Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 16

Ka Nuna Cewa Kana Ƙaunar Allah

Ka Nuna Cewa Kana Ƙaunar Allah

Don ka ci gaba da zama aminin Allah, ya kamata kana magana da shi. Ka saurare shi, shi ma zai saurare ka. Dole ne ka faɗi abin da yake da kyau game da amininka ga wasu. Haka yake da zama aminin Allah. Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai-Tsarki ya ce game da wannan:

Ka yi magana da Jehobah a kai a kai cikin addu’a. “Kuna lizima cikin addu’a.”—Romawa 12:12.

Ka karanta Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki. “Kowane nassi hurare daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa.”—2 Timotawus 3:16.

Ka koya wa wasu game da Allah. “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.”—Matta 28:19, 20.

Ka kusaci aminan Allah. “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima.”—Misalai 13:20.

Ka halarci taro a Majami’ar Mulki. “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka . . . mu gargaɗadda juna.”—Ibraniyawa 10:24, 25.

Ka taimaka wajen tallafa wa aikin Mulki. “Kowane mutum shi aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”—2 Korintiyawa 9:7.