Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 8

Su Waye ne Abokan Gāban Allah?

Su Waye ne Abokan Gāban Allah?

Babban abokin gāban Allah Shaiɗan Iblis ne. Halitta ne na ruhu da ya yi wa Jehobah tawaye. Shaiɗan yana ci gaba da yaƙi da Allah kuma yana jawo wa ’yan Adam matsaloli da yawa. Shaiɗan mugu ne. Maƙaryaci ne kuma mai kisa.—Yohanna 8:44.

Wasu halittun ruhu sun bi Shaiɗan sun yi wa Allah tawaye. Littafi Mai Tsarki ya kira su aljanu. Kamar Shaiɗan, aljanu abokan gāban ’yan Adam ne. Suna yi wa mutane lahani. (Matta 9:32, 33; 12:22) Jehobah zai halaka Shaiɗan da kuma aljanunsa har abada. Nan ba da daɗewa ba, za a hana su wahal da ’yan Adam.—Ru’ya ta Yohanna 12:12.

Idan kana so ka zama aminin Allah, dole ne ka ƙi yin abin da Shaiɗan yake so ka yi. Shaiɗan da aljanunsa ba sa son Jehobah. Abokan gāba ne na Allah, kuma suna so su sa ka zama abokin gāban Allah. Dole ka zaɓi wanda kake so ka faranta wa rai—Shaiɗan ko kuma Jehobah. Idan kana son rai madawwami, dole ne ka zaɓi yin nufin Allah. Shaiɗan yana da hanyoyi da yawa da kuma dabaru da yake ruɗan mutane. Ya yaudari mutane da yawa.—Ru’ya ta Yohanna 12:9.