Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 8

Almasihu Ya Bayyana

Almasihu Ya Bayyana

FIYE da shekara 500 bayan da Daniyel ya yi annabci, mala’ikan Allah, Jibra’ilu ya bayyana ga wata budurwa mai suna Maryamu, wadda zuriyar Sarki Dauda ce. “A gaishe ki, ke da ki ke mai-samun alheri, Ubangiji yana tare da ke,” in ji Jibra’ilu. (Luka 1:28) Sai tsoro ya kama Maryamu. Mece ce gaisuwar Jibra’ilu take nufi?

Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu cewa za ta haifi Almasihu

“Kada ki ji tsoro, Maryamu, gama kin sami tagomashi wurin Allah. Ga shi kuwa, za ki yi ciki, za ki haifi ɗa, za ki ba shi suna Yesu,” Jibra’ilu ya yi bayani. “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki kuma bisa gidan Yakubu har abada; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luka 1:30-33) Wannan labari ne mai ban al’ajabi! Maryamu za ta haifi Almasihu, “zuriya” da ake jira tuntuni!

A shekarar da ta biyo bayan hakan, an haifi Yesu a Bai’talami. A wannan daren, wani mala’ika ya sanar da makiyayan yankin: “Ga shi, na kawo maku bishara ta farinciki maigirma . . . gama yau cikin birnin Dauda an haifa maku Mai-ceto, shi ne Kristi Ubangiji.” (Luka 2:10, 11) Daga baya, iyalin Yesu suka ƙaura zuwa Nazarat, inda ya yi girma.

A shekara ta 29 A.Z., wato, a ainihin shekarar da ya kamata Almasihu ya bayyana, Yesu ya soma hidima a matsayin annabin Allah, “yana wajen shekara talatin.” (Luka 3:23) Mutane da yawa sun fahimci cewa Allah ne ya aiko shi. Sun ce: “Wani annabi mai-girma ya tashi daga cikinmu.” (Luka 7:16, 17) Amma mene ne Yesu ya koyar?

Yesu ya koya wa mutane su ƙaunaci Allah kuma su bauta masa: Ya ce: “Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne: kuma ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka.” (Markus 12:29, 30) Ya kuma ce: “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai za ka bauta wa.”—Luka 4:8.

Yesu ya ƙarfafa mutane su ƙaunaci juna: Ya ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Markus 12:31) Ya kuma ce: “Dukan abu . . . da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma: gama Attaurat ke nan da Annabawa.”—Matta 7:12.

Yesu ya gaya wa mutane game da Mulkin Allah da himma: Ya ce: “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Me ya sa Mulkin Allah yake da muhimmanci haka?

Nassosi sun koyar da cewa Mulkin Allah gwamnati ce da take sama da za ta yi sarauta bisa duniya. Yesu Almasihu, shi ne Sarkin da Allah ya naɗa. Annabi Daniyel ya annabta cewa Allah zai ba Almasihun “sarauta da daraja, da mulki” a sama. (Daniyel 7:14) Wannan Mulkin zai sa Aljanna ta tabbata a duniya gabaki ɗaya kuma zai ba bayin Allah rai na har abada. Wannan shi ne labari mafi daɗi, ko ba haka ba?