SASHE NA 12
Ka Nuna Cewa Kana da Cikakken Imani!
ALLAH ya gargaɗi bayinsa su sa rai cewa za a gwada imaninsu. Kalmarsa ta ce: “Ku yi hankali shinfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bitrus 5:8) Ta yaya Shaiɗan zai yi ƙoƙarin ɓata imaninka?
Shaiɗan zai iya yin amfani da mutane, har da waɗanda kake ƙauna, su hana ka karanta Nassosi Masu Tsarki. Game da hakan, Yesu ya annabta: “Maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.” (Matta 10:36) Waɗanda kuke iyali ɗaya da abokanka wataƙila ba su san wannan gaskiya mai ban al’ajabi da ke cikin Kalmar Allah ba. Ko kuma suna iya jin tsoron abin da wasu suke cewa. Amma dai, Nassosi ya ce: “Tsoron mutum ya kan kawo tarko, amma wanda ya sa danganarsa ga Ubangiji za ya zauna lafiya.” (Misalai 29:25) Idan ka daina ɗaukan darasi daga Nassosi don ka faranta wa mutane rai, kana tunanin cewa hakan zai faranta ran Allah ne? Ko kaɗan! Amma, idan muka nuna cikakken imani, Allah zai taimake mu. “Amma mu ba mu cikin masu-noƙewa zuwa hallaka ba; amma cikin waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.”—Ibraniyawa 10:39.
Ka tuna labarin Dumas da aka ba da da farko. Da farko, matarsa ta yi masa ba’a don imaninsa. Amma daga baya ita ma ta soma koyan Kalmar Allah. Hakazalika, idan ka nace ga yin abin da ke da kyau, za ka iya rinjayar abokanka da ƙaunatattunka su soma yin nazari. A yanayi masu yawa, waɗanda ke cikin iyali da ba su yarda da abin da ake koyarwa ba ‘sun rinjayu ban da magana saboda . . . halaye masu-tsabta tare da tsoro’ na mutumin da ya nuna cikakken imani.—1 Bitrus 3:1, 2.
Shaiɗan har ila yana ƙoƙarin sa mutane su yi tunanin cewa ba su da zarafin yin nazarin Nassosi. Zai so matsi na rayuwa, wato, abubuwan da suka dame ka da damuwa game da kuɗi, su “shaƙe magana” a yanayinka, saboda imaninka ya “zama mara-amfani.” (Markus 4:19) Ka ƙi irin wannan tunanin marar hangen nesa! Nassosi ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Hakika, ci gaba da koyo game da Allah da kuma Yesu, Almasihu, yana da muhimmanci idan mutum yana so ya samu rai na har abada a Aljanna!
Ka yi tunanin Musa, wanda ɗan gidan sarauta ne a ƙasar Masar. Zai iya neman dukiya, suna, da kuma iko. Duk da haka, Musa ya zaɓi a ‘wulakanta shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin nishatsin zunubi domin ’yan kwanaki.’ Me ya sa? “Ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” (Ibraniyawa 11:24, 25, 27) Hakika, Musa yana da imani mai ƙarfi ga Allah. Ya sa yin nufin Allah a gaban biɗar abubuwan son kai, kuma Allah ya albarkace shi sosai. Idan kai ma ka yi hakan, Allah zai albarkace ka.
Shaiɗan zai so ya kama ka a hanyoyi dabam-dabam. Amma bai kamata ka faɗa hannunsa ba. Kalmar Allah ta ƙarfafa mu: “Ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.” (Yaƙub 4:7) Ta yaya za ka iya yin tsayayya da shi?
Ka ci gaba da yin nazarin Nassosi Masu Tsarki. Ka karanta Kalmar Allah a kullum. Ka yi nazarin abin da yake koyarwa. Ka yi amfani da shawararsa. Idan ka yi haka, za ka “ɗauki dukan makamai na Allah,” da za ka iya kāre hare-haren Shaiɗan.—Afisawa 6:13.
Ka yi tarayya da waɗanda suke da cikakken imani. Ka nemi mutanen da ke karanta Nassosi Masu Tsarki, waɗanda suke nazarinsa, kuma suke amfani da shi. Irin waɗannan mutanen suna ‘lura da juna domin su tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka, . . . Suna gargaɗad da juna.’ Za su taimaka maka ka kasance da cikakken imani.—Ibraniyawa 10:24, 25.
Ka kusaci Jehobah. Ka yi addu’a don samun taimakon Allah, kuma ka dogara a gare shi. Kada ka manta cewa, Allah yana so ya taimake ka. “Zuba dukan alhininku a bisansa [Allah], domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:6, 7) “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.”—1Korintiyawa 10:13.
Shaiɗan yana yi wa Allah ba’a, cewa babu wanda zai ci gaba da bauta Masa idan har mutumin zai fuskanci jarrabobi. Amma kana da zarafin tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne! Allah ya ce, “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” (Misalai 27:11) Hakika, ka ƙuduri aniyar nuna cewa kana da cikakken imani!