mutanensa daga ƙasar Masar?
Menene Allah ya gaya wa Musa ya ce idan mutanen suka tambaye shi wanene ya aiko shi?
Ta yaya Musa zai tabbatar da cewa Allah ne ya aiko shi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 3:1-22.
Ta yaya labarin Musa zai ba mu tabbaci cewa idan muka ji kamar ba mu cancanci aikin da Jehobah ya ba mu ba, zai taimake mu? (Fit. 3:11, 13; 2 Kor. 3:5, 6)
Ka karanta 4:1-20.
Wane canji Musa ya yi a halinsa cikin shekara 40 da ya yi a Midiya, kuma wane darasi waɗanda suke burin samun gata a ikilisiya za su koya daga wannan? (Fit. 2:11, 12; 4:10, 13; Mik. 6:8; 1 Tim. 3:1, 6, 10)
Ko da a ce Jehobah ya yi mana horo ta ƙungiyarsa, wane tabbaci misalin Musa zai ba mu? (Fit. 4:12-14; Zab. 103:14; Ibran. 12:4-11)
Musa da Haruna Sun Je Wurin Fir’auna
Yaya mu’ujizai da Musa da Haruna suka yi suka shafi Isra’ilawa?
Menene Musa da Haruna suka gaya wa Fir’auna, Kuma menene amsar Fir’auna?
Kamar yadda aka nuna a hoton nan, Menene ya faru sa’ad da Haruna ya jefar da sandansa?
Ta yaya ne Jehobah ya hori Fir’auna, kuma ta yaya Fir’auna ya amsa?
Menene ya faru bayan annoba ta goma?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 4:27-31 da kuma 5:1-23.
Menene Fir’auna yake nufi sa’ad da ya ce: “Ni ban san Ubangiji ba”? (Fit. 5:2; 1 Sam. 2:12; Rom. 1:21)
Ka karanta Fitowa 6:1-13, 26-30.
A wanne hanya ne Jehobah bai sanar da kansa ga Ibrahim, Ishaku, da Yakubu ba? (Fit. 3:13, 14; 6:3; Far. 12:8)
Yaya muka ji sa’ad da muka sani cewa Jehobah ya yi amfani da Musa, ko da yake Musa yana ganin bai cancanta ba? (Fit. 6:12, 30; Luk 21:13-15)
Ka karanta Fitowa 7:1-13.
Sa’ad da Musa da Haruna suka gabatar da saƙon hukuncin Jehobah ga Fir’auna, wane misali ne suka kafa wa bayin Allah a yau? (Fit. 7:2, 3, 6; A. M. 4:29-31)
Ta yaya Jehobah ya nuna ya fi allolin ƙasar Masar? (Fit. 7:12; 1 Laba. 29:12)
Annoba Guda Goma
Ka yi amfani da hotuna da suke nan ka kwatanta annoba uku na fari da Jehobah ya jawo wa ƙasar Masar.
Menene bambanci da ke tsakanin annoba uku na fari da sauran annobar?
Me ya faru a annoba ta huɗu ta biyar da ta shida?
Ka kwatanta ta bakwai da takwas da kuma ta tara.
Menene Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su yi kafin annoba ta goma?
Mecece annoba ta goma kuma menene ya faru bayan annobar?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 7:19–8:23.
Ko da yake masu sihiri na Masar sun yi irin annoba na biyu na fari, menene suka ce bayan annoba ta uku? (Fit. 8:18, 19; Mat. 12:24-28)
Ta yaya ne annoba ta huɗu ta nuna cewa Jehobah zai iya kāre mutanensa, kuma ta yaya sanin wannan yake sa mutanen Allah su ji sa’ad da suke fuskantar “baban tsanani”? (Fit. 8:22, 23; R. Yoh. 7:13, 14; 2 Laba. 16:9)
Ka karanta Fitowa 8:24; 9:3, 6, 10, 11, 14, 16, 23-25; da kuma 10:13-15, 21-23.
Waɗanne rukunoni biyu ne annoba goma ya fallasa, kuma yaya wannan ya shafi yadda muke ɗaukan waɗannan rukunoni biyun? (Fit. 8:10, 18, 19; 9:14)
Ta yaya Fitowa 9:16 ya taimake mu mu fahimci abin da ya sa Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya wanzu har zuwa yanzu? (Rom. 9:21, 22)
Ka karanta Fitowa 12:21-32.
Ta yaya ƙetare wa ya sa ceto ya yiwu, kuma ga menene ƙetarewan yake nuni? (Fit. 12:21-23; Yoh. 1:29; Rom. 5:18, 19, 21; 1 Kor. 5:7)
Ƙetare Jar Teku
Isra’ilawa maza da mata da yara nawa ne suka bar ƙasar Masar, kuma su waye suka bi su?
Yaya Fir’auna ya ji da ya ƙyale Isra’ilawa su tafi, kuma menene ya yi?
Menene Jehobah ya yi don ya hana Masarawa kai wa mutanensa hari?
Menene ya faru sa’ad Musa ya miƙa sandansa bisa Jar Teku, kuma menene Isra’ilawa suka yi?
Menene ya faru sa’ad da Masarawa suka bi Isra’ilawa cikin teku?
Ta yaya Isra’ilawa suka nuna cewa suna farin ciki kuma suna godiya ga Jehobah domin sun tsira?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 12:33-36.
Ta yaya ne Jehobah ya sa aka biya Mutanensa domin duka shekaru da suka yi suna bauta wa Masarawa? (Fit. 3:21, 22; 12:35, 36)
Ka karanta Fitowa 14:1-31.
Ta yaya ne kalmomin Musa da aka rubuta a Fitowa 14:13, 14 suka shafi bayin Jehobah a yau yayin da suke sauraran yaƙin Armageddon? (2 Laba. 20:17; Zab. 91:8)
Ka karanta Fitowa 15:1-8, 20, 21.
Me ya sa bayin Jehobah za su rera masa waƙar yabo? (Fit. 15:1, 2; Zab. 105:2, 3; R. Yoh. 15:3, 4)
Wane misali ne na yabon Jehobah Maryamu da sauran mata a Jar Teku suka kafa wa mata Kiristoci a yau? (Fit. 15:20, 21; Zab. 68:11)
Sabon Abinci
A wannan hoton menene mutanen suke ɗiba daga ƙasa, kuma menene sunansa?
Wane umurni ne Musa ya bai wa mutanen game da ɗiban manna?
Menene Jehobah ya gaya wa mutanen su yi a rana ta shida, kuma me ya sa?
Wane abin al’ajabi Jehobah yake yi sa’ad da aka adana abincin domin rana ta bakwai?
Jehobah ya ciyar da mutanen da manna na shekara nawa ne?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 16:1-36 da kuma Litafin Lissafi 11:7-9.
Menene Fitowa 16:8 ya nuna game da yadda ya kamata mu daraja waɗanda Allah ya naɗa a ikilisiyar Kiristoci? (Ibran. 13:17)
A cikin daji, ta yaya aka tuna wa Isra’ilawa game da dogararsu ga Jehobah kowace rana? (Fit. 16:14-16, 35; K. Sha 8:2, 3)
Wace ma’ana ce Yesu ya ba wa manna, kuma ta yaya muka amfana daga wannan “gurasa daga cikin sama”? (Yoh. 6:31-35, 40)
Ka karanta 5:10-12.
Shekara nawa ne Isra’ilawa suka yi suna cin manna, kuma ta yaya ne wannan ya gwada su, kuma menene za mu koya daga wannan labarin? (Fit. 16:35; Lit. Lis. 11:4-6; 1 Kor. 10:10, 11)
Jehobah Ya Ba da Dokokinsa
Bayan kamar wata biyu da barin ƙasar Masar, a ina ne Isra’ilawa suka yi zango?
Menene Jehobah ya ce yake so mutanen su yi, kuma yaya suka amsa?
Me ya sa Jehobah ya ba Musa allunan dutse gida biyu?
Ban da Dokoki goman, waɗanne dokoki ne kuma Jehobah ya ba wa Isra’ilawa?
Waɗanne dokoki biyu ne Yesu Kristi ya ce su ne mafiya girma?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 19:1-25; 20:1-21; 24:12-18 da kuma 31:18.
Ta yaya kalmomin da suke rubuce a Fitowa 19:8 suka taimake mu mu fahimci abin da keɓe kai na Kirista ya ƙunsa? (Mat. 16:24; 1 Bit. 4:1-3)
Ka karanta Kubawar Shari’a 6:4-6; Leviticus 19:18; Matta 22:36-40.
Ta yaya ne Kiristoci suke nuna ƙaunarsu ga Allah da kuma maƙwabcinsu? (Mar. 6:34; A. M. 4:20; Rom. 15:2)
Ɗan Maraƙin Zinariya
A hoton, menene mutanen suke yi kuma me ya sa?
Me ya sa Jehobah ya yi fushi, kuma menene Musa ya yi sa’ad da ya ga abin da mutanen suke yi?
Menene Musa ya gaya wa wasu a cikin mazan su yi?
Wane darasi ne ya kamata mu koya daga wannan labarin?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 32:1-35.
Ta yaya wannan labarin ya nuna halin Jehobah game da haɗa bauta ta gaskiya da ta ƙarya? (Fit. 32:4-6, 10; 1 Kor. 10:7, 11)
Me ya sa ya kamata Kiristoci su mai da hankali a wajen irin nishaɗin da suka zaɓa kamar su waƙa da rawa? (Fit. 32:18, 19; Afis. 5:15, 16; 1 Yoh. 2:15-17)
Ta yaya ne ƙabilar Levi ta kasance abin koyi wajen tsayawa tsayin daka ga adalci? (Fit. 32:25-28; Zab. 18:25)
Tanti Domin Bauta
Menene ake kiran ginin da ke hoton nan, kuma menene aike yi a ciki?
Me ya sa Jehobah ya gaya wa Musa ya yi wannan tanti domin a naɗe shi da sauƙi?
Wanene wannan akwati da ke ƙaramin ɗaki a ƙarshen tantin, kuma menene yake cikin akwatin?
Wanene Jehobah ya zaɓa ya zama babban firist, kuma menene aikin babban firist ɗin?
Ka faɗi abubuwa uku da suke cikin babban ɗakin tantin.
Waɗanne abubuwa biyu ne suke filin mazaunin, kuma me ake yi da su?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Fitowa 25:8-40; 26:1-37; 27:1-8; da kuma 28:1.
Menene mala’ikun da suke ‘kan akwatin’ suke wakilta? (Fit. 25:20, 22; Lit. Lis. 7:89; 2 Sar. 19:15)
Ka karanta Fitowa 30:1-10, 17-21; 34:1, 2; da kuma Ibraniyawa 9:1-5.
Me ya sa Jehobah ya nanata muhimmanci tsabta ta jiki ga firistocin da suke hidima a mazauni, kuma ta yaya wannan zai shafe mu a yau? (Fit. 30:18-21; 40:30, 31; Ibran. 10:22)
Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa mazauni da Dokar alkawari sun shuɗe a lokacin da yake rubuta wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa? (Ibran. 9:1, 9; 10:1)
’Yan Leƙen Asiri 12
Me ka lura game da inabi da ke hoton nan, kuma daga ina aka samo shi?
Me ya sa Musa ya aiki ’yan leƙen asiri 12 zuwa ƙasar Kan’ana?
Menene ’yan leƙen asiri goma suka ce sa’ad da suka dawo wurin Musa?
Ta yaya ’yan leƙen asiri biyu suka nuna dogara ga Jehobah, kuma menene sunayensu?
Me ya sa Jehobah ya yi fushi, kuma me ya gaya wa Musa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Litafin Lissafi 13:1-33.
Su waye aka zaɓa su leƙi asirin ƙasar, kuma wane babbar gata ne suka samu? (Lit. Lis. 13:2, 3, 18-20)
Me ya sa ra’ayin Joshuwa da Kaleb ya bambanta da na sauran ’yan leƙen asirin, kuma menene wannan ya koya mana? (Lit. Lis. 13:28-30; Mat. 17:20; 2 Kor. 5:7)
Ka karanta Litafin Lissafi 14:1-38.
Wane gargaɗi ne game yin gunaguni ga waɗanda suke wakiltar Jehobah a duniya ya kamata mu bi? (Lit. Lis. 14:2, 3, 27; Mat. 25:40, 45; 1 Kor. 10:10)
Ta yaya Litafin Lissafi 14:24 ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunar kowane bayinsa? (1 Sar. 19:18; Mis. 15:3)
Sandan Haruna Ya Yi Fure
Su waye ne suka yi wa Musa da Haruna tawaye, kuma menene suka ce wa Musa?
Menene Musa ya gaya wa Korah da mabiyansa mutane 250 su yi?
Menene Musa ya gaya wa mutanen, kuma menene ya faru da ya gama magana?
Menene ya faru da Korah da mabiyansa mutane 250?
Menene Eleazar, ɗan Haruna ya yi da kaskon wuta na mutanen da suka mutu, kuma me ya sa?
Me ya sa Jehobah ya sa sandar Haruna ta yi fure? (Dubi hoto.)
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Litafin Lissafi 16:1-49.
Menene Korah da mabiyansa suka yi, kuma me ya sa hakan tawaye ne ga Jehobah? (Lit. Lis. 16:9, 10, 18; Lev. 10:1, 2; Mis. 11:2)
Wane mugun ra’ayi ne Korah da ‘shugabannin jama’a’ mutane 250 suka kasance da shi? (Lit. Lis. 16:1-3; Mis. 15:33; Isha. 49:7)
Ka karanta Litafin Lissafi 17:1-11 da kuma 26:10.
Menene tafowar sandar Haruna ta nuna, kuma me ya sa Jehobah ya ba da umurni cewa a ajiye shi cikin akwatin? (Lit. Lis. 17:5, 8, 10)
Wane darasi ne mai muhimmanci za mu koya daga tafowar sandar Haruna? (Lit. Lis. 17:10; A. M. 20:28; Filib. 2:14; Ibran. 13:17)
Musa Ya Bugi Dutsen
Ta yaya Jehobah ne ya kula da Isra’ilawa sa’ad da suke cikin daji?
Wace mita ce Isra’ila suka yi sa’ad da suka yi zango a Kedesh?
Ta yaya ne Jehobah ya yi tanadin ruwa ga mutanen da kuma dabbobinsu?
A wannan hoto wanene ne yake nuna kansa, kuma me ya sa ya yi haka?
Me ya sa Jehobah ya yi fushi da Musa da Haruna, kuma ta yaya aka yi musu horo?
Me ya faru a Dutsen Hor, kuma wanene ya zama babban firist na Isra’ila?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Litafin Lissafi 20:1-13, 22-29 da kuma Kubawar Shari’a 29:5.
Menene muka koya daga yadda Jehobah ya kula da Isra’ilawa a daji? (K. Sha 29:5; Mat. 6:31; Ibran. 13:5; Yaƙ. 1:17)
Yaya Jehobah ya ɗauki kasawar Musa da Haruna su ɗaukaka shi a gaban Isra’ilawa? (Lit. Lis. 20:12; 1 Kor. 10:12; R. Yoh. 4:11)
Me za mu koya daga yadda Musa ya karɓi horo daga Jehobah? (Lit. Lis. 12:3; 20:12, 27, 28; K. Sha 32:4; Ibran. 12:7-11)
Macijin Tagulla
A hoto, menene aka naɗe a jikin sanda, kuma me ya sa Jehobah ya gaya wa Musa ya kafa shi a nan?
Ta yaya ne mutanen suka ƙi yi wa Allah godiya domin duka abin da ya yi musu?
Menene mutanen suka ce Musa ya yi bayan Jehobah ya tura majizai masu dafi su yi musu horo?
Me ya sa Jehobah ya gaya wa Musa ya yi macijin tagulla?
Wane darasi za mu koya daga wannan labari?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Litafin Lissafi 21:4-9.
Wane gargaɗi aka ba mu ta wajen gunaguni game da tanadodin Jehobah? (Lit. Lis. 21:5, 6; Rom. 2:4)
A ƙarnuka daga baya, ta yaya suka yi amfani da macijin tagulla, kuma wane mataki ne Sarki Hezekiah ya ɗauka? (Lit. Lis. 21:9; 2 Sar. 18:1-4)
Ka karanta Yohanna 3:14, 15.
Ta yaya kafa macijin tagulla a kan itace ya kwatanta yadda za a kashe Yesu Kristi? (Gal. 3:13; 1 Bit. 2:24)
Jaka Ta Yi Magana
Wannene Balak kuma me ya sa ya aika a kira Balaam?
Me ya sa jakar Balaam ta kwanta a kan hanya?
Menene Balaam ya ji jakar ta ce?
Menene mala’ika ya gaya wa Balaam?
Menene ya faru sa’ad da Balaam ya yi ƙoƙarin ya la’anci Isra’ila?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 21:21-35.
Me ya sa Isra’ila suka yi nasara bisa Sarki Sihon na Amoriyawa da kuma Sarki Og na Bashan? (Lit. Lis. 21:21, 23, 33, 34)
Ka karanta Litafin Lissafi 22:1-40.
Me ya sa Balaam yake so ya la’anci Isra’ilawa, kuma waɗanne darussa za mu koya daga wannan? (Lit. Lis. 22:16, 17; Mis. 6:16, 18; 2 Bit. 2:15; Yahu. 11)
Ka karanta Litafin Lissafi 23:1-30.
Ko da yake Balaam ya yi magana kamar shi mai bauta wa Jehobah ne, ta yaya ayyukansu suka nuna ba ya bauta wa Jehobah? (Lit. Lis. 23:3, 11-14; 1 Sam. 15:22)
Ka karanta Litafin Lissafi 24:1-25.
Ta yaya wannan tarihin Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa bangaskiyarmu game da cika nufin Jehobah? (Lit. Lis. 24:10; Isha. 54:17)
Joshua Ya Zama Shugaba
A wannan hoton waɗanne mutane ne suke tsaye tare da Musa?
Menene Jehobah ya gaya wa Joshua?
Me ya sa Musa ya hau kan Dutsen Nebo, kuma menene Jehobah ya gaya masa?
Musa yana da shekaru nawa ne lokacin da ya mutu?
Me ya sa mutanen baƙin ciki, amma wane dalili ne suke da shi na yin farin ciki?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Litafin Lissafi 27:12-23.
Wane babban aiki ne Jehobah ya ba wa Joshua, kuma ta yaya ne yadda Jehobah yake kula da mutanensa ya bayyana a yau? (Lit. Lis. 27:15-19; A. M. 20:28; Ibran. 13:7)
Ka karanta Kubawar Shari’a 3:23-29.
Me ya sa Jehobah bai ƙyale Musa da Haruna su ƙetare zuwa ƙasar alkawari ba, kuma wane darasi za mu koya daga wannan? (K. Sha 3:25-27; Lit. Lis. 20:12, 13)
Ka karanta Kubawar Shari’a 31:1-8, 14-23.
Ta yaya kalaman ƙarshe na Musa zuwa ga Isra’ila ya nuna cewa ya karɓi horo daga Jehobah? (K. Sha 31:6-8, 23)
Ka karanta Kubawar Shari’a 32:45-52.
Ta yaya ne Kalmar Allah ya kamata ya taɓa rayuwarmu? (K. Sha 32:47; Lev. 18:5; Ibran. 4:12)
Ka karanta Kubawar Shari’a 34:1-12.
Ko da yake Musa bai ta ba gani Jehobah a zahiri ba, menene Kubawar Shari’a 34:10 ta nuna game da dangantakarsa da Jehobah? (Fit. 33:11, 20; Lit. Lis. 12:8)
Rahab Ta Ɓoye ’Yan Leƙen Asiri
A ina ne Rahab take da zama?
Su waye ne waɗannan mutane da suke wannan hoton, kuma me ya kawo su Jericho?
Menene sarkin Jericho ya umurci Rahab ta yi, kuma yaya ta amsa?
Ta yaya Rahab ya taimaki mutanen biyu, kuma wane tagomashi ne ta nema?
Wane alkawari ne ’yan leƙen asiri suka yi wa Rahab?
Ƙarin Tambayoyi:
Ka karanta Joshua 2:1-24.
Ta yaya ne alkawarin Jehobah da ke rubuce a Fitowa 23:28 ya cika sa’ad da Isra’ilawa suka kai wa Jericho hari? (Josh. 2:9-11)
Ka karanta Ibraniyawa 11:31.
Ta yaya ne misalin Rahab ya nanata muhimmancin bangaskiya? (Rom. 1:17; Ibran. 10:39; Yaƙ. 2:25)
Ƙetare Kogin Urdun
Wace mu’ujiza ce Jehobah ya yi domin Isra’ilawa su ƙetare Kogin Urdun?
Wane aikin bangaskiya ne dole Isra’ilawa su yi domin su ƙetare Kogin Urdun?
Me ya sa Jehobah ya gaya wa Joshua ya tara manyan duwatsu 12 daga gefen kogin?
Menene ya faru da firistoci suka fita daga cikin Kogin Urdun ɗin?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Joshua 3:1-17.
Kamar yadda wannan labarin ya nuna menene muke bukatar mu yi dominmu sami taimako da kuma albarka daga Jehobah? (Josh. 3:13, 15; Mis. 3:5; Yaƙ. 2:22, 26)
Yaya ne yanayin Kogin Urdun sa’ad da Isra’ilawa suka ƙetare zuwa Ƙasar Alkawari, kuma ta yaya wannan ya ɗaukaka sunan Jehobah? (Josh. 3:15; 4:18; Zab. 66:5-7)
Ka karanta Joshua 4:1-18.
Menene manufar duwatsu 12 da aka kwasa daga Urdun kuma aka jera a Gilgal? (Josh. 4:4-7)
Ganuwar Jericho
Menene Jehobah ya gaya wa mayaƙa da kuma firistoci su yi na kwana shida?
Menene mutanen za su yi a kwana ta bakwai?
Kamar yadda ka ke gani a wannan hoton, menene yake faruwa da ganuwar Jericho?
Me ya sa aka sa jan zare a tagar wannan gida?
Menene Joshua ya gaya wa mayaƙa su yi wa mutanen da kuma birninsu, amma azurfa, zinariya, jan ƙarfe da kuma ƙarfe fa?
Menene aka gaya wa ’yan leƙen asiri biyu su yi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Joshua 6:1-25.
Ta yaya ne zagayar Isra’ilawa a kwana ta bakwai ta yi daidai da ayyukan wa’azi na Shaidun Jehobah a kwanaki na ƙarshe? (Josh. 6:15, 16; Isha. 60:22; Mat. 24:14; 1 Kor. 9:16)
Ta yaya annabci da aka rubuta a Joshua 6:26 ya cika bayan wajen shekaru 500, kuma menene wannan ya koya mana game da kalmar Jehobah? (1 Sar. 16:34; Isha. 55:11)
Ɓarawo a Isra’ila
A wannan hoton wanene wannan mutumin da yake binne dukiya da ya kwasa daga Jericho, kuma su waye suke taimakonsa?
Me ya sa abin da Achan da iyalinsa suka yi ya tsanani sosia?
Menene Jehobah ya ce sa’ad da Joshua ya tambayi abin da ya sa aka ci Isra’ilawa a yaƙi da A’i?
Bayan an kawo Achan da iyalinsa zuwa wurin Joshua, menene ya same su?
Wane darasi mai muhimmanci ne hukuncin Achan ya koya mana?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Joshua 7:1-26.
Menene addu’ar Joshua ta nuna game da dangantakarsa da Mahaliccinsa? (Josh. 7:7-9; Zab. 119:145; 1 Yoh. 5:14)
Menene misalin Achan ya nuna, kuma ta yaya wannan ya kasance gargaɗi a garemu? (Josh. 7:11, 14, 15; Mis. 15:3; 1 Tim. 5:24; Ibran. 4:13)
Ka karanta 8:1-29.
Wane hakki ne muke da shi ga ikilisiyar Kirista a yau? (Josh. 7:13; Lev. 5:1; Mis. 28:13)
Gibeyonawa Masu Hikima
Ta yaya mutanen Gibeyon suka bambanta da sauran Kan’aniyawa na biranen da ke kusa?
Kamar yadda aka kwatanta a wannan hoton, menene Gibeyonawa suka yi kuma me ya sa?
Wane alkawari ne Joshua da kuma shugabannin Isra’ilawa suka yi wa Gibeyonawa, amma menene suka fahimta bayan kwana uku?
Menene ya faru sa’ad da sarakunan sauran biranen suka ji cewa Gibeyonawa sun yi salama da Isra’ilawa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Joshua 9:1-27.
Tun da Jehobah ya umurci al’ummar Isra’ila ta ‘halaka mazauna ƙasar,’ wane hali ne Jehobah ya nuna sa’da da ya ƙyale Gibeyonawa? (Josh. 9:22, 24; Mat. 9:13; A. M. 10:34, 35; 2 Bit. 3:9)
Ta wajen manne wa alkawarin da ya yi da Gibeyonawa, ta yaya ne Joshua ya kafa misali mai kyau ga Kiristoci a yau? (Josh. 9:18, 19; Mat. 5:37; Afis. 4:25)
Ka karanta Joshua 10:1-5.
Ta yaya ne babban taro a yau ta yi koyi da Gibeyonawa, kuma domin haka sun zama abin fakon wanene? (Josh. 10:4; Zech. 8:23; Mat. 25:35-40; R. Yoh. 12:17)
Rana Ta Tsaya Wuri Ɗaya
A wannan hoto menene Joshua yake faɗa, kuma me ya sa?
Ta yaya ne Jehobah ya taimaki Joshua da mayaƙansa?
Sarakuna nawa ne Joshua ya ci nasara a kansu kuma yaya tsawon lokacin?
Me ya sa Joshua ya raba ƙasar Kan’ana?
Shekarar Joshua nawa ne sa’ad da ya mutu, kuma menene ya faru da mutanen bayan haka?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Joshua 10:6-15.
Sanin Jehobah ya sa rana da wata su tsaya wuri ɗaya domin Isra’ila, ya ba mu wane tabbaci ne yau? (Josh. 10:8, 10, 12, 13; Zab. 18:3; Mis. 18:10)
Ka karanta Joshua 12:7-24.
Wanene ainihi ya yi nasara a kan sarakuna 31 na Kan’ana, kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci a gare mu a yau? (Josh. 12:7; 24:11-13; K. Sha 31:8; Luk 21:9, 25-28)
Ka karanta Joshua 14:1-5.
Ta yaya aka raba ƙasar a tsakanin ƙabilun Isra’ila, kuma menene wannan ya nuna game da gado a Aljanna? (Josh. 14:2; Isha. 65:21; Ezek. 47:21-23; 1 Kor. 14:33)
Ka karanta Joshua 2:8-13.
Kamar Joshua a Isra’ila, waye a yau ya kasance mai kāriya daga ridda? (Alƙa. 2:8, 10, 11; Mat. 24:45-47; 2 Tas. 2:3-6; Tit. 1:7-9; R. Yoh. 1:1; 2:1, 2)
Mata Biyu Marasa Tsoro
Su wanene ne alƙalai, kuma menene sunan wasu cikinsu?
Wace gata ce ta musamman Deborah ta samu, kuma menene wannan ya ƙunsa?
Sa’ad da Sarki Jabin da shugaban sojojinsa Sisera suka yi wa Isra’ila barazana, wane saƙo ne daga Jehobah Deborah ta sanar wa alƙali Barak, kuma wanene ta ce zai sami yabon?
Ta yaya ne Jael ta nuna cewa ita mace ce mai gaba gaɗi?
Menene ya faru bayan Sarki Jabin ya mutu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Alƙalawa 2:14-22.
Ta yaya ne Isra’ilawa suka jawo wa kansu fushin Jehobah, kuma wane darasi za mu koya daga wannan? (Alƙa. 2:20; Mis. 3:1, 2; Ezek. 18:21-23)
Ka karanta Alƙalawa 4:1-24.
Wane darasi ne game da bangaskiya da kuma gaba gaɗi mata Kiristoci za su koya daga misalin Deborah da Jael? (Alƙa. 4:4, 8, 9, 14, 21, 22; Mis. 31:30; 1 Kor. 16:13)
Ka karanta Alƙalawa 5:1-31.
Ta yaya za a iya amfani da waƙar nasara ta Barak da Deborah a addu’a game da yaƙin Har–Magedon mai zuwa? (Alƙa. 5:3, 31; 1 Laba. 16:8-10; R. Yoh. 7:9, 10; 16:16; 19:19-21)
Ruth da Na’omi
Ta yaya ne Na’omi ta soma zama a ƙasar Mowab?
Su waye ne Ruth da Orpah?
Ta yaya ne Ruth da Orpah suka amsa sa’ad da Na’omi ta gaya musu su koma wurin mutanensu?
Wanene Boaz, ta yaya ne ya taimaki Ruth da Na’omi?
Menene sunan ɗan Boaz da Ruth, kuma me ya sa ya kamata mu tuna da shi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ruth 1:1-17.
Wane furci mai kyau na ƙauna ta aminci ne Ruth ta furta? (Ruth 1:16, 17)
Ta yaya halin Ruth ya nuna halin “waɗansu tumaki” ga shafaffu da ke duniya a yau? (Yoh. 10:16; Zech. 8:23)
Ka karanta Ruth 2:1-23.
Ta yaya ne Ruth ta ba da misali mai kyau ga ’yan mata a yau? (Ruth 2:17, 18; Mis. 23:22; 31:15)
Ka karanta Ruth 3:5-13.
Ta yaya Boaz ya ɗauki yadda Ruth ta yarda ta aure shi maimakon saurayi?
Menene halin Ruth ya koya mana game da ƙauna ta aminci? (Ruth 3:10; 1 Kor. 13:4, 5)
Ka karanta Ruth 4:7-17.
Ta yaya maza Kiristoci a yau za su zama kamar Boaz? (Ruth 4:9, 10; 1 Tim. 3:1, 12, 13; 5:8.
Gideon da Mutanensa 300
Ta yaya Isra’ilawa suka shiga masifa da yawa, kuma me ya sa?
Me ya sa Jehobah ya gaya wa Gideon cewa yana da mutane da yawa a rundunarsa?
Maza nawa ne suka rage da Gideon ya gaya wa mutane masu tsoro su koma gida?
Ta wannan hoton, ka bayana yadda Jehobah ya rage adadin rundunar Gideon zuwa maza 300 kawai.
Ta yaya ne Gideon ya tsara mazansa 300, kuma ta yaya Isra’ila ta ci yaƙin?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Alƙalawa 6:36-40.
Ta yaya ne Gideon ya tabbatar da nufin Jehobah?
Ta yaya ne muke sanin nufin Jehobah a yau? (Mis. 2:3-6; Mat. 7:7-11; 2 Tim. 3:16, 17)
Ka karanta Alƙalawa 7:1-25.
Wane darassi za mu koya daga maza 300 da suka kasance a faɗake da waɗanda ba su mai da hankali ba? (Alƙ. 7:3, 6; Rom.13:11, 12; Afi. 5:15-17)
Kamar yadda mutane 300 suka yi koyi ta wurin lura da Gideon, ta yaya ya kamata mu koya ta wajen lura da Yesu Kristi, Gideon Babba? (Alƙ. 7:17; Mat. 11:29, 30; 28:19, 20; 1 Bit. 2:21)
Ta yaya Alƙalawa 7:21 ya taimake mu mu kasance da gamsuwa mu yi hidima a ko’ina da aka sa mu a ƙungiyar Jehobah? (1 Kor. 4:2; 12:14-18; Yaƙ. 4:10)
Ka karanta Alƙalawa 8:1-3.
Idan ya zo ga magance matsaloli da ɗan’uwa ko ’yar’uwa, menene za mu koya daga yadda Gideon ya magance jayayya da ’yan Ephraim? (Mis. 15:1; Mat. 5:23, 24; Luka 9:48)
Alkawarin Jephthah
Wanene Jephthah, kuma wane lokaci ya yi rayuwa?
Wane alkawari ne Jephthah ya yi wa Jehobah?
Me ya sa Jephthah ya yi baƙin ciki sa’ad da ya dawo gida daga cin nasara bisa Ammonawa?
Menene ’yar Jephthah ta ce sa’ad da ta san game da alkawarin babanta?
Me ya sa mutanen suke ƙaunar ’yar Jephthah?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Alƙalawa 10:6-18.
Wane gargaɗi ne daga tarihin Isra’ila na rashin aminci ga Jehobah ya kamata mu bi? (Alƙ. 10:6, 15, 16; Rom. 15:4; R. Yoh. 2:10)
Ka karanta Alƙalawa 11:1-11, 29-40.
Ta yaya muka sani cewa da yake Jephthah ya ba da ’yarsa “hadaya ta ƙonawa” ba ya nufin ya miƙa ta hadaya ta wuta? (Alƙa. 11:31; Lev. 16:24; K. Sha 18:10, 12)
Ta yaya Jephthah ya miƙa ’yarsa hadaya?
Menene muka koya daga halin Jephthah game da alkawarinsa ga Jehobah? (Alƙa. 11:35, 39; M. Wa. 5:4, 5; Mat. 16:24)
Ta yaya ’yar Jephthah ta zama misali mai kyau ga matasa Kiristoci wajen neman hidima ta cikakken lokaci? (Alƙa. 11:36; Mat. 6:33; Filib. 3:8)
Sarkin Ƙarfi
Menene sunan mutum da yake da ƙarfi sosai da ya taɓa rayuwa, wanene ya ba shi ƙarfi?
A wani lokaci, menene Samson ya yi wa babban zaki, yadda kake gani a wannan hoton?
Wane asiri ne Samson yake gaya wa Delilah a wannan hoton, ta yaya wannan ya sa Filistiyawa suka kama shi?
Ta yaya Samson ya kashe Filistiyawa magabta 3,000 a ranar da ya mutu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Alƙalawa 13:1-14.
Ta yaya Manoah da matarsa suka ba da misali mai kyau ga iyaye wajen renon yaransu? (Alƙa. 13:8; Zab. 127:3; Afis. 6:4)
Ka karanta Alƙalawa 14:5-9 da 15:9-16.
Menene labarin yadda Samson ya kashe zaki, ya tsinke sababbin igiya da aka kama shi da su, da yin amfani da ƙashin mummuƙen jaki ya kashe mutane 1,000 suka nuna game da yadda ruhu mai tsarki na Jehobah yake aiki?
Ta yaya ne ruhu mai tsarki yake taimakonmu a yau? (Alƙa. 14:6; 15:14; Zech. 4:6; A. M. 4:31)
Ka karanta Alƙalawa 16:18-31.
Ta yaya tarayya da miyagu ya shafi Samson, menene za mu iya koya daga wannan? (Alƙa. 16:18, 19; 1 Kor. 15:33)
Ɗan Yaro Ya Bauta wa Allah
Menene sunan ɗan yaro da ke cikin wannan hoton, su wanene sauran mutanen?
Wace addu’a ce Hannatu ta yi wata rana da ta je mazaunin Jehobah, kuma ta yaya Jehobah ya amsa mata?
Shekarar Sama’ila nawa ne sa’ad da aka kai shi tantin Jehobah, menene mamarsa take masa kowace shekara?
Menene sunayen ’ya’yan Eli, wane irin mutane ne su?
Ta yaya Jehobah ya kira Sama’ila, kuma wane saƙo ne ya ba shi?
Menene Sama’ila ya zama sa’ad da ya yi girma, kuma menene ya faru sa’ad da ya tsufa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 1:1-28.
Wane misali mai kyau ne Elkanah ya nuna wa shugaban iyalai wajen yin ja-gora a bauta ta gaskiya? (1 Sam. 1:3, 21; Mat. 6:33; Filib. 1:10)
Wane darassi za mu koya daga misalin Hannatu wajen bi da matsala mai wuya? (1 Sam. 1:10, 11; Zab. 55:22; Rom. 12:12)
Ka karanta 1 Samuila 2:11-36.
Ta yaya ne Eli ya ɗaukaka ’ya’yansa fiye da Jehobah, ta yaya wannan zai zama gargaɗi a gare mu? (1 Sam. 2:22-24, 27, 29; K. Sha 21:18-21; Mat. 10:36, 37)
Ka karanta 1 Samuila 4:16-18.
Wane saƙo huɗu na hukunci aka kawo daga filin yaƙi, kuma yaya wannan ya shafi Eli?
Ka karanta 1 Samuila 8:4-9.
Ta yaya ne Isra’ila ta ɓata wa Jehobah rai, kuma ta yaya za mu tallafa wa Mulkinsa a yau? (1 Sam. 8:5, 7; Yoh. 17:16; Yaƙ. 4:4)
Saul, Sarkin Isra’ila na Farko
A wannan hoton, menene Sama’ila yake yi, kuma me ya sa?
Me ya sa Jehobah yake son Saul, kuma wane irin mutumi ne shi?
Menene sunan ɗan Saul, kuma menene ɗan ya yi?
Me ya sa Saul ya miƙa hadaya maimakon ya jira Sama’ila ya yi?
Wane darussa ne za mu iya koya daga labarin Saul?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 9:15-21 da 10:17-27.
Ta yaya halin tawali’u na Saul ya taimake shi ya guji aikata da garaje sa’ad da wasu mutane suka yi magana cikin rashin biyayya game da shi? (1 Sam. 9:21; 10:21, 22, 27; Mis. 17:27)
Ka karanta 1 Samuila 13:5-14.
Wane zunubi ne Saul ya yi a Gilgal? (1 Sam. 10:8; 13:8, 9, 13)
Ka karanta 1 Samuila 15:1-35.
Wane zunubi mai tsanani ne Saul ya yi game da Agag, sarkin Amalek? (1 Sam. 15:2, 3, 8, 9, 22)
Ta yaya Saul ya yi ƙoƙari ya ba da dalilin ayyukansa kuma ya ɗaura wa wasu alhaki? (1 Sam. 15:24)
Wane kashedi ya kamata mu bi a yau sa’ad da aka yi mana gargaɗi? (1 Sam. 15:19-21; Zab. 141:5; Mis. 9:8, 9; 11:2)
Allah Ya Zaɓi Dauda
Menene sunan yaron da ke wannan hoton, ta yaya muka san cewa ba ya jin tsoro?
Ina ne Dauda yake da zama, kuma menene sunan babansa da kakansa?
Me ya sa Jehobah ya gaya wa Sama’ila ya je gidan Jesse a Bai’talami?
Menene ya faru sa’ad da Jesse ya kawo ’ya’yansa bakwai ga Sama’ila?
Sa’ad da aka kawo Dauda, menene Jehobah ya gaya wa Sama’ila?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 17:34, 35.
Ta yaya waɗannan aukuwa suka nanata cewa Dauda yana da gabagaɗi kuma ya dogara ga Jehobah? (1 Sam. 17:37)
Ka karanta 1 Samuila 16:1-14.
Ta yaya kalmomin Jehobah a 1 Samuila 16:7 ya taimake mu kada mu kasance da son kai kuma mu guji wariya ta yadda mutane suke a waje? (A. M. 10:34, 35; 1 Tim. 2:4)
Ta yaya misalin Saul ya nuna cewa sa’ad da Jehobah ya cire ruhunsa mai tsarki daga wajen mutum, mugun ruhu ko kuma sha’awar yin mugunta zai rinjaye shi? (1 Sam. 16:14; Mat. 12:43-45; Gal. 5:16)
Dauda da Goliath
Wane ƙalubale ne Goliath ya yi wa rundunar Isra’ilawa?
Yaya girman Goliath yake, wane lada ne Sarki Saul ya yi alkawari zai ba mutum da ya kashe Goliath?
Menene Dauda ya ce sa’ad da Saul ya gaya masa ba zai iya faɗa da Goliath ba domin shi ɗan yaro ne?
Ta amsa da ya ba Goliath, ta yaya ne Dauda ya nuna ya dogara ga Jehobah?
Kamar yadda ka gani a wannan hoton, da menene Dauda ya kashe Goliath, kuma menene ya faru da Filistiyawa bayan haka?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 17:1-54.
Me ya sa Dauda ba ya jin tsoro, kuma ta yaya za mu yi koyi da gaba gaɗinsa? (1 Sam. 17:37, 45; Afis. 6:10, 11)
Me ya sa ya kamata Kiristoci su guje wa halin gasa kamar na Goliath sa’ad da suke wasanni ko kuma nishaɗi? (1 Sam. 17:8; Gal. 5:26; 1 Tim. 4:8)
Ta yaya kalmomin Dauda suka nuna yana da bangaskiya cewa Allah zai goyi bayansa? (1 Sam. 17:45-47; 2 Laba. 20:15)
Maimakon kwatanta faɗa tsakanin abokan gaba biyu da rundunarsu, ta yaya wannan labarin ya nuna cewa yaƙin ainihi tsakanin allolin ƙarya ne da Jehobah Allah na gaskiya? (1 Sam. 17:43, 46, 47)
Ta yaya shafaffu da suka rage suka yi koyi da misalin Dauda wajen dogara ga Jehobah? (1 Sam. 17:37; Irm. 1:17-19; R. Yoh. 12:17)
Dalilin da Ya Sa Dole Dauda Ya Gudu
Me ya sa Saul yake kishin Dauda, amma ta yaya ne Jonathan ɗan Saul ya yi dabam?
Menene ya faru wata rana da Dauda yake kaɗa wa Saul garaya?
Menene Saul ya faɗa dole Dauda ya yi kafin ya ɗauki ’yarsa Michal ta zama matarsa, kuma me ya sa Saul ya ce hakan?
Sa’ad da Dauda yake kaɗa wa Saul garaya, menene ya faru lokaci na uku, yadda wannan hoton ya nuna?
Ta yaya Michal ta ceci ran Dauda, kuma menene Dauda zai yi na shekara bakwai?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 18:1-30.
Ta yaya ne ƙauna da ba ta ƙarewa da Jonathan ya nuna wa Dauda yake wakiltar ƙauna da ke tsakanin “waɗansu tumaki” da “ƙaramin garke”? (1 Sam. 18:1; Yoh. 10:16; Luk 12:32; Zech. 8:23)
Ko da ya kamata Jonathan ya zama magajin Saul, ta yaya 1 Samuila 18:4 ya nuna cewa Jonathan ya ba da kai na musamman ga wanda aka zaɓa ya zama sarki?
Ta yaya ne misalin Saul ya nuna cewa kishi zai sa mutum ya yi mugun zunubi, wane gargaɗi ne wannan ya ba mu? (1 Sam. 18:7-9, 25; Yaƙ. 3:14-16)
Ka karanta 1 Samuila 19:1-17.
Ta yaya Jonathan ya sa rayuwansa cikin kasada sa’ad da yake fuskantar Saul? (1 Sam. 19:1, 4-6; Mis 16:14)
Abigail da Dauda
Menene sunan matan da take zuwan wajen Dauda a wannan hoton, wace irin mace ce ita?
Wanene Nabal?
Me ya sa Dauda ya aiki wasu cikin mutanensa su je wajen Nabal su nemi abinci?
Menene Nabal ya gaya wa mutanen Dauda, kuma ta yaya Dauda ya amsa?
Ta yaya Abigail ta nuna cewa ita mace mai hikima ce?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 22:1-4.
Ta yaya iyalin Dauda ta ba da misali mai kyau na yadda ya kamata mu tallafa wa juna a ’yan’uwanci na Kirista? (Mis. 17:17; 1 Tas. 5:14)
Ka karanta 1 Samuila 25:1-43.
Me ya sa aka kwatanta cewa Nabal yana da girman kai? (1 Sam. 25:2-5, 10, 14, 21, 25)
Menene matan aure na Kirista za su iya koya daga misalin Abigail? (1 Sam. 25:32, 33; Mis. 31:26; Afis. 5:24)
Waɗanne mummunan abubuwa biyu ne Abigail ta hana Dauda yi? (1 Sam. 25:31, 33; Rom. 12:19; Afis. 4:26)
Ta yaya yadda Dauda ya aikata ga kalmomin Abigail ya taimaki maza a yau su kasance da ra’ayin Jehobah game da mata? (A. M. 21:8, 9; Rom. 2:11; 1 Bit. 3:7)
Dauda Ya Zama Sarki
Menene Dauda da Abishai suka yi sa’ad da Saul yake barci a sansaninsa?
Waɗanne tambayoyi ne Dauda ya yi wa Saul?
Sa’ad da ya bar Saul, ina ne Dauda ya tafi?
Menene ya sa Dauda baƙin ciki, da ya sa ya rubuta waƙa mai daɗi?
Shekarar Dauda nawa ne sa’ad da ya zama sarki a Hebron, menene sunayen wasu cikin ’ya’yansa maza?
Ina ne Dauda ya yi sarauta daga baya?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Samuila 26:1-25.
Furcin Dauda da ke 1 Samuila 26:11 ya nuna wane hali game da tsari na Allah? (Zab. 37:7; Rom. 13:2)
Sa’ad da muka yi iya ƙoƙarinmu mu nuna ƙauna ta alheri, ta yaya kalmomin Dauda da ke 1 Samuila 26:23 ya taimake mu mu kasance da ra’ayin da ya dace? (1 Sar. 8:32; Zab. 18:20)
Ka karanta 2 Samuila 1:26.
Ta yaya Kiristoci a yau suke nuna “ƙauna mai-huruwa zuwa ga juna” da Dauda da Jonathan suka yi wa juna? (1 Bit. 4:8; Kol. 3:14; 1 Yoh. 4:12)
Ka karanta 2 Samuila 5:1-10.
Shekara nawa ne Dauda ya yi sarauta kuma yaya aka raba wannan shekarun? (2 Sam. 5:4, 5)
Menene ya sa Dauda ya kasance da girma, kuma yaya ya zama abin tunawa a gare mu a yau? (2 Sam. 5:10; 1 Sam. 16:13; 1 Kor. 1:31; Filib. 4:13)
Masifa a Gidan Dauda
Da taimakon Jehobah, menene ya faru a ƙasar Kan’ana?
Menene ya faru wata rana da yamma sa’ad da Dauda yake bisa bene na fadarsa?
Me ya sa Jehobah ya yi fushi ƙwarai da Dauda?
A cikin wannan hoton, wanene Jehobah ya aika ya gaya wa Dauda game da zunubansa, kuma menene wannan ya ce zai faru da Dauda?
Wace masifa ce Dauda ya shiga?
Bayan Dauda, wanene ya zama sarkin Isra’ila?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 2 Samuila 11:1-27.
Ta yaya shagalawa cikin hidimar Jehobah kariya ce a gare mu?
Ta yaya Dauda ya shiga cikin zunubi, wane gargaɗi ne wannan yake yi wa bayin Jehobah a yau? (2 Sam. 11:2; Mat. 5:27-29; 1 Kor. 10:12; Yaƙ. 1:14, 15)
Ka karanta 2 Samuila 12:1-18.
Wane darassi ne dattawa da iyaye za su iya koya daga yadda Nathan ya tuntuɓi Dauda don ya ba shi gargaɗi? (2 Sam. 12:1-4; Mis. 12:18; Mat. 13:34)
Me ya sa Jehobah ya yi wa Dauda jinƙai? (2 Sam. 12:13; Zab. 32:5; 2 Kor. 7:9, 10)
Sulemanu Sarki Mai Hikima
Menene Jehobah ya tambayi Sulemanu, kuma wace amsa ce ya ba da?
Domin ya gamsu da roƙon Sulemanu, menene Jehobah ya yi alkawari zai ba shi?
Wace matsala mai wuya ce mata biyu suka kai wa Sulemanu?
Kamar yadda ka ke gani a wannan hoton, ta yaya ne Sulemanu ya magance matsalar?
Yaya sarautar Sulemanu yake, kuma me ya sa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Sarakuna 3:3-28.
Menene maza masu hakki a ƙungiyar Allah a yau za su koya daga furcin da Sulemanu ya yi da dukan zuciyarsa a 1 Sarakuna 3:7? (Zab. 119:105; Mis. 3:5, 6)
Ta yaya roƙon Sulemanu misali mai kyau na abubuwa da ya dace da za a yi addu’a a kansu? (1 Sar. 3:9, 11; Mis. 30:8, 9; 1 Yoh. 5:14)
Wane tabbaci ne yadda Sulemanu ya magance matsala da ke tsakanin mata biyu ya ba mu game da sarautar Sulemanu Babba, wato Yesu Kristi game da nan gaba? (1 Sar. 3:28; Isha. 9:6, 7; 11:2-4)
Ka karanta 1 Sarakuna 4:29-34.
Ta yaya Jehobah ya amsa roƙon Sulemanu don zuciya mai biyayya? (1 Sar. 4:29)
Domin ƙoƙarin da mutanen suka yi don su ji hikimar Sulemanu, me ya kamata ya zama halinmu game da nazarin Kalmar Allah? (1 Sar. 4:29, 34; Yoh. 17:3; 2 Tim. 3:16)
Sulemanu Ya Gina haikali
Tsawon wane lokaci ne ya ɗauki Sulemanu don ya gama gina haikalin Jehobah, kuma me ya sa ginin ya yi tsada sosai?
Ɗakuna nawa ne ke cikin haikalin, kuma me aka sa cikin ɗakuna na ciki?
Menene Sulemanu ya ce a addu’arsa sa’ad da aka gama haikalin?
Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana farin ciki da addu’ar Sulemanu?
Menene matan Sulemanu suka sa ya yi, kuma me ya faru da Sulemanu?
Me ya sa Jehobah ya yi fushi da Sulemanu, menene Jehobah ya ce masa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Labarbaru 28:9, 10.
Domin kalmomin Dauda da aka rubuta a 1 Labarbaru 28:9, 10, me ya kamata mu yi ƙoƙari mu riƙa yi a rayuwarmu ta yau da kullum? (Zab. 19:14; Filib. 4:8, 9)
Ka karanta 2 Labarbaru 6:12-21, 32-42.
Ta yaya Sulemanu ya nuna cewa ba ginin da ’yan adam suka yi da zai iya ɗaukan Allah Maɗaukaki? (2 Laba. 6:18; A. M. 17:24, 25)
Menene kalmomin Sulemanu da ke 2 Labarbaru 6:32, 33 suka nuna game da Jehobah? (A. M. 10:34, 35; Gal. 2:6)
Ka karanta 2 Labarbaru 7:1-5.
Yadda ’ya’yan Isra’ila suka motsa su yi furci na yabo ga Jehobah sa’ad da suka ga ɗaukakarsa, ta yaya yin tunani game da albarkar Jehobah a kan mutanensa ya kamata ya shafe mu a yau? (2 Laba. 7:3; Zab. 22:22; 34:1; 96:2)
Ka karanta 1 Sarakuna 11:9-13.
Ta yaya ne tafarkin rayuwar Sulemanu ya nuna muhimmancin kasancewa da aminci har zuwa ƙarshe? (1 Sar. 11:4, 9; Mat. 10:22; R. Yoh. 2:10)
An Raba Mulkin
Menene sunan mutane biyu da ke cikin hoton, kuma su waye ne?
Menene Ahijah ya yi da rigar da ya saka, kuma menene wannan abin da ya yi yake nufi?
Menene Sulemanu ya yi ƙoƙari ya yi wa Jeroboam?
Me ya sa mutanen suka naɗa Jeroboam sarki bisa ƙabilu goma?
Me ya sa Jeroboam ya yi maraƙi na zinariya guda biyu, menene ya faru da ƙasar ba da daɗewa ba?
Menene ya faru da masarautar ƙabilu biyu da kuma haikalin Jehobah a Urushalima?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Sarakuna 11:26-43.
Wane irin mutumi ne Jeroboam, kuma wane alkawari ne Jehobah ya yi masa idan ya kiyaye dokokinsa? (1 Sar. 11:28, 38)
Ka karanta 1 Sarakuna 12:1-33.
Menene iyaye da dattawa za su iya koya game da ɓata iko daga hali marar kyau na Rehobowam? (1 Sar. 12:13; M. Wa. 7:7; 1 Bit. 5:2, 3)
Wurin waye ne ya kamata matasa a yau su je domin tabbataciyar ja-gora sa’ad da suke tsai da shawara mai muhimmanci a rayuwa? (1 Sar. 12:6, 7; Mis. 1:8, 9; 2 Tim. 3:16, 17; Ibran. 13:7)
Menene ya sa Jeroboam ya kafa wurare biyu don bautar maraƙi, yaya wannan ya nuna rashin bangaskiya ga Jehobah? (1 Sar. 11:37; 12:26-28)
Wanene ya sa mutane na masarauta ƙabilu goma su ƙi bauta ta gaskiya? (1 Sar. 12:32, 33)
Jezebel, Muguwar Sarauniya
Wacece Jezebel?
Me ya sa Sarki Ahab ya yi baƙin ciki wata rana?
Menene Jezebel ta yi don ta samo wa mijinta Ahab gonar Naboth?
Wanene Jehobah ya aika ya yi wa Jezebel horo?
Yadda ka gani a wannan hoton, menene ya faru sa’ad da Jehu ya kai fadar Jezebel?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Sarakuna 16:29-33 da 18:3, 4.
Yaya ne yanayin ya yi muni a Isra’ila a lokacin Sarki Ahab? (1 Sar. 14:9)
Ka karanta 1 Sarakuna 21:1-16.
Ta yaya Naboth ya nuna gabagaɗi da aminci ga Jehobah? (1 Sar. 21:1-3; Lev. 25:23-28)
Daga misalin Ahab, menene za mu koya game da jimre wa ɓacin rai? (1 Sar. 21:4; Rom. 5:3-5)
Ka karanta 2 Sarakuna 9:30-37.
Menene za mu iya koya daga himmar Jehu wajen yin nufin Jehobah? (2 Sar. 9:4-10; 2 Kor. 9:1, 2; 2 Tim. 4:2)
Jehoshaphat Ya Dogara ga Jehobah
Wanene Jehoshaphat, kuma a wane lokaci ne ya yi rayuwa?
Me ya sa Isra’ilawa suka tsorata, kuma menene yawancinsu suka yi?
Wace amsa ce Jehobah ya bai wa addu’ar Jehoshaphat?
Menene Jehobah ya sa ya faru kafin yaƙin?
Wane darasi ne za mu koya daga Jehoshaphat?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 2 Labarbaru 20:1-30.
Ta yaya Jehoshaphat ya nuna abin da ya kamata bawan Allah mai aminci ya kamata ya yi sa’ad da ya fuskanci yanayi mai ban tsoro? (2 Laba. 20:12; Zab. 25:15; 62:1)
Tun da a ko yaushe Jehobah yana amfani da hanyar magana sa’ad da yake sha’ani da mutanensa, wace hanya ce yake amfani da ita a yau? (2 Laba. 20:14, 15; Mat. 24:45-47; Yoh. 15:15)
Sa’ad da Allah ya fara ‘yaƙin babbar rana ta Allah,’ ta yaya yanayinmu zai kasance kamar na Jehoshaphat? (2 Laba. 20:15, 17; 32:8; R. Yoh. 16:14, 16)
Wajen koyi da Lawiyawa, wace irin gudummawa majagaba da waɗanda suke aikin wa’azi a ƙasashen waje suke bayar wa ga aikin wa’azi a yau? (2 Laba. 20:19, 21; Rom. 10:13-15; 2 Tim. 4:2)
Yara Biyu da Suka Sake Rayuwa
Su wanene ne mutane uku da suke wannan hoton, kuma menene ya faru da wannan ɗan yaron?
Menene Iliya ya yi addu’a game da yaron, kuma menene ya faru?
Menene sunan mataimakin Iliya?
Me ya sa aka kira Elisha zuwa gidan wata mata a Shunem?
Menene Elisha ya yi, kuma menene ya faru da yaron da ya mutu?
Wane iko ne Jehobah ya bayar, kamar yadda ya bayyana ta wajen Iliya da Elisha?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Sarakuna 17:8-24.
Ta yaya aka gwada biyayya Iliya da kuma bangaskiyarsa? (1 Sar. 17:9; 19:1-4, 10))
Me ya sa bangaskiyar gwauruwa ’yar Zarephath fitacciya ce? (1 Sar. 17:12-16; Luk 4:25, 26)
Ta yaya abin da gwauruwa ’yar Zarephath ta gani ya tabbatar da gaskiyar kalmomin Yesu da suke rubuce a Matta 10:41, 42? (1 Sarakuna 17:10-12, 17, 23, 24)
Ka karanta 2 Sarakuna 4:8-37.
Menene ’yar Shunem ta koya mana game da karɓan baƙi? (2 Sar. 4:8; Luk 6:38; Rom. 12:13; 1 Yoh. 3:17)
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yi wa bayin Allah a yau kirki? (A. M. 20:35; 28:1, 2; Gal. 6:9, 10; Ibran. 6:10)
Yarinya Ta Taimaki Jarumi
A wannan hoton menene wannan ’yar yarinya take gaya wa wannan matar?
Wacece wannan matar a hoton nan, kuma menene wannan yarinya ƙarama take yi a gidanta?
Menene Elisha ya umurci bawan ya gaya wa Na’aman, kuma me ya sa Na’aman ya yi fushi?
Menene ya faru sa’ad da Na’aman ya saurari bayinsa?
Me ya sa Elisha ya ƙi karɓan kyautar Na’aman amma menene Gehazi ya yi?
Menene ya faru da Gehazi, kuma menene za mu iya koya daga wannan?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 2 Sarakuna 5:1-27.
Ta yaya ne misalin da wannan ’yar yarinya Ba’isra’iliya ta kafa zai ƙarfafa matasa a yau? (2 Sar. 5:3; Zab. 8:2; 148:12, 13)
Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tuna misalin Na’amana sa’ad da ake mana gargaɗi daga Nassosi? (2 Sar. 5:15; Ibran. 12:5, 6; Yaƙ. 4:6)
Wane darasi za mu koya idan muka gwada misalin Elisha da na Gehazi? (2 Sar. 5:9, 10, 14-16, 20; Mat. 10:8; A. M. 5:1-5; 2 Kor. 2:17)
Yunana da Babban Kifi
Wanene Yunana kuma menene Jehobah ya gaya masa ya yi?
Domin baya son ya je wurin da Jehobah ya gaya masa, menene Yunana ya yi?
Menene Yunana ya gaya ma matuƙa jirgin ruwa su yi domin guguwa ta lafa?
Kamar yadda kake gani a wannan hoton menene ya faru sa’ad da Yunana ya nitse cikin ruwa?
Kwana nawa ne Yunana ya yi a cikin babban kifi kuma menene ya yi a cikin kifin?
Ina ne Yunana ya je sa’ad da ya fita daga cikin babban kifin, kuma menene wannan ya koya mana?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Yunana 1:1-17.
Kamar yadda ya bayyana, yaya Yunana ya ji game da aikin da aka ba shi na yi ma mutanen Nineba wa’azi? (Yun. 1:2, 3; Mis. 3:7; M. Wa. 8:12)
Ka karanta Yunana 2:1, 2, 10.
Ta yaya ne abin da Yunana ya fuskanta ya ba mu tabbaci cewa Jehobah zai amsa addu’o’inmu? (Zab. 22:24; 34:6; 1 Yoh. 5:14)
Ka karanta Yunana 3:1-10.
Wace ƙarfafa ce muka samu daga yadda Jehobah ya ci gaba da amfani da Yunana duk da yadda ya kasa cika aiki da aka ba shi da farko? (Zab. 103:14; 1 Bit. 5:10)
Menene labarin Yunana da mutanen Nineba ya koya mana game da hukunta mutane a yankinmu? (Yun. 3:6-9; M. Wa. 11:6; A. M. 13:48)
Allah Ya Yi Alkawarin Aljanna
Wanene Ishaya kuma a wane lokaci ne ya yi rayuwa, menene Jehobah ya nuna masa?
Menene kalmar nan “aljanna” take nufi, kuma menene ta tuna maka?
Menene Jehobah ya gaya wa Ishaya ya rubuta game da sabuwar aljanna?
Me ya sa Adamu da Hauwa suka yi asarar gidansu mai kyau?
Menene Jehobah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ishaya 11:6-9.
Ta yaya Kalmar Allah ya kwatanta salama da za ta kasance tsakanin dabbobi da mutane a sabuwar duniya? (Zab. 148:10, 13; Isha. 65:25; Ezek. 34:25)
Waɗanne kalmomin Ishaya ne suke cika a ruhaniya tsakanin mutanen Jehobah a yau? (Rom. 12:2; Afis. 4:23, 24)
Wa ya cancanci a yaba masa domin canji a halayen mutane a yanzu da kuma a sabuwar duniya? (Isha. 48:17, 18; Gal. 5:22, 23; Filib. 4:7)
Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
Ta yaya Nassosi suka nuna cewa Allah yana zauna tare da mutane yana nufin a alamance ne ba a zahiri ba a duniya? (Lev. 26:11, 12; 2 Laba. 6:18; Isha. 66:1; R. Yoh. 21:2, 3, 22-24)
Wane irin ciwo ne da kuma hawaye za a share? (Luk 8:49-52; Rom. 8:21, 22; R. Yoh. 21:4)
Allah Ya Taimaki Sarki Hezekiah
Wanene ne wannan mutumin na hoton nan, kuma me ya sa ya damu haka ƙwarai?
Waɗanne wasiƙu ne Hezekiah ya ajiye a gaban Allah, kuma menene Hezekiah yake addu’a a kai?
Wane irin sarki ne sarki Hezekiah, kuma wane saƙo ne Jehobah ya aika masa ta bakin annabi Ishaya?
Menene mala’ikan Allah ya yi wa Assuriyawa, kamar yadda aka nuna a wannan hoton?
Ko da yake masarautar ƙabilu biyu sun sami salama na ɗan lokaci, menene ya faru bayan Hezekiah ya mutu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 2 Sarakuna 18:1-36.
Ta yaya ne kakakin Assuriyawa Rabshakeh ya yi ƙoƙarin ya raunana bangaskiyar Isra’ilawa? (2 Sar. 18:19, 21; Fit. 5:2; Zab. 64:3)
Ta yaya Shaidun Jehobah suke bin misalin Hezekiah sa’ad da suke bi da ’yan hamayya? (2 Sarakuna 18:36; Zabura 39:1; Misalai 26:4; 2 Timothawus 2:24)
Ka karanta 2 Sarakuna 19:1-37.
Ta yaya mutanen Jehobah a yau suke koyi da Hezekiah a lokacin masifa? (2 Sar. 19:1, 2; Mis. 3:5, 6; Ibran. 10:24, 25; Yaƙ. 5:14, 15)
Waɗanne nasarori uku ne aka yi a kan Sennacherib, kuma ya bi misalin wanene a annabce? (2 Sar. 19:32, 35, 37; R. Yoh. 20:2, 3)
Ka karanta 2 Sarakuna 21:1-6, 16.
Me ya sa za a iya cewa Manasseh yana ɗaya daga cikin miyagun sarakuna da suka yi sarauta a Urushalima? (2 Laba. 33:4-6, 9)
Sarkin Kirki na Ƙarshe a Isra’ila
Josiah yana ɗan shekara nawa ne sa’ad da ya zama sarki, menene ya fara yi sa’ad da ya kai shekara bakwai yana sarauta?
Menene ka ga Josiah yake yi a wannan hoton?
Menene babban firist ya samu sa’ad da ake yi wa haikali gyara?
Menene ya sa Josiah ya yaga rigarsa?
Waɗanne saƙonni ne daga Jehobah annabi Huldah ya gaya wa Josiah?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 2 Labarbaru 34:1-28.
Wane misali ne Josiah ya kafa wa waɗanda dole ne su jimre wa yaranta mai wuya? (2 Laba. 33:21-25; 34:1, 2; Zab. 27:10)
Wane mataki ne mai muhimmanci Josiah ya ɗauka domin ya faɗaɗa bauta ta gaskiya a shekara ta 8, 12, da kuma 18 na sarautarsa? (2 Laba. 34:3, 8)
Wane darasi ne za mu koya game da kula da wajen bautarmu daga misalin Sarki Josiah da kuma babban firist Hilkiah? (2 Laba. 34:9-13; Mis. 11:14; 1 Kor. 10:31)
Mutumin da Baya Tsoro
Wanene wannan saurayi da ke wannan hoto?
Wane tunani ne Irmiya ya yi game da zama annabi, amma menene Jehobah ya gaya masa?
Wane saƙo ne Irmiya ya ci gaba da gaya wa mutane?
Ta yaya firistoci suka yi ƙoƙarin hana Irmiya, amma ta yaya ya nuna cewa baya tsoro?
Menene ya faru sa’ad da Isra’ilawa suka ƙi canja miyagun halayensu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Irmiya 1:1-8.
Kamar yadda misalin Irmiya ya nuna, menene yake sa mutum ya cancanci bauta wa Jehobah? (2 Kor. 3:5, 6)
Wane ƙarfafa ne misalin Irmiya ya yi wa matasa a ikilisiyar Kirista a yau? (M. Wa. 12:1; 1 Tim. 4:12)
Ka karanta Irmiya 10:1-5.
Wane kwananci ne mai muhimmanci Irmiya ya yi amfani da shi ya nuna wautar dogara ga gumaka? (Irm. 10:5; Isha. 46:7; Hab. 2:19)
Ka karanta Irmiya 26:1-16.
Sa’ad da suke sanar da saƙon gargaɗi a yau, ta yaya raguwar shafaffu suke tuna umurnin Jehobah ta bakin Irmiya ‘kada ka rage kome magana ɗaya’? (Irm. 26:2; K. Sha 4:2; A. M. 20:27)
Wane misali ne mai kyau Irmiya ya yi tanadi ga Shaidun Jehobah a yau wajen sanar da gargaɗin Jehobah ga al’ummai? (Irm. 26:8, 12, 14, 15; 2 Tim. 4:1-5)
Ka karanta 2 Sarakuna 24:1-17.
Wane mugun sakamako ne Yahuda ta samu domin rashin amincinta ga Jehobah? (2 Sar. 24:2-4, 14)
Yara Huɗu a Babila
Su wanene ne waɗannan yara huɗu a hoton, kuma me ya kawo su Babila?
Wane shiri ne Nebuchadnezzar yake da shi domin yara huɗun, kuma wace doka ce ya ba bayinsa?
Wane roƙo ne Daniel ya yi game da abinci da abin sha domin kansa da kuma abokansa uku?
Bayan sun ci mabunƙusa ƙasa na kwanaki goma, menene bambancin Daniel da abokansa uku indan aka gwada su da sauran matasan?
Ta yaya Daniel da abokansa uku suka zo suka kasance a cikin fadar sarki, kuma a wace hanya ce suka fi firistoci da kuma masu hikima?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Daniel 1:1-21.
Wane irin ƙoƙari ne ake bukata idan muna so mu tsayayya wa jaraba da kuma raunana? (Dan. 1:8; Far. 39:7, 10; Gal. 6:9)
A waɗanne hanyoyi ne za a iya jarabtar matasa a yau ko kuma a matsa musu su saka hannu cikin abin da wasu suke ɗauka ‘abinci mai armashi’? (Dan. 1:8; Mis. 20:1; 2 Kor. 6:17–7:1)
Menene labarin Littafi Mai Tsarki na matasa Yahudawa huɗu ya koya mana game da neman ilimi na duniya? (Dan. 1:20; Isha. 54:13; 1 Kor. 3:18-20)
An Halaka Urushalima
Menene yake faruwa da Urushalima da kuma Isra’ilawa da aka nuna a wannan hoton?
Wanene Ezekiel, kuma wani abin mamaki ne Jehobah ya nuna masa?
Domin Isra’ilawa ba su daraja Jehobah ba, menene ya yi musu alkawari?
Menene Sarki Nebuchadnezzar ya yi bayan da Isra’ilawa suka yi masa tawaye?
Me ya sa Jehobah ya ƙyale irin wannan muguwar halaka ta sami Isra’ilawa?
Ta yaya aka bar ƙasar Isra’ila babu kowa cikinta, kuma har na shekara nawa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 2 Sarakuna 25:1-26.
Wanene Zedekiah, kuma menene ya same shi, kuma ta yaya ne wannan ya cika annabcin Littafi Mai Tsarki? (2 Sar. 25:5-7; Ezek. 12:13-15)
Waye Jehobah ya kama da hakkin dukan rashin amincin da Isra’ila ta nuna? (2 Sar. 25:9, 11, 12, 18, 19; 2 Laba. 36:14, 17)
Ka karanta Ezekiel 8:1-18.
Ta yaya Kiristendam suka yi koyi da Isra’ilawa da suka yi ridda suke bauta wa rana? (Ezek. 8:16; Isha. 5:20, 21; Yoh. 3:19-21; 2 Tim. 4:3)
Sun Ƙi Yin Sujada
Wace doka ce Nebuchadnezzar, sarkin Babila ya bai wa mutane?
Me ya sa Daniel da kuma abokanansa uku suka ƙi yi wa gunkin zinariya sujada?
Sa’ad da Nebuchadnezzar ya bai wa Ibraniyawa ukun wani zarafin su yi sujada, ta yaya suka nuna dogararsu ga Jehobah?
Menene Nebuchadnezzar ya sa mutane su yi wa Shadrach, Meshach, da kuma Abednego?
Menene Nebuchadnezzar ya gani sa’ad da ya dubi cikin tanderun?
Me ya sa sarkin ya yabi Allahn Shadrach, Meshach, da Abednego, kuma wane misali ne suka yi mana tanadi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Daniel 3:1-30.
Wane hali ne da Ibraniyawa uku suka nuna ya kamata dukan bayin Allah su yi koyi da shi sa’ad da suke fuskantar gwajin imaninsu? (Dan. 3:17, 18; Mat. 10:28; Rom. 14:7, 8)
Wane darasi ne mai muhimmanci Jehobah ya koya wa Nebuchadnezzar? (Dan. 3:28, 29; 4:34, 35)
Rubutun Hannu a Bango
Menene ya faru sa’ad da sarkin Babila ya yi wani babban biki kuma ya yi amfani da kofinan da kwanukan da aka kwaso daga haikalin Jehobah a Urushalima?
Menene Belshazzar ya gaya wa masu hikimarsa, amma menene ba su iya yi ba?
Menene mamar sarkin ta ce masa ya yi?
Bisa ga abin da Daniel ya gaya wa sarkin, me ya sa Allah ya aiki hannun ya yi rubutu a bango?
Yaya Daniel ya yi bayanin game da ma’anar kalmomin da ke kan bangon?
Menene ya faru sa’ad da Daniel yake magana?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Daniel 5:1-31.
Ka bambanta tsoro ta ibada da irin tsoron da Belshazzar ya ji sa’ad da ya ga hannu yana rubutu a bango. (Dan. 5:6, 7; Zab. 19:9; Rom. 8:35-39)
Ta yaya Daniel ya nuna gaba gaɗi ƙwarai sa’ad da yake magana da Belshazzar da kuma baƙinsa? (Dan. 5:17, 18, 22, 26-28; A. M. 4:29)
A wace hanya ce Daniel sura 5 ta nuna ikon Jehobah bisa dukan sararin samaniya? (Dan. 4:17, 25; 5:21)
Daniel Cikin Ramin Zakuna
Wanene Darius, kuma yaya ya ɗauki Daniel?
Menene wasu mutane masu kishi suka sa Darius ya yi?
Menene Daniel ya yi sa’ad da sami labari game da sabuwar doka?
Me ya sa ran Darius ya ɓaci sosai har ya kasa barci, kuma menene ya yi washegari?
Ta yaya Daniel ya amsa wa Darius?
Menene ya sami miyagun mutane da suka yi ƙoƙari su kashe Daniel, kuma menene Darius ya rubuta wa dukan mutane da suke masarautarsa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Daniel 6:1-28.
Ta yaya haɗin baki a kan Daniel ya tuna mana abin da ’yan hamayya suka yi domin su hana aikin Shaidun Jehobah a zamani nan? (Dan. 6:7; Zab. 94:20; Isha. 10:1; Rom. 8:31)
Ta yaya bayin Allah a yau za su yi koyi da Daniel su kasance masu ‘bin doka?’ (Dan. 6:5, 10; Rom. 13:1; A. M. 5:29)
Ta yaya za mu yi koyi da misalin Daniel na bauta wa Jehobah “kullum”? (Dan. 6:16, 20; Filib. 3:16; R. Yoh. 7:15)
Mutanen Allah Suna Fitowa Daga Babila
Kamar yadda aka kwatanta a hoton, menene Isra’ilawa suke yi?
Ta yaya Cyrus ya cika annabcin Jehobah ta bakin Ishaya?
Menene Cyrus ya gaya wa Isra’ilawa da ba za su iya komawa Urushalima ba?
Menene Cyrus ya bai wa mutanen su koma Urushalima da shi?
Shekara nawa ne Isra’ilawa suka yi kafin suka koma ƙasarsu?
Shekaru nawa ne suka shige ƙasar ta kasance babu kowa a cikinta?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ishaya 44:28 da 45:1-4.
Ta yaya Jehobah ya nanata tabbacin cikar annabci game da Cyrus? (Isha. 55:10, 11; Rom. 4:17)
Menene annabcin Ishaya game da Cyrus ya nuna game da iyawar Jehobah na faɗin abin da ke zuwa a nan gaba? (Isha. 42:9; 45:21; 46:10, 11; 2 Bit. 1:20)
Ka karanta Ezra 1:1-11.
Bin misalin waɗanda suka ƙasa zuwa Urushalima, ta yaya za mu ‘ƙarfafa hannun’ waɗanda suka sami damar shiga hidima na cikakken lokaci? (Ezra 1:4, 6; Rom. 12:13; Kol. 4:12)
Dogara ga Taimakon Allah
Mutane nawa ne suka yi doguwar tafiya daga Babila zuwa Urushalima, kuma menene suka gani sa’ad da suka isa?
Menene Isra’ilawa suka fara ginawa sa’ad da suka isa, kuma menene abokan gabansu suka yi?
Su wanene Haggai da Zachariah, kuma menene suka gaya wa mutanen?
Me ya sa Tattenai ya aika da wasiƙa zuwa Babila, kuma wace amsa aka ba shi?
Menene Ezra ya yi da ya sami labarin bukatar gyara haikalin Allah?
Menene Ezra yake addu’a a kai a wannan hoton, kuma ta yaya aka amsa addu’arsa, kuma menene wannan ya koya mana?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ezra 3:1-13.
Idan muka sami kanmu a wurin da babu ikilisiyar mutanen Allah, menene ya kamata mu ci gaba da yi? (Ezra 3:3, 6; A. M. 17:16, 17; Ibran. 13:15)
Ka karanta Ezra 4:1-7.
Wane misali ne Zerubbabel ya kafa wa mutanen Jehobah game da shirka? (Fit. 34:12; 1 Kor. 15:33; 2 Kor. 6:14-17)
Ka karanta Ezra 5:1-5, 17 da kuma 6:1-22.
Me ya sa abokan gaba suka kasa hana aikin gina haikali? (Ezra 5:5; Isha. 54:17)
Ta yaya abin da dattawa Yahudawa suka yi ya ƙarfafa dattawa Kiristoci su biɗi ja-gorar Jehobah sa’ad da suke fuskantar hamayya? (Ezra 6:14; Zab. 32:8; Rom. 8:31; Yaƙ. 1:5)
Ka karanta Ezra 8:21-23, 28-36.
Kafin mu yi wani abu, wane misali ne na Ezra ya kamata mu yi koyi da shi? (Ezra 8:23; Zab. 127:1; Mis. 10:22; Yaƙ. 4:13-15)
Mordekai da Esther
Su wanene Mordekai da Esther?
Me ya sa Sarki Ahasuerus ya bukaci ya yi aure, kuma wacece ya zaɓa?
Wanene Haman, kuma me ya sa ya yi fushi sosai?
Wace doka ce aka kafa, kuma menene Esther ta yi bayan ta sami saƙo daga Mordekai?
Menene ya sami Haman kuma menene ya sami Mordekai?
Ta yaya aka ceci Isra’ilawa daga abokan gabansu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Esther 2:12-18.
Ta yaya Esther ta nuna muhimmancin kasancewa da “ruhu mai-ladabi mai-lafiya”? (Esther 2:15; 1 Bit. 3:1-5)
Ka karanta Esther 4:1-17.
Kamar yadda aka bai wa Esther zarafin ɗaukan mataki domin bauta ta gaskiya, wane zarafi ne aka ba mu a yau mu furta ibadarmu da kuma amincinmu ga Jehobah? (Esther 4:13, 14; Mat. 5:14-16; 24:14)
Ka karanta Esther 7:1-6.
Ta yaya mutanen Allah da yawa a yau suke fuskantar tsanantawa kamar yadda, Esther ta fuskanta? (Esther 7:4; Mat. 10:16-22; 1 Bit. 2:12)
Ganuwar Urushalima
Yaya Isra’ilawa suka ji domin birnin su Urushalima ba ta da ganuwa?
Wanene Nehimiah?
Menene aikin Nehemiah, kuma me ya sa yake da muhimmanci?
Wane labari ne ya sa Nehemiah baƙin ciki, kuma me ya yi?
Ta yaya Sarki Artaxerxes ya yi wa Nehemiah kirki?
Ta yaya Nehemiah ya shirya aikin gini saboda abokan gaban Isra’ilawa kada su hana aikin?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Nehemiah 1:4-6 da kuma 2:1-20.
Ta yaya Nehemiah ya biɗi ja-gorar Jehobah? (Neh. 2:4, 5; Rom. 12:12; 1 Bit. 4:7)
Ka karanta Nehemiah 3:3-5.
Menene dattawa da kuma bayi masu hidima za su koya daga bambanci da ke tsakanin Tekoiyawa da kuma “hakimansu”? (Neh. 3:5, 27; 2 Tas. 3:7-10; 1 Bit. 5:5)
Ka karanta Nehemiah 4:1-23.
Me ya motsa Isra’ilawa su ci gaba da gini duk da hamayya da suke fuskanta? (Neh. 4:6, 8, 9; Zab. 50:15; Isha. 65:13, 14)
A wace hanya ce misalin Isra’ilawa yake motsa mu a yau?
Ka karanta Nehemiah 6:15.
Menene gina ganuwar Urushalima cikin watanni biyu ya nuna game da ikon bangaskiya? (Zab. 56:3, 4; Mat. 17:20; 19:26)
Mala’ika Ya Ziyarci Maryamu
Wacece wannan matar a wannan hoton?
Menene Jibrailu, ya gaya wa Maryamu?
Ta yaya Jibrailu ya yi wa Maryamu bayani cewa za ta haifi jariri ko da yake ba ta taɓa zama da na miji ba?
Menene ya faru sa’ad da Maryamu ta ziyarci ’yan’uwarta Alisabatu?
Menene Yusufu ya yi tunaninsa sa’ad da ya fahimci cewa Maryamu za ta haifi jariri, amma me ya sa ya canza ra’ayinsa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Luka 1:26-56.
Menene Luka 1:35 ya nuna game da duka wani ajizanci na Adamu a cikin Maryamu sa’ad da aka ƙaurar da ran Ɗan Allah daga duniya ta ruhu? (Hag. 2:11-13; Yoh. 6:69; Ibran. 7:26; 10:5)
Ta yaya aka daraja Yesu kafin ma a haife shi? (Luk 1:41-43)
Wane misali ne mai kyau Maryamu ta yi wa Kiristoci waɗanda suke da gata na musamman tanadi? (Luk 1:38, 46-49; 17:10; Mis. 11:2)
Ka karanta Matta 1:18-25.
Ko da yake an ba wa Yesu suna Immanuel, ta yaya aikinsa na mutum ya cika ma’anar wannan suna? (Mat. 1:22, 23; Yoh. 14:8-10; Ibran. 1:1-3)
An Haifi Yesu a Barga
Wanene jaririn da ke wannan hoto, kuma a ina ne Maryamu take kwantar da shi?
Me ya sa aka haifi Yesu a cikin barga na dabbobi?
A cikin hoton nan waɗanne mutane ne suke shiga cikin bargar, kuma menene mala’ika ya gaya musu?
Me ya sa Yesu ɗa ne na musamman?
Me ya sa za a iya kiran Yesu Ɗan Allah?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Luka 2:1-20.
Menene Kaisar Agustus ya yi wajen cika annabci game da haihuwar Yesu? (Luk 2:1-4; Mi. 5:2)
Ta yaya mutum zai kasance cikin waɗanda aka kira “mutanen da ya ke murna da su sarai”? (Luk 2:14; Mat. 16:24; Yoh. 17:3; A. M. 3:19; Ibran. 11:6)
Idan Yahudawa makiyaya suna da dalilin farin ciki domin haihuwar Mai Ceto, wane babban dalili ne bayin Allah a yau suke da shi na farin ciki? (Luka 2:10, 11; Afisawa 3:8, 9; Ru’ya ta Yohanna 11:15; 14:6)
Masu Bin Taurari
Su wanene waɗannan mutane a wannan hoton, kuma me ya sa ɗayansu yake nuna tauraro mai haske da hannunsa?
Me ya sa Sarki Hirudus ya yi fushi, kuma menene ya yi?
Ina ne tauraron nan mai haske ya kai mutanen, kuma me ya sa suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam?
Wace doka ce Hirudus ya bayar kuma me ya sa?
Menene Jehobah ya gaya wa Yusufu ya yi?
Waye ya sa sabon tauraron ya yi haske kuma me ya sa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 2:1-23.
Yesu yana da shekara nawa ne kuma a ina suke da zama sa’ad da masu bin taurarin suka ziyarce shi? (Mat. 2:1, 11, 16)
Saurayi Yesu a Haikali
Shekarar Yesu nawa ne a wannan hoton, kuma a ina yake?
Menene Yusufu da iyalinsa suka yi kowace shekara?
Bayan sun yi yini suna tafiyar komawa gida, me ya sa Yusufu da Maryamu suka koma Urushalima?
A ina ne Yusufu da Maryamu suka samu Yesu, kuma me ya sa mutane da suke wajen suka yi mamaki?
Menene Yesu ya gaya wa mamarsa, Maryamu?
Ta yaya za mu zama kamar Yesu sa’ad da muke koyo game da Allah?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Luka 2:41-52.
Ko da Dokar tana bukatar maza kaɗai su halarci idodi kowace shekara, wane misali ne mai kyau Yusufu da Maryamu suka nuna wa iyaye a yau? (Luk 2:41; K. Sha 16:16; 31:12; Mis. 22:6)
Ta yaya Yesu ya kafa misali mai kyau ga matasa a yau wajen yi wa iyayensu biyayya? (Luk 2:51; K. Sha 5:16; Mis. 23:22; Kol. 3:20)
Ka karanta Matta 13:53-56.
Waɗanne ’yan’uwan Yesu huɗu ne aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, ta yaya aka yi amfani da biyu cikinsu a cikin ikilisiyar Kirista daga baya? (Mat. 13:55; A. M. 12:17; 15:6, 13; 21:18; Gal. 1:19; Yaƙ. 1:1; Yahu. 1)
Yohanna Ya Yi wa Yesu Baftisma
Su waye ne waɗannan maza biyu a wannan hoton?
Ta yaya ake yi wa mutum baftisma?
Su wanene ainihi Yohanna yake wa baftisma?
Don wane dalili na musamman ne Yesu ya gaya wa Yohanna ya yi masa baftisma?
Ta yaya Allah ya nuna cewa ya yi farin ciki da Yesu ya yi baftisma?
Menene ya faru sa’ad da Yesu ya tafi wurin da ba kowa na kwana 40?
Su waye ne mabiyan Yesu na farko, ko kuma almajirai, wace mu’ujiza ta farko ne ya yi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 3:13-17.
Wane gurbi ne Yesu ya kafa don baftisma na almajiransa? (Zab. 40:7, 8; Mat. 28:19, 20; Luk 3:21, 22)
Ka karanta Matta 4:1-11.
Ta yaya yadda Yesu ya yi amfani da Nassosi da kyau yake ƙarfafa mu mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai? (Mat. 4:5-7; 2 Bit. 3:17, 18; 1 Yoh. 4:1)
Ka karanta Yohanna 1:29-51.
Wurin wa Yohanna mai Baftisma ya ja-goranci almajiransa, ta yaya za mu yi koyi da shi a yau? (Yoh. 1:29, 35, 36; 3:30; Mat. 23:10)
Ka karanta Yohanna 2:1-12.
Ta yaya mu’ujizar Yesu na farko ya nuna cewa Jehobah ba ya hana bayinsa kowane abu mai kyau? (Yoh. 2:9, 10; Zab. 84:11; Yaƙ. 1:17)
Yesu ya Tsabtace Haikali
Me ya sa ake sayar da dabbobi a cikin haikali?
Menene ya sa Yesu fushi?
Yadda ka gani a wannan hoton, menene Yesu ya yi, wane umurni ne ya ba mutanen da suke sayar da kurciyoyi?
Sa’ad da mabiyan Yesu suka ga abin da yake yi, menene suka tuna?
Wane yanki ne Yesu ya yi tafiya a ciki da yake koma Galili?
Ƙarin tambayoyi?
Ka karanta Yohanna 2:13-25.
Yin la’akari da yadda Yesu ya yi fushi da masu canja kuɗi a haikali, wane ra’ayi ne da ya dace ya kamata mu kasance da shi game da ayyukan kasuwanci a Majami’ar Mulki? (Yoh. 2:15, 16; 1 Kor. 10:24, 31-33)
Da Mace a Bakin Rijiya
Me ya sa Yesu ya tsaya a rijiya da ke Samariya, menene yake gaya wa matar da ke wurin?
Me ya sa matar take mamaki, menene Yesu ya gaya mata, kuma me ya sa?
Wane irin ruwa ne matar take tunani Yesu yake magana, amma wane ruwa ne ainihi yake nufi?
Me ya sa matar take mamaki don abin da Yesu ya sani game da ita, kuma ta yaya ya samu wannan bayani?
Waɗanne darussa za mu iya koya daga labarin matar da ke rijiya?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Yohanna 4:5-43.
Ta wurin bin misalin Yesu, wane hali ne ya kamata mu nuna wa mutane daga wata ƙasa ko yanayin zama? (Yoh. 4:9; 1 Kor. 9:22; 1 Tim. 2:3, 4; Tit. 2:11)
Wane amfani na ruhaniya ne mutumin da ya zama almajirin Yesu yake samu? (Yoh. 4:14; Isha. 58:11; 2 Kor. 4:16)
Ta yaya za mu nuna godiya kamar na mata Basamariya, wadda ta yi dokin gaya wa mutane abin da ta koya? (Yoh. 4:7, 28; Mat. 6:33; Luk 10:40-42)
Yesu Yana Koyarwa a Kan Dutse
A wannan hoton, a ina ne Yesu yake koyarwa, kuma su waye suka zauna kusa da shi?
Menene sunayen manzanni 12?
Menene Mulkin da Yesu yake wa’azi game da shi?
Menene Yesu ya koya wa mutanen su yi addu’a a kai?
Menene Yesu ya ce game da yadda ya kamata mutane su bi da juna?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 5:1-12.
A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa mun san bukatarmu ta ruhaniya? (Mat. 5:3; Rom. 10:13-15; 1 Tim. 4:13, 15, 16)
Ka karanta Matta 5:21-26.
Ta yaya Matta 5:23, 24 ta nuna cewa dangantakarmu da ’yan’uwanmu yana shafan dangantakarmu da Jehobah? (Mat. 6:14, 15; Zab. 133:1; Kol. 3:13; 1 Yoh. 4:20)
Ka karanta Matta 6:1-8.
Waɗanne irin adalcin kai ne Kiristoci za su guje wa? (Luk 18:11, 12; 1 Kor. 4:6, 7; 2 Kor. 9:7)
Ka karanta Matta 6:25-34.
Menene Yesu ya koyar game da dogara ga Jehobah don biyan bukata? (Fit. 16:4; Zab. 37:25; Filib. 4:6)
Ka karanta Matta 7:1-11.
Menene kwatanci da ke Matta 7:5 ya koya mana? (Mis. 26:12; Rom. 2:1; 14:10; Yaƙ. 4:11, 12)
Yesu Ya Ta da Matattu
Wanene baban yarinyar a wannan hoton, kuma me ya sa shi da matarsa suka damu?
Menene Yariyus ya yi sa’ad da ya sami Yesu?
Menene ya faru sa’ad da Yesu yake zuwan gidan Yariyus, wane saƙo ne Yariyus ya samu a hanya?
Me ya sa mutane da ke gidan Yariyus suka yi wa Yesu dariya?
Bayan ya ɗauki manzanni uku da iyayen yarinyar zuwa dakin yarinyar, menene Yesu ya yi?
Wanene Yesu ya ta da daga matattu, kuma menene wannan ya nuna?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Luka 8:40-56.
Ta yaya Yesu ya nuna juyayi da sanin ya kamata ga matar da ke zuban jini, menene dattawa Kirista a yau za su koya daga wannan? (Luk 8:43, 44, 47, 48; Lev. 15:25-27; Mat. 9:12, 13; Kol. 3:12-14)
Ka karanta Luka 7:11-17.
Me ya sa waɗanda suka yi rashin waɗanda suke ƙauna a mutuwa suka sami ta’aziyya ta abin da Yesu ya yi wa gwauruwa daga garin Nayin? (Luk 7:13; 2 Kor. 1:3, 4; Ibran. 4:15)
Ka karanta Yohanna 11:17-44.
Ta yaya Yesu ya nuna ya yi daidai mutum ya yi makoki domin mutuwar ƙaunatacce? (Yoh. 11:33-36, 38; 2 Sam. 18:33; 19:1-4)
Yesu ya Ciyar da Mutane Masu Yawa
Wane mugun abu ne ya faru da Yohanna mai Baftisma, kuma yaya Yesu ya ji game da wannan?
Ta yaya Yesu ya ciyar da mutane da suka bi shi, kuma yaya ne yawan abinci da aka rage?
Me ya sa almajiran suka ji tsoro daddare, kuma me ya faru da Bitrus?
Ta yaya Yesu ya ciyar da dubban mutane a lokaci na biyu?
Me ya sa zai zama abin ban al’ajabi idan Yesu ya yi sarautar duniya a matsayin Sarkin Allah?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 14:1-32.
Labarin Matta 14:23-32 ya ba da wane fahimi ne game da mutuntakar Bitrus?
Ta yaya labarin Nassi ya nuna cewa Bitrus ya manyanta kuma ya sha kan halinsa na motsin rai? (Mat. 14:27-30; Yoh. 18:10; 21:7; A. M. 2:14, 37-40; 1 Bit. 5:6, 10)
Ka karanta Matta 15:29-38.
Ta yaya Yesu ya nuna daraja ga tanadi na ruhaniya da Babansa yake yi? (Mat. 15:37; Yoh. 6:12; Kol. 3:15)
Ka karanta Yohanna 6:1-21.
Ta yaya Kiristoci a yau za su bi misalin Yesu game da gwamnati? (Yoh. 6:15; Mat. 22:21; Rom. 12:2; 13:1-4)
Yesu Yana Ƙaunar Yara Ƙanana
Menene manzanni suke gardama a kai da suke komawa gida daga doguwar tafiya?
Me ya sa Yesu ya kira yaro ƙarami ya tsayar da shi a tsakiyar manzannin?
A wace hanya ce ya kamata manzanni su koya su zama kamar yara?
’Yan watanni daga baya, ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar yara?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 18:1-4.
Me ya sa Yesu ya yi amfani da kwatanci wajen koyarwa? (Mat. 13:34, 36; Mar. 4:33, 34)
Ka karanta Matta 19:13-15.
Waɗanne halaye ne na yara dole mu yi koyi da shi idan za mu sami albarka ta Mulki? (Zab. 25:9; 138:6; 1 Kor. 14:20)
Ka karanta Markus 9:33-37.
Menene Yesu ya koya wa almajiransa game da son matsayi? (Mar. 9:35; Mat. 20:25, 26; Gal. 6:3; Filib. 2:5-8)
Ka karanta Markus 10:13-16.
Menene dattawa na Kirista za su iya koya daga misalin Yesu na yadda mutane suke zuwan wajensa? (Markus 6:30-34; Filib. 2:1-4; 1 Tim. 4:12)
Yadda Yesu Yake Koyarwa
Wace tambaya ce wani mutum ya yi wa Yesu, kuma me ya sa?
Da me Yesu wani lokaci yake amfani da shi wajen koyarwa, kuma menene muka koya game da Yahudawa da Samariyawa?
A labarin da Yesu ya gaya mana, menene ya faru da Bayahude da yake tafiya a kan hanyar zuwa Jericho?
Menene ya faru sa’ad da firist Bayahude da Balawi suke wuce wa a hanya?
A cikin hoton, wanene yake taimakon Bayahude da aka ji masa rauni?
Bayan da Yesu ya gama labarin, wace tambaya ce ya yi, kuma yaya mutumin ya amsa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Luka10:25-37.
Maimako ya ba da amsa kai tsaye, ta yaya Yesu ya taimaki masanin Attaurat ya yi tunani game da batun? (Luk 10:26; Mat. 16:13-16)
Ta yaya Yesu ya yi amfani da kwatanci ya sa masu sauraronsa su sha kan wariya? (Luk 10:36, 37; 18:9-14; Tit. 1:9)
Yesu Ya Warkar da Marasa Lafiya
Menene Yesu yake yi yayin da yake tafiya a dukan ƙasar?
Shekara uku bayan Yesu ya yi baftisma, menene ya gaya wa manzanninsa?
Su waye ne mutane da suke cikin wannan hoton, kuma menene Yesu ya yi wa matar?
Me ya sa yadda Yesu ya amsa wani hani na shugabannan addinai ya sa su kunya?
Sa’ad da Yesu da manzanninsa suka kusa Jericho, menene Yesu ya yi wa maroƙa makafi biyu?
Me ya sa Yesu ya yi mu’ujizai?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 15:30, 31.
Wane ikon Jehobah na musamman ne aka bayyana ta Yesu, yaya ya kamata wannan ya shafi fahiminmu ga abin da Jehobah ya yi alkawarinsa don sabuwar duniya? (Zab. 37:29; Isha. 33:24)
Ka karanta Luka 13:10-17.
Ta yaya gaskiyar cewa Yesu ya yi wasu cikin mu’ujizai na musamman a ranar Asabarci ya nuna cewa zai kawo sauƙi ga ’yan adam a lokacin Sarautarsa na Shekara Dubu? (Luk 13:10-13; Zab. 46:9; Mat. 12:8; Kol. 2:16, 17; R. Yoh. 21:1-4)
Ka karanta Matta 20:29-34.
Ta yaya wannan labarin ya nuna cewa Yesu bai shagala ba da ba zai iya taimakon mutane ba, menene za mu koya daga wannan? (Kubawar Shari’a 15:7; Yaƙub 2:15, 16; 1 Yohanna 3:17)
Yesu Ya Shigo Kamar Sarki
Sa’ad da Yesu ya shigo wani ƙaramin ƙauye kusa da Urushalima, menene ya gaya wa almajiransa su yi?
A wannan hoton, menene ya faru sa’ad da Yesu ya kusa da birnin Urushalima?
Menene yara suka yi sa’ad da suka ga Yesu yana warkar da makafi da naƙasassu?
Menene Yesu ya gaya wa firistoci masu fushi?
Ta yaya za mu zama kamar yara da suka yabi Yesu?
Menene almajiran suke son su sani?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 21:1-17.
Ta yaya yadda Yesu ya shiga Urushalima a matsayin Sarki ya bambanta da na sarakunan Romawa na lokacin? (Mat. 21:4, 5; Zech. 9:9; Filib. 2:5-8; Kol. 2:15)
Wane darassi ne matasa za su koya daga yara Isra’ilawa da suka yi ƙaulin Zabura ta 118 sa’ad da Yesu ya shiga haikalin? (Mat. 21:9, 15; Zab. 118:25, 26; 2 Tim. 3:15; 2 Bit. 3:18)
Ka karanta Yohanna 12:12-16.
Ganyayen dabino da mutanen da suka yabi Yesu suka yi amfani da shi yana wakiltar menene? (Yoh. 12:13; Filib. 2:10; R. Yoh. 7:9, 10)
A Kan Dutsen Zaitun
A wannan hoton, wanene Yesu, su waye suke tare da shi?
Menene firistoci suke ƙoƙarin yi wa Yesu a Haikali, kuma me ya ce musu?
Menene manzannin suka tambayi Yesu?
Me ya sa Yesu ya gaya wa manzaninsa wasu cikin abubuwa da za su faru a duniya sa’ad da yake sarauta a sama?
Menene Yesu ya ce zai faru kafin ya kawo ƙarshen mugunta a duniya?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 23:1-39.
Ko da yake Nassosi ya nuna cewa yin amfani da laƙabi ya dace, menene kalmomin Yesu da ke Matta 23:8-11 ya nuna game da yin amfani da laƙabi a cikin ikilisiyar Kirista? (A. M. 26:25; Rom. 13:7; 1 Bit. 2:13, 14)
Menene Farisawa suka yi amfani da shi don su yi ƙoƙari su hana mutane zama Kiristoci, kuma yaya shugabannan addinai suke amfani da irin wannan dabara a zamani? (Mat. 23:13; Luk 11:52; Yoh. 9:22; 12:42; 1 Tas. 2:16)
Ka karanta Matta 24:1-14.
Ta yaya aka nanata muhimmancin jimiri a Matta 24:13?
Menene wannan furcin “matuƙa” da ke Matta 24:13 yake nufi? (Mat. 16:27; Rom. 14:10-12; 2 Kor. 5:10)
Ka karanta Markus 13:3-10.
Wane furci ne da ke Markus 13:10 ya nuna gaggawar wa’azin bishara, ta yaya ya kamata kalmomin Yesu su shafe mu? (Rom. 13:11, 12; 1 Kor. 7:29-31; 2 Tim. 4:2)
A Ɗaki a Gidan Sama
Kamar yadda aka nuna a hoto, me ya sa Yesu da manzanninsa 12 suke babban ɗaki a gidan sama?
Wane mutum ne yake fita, menene zai yi?
Wane abinci na musamman ne Yesu ya soma da aka gama jibin Ƙetarewa?
Idin Ƙetarewan ya tuna wa Isra’ilawa game da wane aukuwa ne, kuma menene wannan abinci na musamman ya tuna wa mabiyan Yesu?
Bayan Jibin Maraice na Ubangiji, menene Yesu ya gaya wa mabiyansa, kuma menene suka yi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 26:14-30.
Ta yaya Matta 26:15 ya nuna cewa Yahuda Iskariyoti ya ci amanar Yesu da ganga?
Wane manufa biyu ne jinin da Yesu ya zubar ya cika? (Mat. 26:27, 28; Irm. 31:31-33; Afis. 1:7; Ibran. 9:19, 20)
Ka karanta Luka 22:1-39.
A wane azanci ne Shaiɗan ya shiga wurin Yahuda? (Luk 22:3; Yoh. 13:2; A. M. 1:24, 25)
Ka karanta Yohanna 13:1-20.
Domin labarin da ke Yohanna 13:2, Yahuda ya yi laifi ne don abin da ya yi, wane darassi ne bayin Allah za su koya daga wannan? (Far. 4:7; 2 Kor. 2:11; Gal. 6:1; Yaƙ. 1:13, 14)
Wane darassi ne mai muhimmanci Yesu ya koyar? (Yoh. 13:15; Mat. 23:11; 1 Bit. 2:21)
Ka karanta Yohanna 17:1-26.
A wane azanci ne Yesu ya yi addu’a don mabiyansa su “zama ɗaya”? (Yoh. 17:11, 21-23; Rom. 13:8; 14:19; Kol. 3:14)
Yesu a Cikin Gadina
Ina ne Yesu da manzanninsa suka tafi bayan sun bar gidan bene, menene ya gaya musu su yi?
Menene Yesu ya gan almajiransa suke yi sa’ad da ya koma inda suke, sau nawa ne wannan ya faru?
Wanene ya shiga gadina ɗin, menene Yahuda Iskariyoti ya yi, yadda aka nuna a wannan hoton?
Me ya sa Yahuda ya yi wa Yesu sumba, menene Bitrus ya yi?
Menene Yesu ya gaya wa Bitrus, me ya sa Yesu bai gaya wa Allah ya aika mala’iku ba?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 26:36-56.
Ta yaya yadda Yesu ya gargaɗi almajiransa ya zama misali mai kyau ga dattawa Kirista a yau? (Mat. 20:25-28; 26:40, 41; Gal. 5:17; Afis. 4:29, 31, 32)
Ta yaya Yesu ya ɗauki yin amfani da makamai ga ’yan’uwa? (Mat. 26:52; Luk 6:27, 28; Yoh. 18:36)
Ka karanta Luka 22:39-53.
Sa’ad da mala’ika ya bayyana ga Yesu a gadina na Jathsaimani ya ƙarfafa shi, wannan ya nuna cewa Yesu bai tsaya da ƙarfi a kan bangaskiyarsa ba ne? Ka ba da bayani. (Luk 22:41-43; Isha. 49:8; Mat. 4:10, 11; Ibran. 5:7)
Ka karanta Yohanna 18:1-12.
Ta yaya Yesu ya kāre almajiransa daga masu hamayyarsa, menene za mu koya daga wannan misalin? (Yohanna 10:11, 12; 18:1, 6-9; Ibraniyawa 13:6; Yaƙub 2:25)
An Kashe Yesu
Wanene ainihi yake da alhakin mutuwar Yesu?
Menene manzannin suka yi sa’ad da shugabannan addinai suka ɗauki Yesu?
Menene ya faru a gidan Kayafa, babban firist?
Me ya sa Bitrus ya fita ya yi kuka?
Bayan da aka mayar da Yesu zuwa wurin Bilatus, ihun menene shugaban firistoci suka yi?
Menene ya faru da Yesu ranar Jumma’a da rana, wane alkawari ne ya yi wa wani mai laifi da aka rataye kusa da shi?
A ina ne Aljanna da Yesu ya yi maganarsa za ta kasance?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 26:57-75.
Ta yaya waɗanda suke cikin babban kotu na Yahudawa suka nuna cewa zuciyarsu na da mugunta? (Mat. 26:59, 67, 68)
Ka karanta Matta 27:1-50.
Me ya sa za mu ce tuban Yahuda ba na gaskiya ba ne? (Mat. 27:3, 4; Mar. 3:29; 14:21; 2 Kor. 7:10, 11)
Ka karanta Luka 22:54-71.
Menene za mu koya daga yadda Bitrus ya yi musun sanin Yesu a daren da aka ci amanarsa kuma aka kama shi? (Luk 22:60-62; Mat. 26:31-35; 1 Kor. 10:12)
Ka karanta Luka 23:1-49.
Ta yaya Yesu ya aikata ga rashin gaskiya da aka yi masa, wane darassi za mu iya koya daga wannan? (Luk 23:33, 34; Rom. 12:17-19; 1 Bit. 2:23)
Ka karanta Yohanna 18:12-40.
Ko da Bitrus ya ji tsoron ’yan adam na ɗan lokaci, menene ya nuna cewa ya farfaɗo kuma ya zama manzo fitacce? (Yoh. 18:25-27; 1 Kor. 4:2; 1 Bit. 3:14, 15; 5:8, 9)
Ka karanta Yohanna 19:1-30.
Wane daidaitaccen ra’ayi ne Yesu yake da shi game da abin duniya? (Yoh. 2:1, 2, 9, 10; 19:23, 24; Mat. 6:31, 32; 8:20)
Ta yaya kalmomin da Yesu ya furta sa’ad da yake son ya mutu ya nuna cewa ya yi nasara wajen ɗaukaka ikon mallakar Jehobah? (Yoh. 16:33; 19:30; 2 Bit. 3:14; 1 Yoh. 5:4)
Yesu Yana da Rai
Wacece matar da ke wannan hoton, su wanene maza biyun, ina suke kuma?
Me ya sa Bilatus ya gaya wa firistoci su aika sojoji su tsare kabarin Yesu?
Menene mala’ika ya yi da sassafe a rana ta uku bayan mutuwar Yesu, amma menene firistocin suka yi?
Me ya sa wasu mata suka yi mamaki sa’ad da suka ziyarci kabarin Yesu?
Me ya sa Bitrus da Yohanna suka gudu zuwa kabarin Yesu, kuma me suka gani?
Menene ya faru da jikin Yesu, menene ya yi don ya nuna wa almajiran cewa yana da rai?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Matta 27:62-66 da 28:1-15.
A lokacin tashin Yesu daga matattu, ta yaya shugaban firistoci, Farisawa da manyan malamai suka yi zunubi ga ruhu mai tsarki? (Mat. 12:24, 31, 32; 28:11-15)
Ka karanta Luka 24:1-12.
Ta yaya labarin tashin Yesu daga matattu ya nuna cewa Jehobah ya ɗauki mata a matsayin tabbatattun shaidu? (Luka 24:4, 9, 10; Mat. 28:1-7)
Ka karanta Yohanna 20:1-12.
Ta yaya Yohanna 20:8, 9 ya taimake mu mu ga bukatar yin haƙuri idan ba mu fahimci cikar annabci na Littafi Mai Tsarki ba? (Mis. 4:18; Mat. 17:22, 23; Luk 24:5-8; Yoh. 16:12)
Cikin Ɗakin da Ke Kulle
Menene Maryamu ta ce wa mutum da take tsammani gadina ne, amma menene ya sa ta fahimci cewa ainihi Yesu ne?
Menene ya faru da almajirai biyu da suke tafiya zuwa ƙauyen Imwasu?
Wane abin mamaki ne ya faru sa’ad da almajirai biyu suka gaya wa manzannin cewa sun ga Yesu?
Sau nawa ne Yesu ya bayana ga manzanninsa?
Menene Toma ya ce sa’ad da ya ji cewa almajiran sun ga Ubangiji, amma menene ya faru kwanaki takwas bayan hakan?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Yohanna 20:11-29.
Yesu yana faɗa a Yohanna 20:23 cewa ’yan adam suna da ikon gafarta zunubai ne? Ka ba da bayani. (Zab. 49:2, 7; Isha. 55:7; 1 Tim. 2:5, 6; 1 Yoh. 2:1, 2)
Ka karanta Luka 24:13-43.
Ta yaya za mu shirya zuciyarmu domin ta karɓi gaskiya ta Littafi Mai Tsarki? (Luk 24:32, 33; Ezra 7:10; Mat. 5:3; A. M. 16:14; Ibran. 5:11-14)
Yesu Ya Koma Sama
Almajirai nawa ne suka ga Yesu a wani lokaci, menene ya gaya musu?
Menene Mulkin Allah, yaya rayuwa za ta zama a duniya sa’ad da Yesu ya yi sarauta na shekara dubu?
Kwanaki nawa ne Yesu ya bayyana wa almajiransa, amma yanzu lokaci ya kai na yin menene?
Kafin ya bar almajiransa, menene Yesu ya gaya musu su yi?
Menene yake faruwa a wannan hoton, kuma ta yaya Yesu ya ɓace ba a sake ganinsa ba?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta 1 Korinthiyawa 15:3-8.
Me ya sa manzo Bulus ya yi magana da gabagaɗi game da tashin Yesu daga matattu, a kan menene Kiristoci a yau suke magana da gabagaɗi? (1 Kor. 15:4, 7, 8; Isha. 2:2, 3; Mat. 24:14; 2 Tim. 3:1-5)
Ka karanta Ayukan Manzanni 1:1-11.
Ta yaya aka yaɗa aikin wa’azi, yadda aka furta a Ayukan Manzanni 1:8? (A. M. 6:7; 9:31; 11:19-21; Kol. 1:23)
Suna Jira a Urushalima
Yadda wannan hoton ya nuna, menene ya faru da mabiyan Yesu da suke jira a Urushalima?
Wane abin mamaki ne baƙi suka gani a Urushalima?
Menene Bitrus ya bayyana wa mutanen?
Yaya mutane suka ji bayan sun saurari Bitrus, kuma menene ya gaya musu?
Mutane nawa ne suka yi baftisma a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z.?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayukan Manzanni 2:1-47.
Ta yaya kalmomin Bitrus da ke Ayukan Manzanni 2:23, 36, ya nuna cewa dukan al’ummar Yahudawa ne suke da alhakin mutuwar Yesu? (1 Tas. 2:14, 15)
Ta yaya Bitrus ya kafa misali mai kyau a wajen yin mahawara daga Nassosi? (A. M. 2:16, 17, 29, 31, 36, 39; Kol. 4:6)
Ta yaya Bitrus ya yi amfani da “maƙulai na mulkin sama,” da Yesu ya yi alkawari zai ba shi? (A. M. 2:14, 22-24, 37, 38; Mat. 16:19)
An ’Yantar da Su Daga Kurkuku
Menene ya faru da Bitrus da Yohanna wata rana sa’ad da suke zuwa haikali?
Menene Bitrus ya ce wa wani gurgu, kuma menene Bitrus ya ba shi da ya fi kuɗi amfani?
Me ya sa shugabannan addinai suka yi fushi, menene suka yi wa Bitrus da Yohanna?
Menene Bitrus ya gaya wa shugabannan addinai, kuma wane gargaɗi ne manzannin suka karɓa?
Me ya sa shugabanan addinai suke kishi, menene ya faru sa’ad da aka saka manzannin cikin kurkuku lokaci na biyu?
Ta yaya manzannin suka amsa sa’ad da aka kawo su majami’ar Majalisa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayyukan Manzanni 3:1-10.
Ko da ba mu da ikon yin mu’ujizai a yau, ta yaya kalmomin Bitrus da ke Ayukan Manzanni 3:6, ya taimake mu mu ga amfanin saƙon Mulkin? (Yoh. 17:3; 2 Kor. 5:18-20; Filib. 3:8)
Ka karanta Ayukan Manzanni 4:1-31.
Sa’ad da muka fuskanci hamayya a hidimarmu, a wace hanya ce ya kamata mu yi koyi da ’yan’uwanmu na ƙarni na farko? (A. M. 4:29, 31; Afis. 6:18-20; 1 Tas. 2:2)
Ka karanta Ayukan Manzanni 5:17-42.
Ta yaya wasu da ba Shaidu ba ne a yanzu da kuma dā suka nuna sanin ya kamata game da aikin wa’azi? (A. M. 5:34-39)
An Jejjefi Istafanus
Wanene Istafanus, menene Allah yake taimakon shi ya yi?
Menene Istafanus ya faɗa da ya sa shugabanan addinai fushi?
Sa’ad da mutane suka ja Istafanus zuwa bayan gari, menene suka yi masa?
A cikin wannan hoton, wanene saurayin da ke tsaye kusa da tufafi?
Kafin ya mutu, menene Istafanus ya yi wa Jehobah addu’a a kai?
Ta yin koyi da Istafanus, menene ya kamata mu yi sa’ad da wani ya yi mana laifi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayukan Manzanni 6:8-15.
Waɗanne ayyukan ruɗu ne shugabanan addinai suka yi amfani da shi don su daina aikin wa’azi na Shaidun Jehobah? (A. M. 6:9, 11, 13)
Ka karanta Ayukan Manzanni 7:1-60.
Menene ya taimaki Istafanus ya ba da amsa da kyau game da bisharar a gaban Majalisa, menene za mu koya daga misalinsa? (A. M. 7:51-53; Rom. 15:4; 2 Tim. 3:14-17; 1 Bit. 3:15)
Wane hali ne ya kamata mu kasance da shi game da masu hamayya da aikinmu? (A. M. 7:58-60; Mat. 5:44; Luk 23:33, 34)
A Hanyar Zuwa Dimaska
Menene Shawulu ya yi bayan aka kashe Istafanus?
Sa’ad da Shawulu yake hanya zuwa Dimaska, wane abin mamaki ne ya faru?
Menene Yesu ya gaya wa Shawulu ya yi??
Wane umurni ne Yesu ya ba wa Ananias, ta yaya Shawulu ya soma gani kuma?
Da wane suna ne aka san Shawulu da shi, kuma yaya aka yi amfani da shi?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayukan Manzanni 8:1-4.
Ta yaya hamayya da ta faɗa wa ikilisiyar Kirista da aka kafa sabo ya sa aka yaɗa bangaskiya ta Kirista, kuma yaya hakan ya faru a wannan zamani? (A. M. 8:4; Isha. 54:17)
Ka karanta Ayukan Manzanni 9:1-20.
Wane irin aiki uku ne Yesu ya bayyana yake son Shawulu ya yi? (A. M. 9:15; 13:5; 26:1; 27:24; Rom. 11:13)
Ka karanta Ayukan Manzanni 22:6-16.
Ta yaya za mu zama kamar Ananias, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci? (A. M. 22:12; 1 Tim. 3:7; 1 Bit. 1:14-16; 2:12)
Ka karanta Ayukan Manzanni 26:8-20.
Ta yaya tuban Shawulu zuwa Kiristanci ya zama abin ƙarfafa ga waɗanda abokan aurensu ba masu bi ba ne? (A. M. 26:11; 1 Tim. 1:14-16; 2 Tim. 4:2; 1 Bit. 3:1-3)
Bitrus Ya Ziyarci Karniliyus
Wanene mutumin da ya durƙusa a cikin wannan hoton?
Menene mala’ika ya gaya wa Karniliyus?
Menene Allah ya sa Bitrus ya gani sa’ad da yake kan daɓen rufin gidan Siman a Yafa?
Me ya sa Bitrus ya gaya wa Karniliyus kada ya durƙusa ya bauta masa?
Me ya sa almajirai Yahudawa da suke tare da Bitrus suka yi mamaki?
Wane darassi mai muhimmanci ya kamata mu koya daga ziyarar Bitrus ga Karniliyus?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayukan Manzanni 10:1-48.
Menene kalmomin Bitrus da ke A. M. 10:42 ya nuna game da aikin wa’azin bishara na Mulkin? (Mat. 28:19; Mar. 13:10; A. M. 1:8)
Ka karanta A. M. 11:1-18.
Wane hali ne Bitrus ya nuna sa’ad da ja-gorar Jehobah game da ’yan Al’umma ya zama a bayane, ta yaya za mu yi koyi da misalinsa? (A. M. 11:17, 18; 2 Kor. 10:5; Afis. 5:17)
Timothawus, Sabon Mataimakin Bulus
Wanene matashi da ke wannan hoton, ina yake zama, menene sunan mamarsa da kakarsa?
Menene Timothawus ya ce sa’ad da Bulus ya tambaye shi ko zai so ya bi shi da Sila wajen yi wa mutane a wasu ƙasashe wa’azi?
Ina ne aka soma kiran mabiyan Yesu Kiristoci?
Bayan da Bulus da Barnaba suka bar Antakiya, waɗanne birane ne suka kai ziyara?
Ta yaya Timothawus ya taimaki Bulus, wace tambaya ce ya kamata matasa a yau su tambayi kansu?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta A. M. 9:19-30.
Ta yaya manzo Bulus ya yi amfani da basira sa’ad da ya fuskanci hamayya ga bishara? (A. M. 9:22-25, 29, 30; Mat. 10:16)
Ka karanta A. M. 11:19-26.
Ta yaya labarin da ke A. M. 11:19-21, 26 ya nuna cewa ruhun Jehobah yana yi wa aikin wa’azi ja-gora?
Ka karanta Ayukan Manzanni 13:13-16, 42-52.
Ta yaya A. M. 13:51, 52 ya nuna cewa almajirai ba su ƙyale hamayya ta sa su sanyin gwiwa ba? (Mat. 10:14; A. M. 18:6; 1 Bit. 4:14)
Ka karanta A. M. 14:1-6, 19-28.
Ta yaya furci nan “suka danƙa su ga Ubangiji” yake taimaka wajen sauƙaƙa mu daga alhini da bai dace ba sa’ad da muke taimakon sababbi? (A. M. 14:21-23; 20:32; Yoh. 6:44)
Ka karanta A. M. 16:1-5.
Ta yaya yadda Timothawus ya yi biyayya da yin kaciya ya nanata muhimmancin yin “abu duka sabili da bishara”? (A. M. 16:3; 1 Kor. 9:23; 1 Tas. 2:8)
Ka karanta A. M. 18:1-11, 18-22.
Menene A. M. 18:9, 10 ya nuna game da yadda Yesu ya sa hannu kai tsaye a aikin wa’azi, wane tabbaci ne wannan ya ba mu a yau? (Mat. 28:20)
Yaro da Ya Yi Barci
A wannan hoton, wane yaro ne yake kwanciya a ƙasa, menene ya faru da shi?
Menene Bulus ya yi sa’ad da ya ga cewa yaron ya mutu?
Ina ne Bulus, Timothawus, da waɗanda suke tafiya da su suke zuwa, kuma menene ya faru sa’ad da suka tsaya a Militus?
Wane kashedi ne annabi Agabus ya ba Bulus, kuma yaya abin da annabin ya faɗa ya faru?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta A. M. 20:7-38.
Ta yaya za mu zama “kuɓutace ne daga jinin dukan mutane,” bisa ga kalmomin Bulus da ke A. M. 20:26, 27? (Ezek. 33:8; A. M. 18:6, 7)
Me ya sa ya kamata dattawa su ‘riƙe amintacciyar magana’ sa’ad da suke koyarwa? (A. M. 20:17, 29, 30; Tit. 1:7-9; 2 Tim. 1:13)
Ka karanta A. M. 26:24-32.
Ta yaya Bulus ya yi amfani da zama ɗan Roma wajen cika aikin wa’azi da Yesu ya ba shi? (A. M. 9:15; 16:37, 38; 25:11, 12; 26:32; Luk 21:12, 13)
Jirgi Ya Yi Haɗari a Tsibiri
Menene ya faru da jirgi da Bulus yake ciki sa’ad da suka kusa tsibirin Karita?
Menene Bulus ya gaya wa waɗanda suke cikin jirgin?
Ta yaya jirgin ya farfashe?
Wane umurni ne hafsan sojoji mai kula da jirgin ya bayar, mutane nawa ne suka kai gaɓar tekun?
Menene sunan tsibirin da suka sauka, menene ya faru da Bulus sa’ad da yanayin ya yi kyau?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta A. M. 27:1-44.
Ta yaya aka ƙarfafa amincinmu ga gaskiyar Littafi Mai Tsarki sa’ad da muka karanta labarin tafiyar Bulus zuwa Roma? (A. M. 27:16-19, 27-32; Luk 1:3; 2 Tim. 3:16, 17)
Ka karanta A. M. 28:1-14.
Idan arna mazaunan Malita sun motsa su nuna wa manzo Bulus da abokansa da ke cikin jirgi “alheri irin da ba a kan saba yi ba,” ya kamata Kiristoci su nuna menene kuma a wace hanya? (A. M. 28:1, 2; Ibran. 13:1, 2; 1 Bit. 4:9)
Bulus a Roma
Wanene Bulus ya yi wa wa’azi da yake fursuna a Roma?
A cikin wannan hoton, wanene baƙo da yake rubutu a kan teburi, menene yake wa Bulus?
Wanene Abafroditus, menene ya ɗauka sa’ad da ya koma Filibbi?
Me ya sa Bulus ya rubuta wa Filimon abokinsa na kud da kud wasiƙa?
Menene Bulus ya yi sa’ad da aka ’yantar da shi, menene ya faru da shi bayan haka?
Wanene Jehobah ya yi amfani da shi ya rubuta wasiƙu na ƙarshe na Littafi Mai Tsarki, menene littafin Ru’ya ta Yohanna ya yi magana a kai?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ayukan Manzanni 28:16-31 da Filibbiyawa 1:13.
Ta yaya Bulus ya yi amfani da lokacinsa sa’ad da yake fursuna a Roma, kuma yaya bangaskiyarsa mai ƙarfi ta shafi ikilisiyar Kirista? (A. M. 28:23, 30; Filib.1:14)
Ka karanta Filibbiyawa 2:19-30.
Wane furci na godiya ne Bulus ya yi game da Timothawus da Abafroditus, ta yaya za mu yi koyi da misalin Bulus? (Filib. 2:20, 22, 25, 29, 30; 1 Kor. 16:18; 1 Tas. 5:12, 13)
Ka karanta Filimon 1-25.
A kan menene Bulus ya aririci Filimon ya yi abin da ya dace, yaya wannan ya zama abin ja-gora ga dattawa a yau? (Fil. 9; 2 Kor. 8:8; Gal. 5:13)
Ta yaya furcin Bulus da ke Filimon 13, 14 ya nuna cewa yana daraja lamirin wasu a cikin ikilisiya? (1 Kor. 8:7, 13; 10:31-33)
Ka karanta 2 Timothawus 4:7-9.
Kamar manzo Bulus, ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai saka mana idan mun kasance da aminci har ƙarshe? (Mat. 24:13; Ibran. 6:10)
Ƙarshen Dukan Mugunta
Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi maganar dawakai a sama?
Menene sunan yaƙin Allah da mugaye a duniya, menene manufar wannan yaƙin?
Daga wannan hoton, wanene zai shugabancin yaƙin, me ya sa ya saka kambi, menene takobinsa yake nufi?
Bisa ga abin da aka tattauna a Labarai na 10 da 15, me ya sa bai kamata mu yi mamaki ba cewa Allah zai halaka mugayen mutane?
Ta yaya Labari na 33, 36, da 76 suka nuna mana cewa Allah zai halaka mugaye ko idan suna da’awa suna bauta masa?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 19:11-16.
Ta yaya Nassosi ya bayana sarai cewa Yesu Kristi shi ne matuƙin farin doki? (R. Yoh. 1:5; 3:14; 19:11; Isha. 11:4)
Ta yaya jini da aka yafa a tufar Yesu ya tabbatar cewa zai gama cin nasara? (R. Yoh. 14:18-20; 19:13; Isha. 63:1-6)
Su wanene wataƙila za a haɗa cikin rundunar da suka bi Yesu a farin dokinsa? (R. Yoh. 12:7; 19:14; Mat. 25:31, 32)
Sabuwar Aljanna a Duniya
Wane yanayi ne Littafi Mai Tsarki ya nuna za mu more a cikin Aljanna a duniya?
Wane alkawari ne Littafi Mai Tsarki ya yi don waɗanda za su yi rayuwa a cikin Aljanna?
Yaushe ne Yesu zai ga cewa waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi sun faru?
Sa’ad da Yesu yake duniya, menene ya yi da ya nuna abin da zai yi idan ya zama Sarki na Mulkin Allah?
Menene Yesu da abokansa na sama za su tabbata su yi sa’ad da suka soma sarauta daga sama bisa duniya?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.
Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa waɗanda za su yi sarauta bisa duniya a lokacin Sarauta na Shekara Dubu za su zama sarakuna da firistoci masu tausayi da jinƙai? (Afis. 4:20-24; 1 Bit. 1:7; 3:8; 5:6-10)
Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 14:1-3.
Menene ake nufi cewa an rubuta sunan Uba da sunan Ɗan Rago a goshin mutane 144,000? (1 Kor. 3:23; 2 Tim. 2:19; R. Yoh. 3:12)
Yadda Za Mu Rayu Har Abada
Menene ya kamata mu sani idan za mu rayu har abada?
Ta yaya za mu koya game da Jehobah Allah da Yesu, yadda ƙaramar yariyar nan da abokanta suka nuna a wannan hoton?
Wane littafi ne kuma ka gani a wannan hoton, me ya sa ya kamata mu karanta shi koyaushe?
Ban da koya game da Jehobah da Yesu, menene kuma ake bukata don a sami rai na har abada?
Wane darassi muka koya daga Labari na 69?
Menene misali mai kyau na yaro Sama’ila a Labari na 55 ya nuna?
Ta yaya za mu bi misalin Yesu Kristi, idan muka yi hakan, menene za mu iya yi nan gaba?
Ƙarin tambayoyi:
Ka karanta Yohanna 17:3.
Ta yaya Nassosi ya nuna cewa samun cikakken sani na Jehobah Allah da Yesu Kristi ba haddace gaskiya ba ne kawai? (Mat. 7:21; Yaƙ. 2:18-20; 1 Yoh. 2:17)
Ka karanta Zabura 145:1-21.
Waɗanne dalilai ne muke da su na bauta wa Jehobah? (Zab. 145:8-11; R. Yoh. 4:11)
Ta yaya Jehobah “mai-alheri ne ga dukan mutane,” kuma ta yaya wannan ya kamata ya sa mu matsa kusa sosai da shi? (Zab. 145:9; Mat. 5:43-45)
Idan muna ƙaunar Jehobah sosai, menene wannan zai motsa mu mu yi? (Zab. 119:171, 172, 175; 145:11, 12, 21)