Ya dace in yi baftisma ne?
BABI NA 37
Ya dace in yi baftisma ne?
Ka yi maki ko wadannan furucin gaskiya ne ko karya:
Dole ne Kirista ya yi baftisma.
□ Gaskiya
□ Karya
Ainihin dalilin da ya sa ya kamata ka yi baftisma shi ne ya kāre ka daga yin zunubi.
□ Gaskiya
□ Karya
Baftisma za ta sa ka sami ceto.
□ Gaskiya
□ Karya
Idan ba ka yi baftisma ba, ba ka da hakki a gaban Allah.
□ Gaskiya
□ Karya
Idan abokanka suna baftisma, hakan ya nuna cewa kai ma ka isa ka yi baftisma.
□ Gaskiya
□ Karya
IDAN kana bin ka’idodin da ke Littafi Mai Tsarki kuma ka kulla dangantaka da Allah kuma kana gaya wa mutane abubuwan da ka yi imani da su, babu shakka tunanin yin baftisma zai shigo zuciyarka. Amma ta yaya za ka san cewa ka shirya dauka wannan matakin? Kafin mu iya amsa tambayar nan, bari mu ga amsoshin furucin da ke sama.
● Dole ne Kirista ya yi baftisma.
Gaskiya. Yesu ya umurci mabiyansa su yi baftisma. (Matiyu 28:19, 20) Yesu da kansa ma an yi masa baftisma. Idan kana so ka zama mabiyin Kristi, dole ne ka yi baftisma idan ka kai shekarun da ka za ka iya yanke wannan shawarar kuma kana da dalilai masu kyau na yin hakan.
● Ainihin dalilin da ya sa ya kamata ka yi baftisma shi ne ya kāre ka daga yin zunubi.
Karya. Baftisma tana nuna wa mutane cewa ka yi wa Jehobah alkawarin bauta masa. Ba za ka yi alkawarin bauta wa Jehobah don ya hana ka yin abubuwan da kake so ka yi a boye ba. Amma za ka yi hakan ne don kana so ka yi rayuwa bisa ga ka’idodin Jehobah.
● Baftisma za ta sa ka sami ceto.
Gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce baftisma tana cikin abubuwa masu muhimmanci da za su sa mu sami ceto. (1 Bitrus 3:21) Amma hakan ba ya nufin cewa baftisma tana kama da inshora da za ka yi amfani da ita ka kāre kanka sa’ad da bala’i ya auku. Za ka yi baftisma ne don kana kaunar Jehobah kuma kana so ka bauta masa da dukan zuciyarka har abada.—Markus 12:29, 30.
● Idan ba ka yi baftisma ba, ba ka da hakki a gaban Allah.
Karya. Littafin Yakub 4:17 ta ce: “Saboda haka duk wanda ya san abin da ya kamata ya yi amma ya ki yi, ya yi zunubi ke nan,” ko da ya yi baftisma ko a’a. Idan ka san abin da ya kamata ka yi kuma ka isa ka soma tunani game da rayuwarka, kana bukatar ka tattauna da iyayenka ko kuma wani Kirista da ya manyanta. Za su gaya maka matakan da za ka dauka don ka cancanci yin baftisma.
● Idan abokanka suna baftisma, hakan ya nuna cewa kai ma ka isa ka yi baftisma.
Karya. Kai da kanka ne ya kamata ka yanke shawarar yin baftisma. (Zabura 110:3) Zai dace ka zama Mashaidin Jehobah a lokacin da ka san abin da zama Mashaidin Jehobah ya kunsa kuma ka tabbata cewa kana shirye ka yi wadannan abubuwan.—Mai-Wa’azi 5:4, 5.
Baftisma Za Ta Canja Rayuwarka
Idan ka yi baftisma, rayuwarka za ta canja kuma za ka sami albarka sosai. Amma hakan babban hakki ne, wato cika alkawarin da ka yi wa Jehobah cewa za ka bauta masa shi kadai.
Shin ka kusan yin baftisma? To, hakan abin farin ciki ne sosai. Abin da ya rage maka kadai shi ne ka bauta wa Jehobah da dukan zuciya kuma ka yi rayuwar da za ta nuna cewa shi kadai kake bauta masa.—Matiyu 22:36, 37.
A BABI NA GABA Za ka koyi yadda za ka kafa makasudai da za su sa ka yi rayuwar da ta dace.
NASSOSSI
“Ku mika kanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki, da kuma abin karba ga Allah. Wannan kuwa ita ce hanyar da za ku yi wa Allah hidima ta ainihi.”—Romawa 12:1.
SHAWARA
Ka ce wa iyayenka su taimaka maka ka samo wani a ikilisiya da zai taimaka maka ka sami ci gaba a bautarka ga Jehobah.—Ayyukan Manzanni 16:1-3.
KA SAN CEWA . . .
Yin baftisma yana da muhimmanci domin zai sa ka sami “lambar shaida” da za ta sa ka sami ceto.—Ezekiyel 9:4-6.
ABIN DA ZA KA IYA YI!
Don in cancanci yin baftisma, zan kara sanin wadannan koyarwar Littafi Mai Tsarki:
Abin da zan so in tambayi iyayena game da wannan batun shi ne
ME RA’AYINKA?
● Me ya sa baftisma ba abin wasa ba ne?
● Wadanne abubuwa ne za su iya sa matasa su yi hanzarin yin baftisma?
● Mene ne zai iya sa matashi ya ki yin alkawarin bauta wa Allah da kuma baftisma?
[Akwati]
Sanin cewa na yi baftisma ya taimaka mini in yanke shawarwari masu kyau kuma ya kāre ni daga yin abubuwan da za su sa in shiga matsala.—Holly
[Akwati/Hoto]
Tambayoyin da ake yawan yi game da baftisma
Me baftisma take wakilta? Nitsar da kai cikin ruwa da daga ka yana wakiltar ka bar halayenka na dā, yanzu kuma kana yin nufin Allah a rayuwarka.
Mene ne yin alkawarin bauta wa Jehobah yake nufi? Yana nufin ka ba da kanka ga Allah kuma ka yi alkawari cewa za ka sa yin nufinsa kan gaba fiye da kowane abu. (Matiyu 16:24) Zai dace ka yi alkawarin bauta wa Jehobah a addu’a kafin ka yi baftisma.
Yaya ya kamata ka yi rayuwa kafin baftisma? Zai dace ka yi rayuwar da ta jitu da Kalmar Allah kuma ka rika gaya wa mutane abin da ka yi imani da shi. Ka kulla dangantaka da Allah ta wurin addu’a da kuma nazarin Kalmarsa. Zai dace ka bauta wa Jehobah domin kana so ka yi hakan ba wai wasu ne suke tilasta maka ka yi hakan ba.
Sai ka kai wasu shekaru ne kafin ka yi baftisma? Babu wata shekara da ya kamata mutum ya kai kafin ya yi baftisma. Amma zai dace ka kai shekarun da za ka fahimci ma’anar yin alkawarin bauta wa Jehobah.
Me za ka yi idan kana so ka yi baftisma amma iyayenka suka ce ka dan dakata? Watakila suna so ka manyanta sosai kafin ka yi hakan. Ka amince da shawararsu kuma ka yi amfani da lokacin don ka karfafa dangantakarka da Jehobah.—1 Sama’ila 2:26.
[Akwati]
Worksheet
KANA SO KA YI BAFTISMA?
Ka yi la’akari da tambayoyi da kuma furucin da ke kasa don su taimaka maka ka san ko ka cancanci yin baftisma. Ka tabbata cewa ka karanta nassosin kafin ka rubuta amsarka.
A wadanne hanyoyi ne kake nuna cewa ka dogara ga Jehobah?—Zabura 71:5. ․․․․․
Ta yaya kake nuna cewa kana amfani da hankalinka don ka bambanta nagarta da mugunta?—Ibraniyawa 5:14. ․․․․․
Sau nawa kake yin addu’a?
Me kake ambatawa a addu’arka kuma mene ne hakan ya nuna game da kaunarka ga Jehobah?—Zabura 17:6. ․․․․․
Ka rubuta abubuwan da za ka yi don ka inganta addu’arka. ․․․․․
Kana nazarin Littafi Mai Tsarki da kanka a kai a kai?—Yoshuwa 1:8. ․․․․․
Me da me kake amfani da su sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki? ․․․․․
Ka rubuta abubuwan da za ka yi don ka inganta yadda kake nazari.
Yaya wa’azinka yake? (Alal misali: Za ka iya bayyana ma mutane muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki? Kana komawa ka ziyarci wadanda suka saurare ka? Kana kokari don ka soma nazari da mutane?)
□ E □ A’a
Kana zuwa wa’azi ko da iyayenka ba su je ba?—Ayyukan Manzanni 5:42.
□ E □ A’a
Ka rubuta abubuwan da za ka yi don ka inganta yadda kake wa’azi.—2 Timoti 2:15. ․․․․․
Kana zuwa taro a kai a kai ko a’a?—Ibraniyawa 10:25. ․․․․․
Kakan yi kalami da wasu ayyuka a taro kuwa? ․․․․․
Kana zuwa taro ko da iyayenka ba su je ba (idan ba su hana ka zuwa ba)?
□ E □ A’a
Kana marmarin yin abin da Allah yake so?—Zabura 40:8.
□ E □ A’a
Za ka iya rubuta lokutan da ka ki bin halin tsaranka?—Romawa 12:2. ․․․․․
Wadanne abubuwa ne za ka rika yi don ka ci gaba da kaunar Jehobah sosai?—Yahuda 20, 21. ․․․․․
Za ka ci gaba da bauta wa Jehobah ko da iyayenka da abokanka sun daina yin hakan?—Matiyu 10:36, 37.
□ E □ A’a
Kamar yadda aure ke canja rayuwar mutum, haka ma, idan mutum ya yi baftisma, rayuwarsa za ta canja. Don haka, bai kamata a yanke shawarar yin baftisma cikin gaggawa ba