Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 11

Ka Ki Addinin Karya!

Ka Ki Addinin Karya!

Shaiɗan da aljanunsa ba sa so ka bauta wa Allah. Suna so su janye kowa daga Allah idan za su iya. Ta yaya suke ƙoƙarin yin wannan? Hanya ɗaya da suke yin wannan ita ce ta addinin ƙarya. (2 Korintiyawa 11:13-15) Addinin da ba ya koyar da gaskiya daga Littafi Mai Tsarki, addinin ƙarya ne. Addinin ƙarya yana kama da jabun kuɗi—jabun kuɗi yana kama da kuɗin gaske, amma ba shi da amfani. Zai iya jefa ka cikin matsala.

Koyarwar addinan ƙarya ba za ta taɓa faranta wa Jehobah rai ba. Lokacin da Yesu yake duniya, akwai rukunin addinai da suke so su kashe shi. Suna ganin cewa hanyar bautarsu ita ce daidai. Suka ce: “Muna da Uba ɗaya, Allah.” Yesu ya yarda ne? A’a! Ya ce masu: “Ku na ubanku Shaiɗan ne.” (Yohanna 8:41, 44) A yau, mutane da yawa suna tunanin cewa suna bauta wa Allah, amma da gaske suna bauta wa Shaiɗan ne da aljanunsa!—1 Korintiyawa 10:20.

Kamar yadda ruɓaɓɓen itace yake ba da ’ya’ya da ba su da kyau, haka ma addinan ƙarya suna haifar da mugayen mutane. Duniya tana cike da masifa domin munanan abubuwa da mutane suke yi. Ana lalata da faɗa da sata da zalunci da ƙisa, da kuma fyaɗe. Yawancin waɗanda suke yin abubuwan nan da ba su da kyau suna da addini, amma addininsu bai motsa su su yi abin da yake nagari ba. Ba za su zama aminan Allah ba sai sun daina yin munanan abubuwa.—Matta 7:17, 18.

Addinan ƙarya suna ƙarfafa mutane su yi addu’a ga gumaka. Allah ya ce kada ka yi addu’a ga gumaka. Wannan daidai ne. Za ka so idan wani ba ya yi maka magana sai hotonka kawai yake yi wa magana? Wannan mutumin zai zama amininka na gaskiya? A’a, ba zai zama ba. Jehobah yana so mutane su yi masa magana, ba don su yi magana da sifa ko hoto ba, waɗanda ba su da rai.—Fitowa 20:4, 5.

Addinan ƙarya suna koyar da cewa daidai ne a kashe wasu a lokacin yaƙi. Yesu ya ce aminan Allah za su nuna ƙauna a tsakaninsu. Ba za mu kashe mutane da muke ƙauna ba. (Yohanna 13:35) Ba daidai ba ne mu kashe miyagun mutane. Lokacin da abokan gāban Yesu suka zo za su kama shi, bai bari almajiransa su yi faɗa don su kāre shi ba.—Matta 26:51, 52.

Addinin ƙarya suna koyar da cewa za a gana wa mugayen mutane azaba cikin wutar jahannama. Amma, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa zunubi yana kai wa ga mutuwa. (Romawa 6:23) Jehobah Allah ne mai ƙauna. Allah mai ƙauna zai azabtar da mutane har abada ne? Babu shakka ba zai yi ba! A cikin Aljanna, addini ɗaya kawai za a bi, wanda Jehobah ya amince da shi. (Ru’ya ta Yohanna 15:4) Dukan addinai da suke koyar da ƙarya ba za su tsira ba.