Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 9

Su Waye Aminan Allah?

Su Waye Aminan Allah?

Yesu Kristi Ɗan Jehobah ne kuma amininsa ne da suka shaƙu. Kafin Yesu ya zo duniya a matsayin mutum, ya yi rayuwa a sama a matsayin halittan ruhu mai iko. (Yohanna 17:5) Ya zo duniya ne don ya koya wa mutane gaskiya game da Allah. (Yohanna 18:37) Ya bayar da ransa kuma don ya ceci mutane masu biyayya daga zunubi da kuma mutuwa. (Romawa 6:23) Yanzu Yesu shi ne Sarki na Mulkin Allah, gwamnati ta sama wadda za ta mai da wannan duniyar ta zama Aljanna.—Ru’ya ta Yohanna 19:16.

Mala’iku ma aminan Allah ne. Mala’iku ba su soma rayuwarsu a duniya ba kamar mutane. Allah ya halicce su a sama kafin ya halicci duniya. (Ayuba 38:4-7) Akwai miliyoyin mala’iku. (Daniyel 7:10) Waɗannan aminan Allah na sama suna so mutane su koyi gaskiya game da Jehobah.—Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.

Allah kuma yana da aminai a duniya; ya kira su shaidunsa. Mai ba da shaida a kotu yana faɗan abin da ya sani game da wani ko wani abu. Shaidun Jehobah suna gaya wa mutane abin da suka sani game da Jehobah da kuma nufinsa. (Ishaya 43:10) Kamar mala’iku, Shaidun Jehobah suna so su taimake ka ka koyi gaskiya game da Jehobah. Suna so kai ma ka zama aminin Allah.