Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 14

Ku Zama Masu Gaskiya a Kowane Abu

Ku Zama Masu Gaskiya a Kowane Abu

“Kowa ya dinga faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya.”​—AFISAWA 4:25.

1, 2. Yaya Jehobah yake ji idan ya ga cewa muna iya ƙoƙarinmu don mu kasance da gaskiya?

WATA rana wani yaro yana dawowa daga makaranta, sai ya tsinci kuɗin wani mutum a ƙasa. Me zai yi da shi? Zai iya amfani da kuɗin, amma bai yi hakan ba. Ya mayar wa mai shi kuɗin. Da mahaifiyarsa ta ji abin da ya yi, ta yi farin ciki sosai.

2 Iyaye da yawa suna farin ciki idan yaransu suna faɗin gaskiya. Ubanmu Jehobah, “Allah na gaskiya” ne kuma yana farin ciki idan ya ga cewa muna faɗin gaskiya. (Zabura 31:​5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Mu ma muna so mu faranta masa rai kuma mu ‘dinga faɗin . . . gaskiya’ a kowane abu. (Afisawa 4:25) Bari mu tattauna hanyoyi guda huɗu da za su iya sa faɗin gaskiya ya mana wuya. Bayan haka, za mu tattauna albarkar da za mu samu idan muna faɗin gaskiya.

MU SAN KASAWARMU

3-5. (a) Me ya sa muke bukatar mu san kanmu sosai? (b) Mene ne zai taimaka mana mu san kanmu sosai kuma mu yi gyara?

3 Kafin mu iya zama masu faɗin gaskiya muna bukatar mu bincika kanmu don mu san ko mu masu gaskiya ne. Hakan zai iya kasance da wuya. A ƙarni na farko, ’yan’uwan da ke Lawudikiya sun ruɗi kansu cewa suna faranta ma Allah rai, amma hakan ba gaskiya ba ne. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:17) Mu ma za mu iya yaudarar kanmu game da halayen da muke da su.

4 Manzo Yaƙub ya ce: “Idan wani yana tsammani shi mai addini ne sosai, amma ba ya kame bakinsa, to, yana ruɗin kansa ne, addininsa kuma banza ne.” (Yaƙub 1:26) Za mu iya ruɗin kanmu cewa idan muna yin wasu abubuwa masu kyau, Allah zai amince da mu ko da muna rena mutane ko gaya musu baƙar magana ko kuma muna musu ƙarya. Mene ne zai taimaka mana mu guji ruɗin kanmu?

5 Idan muka kalli madubi, mukan ga yadda kamaninmu yake. Haka nan ma, in muka karanta Littafi Mai Tsarki, mukan ga irin halayen da muke da su. Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu san iyawarmu da kuma kasawarmu. Za mu koyi yadda za mu daidaita tunaninmu da ayyukanmu kuma mu san yadda za mu yi furucin da ya dace. (Karanta Yaƙub 1:​23-25.) Idan muna ganin cewa ba mu da wata matsala, ba za mu iya yin gyarar da muke bukata ba. Don haka, muna bukatar mu bincika kanmu ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki. (Makoki 3:40; Haggai 1:5) Yin addu’a zai taimaka mana mu san halayenmu. Za mu iya roƙan Jehobah ya bincika mu kuma ya taimaka mana mu ga inda muke bukatar gyara. (Zabura 139:​23, 24) Mu tuna cewa “Yahweh yana ƙyamar mai halin ruɗu, amma yana amincewa da mai gaskiya a zuci.”​—Karin Magana 3:32.

KU ZAMA MASU GASKIYA A IYALI

6. Me ya sa ma’aurata suke bukatar su zama masu gaskiya?

6 Yana da kyau a riƙa faɗin gaskiya a cikin iyali. Idan miji da mata suna gaya wa juna gaskiya, hakan zai sa su yarda da juna sosai. Akwai hanyoyi da yawa da ma’aurata za su iya zama marasa gaskiya. Alal misali, matar ko mijin zai iya zama mai son mata ko kallon batsa ko kuma ya soma soyayya da wata a ɓoye. Ka lura da abin da marubucin zabura ya ce: ‘Ba na sha’ani da [mayaudara], ba ruwana da munafukai.’ (Zabura 26:4) Idan ba gaskiya a tsakanin ma’aurata, hakan zai ɓata aurensu.

Ku guji duk wani abin da zai iya ɓata aurenku

7, 8. Ta yaya za ku yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ku koya wa yara muhimmancin faɗin gaskiya?

7 Yara ma suna bukatar su san cewa faɗin gaskiya yana da muhimmanci sosai. Iyaye za su iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su koya musu hakan. Akwai labaran mutanen da ba su yi gaskiya ba kamar Akan, wanda ya zama ɓarawo, da Gehazi wanda ya yi ƙarya don ya sami kuɗi, da kuma Yahuda Iskariyoti, wanda ya saci kuɗi kuma ya ci amanar Yesu a kan azurfa 30.​—Yoshuwa 6:​17-19; 7:​11-25; 2 Sarakuna 5:​14-16, 20-27; Matiyu 26:​14, 15; Yohanna 12:6.

8 Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan mutane da yawa masu gaskiya kamar Yakubu, wanda ya gaya wa yaransa su mayar da kuɗin da suka samu a buhunansu. Ban da shi, akwai Yefta da ’yarsa, waɗanda suka cika alkawarinsu ga Allah, da kuma Yesu, wanda ya faɗi gaskiya a mawuyacin yanayi. (Farawa 43:12; Alƙalai 11:​30-40; Yohanna 18:​3-11) Misalan nan za su taimaka wa yara su ga muhimmancin zama masu gaskiya.

9. Ta yaya iyaye suke taimaka wa yaransu idan suna faɗin gaskiya?

9 Iyaye za su iya koyan darasi daga wannan ƙa’idar Littafi Mai Tsarki: “Kai fa mai koya wa wani, ba ka koya wa kanka ba? kai da ka ke yin wa’azi kada a yi sata, kana yin sata?” (Romawa 2:​21, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Idan iyaye ba sa aikata abin da suke gaya wa yaransu, yaran suna ganin hakan. Idan muna gaya wa yaranmu su riƙa faɗin gaskiya amma mu ba ma faɗin gaskiya, hakan zai riƙitar da su. Idan yara suka ga cewa iyayensu suna ƙarya, su ma za su riƙa yin hakan. (Karanta Luka 16:10.) Amma idan yara suka ga cewa iyayensu suna faɗin gaskiya, hakan zai taimaka musu su ma su zama iyaye nagari a nan gaba.​—Karin Magana 22:6; Afisawa 6:4.

FAƊIN GASKIYA A CIKIN IKILISIYA

10. Ta yaya za mu riƙa gaya wa ’yan’uwanmu gaskiya?

10 Muna bukatar mu riƙa gaya wa ’yan’uwanmu gaskiya. Yana da sauƙi mu soma gulmar mutane ko kuma mu soma wasu maganganu don mu ɓata sunansu. Idan ba mu san gaskiya game da wani batu ba kuma muka soma yaɗawa, muna yaɗa ƙarya ke nan. Don haka, zai dace mu ‘kame bakinmu.’ (Karin Magana 10:19) Faɗin gaskiya ba ya nufin za mu riƙa faɗan dukan abin da muke zato ko muka gani ko kuma muka ji. Ko da abin da muke so mu faɗa gaskiya ne, wataƙila batun bai shafe mu ba ko kuma ba zai dace mu riƙa yaɗawa ba. (1 Tasalonikawa 4:11) Wasu sukan yi wa mutane baƙar magana kuma su ce: “Ai, gaskiya nake faɗa.” Amma mu bayin Jehobah muna furta kalaman da suka dace a kowane lokaci.​—Karanta Kolosiyawa 4:6.

11, 12. (a) Me ya sa bai kamata wanda ya yi zunubi mai tsanani ya ɓoye ko kuma ya yi ƙarya ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu? (c) Ta yaya za mu yi gaskiya a ƙungiyar Jehobah?

11 Jehobah ya ba wa dattawa hakkin kula da kuma taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya. Idan muka faɗi gaskiya, hakan zai iya sa dattawan su taimaka mana. Ta yaya? Alal misali, a ce ba ka da lafiya kuma ka je asibiti ganin likita. Shin za ka ɓoye wasu daga cikin abubuwan da suke damun ka? Idan ka yi hakan, likitan ba zai iya taimaka maka yadda ya kamata ba. Haka ma, idan muka yi zunubi mai tsanani, bai kamata mu ɓoye ko mu yi ƙarya ba. Mu je mu gaya wa dattawa kuma mu faɗi gaskiya game da lamarin. (Zabura 12:2; Ayyukan Manzanni 5:​1-11) Bari mu ba da wani misali kuma: A ce ka san cewa wani abokinka ya yi zunubi mai tsanani. (Maimaitawar Shari’a 13:8) Shin za ka ce: “Abokina ne don hakan zan rufa masa asiri”? Ko kuma za ka je wurin dattawa don ka san cewa za su iya taimaka masa ya gyara dangantakarsa da Jehobah?​—Ibraniyawa 13:17; Yaƙub 5:​14, 15.

12 Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa gaya wa ƙungiyarmu gaskiya a lokacin da muke ba da rahoto kamar rahotonmu na wa’azi. Mu zama masu gaskiya sa’ad da muke cika fam na hidimar majagaba ko kuma wata hidima dabam.​—Karanta Karin Magana 6:​16-19.

13. Ta yaya za mu zama masu gaskiya sa’ad da muke yin kasuwanci da ’yan’uwanmu?

13 Bai kamata ’yan’uwa su riƙa haɗa ibada da kasuwanci ba. Alal misali, kada mu yi kasuwanci sa’ad da muke Majami’ar Mulki ko kuma wa’azi. Kuma kada mu cuci ’yan’uwanmu da muke kasuwanci da su. Idan ka ɗauki ɗan’uwanka aiki, ka biya shi a kan lokaci kuma ka ba shi daidai kuɗin da kuka yarda a kai, tare da wasu abubuwan da doka ta bukace ka ka yi masa. (1 Timoti 5:18; Yaƙub 5:​1-4) Idan kana aiki a ƙarƙashin wani Mashaidi, kada ka ɗauka cewa zai bi da kai fiye da yadda yake bi da sauran ma’aikatan. (Afisawa 6:​5-8) Ka yi aiki na daidai lokacin da aka ba ka kuma ka yi hakan da dukan zuciyarka.​—2 Tasalonikawa 3:10.

14. Me ya kamata Kiristoci su yi kafin su soma wata sana’a tare?

14 Idan muka soma wata sana’a da wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa kuma fa? Wataƙila mun haɗa jari ko mun karɓi bashi don mu yi hakan. A irin wannan yanayin, bin wannan ƙa’idar Littafi Mai Tsarki zai taimaka: Ku rubuta yarjejeniyar da kuka yi. A lokacin da annabi Irmiya ya sayi wani fili, ya rubuta yarjejeniyar da suka yi guda biyu. Ya ajiye ɗaya don nan gaba, ɗaya kuma ya ba wa masu shaida su sa hannu. (Irmiya 32:​9-12; ka kuma duba Farawa 23:​16-20.) Wasu suna ganin cewa rubuta yarjejeniyar zai nuna kamar ba su yarda da ɗan’uwansu ba. Amma a gaskiya, yin hakan zai hana matsala tasowa a tsakaninsu. Sa’ad da kuke kasuwanci, ku tuna cewa zaman lafiya da ’yan’uwa a ikilisiya ya fi kowane irin kasuwanci muhimmanci.​—1 Korintiyawa 6:​1-8; ka duba Ƙarin Bayani na 30.

YIN GASKIYA A SHA’ANINMU NA YAU DA KULLUM

15. Yaya Jehobah yake ji game da cucin da ake yi a kasuwanci?

15 Ba ’yan’uwanmu Kiristoci ne kawai za mu riƙa faɗa musu gaskiya ba amma har da kowa da kowa. Jehobah yana so mu riƙa yin gaskiya. “Yahweh yana ƙyamar masu awo da mudun ƙarya, amma yana jin daɗin masu awo da mudun gaskiya.” (Karin Magana 11:1; 20:​10, 23) A zamanin dā, mutane suna amfani da mudun awo wajen saya da sayarwa. Amma wasu ’yan kasuwa suna cucin kwastomominsu. Suna karɓan kuɗi fiye da wanda ya kamata su karɓa ko kuma su ba wa kwastomominsu kayan da bai kai kuɗin da suka bayar ba. A yau ma, mutane suna cucin juna a kasuwanci. Kamar yadda Jehobah ya tsani cucin mutane a dā, har yanzu yana ƙin hakan.

16, 17. Waɗanne ayyukan rashin gaskiya ne muke bukatar mu guje wa?

16 Akwai wasu yanayi da yawa da za su iya sa mu yi ƙarya, kamar sa’ad da muke neman aiki, ko muke cika wani fam na gwamnati ko kuma sa’ad da muke rubuta jarrabawa a makaranta. Mutane da yawa suna ganin ba laifi ba ne mu yi ƙarya, ko mu ƙara gishiri a wani batu ko kuma mu ruɗi mutane. Hakan ba abin mamaki ba ne domin Littafi Mai Tsarki ya riga ya gaya mana cewa mutane a zamanin ƙarshe za su zama “masu sonkansu, masu son kuɗi, . . . masu ƙin nagarta.”​—2 Timoti 3:​1-5.

17 Ko da yake a wasu lokuta, za mu ga kamar masu cucin mutane ne suka fi yin nasara a rayuwa. (Zabura 73:​1-8) Za a iya koran Kirista daga wajen aikinsa don yana faɗin gaskiya ko a cuce shi ko kuma a riƙa masa wulakanci a wajen aiki. Duk da haka, albarkar da faɗin gaskiya yake kawowa ya fi duk wahalar da za mu sha. Ta yaya?

ALBARKAR FAƊIN GASKIYA

18. Me ya sa yin gaskiya yake da kyau sosai?

18 Yana da kyau sosai mutum ya kasance mai gaskiya, amma a duniyar nan yana da wuya a sami mutum mai gaskiya. Amma dukanmu za mu iya zama masu gaskiya. (Mika 7:2) Wasu mutane za su iya maka ba’a ko su kira ka wawa don kana faɗin gaskiya. Duk da haka, akwai mutanen da za su so ka don wannan halin kuma su amince da kai. Mutane a faɗin duniya sun san cewa Shaidun Jehobah masu gaskiya ne. Wasu mutane sun fi so su ba wa Shaidun Jehobah aiki don su masu gaskiya ne. A wasu lokuta, ana koran mutane daga aikinsu don ba sa yin gaskiya, amma ba a koran Shaidun Jehobah.

Za mu iya ɗaukaka Jehobah ta ayyukanmu

19. Yaya dangantakarka da Jehobah za ta kasance idan kana faɗin gaskiya?

19 Yin gaskiya a kowane abu zai sa ka kasance da kwanciyar hankali kuma zuciyarka ba za ta riƙa damunka ba. Za mu iya zama kamar Bulus wanda ya ce: “Mun tabbata cewa tunanin zuciyarmu ba ta damunmu game da wani laifi.” (Ibraniyawa 13:18) Mafi muhimmanci ma, Jehobah Ubanmu mai ƙauna yana ganin ƙoƙarin da kake yi don ka zama mai gaskiya kuma zai yi maka albarka.​—Karanta Zabura 15:​1, 2; Karin Magana 22:1.