Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 11

An Fallasa Makiyin Imani

An Fallasa Makiyin Imani

A YAU, mutane da yawa suna da’awar cewa suna da imani. Amma Yesu ya faɗi cewa mutane ƙalilan ne za su kasance da cikakken imani. Ya ce: “Hanya kuwa da fāɗi, wadda ta nufa wajen hallaka, mutane dayawa fa suna shiga ta wurinta. Gama ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.”—Matta 7:13, 14.

Ta yaya mutane a yau suke nuna cewa suna da cikakken imani? “Bisa ga ’ya’yansu za ku sansance su,” in ji Yesu. “Kowane itacen kirki ya kan fitarda ’ya’yan kirki; amma mumunan itace ya kan fitarda munanan ’ya’ya.” (Matta 7:16, 17) Saboda haka, cikakken imani yana yin “’ya’yan kirki.” Yana motsa mutane su nuna halayen da Allah ke so. Ta yaya suke yin hakan?

Ka Yi Amfani da Iko Yadda ya Kamata

Mutanen da suke da cikakken imani suna yin amfani da ikonsu da kuma matsayinsu don daraja Allah har kuma wasu su amfana. Yesu ya koyar da cewa: “Dukan wanda ya ke so shi zama babba a cikinku, bawanku za ya zama.” (Markus 10:43) Hakazalika, mutane masu cikakken imani ba sa zalunci a gida ko a waje. Suna daraja matansu, suna girmama su, kuma suna biyan bukatunsu cikin ƙauna. Nassosi sun ce: “Ku mazaje, ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.” (Kolosiyawa 3:19) “Mazaje, ku zauna da matayenku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi, da kuma masu-tarayyan gado na alherin rai: domin kada addu’o’inku su hanu.”—1 Bitrus 3:7.

A wani ɓangaren kuma, matar da take da cikakken imani za ta “ladabta wa mijinta.” (Afisawa 5:33, Littafi Mai Tsarki) Ya kamata mata su “yi ƙaunar mazajensu” kuma “su yi ƙaunar ’ya’yansu.” (Titus 2:4) Baba da mama da suke da cikakken imani suna kasancewa tare da ’ya’yansu sosai kuma suna koya musu dokokin Allah da ƙa’idodinsa. Suna daraja da kuma girmama kowa a gida, a wajen aiki, da kuma ko’ina. Suna bin shawarar Nassosi da ta ce: “Wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan’uwansa.”—Romawa 12:10, LMT.

Bayin Allah suna bin shawarar Nassosi da ta ce: ‘Kada ku karɓi rashawa.’ (Fitowa 23:8) Ba su taɓa yin amfani da matsayinsu don arzuta kansu ba. Maimakon haka, suna neman zarafi su taimaki wasu, musamman mabukata. Suna bin shawarar nan: “Kada ku manta da yin alheri da zumuntar tarayya: gama da irin waɗannan hadayu Allah yana jin daɗi.” (Ibraniyawa 13:16) Saboda haka, suna shaida gaskiyar kalmar Yesu: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayyukan Manzanni 20:35.

Ka Bi Mizanin Allah na Adalci

Mutane masu cikakken imani suna yin biyayya ga dokokin Allah, kuma “dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba” a garesu. (1 Yohanna 5:3) Sun san cewa “shari’a ta Ubangiji cikakkiya ce . . . Dokokin Ubangiji madaidaita ne, masu-faranta zuciya: umurnin Ubangiji tsatsarka ne, yana haskaka idanu.”—Zabura 19:7, 8.

Cikakken imani yana kuma motsa su su ƙi duk wani nau’in ƙiyayya. Ba sa ɗaukaka wata launin fata, ƙasa, ko matsayin mutane fiye da wani, maimakon haka, suna yin koyi da Allah. “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.”—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.

Cikakken imani yana motsa mutane su “yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibraniyawa 13:18) Mutumin da ke da cikakken imani yana kuma guje wa yin muguwar gulma da tsegumi. Game da irin mutumin da Allah ya amince da shi, mai zabura Dauda ya rubuta: “Shi wanda ba ya yin tsegumi da harshensa, ba ya yi wa abokinsa mugunta.”—Zabura 15:3.

Ka Nuna Hikima Irin ta Allah

Waɗanda suke da cikakken imani sun yi imani ne da Nassosi Masu Tsarki. Sun gaskata cewa “kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci.” (2 Timotawus 3:16) A dangantakarsu da wasu, suna nuna “hikima mai-fitowa daga bisa,” wadda ‘tsatsarka ce, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya.’ (Yaƙub 3:17) Suna yin watsi da al’adun da Allah ba ya so da kuma sihiri kuma suna “’tsare kan[su] daga gumaka.”—1 Yohanna 5:21.

Ka Nuna Ƙauna ta Gaske

Annabi Musa ya ce: “Za ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka.” (Kubawar Shari’a 6:5) Mutane masu cikakken imani suna nuna irin wannan ƙaunar ga Allah. Suna daraja sunan Allah, Jehobah. Suna ‘yin godiya ga Jehobah,’ suna kuma “kira bisa sunansa” cikin imani. (Zabura 105:1) Bayin Allah suna kuma yin biyayya ga umurninsa: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Leviticus 19:18) Suna ƙin mugunta kuma suna ƙoƙarin “zama lafiya da dukan mutane.” (Romawa 12:18) A alamance, sun “bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna.” (Ishaya 2:4) A sakamakon hakan, suna nuna “ƙauna ga junan[su]” kuma suna more ’yan’uwanci na dukan duniya. (Yohanna 13:35) Za ka iya gane waɗannan mutanen a yau kuwa?