Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 10

An Fallasa Maƙiyin Imani

An Fallasa Maƙiyin Imani

TUN kafin Ya halicci duniya, Jehobah Allah ya halicci mala’iku a sama. Amma daga baya, sai wani mala’ika ya soma sha’awar bautar da ta cancanci Allah kaɗai. Ta wajen cika muradinsa, ya mai da kansa Shaiɗan, wanda ke nufin “Ɗan Hamayya,” wato, wanda ke hamayya da Allah. Ta yaya Shaiɗan ya yi hamayya da Allah?

Shaiɗan ya yi amfani da maciji ya ruɗi Hauwa’u

Ta wajen yin magana ta hanyar maciji, Shaiɗan ya yaudari Hauwa’u ta yi rashin biyayya ga Allah. Cikin dabara, ya ambata cewa Jehobah Allah yana hana ta wani abu mai kyau ne ta wajen hana ta ci daga wani itace. Da gabagaɗi ba kunya ya ƙira Allah maƙaryaci kuma ya ce Hauwa’u ta ƙi ja-gorancin Allah, yana cewa: “Gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” (Farawa 3:5) Saboda wawanci, Hauwa’u ta yarda da ƙaryan Shaiɗan. Ta ƙarya dokar Allah kuma ta rinjayi Adamu ya yi hakan. Tun daga lokacin, Shaiɗan ya ci gaba da zama abokin gāban masu cikakken imani. Kuma har yanzu bai daina yaudarar mutane ba. Ta yaya?

Gurɓataccen Imani ya Yaɗu

Shaiɗan ya yi amfani da bautar gumaka da kuma al’adun ’yan Adam wajen yaudarar mutane

Shaiɗan ya yi amfani da bautar gumaka da al’adun ’yan Adam don ya gurɓata imanin ’ya’yan Isra’ila. Yesu Almasihu, ya gaya wa malaman addini cewa domin suna koyar da “dokokin mutane,” bautarsu ta zama banza. (Matta 15:9) Sa’ad da wannan al’ummar ta ƙi Almasihu, Allah ya ƙi su. Yesu ya gaya musu: “Za a amshe mulkin Allah daga hannunku, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Matta 21:43) Sai mabiyan Yesu suka zama mutanen da Allah ya amince da su.

Bayan haka, Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya gurɓata imanin mabiyan Yesu. Ya yi nasara kuwa? Yesu ya annabta abin da zai faru da kwatanci na annabci. A cikin kwatancin, wani mutum ya shuka alkama mai kyau a gona. Daga baya, wani maƙiyi ya shuka zawan a tsakanin alkamar. An ƙyale shuke-shuke biyu su yi girma tare har lokacin girbi. Bayan girbin, an ware zawan daga alkamar kuma aka ƙona zawan. Sai aka tattara alkamar cikin rumbun mai ita.

Yesu ya bayyana abin da kwatancin ke nufi ga almajiransa. Shi da kansa ne Mai shukar. Ya ci gaba da cewa, “iri mai-kyau ’ya’yan mulki ke nan; zawan kuma ’ya’yan Mugun ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala’iku ne.” (Matta 13:38, 39) Yesu ya kamanta almajiransa na gaskiya da alkama. Amma Shaiɗan ya shuka almajiran ƙarya, kamar zawan a tsakanin mabiyan Yesu na gaskiya. Da haka, kamar yadda Yesu da kansa ya annabta, ƙarnuka bayan mutuwarsa, almajiran ƙarya suka bayyana. Hakan ya ɗaukaka koyarwan ’yan ridda, kamar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya. Almajiran ƙaryan suka soma bauta wa gumaka kuma suka yi katsalandan cikin siyasa. Mutane kaɗan ne kawai suka manne wa koyarwan Yesu.

An Kāre Cikakken Imani

Kamar yadda Yesu ya bayyana, za a samu canji daga baya. Mala’ikun Allah za su ware waɗanda ba su da cikakken imani don a halaka su. Bayan haka, masu cikakken imani ba za su yi wuyan ganewa ba. A ƙarshe, za a halaka Shaiɗan Iblis, wanda shi ne maƙiyi na ainihi na cikakken imani. Hakika, cikakken imani zai yi nasara!

Amma, ta yaya za ka iya gane mutanen da suke da cikakken imani a yau? Za mu tattauna amsar wannan tambayar a gaba.

Mala’ikun Allah suna neman mutanen da suke da muradin kasancewa da cikakken imani