Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 5

Sanin Halayen Allah Masu Kyaun Gaske

Sanin Halayen Allah Masu Kyaun Gaske

NASSOSI Masu Tsarki sun bayyana halayen Allah masu ban mamaki, kuma hakan ya ba mu damar saninsa. Alal misali, Nassosi sun gaya mana game da halaye guda huɗu na musamman na Allah, wato, iko, adalci, hikima, da ƙauna. Bari mu bincika kowannensu.

Iko Marar Iyaka

Allah maɗaukaki ne cikin iko

Jehobah ya gaya wa Ibrahim: “Ni ne Allah Alƙadiru.” (Farawa 17:1) Ikonsa ba shi da na biyu, ba shi da iyaka, kuma ba ya ƙarewa. Allah ya halicci dukan sararin samaniya ta wajen yin amfani da ikonsa.

Allah bai taɓa wulakanta ikonsa ba. A koyaushe, yana amfani ne da ikonsa a hanyar da ta dace kuma da manufa. Yana daidaita yadda yake amfani da ikonsa da adalcinsa, hikimarsa, da ƙaunarsa.

Jehobah yana yin amfani da ikonsa sosai a madadin bayinsa masu aminci. “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Shin, ba ka sha’awar kusantar wannan Allah mai kula duk da ikonsa?

Allah Mai Adalci

“Ubangiji yana son shari’a [adalci NW].” (Zabura 37:28) A koyaushe yana yin abin da ke daidai bisa ga cikakken mizaninsa.

Allah ba ya nuna son kai

Allah ya tsane rashin adalci. “Ba ya tara, ba ya kuwa karɓan rishuwa.” (Kubawar Shari’a 10:17) Yana gāba da waɗanda suke zaluntar wasu, yana ɗaukan mataki a madadin marasa galihu, har da ‘kowace gwauruwa ko maraya.’ (Fitowa 22:22) Allah ba ya nuna wa ’yan Adam bambanci. “Allah ba mai tara ba ne; amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.”—Ayyukan manzanni 10:34, 35.

Adalcin Jehobah kamiltacce ne. Ba ya yawan ragwanta wa, kuma ba ya yawan tsananta wa. Yana yi wa masu zunubi da suka ƙi tuba horo amma yana yi wa waɗanda suka tuba jin ƙai. “Ubangiji cike da tausayi ya ke, mai-nasiha, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai kuma. Ba za shi tsautawa kullum ba; ba kuwa za shi nuƙura har abada ba. Ba ya aika mamu gwalgwadon zunubanmu ba, ba ya sāka mamu gwalgwadon laifofinmu ba.” (Zabura 103:8-10) Allah yana tunawa da ayyukan adalci na bayinsa masu aminci kuma yana saka musu. Ya kamata ka amince da Allah mai irin wannan adalcin, ko ba haka ba?

Allah Mai Hikima

Nassosi Masu Tsarki suna ɗauke da hikimar Allah

Jehobah ne Tushen dukan hikima. “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa!” (Romawa 11:33) Babu mai irin hikimarsa kuma hikimarsa ba ta da iyaka.

Hikimar Allah ta bayyana dalla-dalla a halitarsa na duniya. “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu!” in ji mai zabura. “Da hikima ka yi su duka.”—Zabura 104:24.

An kuma bayyana hikimar Allah a cikin Nassosi Masu Tsarki. Sarki Dauda ya rubuta: “Shari’a ta Ubangiji cikakkiya ce, tana sa mara-sani ya zama mai-hikima.” (Zabura 19:7) Ka ga, kana iya amfana daga hikima marar iyaka na Allah! Za ka yi amfani da wannan daman?

“Allah Ƙauna Ne”

Fitacce a cikin halayen Allah shi ne ƙauna. Nassosi sun gaya mana cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Ƙauna ce ke motsa shi a dukan abubuwan da yake yi kuma ita ce ke yi masa ja-gora.

Allah yana nuna mana ƙaunarsa a hanyoyi masu yawan gaske. Yana ba mu abubuwa masu kyau. “Yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farinciki.” (Ayyukan Manzanni 14:17) Hakika, “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke, tana sabkowa daga wurin Uban haskoki.” (Yaƙub 1:17) Ta hanyar Nassosi wanda kyauta ne mai girma da aka ba mu, Allah ya bayyana mana gaskiya game da kansa kuma ya koya mana dokokinsa da fa’idodinsa na ƙauna. “Maganarka ita ce gaskiya,” in ji Yesu a cikin addu’a.—Yohanna 17:17.

Hikimar Allah a halitta abin mamaki ne

Allah yana kuma taimaka mana sa’ad da muka fuskanci matsaloli. “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka: ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.” (Zabura 55:22) Yana gafarta zunubanmu. “Gama nagari ne kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa, mai-yawan jinƙai ga dukan waɗanda su ke kira gareka.” (Zabura 86:5) Kuma ya yi mana alkawarin rai na har abada. “Zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Mene ne za ka yi game da ƙaunar Allah? Kai ma za ka ƙaunace shi?

Ka Kusaci Allah

Yin addu’a da bimbini a kan halayen Allah zai sa ka kusace shi

Allah yana so ka san shi sosai. Kalmarsa ta ƙarfafa ka: ‘Ka kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ka.’ (Yaƙub 4:8) Allah ya kira annabi Ibrahim mai aminci “aminina.” (Ishaya 41:8) Jehobah yana so ka zama amininsa.

Yayin da kake ƙara koya game da Allah, hakan zai sa ka ƙara kusantarsa kuma farin cikinka ya ƙaru. “Mai-albarka ne mutum” wanda “marmarinsa cikin shari’a ta Ubangiji ya ke; kuma a cikin shari’arsa ya kan riƙa tunani dare da rana.” (Zabura 1:1, 2) Saboda haka, ka ci gaba da yin nazarin Nassosi Masu Tsarki. Ka yi bimbini a kan halayen Allah da ayyukansa. Ka nuna ƙaunarka ga Allah ta wajen yin amfani da abin da ka koya. “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo.” (1 Yohanna 5:3) Saboda haka, kamar mai zabura, ka yi addu’a: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka; ka koya mini hanyoyinka.” (Zabura 25:4, 5) Za ka ga cewa Allah “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.”—Ayyukan Manzanni 17:27.