Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 7

Gargadi Daga Abin da Ya Faru a Dā

Gargadi Daga Abin da Ya Faru a Dā

Jehobah ba zai bari miyagun mutane su lalata Aljanna ba. Aminansa ne kawai za su zauna a ciki. Me zai faru da miyagun mutane? Don mu san amsar, bari mu bincika labarin Nuhu. Nuhu ya rayu shekaru dubbai da suka shige. Mutumin kirki ne da ya yi ƙoƙari sosai ya yi nufin Jehobah. Amma wasu mutane a duniya suna yin abubuwan da ba su da kyau. Sai Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa zai sa ambaliya ta halaka dukan waɗannan miyagun mutane. Ya gaya wa Nuhu ya gina jirgi saboda kar shi da iyalinsa su mutu lokacin da Ambaliyar ta fara.—Farawa 6:9-18.

Nuhu da iyalinsa sun gina jirgin. Nuhu ya yi wa mutane gargaɗi cewa Ambaliya tana zuwa, amma ba su saurare shi ba. Sun ci gaba da yin abubuwa da ba su da kyau. Bayan sun gama gina jirgin, Nuhu ya kwashi dabbobi ya saka su a cikin jirgin, kuma shi da iyalinsa suka shiga ciki. Sai Jehobah ya sa aka yi ruwan sama na kwana 40 da dare 40. Ruwan ya zama ambaliya a dukan duniya.—Farawa 7:7-12.

An hallaka miyagun mutane, amma Nuhu da iyalinsa sun tsira. Jehobah ya cece su daga Ambaliyar kuma suka zauna a cikin duniyar da aka kawar da masu mugunta. (Farawa 7:22, 23) Littafi Mai Tsarki ya ce lokaci yana zuwa kuma da Jehobah zai halaka waɗanda suka ƙi su yi abin da yake nagari. Ba za a halaka mutanen kirki ba. Za su rayu har abada a Aljanna.—2 Bitrus 2:5, 6, 9.

A yau mutane da yawa suna yin abubuwan da ba su da kyau. Duniya tana cike da damuwa. Jehobah ya aike Shaidunsa a kai a kai su gargaɗi mutane, duk da haka yawancinsu ba sa so su saurari kalmomin Jehobah. Ba sa so su canja halayensu. Ba sa so su yarda da abin da Allah ya ce yana da kyau da kuma abin da ya ce ba ya da kyau. Me zai faru da waɗannan mutanen? Za su canja ne wata rana? Da yawa ba za su taɓa canjawa ba. Lokaci yana zuwa da za a halaka miyagun mutane, ba za su sake rayuwa ba kuma.—Zabura 92:7.

Duniya ba za ta halaka ba; za a mayar da ita ta zama aljanna. Waɗanda suka zama aminan Allah za su zauna a cikin Aljanna har abada a duniya.—Zabura 37:29.