Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 6

Aljanna Ta Yi Kusa!

Aljanna Ta Yi Kusa!

Miyagun abubuwa da suke faruwa yanzu sun nuna cewa Aljanna ta yi kusa. Littafi Mai Tsarki ya ce za mu ga lokutan bala’i kafin Aljanna ta zo. Muna rayuwa ne yanzu a waɗannan lokuta! Ga wasu abubuwa da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru:

Yaƙe-yaƙe masu tsanani. “Al’umma za ta tasa ma al’umma, mulki kuma za ya tasa ma mulki.” (Matta 24:7) Wannan annabcin ya kasance gaskiya. Tun daga shekara ta 1914, an yi yaƙin duniya guda biyu da kuma ƙananan yaƙe-yaƙe da yawa. Miliyoyin mutane sun mutu a wurin yaƙi.

Yaɗuwar cututtuka. Za a yi a “wuri dabam dabam . . . annoba.” (Luka 21:11) Wannan ya kasance gaskiya kuwa? Hakika. Cutar Kansa, ciwon zuciya, tarin fuka, zazzaɓi, ƙanjamau da kuma wasu cututtuka sun kashe miliyoyin mutane.

Rashin abinci. A dukan duniya akwai mutane waɗanda ba su da isashen abinci da za su ci. Miliyoyin mutane suna mutuwa don yunwa kowace shekara. Wannan wata alama ce cewa Aljanna za ta zo ba da jimawa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za a yi yunwa.”—Markus 13:8.

Girgizar ƙasa. ‘Za a yi . . . girgizar ƙasa wurare dabam dabam.’ (Matta 24:7) Wannan ma ya kasance gaskiya a zamaninmu. Mutane fiye da miliyan ɗaya sun mutu a girgizar ƙasa da dama da suka auku tun daga shekara ta 1914.

Miyagun mutane. Mutane za su zama “masu-son kuɗi” kuma “masu-son kansu.” Za su zama “ma-fiya son annashuwa da Allah.” Yara za su zama “marasa-bin iyaye.” (2 Timotawus 3:1-5) Ba ka yarda cewa akwai irin waɗannan mutane a yau ba? Ba sa daraja Allah, kuma suna adawa da waɗanda suke so su koya game da Allah.

Yin laifi. Mugunta za ta “yawaita.” (Matta 24:12) Wataƙila ka yarda cewa mugunta ta yi tsanani fiye da dā. Mutane suna cutar juna, suna fāshi, kuma yawanci suna fargaba cewa za a yi musu lahani.

Dukan waɗannan sun nuna cewa Mulkin Allah ya yi kusa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Lokacin da kun ga waɗannan al’amura suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya kusa.” (Luka 21:31) Menene Mulkin Allah? Gwamnati ce ta Allah a sama wadda za ta kawo Aljanna ga wannan duniyar. Mulkin Allah zai sauya gwamnatin mutane.—Daniyel 2:44.