DARASI NA 13
Sihiri da Maita Ba Su da Kyau
Shaiɗan yana so ka riƙa yin sihiri. Mutane da yawa suna yin hadaya ga kakaninsu da suka mutu ko iskoki su tsare kansu daga lahani. Suna yin haka ne domin suna tsoro kada ruhohin kakaninsu su yi musu lahani. Suna saka zobba da kuma kambuna. Suna shan “magani” na sihiri ko kuwa su shafa a jikinsu. Wasu sukan ɓoye magungunan a gidajensu ko su binne a wani wuri dabam domin sun gaskata cewa hakan zai kāre su. Wasu suna amfani da “magani” domin sun gaskata cewa zai kawo kasuwa, zai ba da nasara a jarabawa ta makaranta, ko kuma wajen zawarci.
Abin da zai kāre mu daga tarkon Shaiɗan shi ne zama aminin Jehobah. Jehobah Allah da mala’ikunsa sun fi Shaiɗan da aljanunsa ƙarfi. (Yaƙub 2:19; Ru’ya ta Yohanna 12:9) A shirye Jehobah yake ya nuna ikonsa wajen tsare aminansa—waɗanda suke da aminci ƙwarai a wurinsa.—2 Labarbaru 16:9.
Kalmar Allah ta ce: ‘Kada ku yi sihiri.’ Jehobah ya la’anci yin sihiri da kuma maita domin waɗannan abubuwa za su iya saka mutum a ƙarƙashin ikon Shaiɗan Iblis.—Levitikus 19:26.