DARASI NA 12
Me Ke Faruwa Bayan Mutuwa?
Mutuwa tana akasi da rai. Mutuwa tana kama da barci mai zurfi. (Yohanna 11:11-14) Matattu ba za su iya jin magana, gani, yi magana, ko kuma su yi tunanin wani abu ba. (Mai-Wa’azi 9:5, 10) Addinan ƙarya suna koyar da cewa matattu sun je lahira su zauna da kakaninsu. Wannan ba abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar ba ne.
Waɗanda suka mutu ba za su iya taimakonmu ba, kuma ba za su iya yi mana lahani ba. Abu ne mai sauƙi mutane su yi tsafi da kuma hadaya don suna ganin cewa za su faranta wa matattu rai. Wannan yana ɓata wa Allah rai domin yana ɗaya daga cikin ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan yake yaɗawa. Ba zai faranta wa matattun rai ba, tun da ba su da rai. Bai kamata mu ji tsoron matattu ba ko kuma mu bauta musu. Ya kamata mu bauta wa Allah ne kawai.—Matta 4:10.
Matattu za su sake rayuwa. Jehobah zai tashe matattu a duniya da ta zama aljanna. Wannan lokaci har yanzu yana gaba. (Yohanna 5:28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15) Allah zai iya tasan waɗanda suka mutu kamar yadda za ka iya tasan mutum daga barci babu wata shakka.—Markus 5:22, 23, 41, 42.
Batun cewa ba ma mutuwa, ƙarya ne da Shaiɗan Iblis yake yaɗawa. Shaiɗan da aljanunsa suna sa mutane suna gani kamar matattu suna fatalwa da ke rayuwa bayan mutuwa kuma suna haddasa cututtuka da kuma wasu bala’i. Shaiɗan yana yaudarar mutane, wasu lokuta ta mafarki da kuma wahayi. Jehobah ya la’anci waɗanda suke ƙoƙarin su yi magana da matattu.—Kubawar Shari’a 18:10-12.