Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 4

Wane ne Allah

Wane ne Allah

MUTANE suna bauta wa alloli masu yawa. Amma Nassosi Masu Tsarki sun koyar da cewa Allah na gaskiya guda ɗaya ne tak. Ba shi da makamanci, shi ne maɗaukaki, kuma madawwami. Shi ne ya halicci komi a sama da ƙasa, kuma ya ba mu rai. Saboda haka, shi kaɗai ne ya cancanci mu bauta ma wa.

An ba da Dokar ta hanyar annabi Musa ne a matsayin “maganan wanda aka faɗi ta bakin mala’iku”

Allah yana da suna. Kuma sunan shi ne JEHOBAH. Allah ya gaya wa Musa: “Hakanan za ka ce ma ’ya’yan Isra’ila, Yahweh, [“Jehobah” NW] Allah na ubanninku, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub, ya aike ni gareku: wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.” (Fitowa 3:15) Sunan nan Jehobah ya bayyana sau 7,000 a cikin Nassosi Masu Tsarki. Kamar yadda Zabura 83:18 ta ce game da Allah, ‘kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’

Rubutaccen nassi na Dead Sea Scroll na dā da ke ɗauke da sunan Allah

Babu ɗan Adam ɗin da ya taɓa ganin Allah. Allah ya gaya wa Musa: “Ba ka da iko ka ga fuskata: gama mutum ba shi ganina shi rayu.” (Fitowa 33:20) Allah yana zaune ne a sama kuma ’yan Adam ba za su iya ganinsa ba. Zunubi ne a ƙera ko kuma a yi addu’a ga gunki, hoto ko kuwa siffar Allah. Jehobah Allah ya ba da doka ta hanyar annabi Musa: “Ba za ka misalta wata ƙira, ko surar abin da ke cikin sama daga bisa, ko abin da ke cikin duniya daga ƙasa, ko kuwa abin da ke cikin ruwa daga ƙarƙashin ƙasa: ba za ka yi sujada garesu ba, ba kuwa za ka bauta musu ba: gama ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.” (Fitowa 20:2-5) Bayan haka, ta bakin annabi Ishaya, Allah ya ce: “Ni ne Ubangiji [“Jehobah” NW]; wannan ne sunana: ba ni kuwa bada ɗaukakata ga wani, yabona kuma ga sifofi sassaƙaƙu.”—Ishaya 42:8.

Wasu sun yi imani da Allah amma suna iya ɗaukansa a matsayin wanda ba za a iya sani ba balle a kusace shi, wanda za a ji tsoronsa maimakon a ƙaunace shi. Mene ne ra’ayinka? Allah ya damu da kai kuwa? Za ka iya saninsa kuwa da gaske, har ma ka kusace shi? Bari mu ga abin da Nassosi suka ce game da ainihin halayen Allah.