Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 10

Yadda Za Ka Gane Addini na Gaskiya

Yadda Za Ka Gane Addini na Gaskiya

Idan kana so ka zama aminin Allah, dole ne ka bi addinin da Allah ya amince da shi. Yesu ya ce “masu-yin sujada da gaskiya” za su bauta wa Allah cikin “gaskiya.” (Yohanna 4:23, 24) Hanyar bauta wa Allah guda ɗaya ce kawai ta yi daidai. (Afisawa 4:4-6) Addinin gaskiya yana kai wa ga rai madawwami, na ƙarya kuma yana kai wa ga halaka.—Matta 7:13, 14.

Za ka gane addini na gaskiya ta wajen lura da mabiyansa. Tun da Jehobah yana da kirki, waɗanda suke bauta masa da gaskiya dole ne su zama mutanen kirki. Kamar yadda itacen lemu mai kyau yake ba da ’ya’yan lemu masu kyau, addinin gaskiya yana ba da mutanen kirki.—Matta 7:15-20.

Aminan Allah suna daraja Littafi Mai Tsarki sosai. Sun san cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. Suna bin ja-gorancinsa a rayuwarsu, suna barin ƙa’idodinsa ya taimaka musu su magance matsalolinsu, kuma yana taimaka musu su koya game da Allah. (2 Timotawus 3:16) Suna ƙoƙari su yi abin da suke wa’azinsa.

Aminan Jehobah suna ƙaunar junansu. Yesu ya nuna ƙauna wa mutane ta wajen koya musu game da Allah, da kuma warkar da waɗanda suke ciwo. Waɗanda suke bin addinin gaskiya su ma suna ƙaunar mutane. Kamar Yesu, ba sa rena matsiyata ko kuma waɗanda ba ƙabilunsu ba. Yesu ya ce mutane za su san almajiransa ta wajen ƙauna da suke nuna wa juna.—Yohanna 13:35.

Aminan Allah suna ɗaukaka sunan Allah, Jehobah. Idan wani ya ƙi ya kira sunanka, wannan mutumin zai zama amininka na kusa kusa? A’a! Lokacin da muka yi amini, muna kiran sunansa kuma muna gaya wa wasu abubuwa masu kyau game da shi. Saboda haka waɗanda suke so su zama aminan Allah ya kamata suna kiran sunansa kuma suna gaya wa wasu game da shi. Jehobah yana so mu yi haka.—Matta 6:9; Romawa 10:13, 14.

Kamar Yesu, aminan Allah suna koya wa mutane game da Mulkin Allah. Mulkin Allah gwamnati ce ta sama wadda za ta mayar da duniya ta zama aljanna. Aminan Allah suna gaya wa wasu wannan bisharar game da Mulkin Allah.—Matta 24:14.

Shaidun Jehobah suna ƙoƙari su zama aminan Allah. Suna daraja Littafi Mai Tsarki kuma suna da ƙauna a tsakaninsu. Suna yin amfani da sunan Allah suna ɗaukaka shi kuma suna koya wa wasu game da Mulkin Allah. Shaidun Jehobah ne suke bin addini na gaskiya a yau.