Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 10

Aure Kyauta Ne Daga Allah

Aure Kyauta Ne Daga Allah

‘Igiya ɗaya . . . da aka saƙa da igiyoyi uku tana da wuya a tsinke ta da sauri.’​—MAI-WA’AZI 4:12.

1, 2. (a) Wane fata ne sabbin ma’aurata sukan yi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan babin?

IDAN ka je bikin aure, za ka ga amarya da ango suna cike da farin ciki kuma suna fatan cewa za su zauna lafiya da juna. Ƙari ga haka, suna sa rai cewa za su zauna tare har iya rayuwarsu.

2 Ma’aurata da yawa sun fara da kyau, amma daga baya kome ya lalace. Idan ma’aurata suna so su ji daɗin aurensu, dole ne su bi dokokin Allah. Bari mu tattauna yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyin nan: Wace albarka ce aure yake kawowa? Ta yaya za ka zaɓi mace ko mijin kirki? Ta yaya za ki zama mace ko mijin kirki? Kuma me zai sa ma’aurata su ji daɗin aurensu?​—Karanta Karin Magana 3:​5, 6.

IN YI AURE NE KO KAR IN YI?

3. Kana ganin sai mutum ya yi aure kafin ya yi farin ciki ne? Ka bayyana.

3 Wasu sun ce sai mutum ya yi aure kafin ya san yadda rayuwa take da daɗi. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Yesu ya nuna cewa mutum zai iya yin farin ciki ko bai yi aure ba. (Matiyu 19:​11, 12) Manzo Bulus ma ya faɗi albarkar da marasa aure suke samuwa. (1 Korintiyawa 7:​32-38) Kowane mutum yana da ’yancin zaɓa ko zai yi aure ko ba zai yi ba. Saboda haka, kada ka yarda abokanka ko ’yan’uwanka ko kuma al’adarku su matsa maka ka yi aure.

4. Waɗanne albarka ne aure mai kyau yake kawowa?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce aure kyauta ne daga Allah kuma yana kawo albarka. Ga abin da Jehobah ya faɗa game da mutum na farko, wato Adamu: ‘Bai yi kyau mutumin ya kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakiya wadda ta dace da shi.’ (Farawa 2:18) Jehobah ya halicci Hauwa’u domin ta zama matar Adamu kuma su ne suka zama iyali na farko. Idan ma’aurata suna da yara, su tabbata cewa sun yi shiri mai kyau don su iya renon yaran. Amma haifan yara ba shi ne kawai dalilin yin aure ba.​—Zabura 127:3; Afisawa 6:​1-4.

5, 6. Me zai sa aure ya zama kamar ‘igiya ɗaya wadda an saƙa da igiyoyi uku’?

5 Sarki Sulemanu ya rubuta cewa: ‘Gwamma mutum biyu da mutum ɗaya, gama amfanin aikin mutane biyu ya fi na mutum ɗaya. Gama idan ɗaya ya fāɗi, ɗaya zai taimaka ya ɗaga ɗayan. Amma kaiton wanda yana nan shi kaɗai, in ya fāɗi ba wanda zai taimaka ya ɗaga shi. . . . Igiya ɗaya wadda an saƙa da igiyoyi uku tana da wuya a tsinke ta da sauri.’​—Mai-Wa’azi 4:​9-12.

6 Aure mai kyau yana sa mata da miji su kasance da zumunci, su taimaka ma juna da ƙarfafa juna da kuma kāre juna. Ƙauna takan kyautata zaman aure, amma aure zai fi kyau idan mata da miji suna bauta wa Jehobah. Aurensu zai zama kamar ‘igiya ɗaya wadda an saƙa da igiyoyi uku.’ Irin wannan igiyar tana da ƙarfi fiye da wadda aka saƙa da igiyoyi biyu. Idan an yi aure daidai da nufin Jehobah, auren zai yi kyau da kuma daɗi.

7, 8. Wace shawara ce Bulus ya bayar game da aure?

7 Bayan mata da miji sun yi aure, za su iya jin daɗin yin jima’i da juna. (Karin Magana 5:18) Amma idan mutum yana so ya yi aure saboda sha’awar yin jima’i kawai, zai yi masa wuya ya zaɓi mata ko mijin kirki. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce kafin mutum ya yi aure, ya jira har sai ya wuce lokacin da sha’awar jima’i take da ƙarfi sosai. Ya dace mutum ya ɗan dakata har sai lokacin da sha’awar ta ɗan ragu. Hakan zai sa shi ya yi tunani da kyau kuma ya yi zaɓin da ya dace.​—1 Korintiyawa 7:9; Yaƙub 1:15.

8 Idan kana shirin yin aure, zai dace ka kasance da sanin-ya-kamata. Wato, ka san cewa a kowane aure akwai matsaloli. Manzo Bulus ya ce “waɗanda suka yi aure za su sha wahala a rayuwar nan.” (1 Korintiyawa 7:28) Za ka ɗan fuskanci matsaloli ko da ka yi zaɓi mai kyau. Saboda haka, idan kana so ka yi aure, ka yi ƙoƙari ka yi zaɓi mai kyau.

WA ZAN AURA?

9, 10. Me zai faru idan muka auri wanda ba ya bauta ma Jehobah?

9 Ga wata ƙa’idar Littafi Mai Tsarki da ya kamata mu tuna idan muna neman aure: “Kada ku haɗa kai da mutanen da ba sa bin Ubangiji.” (2 Korintiyawa 6:14) Za mu iya kwatanta hakan da dabbobin da ake noma da su. Manomi ba zai haɗa shanu da jaki su ja kunya tare ba domin idan ya yi hakan, duka dabbobin za su sha wahala. Haka ma, idan wanda yake bauta wa Jehobah ya auri wadda ba ta bauta ma Jehobah, za su yi ta fama da matsaloli. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu, mu auri “mai bin Ubangiji” kaɗai.​—1 Korintiyawa 7:39.

10 Wasu Kiristoci sukan ce gwamma su auri wanda ba ya bauta wa Jehobah da su kasance marasa aure. Amma ƙin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yakan jawo baƙin ciki. A matsayinmu na bayin Jehobah, bauta masa ne abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Shin za ka yi farin ciki idan kai da matarka ko ke da mijinki ba ku bauta wa Jehobah tare? Kiristoci da yawa sun gwammace kada su yi aure da su auri wanda ba ya bauta wa Jehobah.​—Karanta Zabura 32:8.

11. Ta yaya za ka zaɓi mata ko mijin kirki?

11 Hakan ba ya nufin cewa duk wanda yake bauta wa Jehobah zai zama mata ko mijin kirki. Idan kana da niyyar yin aure, ka nemi wadda kake so sosai da kuka fahimci juna da kyau. Ka yi haƙuri har sai ka sami wadda kuke da manufa ɗaya kuma tana sa bautar Jehobah farko a rayuwarta. Ka kuma bincika littattafan da bawan nan mai aminci ya wallafa don ka ga shawarwarin da za su taimaka maka.​—Karanta Zabura 119:105.

12. Me muka koya daga yadda Ibrahim ya nema ma yaronsa mata?

12 A wasu al’adu, iyaye ne suke zaɓa ma yaransu wadda za su aura. Domin a ganinsu, iyaye ne suka san wadda za ta dace da yaronsu. Ko a cikin Littafi Mai Tsarki ma akwai misalan hakan. Idan iyalinka suna bin irin wannan al’adar, Littafi Mai Tsarki zai taimaka musu su san irin halaye masu kyau da za su duba. Alal misali, sa’ad da Ibrahim yake zaɓa wa yaronsa Ishaku mata, bai mai da hankali ga ’yar masu kuɗi ba, amma ya mai da hankali ga wadda take ƙaunar Jehobah.​—Farawa 24:​3, 67; ka duba Ƙarin Bayani na 25.

TA YAYA ZAN YI SHIRI KAFIN IN YI AURE?

13-15. (a) Wane shiri ne mutum zai yi don ya zama mijin kirki? (b) Wane shiri ne mace za ta yi don ta zama matar kirki?

13 Idan kana so ka yi aure, ka tabbata cewa ka shirya. Za ka iya ɗauka cewa a shirye kake, amma bari mu tattauna abin da yin shiri kafin aure ya ƙunsa. Amsar za ta iya ba ka mamaki.

Ka ɗau lokaci ka yi tunani a kan shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da aure

14 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya ba mata da miji hakki dabam-dabam a iyali. Hakan yana nufin cewa yadda namiji zai shirya aure zai bambanta da shirin da mace za ta yi. Idan namiji yana so ya yi aure, ya kamata ya tambayi kansa ko a shirye yake ya zama maigida. Jehobah yana so maigida ya riƙa biyan bukatun matarsa da yaransa ya kuma kula da su. Ƙari ga haka, maigidan ne zai riƙa ja-gorar yadda iyalinsa take bauta wa Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce wanda ba ya kula da iyalinsa ya fi “marar ba da gaskiya muni.” (1 Timoti 5:8) Idan kana shirin yin aure, ka yi tunani a kan yadda za ka bi ƙa’idar nan da ta ce: “Ka shirya aikin waje tukuna, ka gyara gonakinka, daga baya kuma ka gina gidanka.” Wato kafin ka yi aure, ka tabbata cewa za ka iya kula da iyalinka yadda Jehobah yake so.​—Karin Magana 24:27.

15 Idan kuma mace tana so ta yi aure, ta tambayi kanta ko za ta iya cika hakkin da Jehobah ya ba wa matan aure ko mahaifiya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana hanyoyin da macen kirki take kula da mijinta da kuma yaranta. (Karin Magana 31:​10-31) A yau, mutane sun fi mai da hankali kawai a kan abin da matansu ko kuma mazajensu za su yi musu. Amma Jehobah yana so mata da miji su yi tunani a kan abin da za su yi wa juna.

16, 17. Idan kana so ka yi aure, me ya kamata ka yi tunani a kai?

16 Kafin ka yi aure, ka yi tunani a kan hakkin da Jehobah ya ba wa mata da miji. Kasancewa kan iyali ba ya nufin cewa mijin zai riƙa cin zalin matarsa. Mijin kirki yana bin halin Yesu. Yesu yana ƙaunar waɗanda suke ƙarƙashinsa da kuma yi musu kirki. (Afisawa 5:23) Macen kuma ya kamata ta yi tunani a kan yadda za ta riƙa goyon bayan shawarar da maigidanta ya yanke. (Romawa 7:2) Ya kamata ta tambayi kanta ko za ta yi farin ciki idan ta miƙa kanta ga maigidanta wanda shi ma ajizi ne. Idan ta ga cewa ba za ta iya ba, za ta iya yanke shawarar kasancewa marar aure.

17 Ya kamata ma’aurata su fi mai da hankali ga yadda za su faranta ma juna rai. (Karanta Filibiyawa 2:4.) Manzo Bulus ya ce: “Kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta girmama mijinta.” (Afisawa 5:​21-33) Ya kamata mata da miji su ƙaunaci juna su kuma daraja juna. Amma don su ji daɗin aurensu, ya kamata macen ta riƙa daraja mijinta, mijin kuma ya riƙa nuna ma matarsa cewa yana ƙaunarta.

18. Me ya sa ya kamata namiji da ta mace da suke soyayya su yi hankali?

18 Lokacin da saurayi da budurwa suke soyayya, lokacin farin ciki ne kuma su yi ƙoƙari su fahimci juna da kyau. A wannan lokacin, ya kamata su gaya wa juna gaskiya don su san ko za su dace da juna. Ya kamata saurayi da budurwa su yi amfani da wannan lokacin don su tattauna da kyau kuma su san abin da ke zuciyar junansu. Yayin da suka ci gaba da kasancewa tare, soyayyarsu za ta ci gaba da yin ƙarfi. Amma ya kamata su yi hankali da yadda suke nuna wa juna ƙauna domin kada su yi wani abin da bai dace ba. Ƙauna ta gaskiya za ta sa su kasance da kamun kai kuma za ta sa kada su yi abin da zai ɓata dangantakarsu da juna da kuma dangantakarsu da Jehobah.​—1 Tasalonikawa 4:6.

A lokacin da saurayi da budurwa suke soyayya, za su iya koyan yadda za su riƙa tattaunawa da juna

TA YAYA ZAN ZAUNA LAFIYA DA MATATA KO MIJINA?

19, 20. Ta yaya Kiristoci suke ɗaukan aure?

19 Yawancin littattafai da fina-finai sukan kammala da bikin aure mai daɗi. Amma a gaskiya, bikin aure soma taɓi ne kawai. Jehobah yana so ma’aurata su zauna tare har iya rayuwarsu.​—Farawa 2:24.

20 A yau, mutane ba sa ɗaukan aure da muhimmanci sosai, suna ɗaukansa kamar zumunci na ɗan lokaci ne kawai. Yin aure da kashe aure abu mai sauki ne a wurin su. Wasu suna ganin idan matsala ta taso, abin da za su yi shi ne su kashe auren. Amma ka tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya kwatanta aure da igiyar da aka saƙa ta da igiyoyi guda uku. Irin wannan igiyar ba za ta tsinke da wuri ba ko da an matsa mata. Idan muka roƙi Jehobah ya taimaka mana, aurenmu ba zai mutu ba. Yesu ya ce: “Abin da Allah ya haɗa, kada wani ya raba.”​—Matiyu 19:6.

21. Me zai sa ma’aurata su ƙaunaci juna?

21 Kowannenmu yana da iyawa da kuma kasawa. Yana da sauƙi mu mai da hankali ga kasawar mutane musamman ta matarmu ko kuma na mijinmu. Amma yin hakan zai sa mu riƙa baƙin ciki. Ma’aurata za su yi farin ciki idan suka mai da hankali ga halaye masu kyau na junansu. Ya kuma dace su riƙa tuna cewa dukansu ajizai ne. Me ya sa hakan yake da kyau? Domin Jehobah ma ya san cewa mu ajizai ne, amma ya fi mai da hankali ga halayenmu masu kyau. Me kake ganin zai faru idan Jehobah bai san cewa mu ajizai ba ne? Mai zabura ya ce: “Ya Ubangiji, idan kana lissafa laifofi, wa zai tsaya?” (Zabura 130:3) Ya kamata mata da miji su koyi darasi daga wurin Jehobah ta mai da hankali ga halayen juna masu kyau kuma su riƙa saurin gafarta wa juna.​—Karanta Kolosiyawa 3:13.

22, 23. Wane misali mai kyau ne ma’aurata za su iya koya daga wurin Ibrahim da matarsa Saratu?

22 Da shigewar lokaci, aure zai ci gaba da yin ƙarfi. Ibrahim da Saratu sun zauna lafiya tare har iya rayuwarsu. Da alama Saratu ta kai shekara 60 a lokacin da Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa su fita daga inda suke, wato birnin Ur. Babu shakka, bai yi mata sauƙi ta bar inda ta saba kuma ta koma zama a tanti ba. Amma Saratu tana ƙaunar mijinta kuma tana daraja shi. Saboda haka, ta amince da shawarar da mijinta ya yanke kuma ta taimaka masa ya yi nasara.​—Farawa 18:12; 1 Bitrus 3:6.

23 Hakika, ba a kullum ba ne mata da mijin kirki suke yarda da abin da ɗayansu ya faɗa ba. Akwai lokacin da Ibrahim ya ƙi yarda da abin da matarsa Saratu ta faɗa, amma Jehobah ya ce masa: “Ka saurari Saratu.” Ibrahim ya saurare ta kuma hakan ya kawo albarka. (Farawa 21:​9-13) Saboda haka, idan matarka ba ta yarda da shawararka a wasu lokuta ba ko mijinki bai yarda da shawararki ba, kada ku yi sanyin gwiwa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ku ci gaba da ƙauna da kuma daraja juna.

Ku bar Kalmar Allah ta riƙa muku ja-goranci a aurenku

24. Ta yaya aurenmu zai ɗaukaka Jehobah?

24 Akwai dubban ma’aurata a cikin ikilisiyar Kirista da suke jin daɗin aurensu. Idan kana so ka yi aure, ka tuna cewa zaɓan wadda za ka aura shi ne ɗaya daga cikin zaɓi mafi muhimmanci da za ka yi. Zaɓin zai shafe ka har iya rayuwarka. Shi ya sa ya kamata ka nemi ja-gorancin Jehobah. Shi zai taimaka maka ka yi zaɓin da ya dace, ka shirya auren da kyau kuma ka yi ƙoƙari don ku zauna lafiya da matarka kuma aurenku ya ɗaukaka sunan Jehobah.