SASHE NA 7
Alkawuran da Allah Ya Yi ta Bakin Annabawa
ANNABAWAN dā sun yi imani ga Allah. Sun gaskata da alkawuransa kuma sun sa rayuwarsu ta jitu da alkawuran. Mene ne waɗannan alkawuran suka ƙunsa?
Bayan Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye, nan da nan Allah ya yi alkawari cewa zai naɗa wani ya ƙuje kan “macijin,” wanda ke wakiltar “babban maciji, . . . tsohon macijin nan, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaitan,” ya halaka shi har abada. (Farawa 3:14, 15; Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Wane ne Wanin da zai zo?
Bayan shekaru 2,000 da yin wannan annabcin na farko, Jehobah ya yi wa annabi Ibrahim alkawari cewa Wanin nan da zai zo zai fito ne daga zuriyarsa. Allah ya gaya wa Ibrahim: “Cikin zuriyarka [ko, ’ya’yanka] kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka; domin ka yi biyayya da maganata.”—Farawa 22:18.
A shekara ta 1473 K.Z., Allah ya yi wa annabi Musa ƙarin bayani game da “zuriyar.” Musa ya gaya wa ’ya’yan Isra’ila: ‘Ubangiji Allahnku za ya tayas maku da wani annabi daga tsakiyarku, a cikin ’yan’uwanku, kamar ni; a gareshi za ku saurara.’ (Kubawar Shari’a 18:15) Kamar Musa, annabin da zai zo zai taso ne daga ’ya’yan Ibrahim.
Wannan annabin zai kuma zama zuriyar Sarki Dauda kuma zai zama sarki mai girma. Allah ya yi wa Sarki Dauda alkawari: ‘Zan kafa zuriyarka daga bayanka, zan kuma kafa mulkinsa. Ni kuma zan tabbatar da kursiyin mulkinsa har abada.’ (2 Sama’ila 7:12, 13) Allah ya kuma bayyana cewa za a kira wannan zuriya na Dauda “Sarkin Salama,” ya kuma daɗa cewa: “Ƙaruwar mulkinsa da salama ba ta da iyaka, a bisa kursiyin Dauda, da bisa mulkinsa, domin a kafa shi, a tabbatar da shi ta wurin gaskiya da adalci daga nan gaba kuma har abada.” (Ishaya 9:6, 7) Hakika, wannan Shugaba mai adalci zai mai do salama da adalci a dukan duniya. Amma a wane lokaci ne zai zo?
Daga baya mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa annabin Allah, Daniyel cewa: “Ka sani fa, ka fahimta kuma, tun daga loton fitowar doka a maida Urushalima, a gine ta kuma, har zuwa loton Masiya sarki, za a yi bakwai bakwai: cikin bakwai sattin da biyu.” (Daniel 9:25) Waɗannan makonnin 69 na shekara ne, wato, shekara bakwai bakwai, adadinsa shekaru ɗari huɗu da tamanin da uku. Sun soma ne daga shekara ta 455 K.Z. zuwa shekara ta 29 A.Z. a
Shin Almasihu, wanda annabi ne kamar Musa kuma “zuriyar” da ake jira tun da daɗewa, ya zo ne a shekara ta 29 A.Z. kuwa? Bari mu gani.
a Duba Ka duba ƙarin bayani na 2, shafi na 255 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.