Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 1

Allah Yana Gayyatarka Ka Zama Amininsa

Allah Yana Gayyatarka Ka Zama Amininsa

Allah yana so ka zama amininsa. Ka taɓa tunanin za ka zama aminin Wanda ya fi girma a dukan duniyar nan? Ibrahim, wanda ya rayu a can dā, an kira shi aminin Allah. (Yaƙub 2:23) Wasu da aka yi maganarsu a cikin Littafi Mai-Tsarki, aminan Allah ne kuma sun sami albarka ƙwarai. A yau, mutane daga dukan ɓangarorin duniya sun zama aminan Allah. Kai ma, za ka iya zama aminin Allah.

Zama aminin Allah ya fi zama aminin mutum. Allah bai taɓa kasa biyan burin aminansa ba. (Zabura 18:25) Zama aminin Allah ya fi samun arziki. Lokacin da mai arziki ya mutu, kuɗaɗensa za su zama na wasu. Amma, aminan Allah suna da dukiyar da babu wanda zai iya ƙwacewa.—Matta 6:19.

Wasu mutane za su yi ƙoƙarin su hana ka koya game da Allah. Wasu abokanka da iyalinka za su yi ƙoƙarin wannan. (Matta 10:36, 37) Idan wasu suka yi maka dariya ko kuma suka yi maka barazana, ka tambayi kanka, ‘Waye na ke so na faranta wa rai—mutane ko kuma Allah?’ Ka yi tunani game da wannan: Idan wani ya gaya maka ka daina cin abinci, za ka yi masa biyayya ne? Babu shakka ba za ka yi ba! Kana bukatan abinci don ka rayu. Amma Allah zai iya sa ka rayu har abada! Don haka kada ka bar kowa ya hana ka koyon yadda za ka zama aminin Allah.—Yohanna 17:3.