Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 8

Jehobah Yana So Bayinsa Su Kasance da Tsabta

Jehobah Yana So Bayinsa Su Kasance da Tsabta

‘Ga mai tsabta, kakan nuna kanka mai tsabta.’​—ZABURA 18:26.

1-3. (a) Me ya sa uwa take tabbata cewa yaronta yana da tsabta? (b) Me ya sa Jehobah yake so bayinsa su kasance da tsabta?

IDAN uwa tana shirya yaronta zuwa makaranta, za ta masa wanka ta kuma saka masa kaya masu kyau da tsabta. Hakan zai sa yaron ya kasance da ƙoshin lafiya kuma mutane za su ga cewa iyayensa suna kula da shi.

2 Ubanmu Jehobah yana so mu kasance da tsabta. (Zabura 18:26) Ya san cewa idan muka kasance da tsabta, za mu amfana. Kuma idan muna da tsabta, za a girmama shi.​—Ezekiyel 36:22; karanta 1 Bitrus 2:12.

3 Me kasancewa da tsabta yake nufi? Ta yaya muke amfana idan muka kasance da tsabta? Yayin da muke tattauna waɗannan tambayoyin, za mu gane wasu canje-canjen da ya kamata mu yi.

ME YA SA MUKE BUKATAR MU ZAMA MASU TSABTA?

4, 5. (a) Me ya sa muke bukatar mu kasance da tsabta? (b) Me muka koya daga halittu a kan yadda Jehobah yake ɗaukan tsabta?

4 Jehobah mai tsabta ne ko kuma tsarki. (Littafin Firistoci 11:​44, 45) Saboda haka, dalilin da ya sa muke bukatar mu kasance da tsarki ko tsabta shi ne muna so mu bi ‘misalin’ Allah.​—Afisawa 5:1.

5 Halittu suna koya mana ra’ayin Jehobah game da tsabta ko tsarki. Jehobah ya yi wani tsari na tsabtace ruwa da iska. Akwai hanyoyi da yawa da duniya take tsabtace kanta idan an ɓatar da ita. (Irmiya 10:12) Alal misali, Jehobah ya yi ƙananan halittu da ba a iya ganin su sai da madubin ƙara girma. Waɗannan ƙananan halittun suna tsabtace abubuwan da suke da illa. Wannan tsarin yana da kyau sosai. ’Yan kimiyya suna yin amfani da ƙananan halittun nan wajen tsabtacce ruwa da iska idan aka ɓatar da su.​—Romawa 1:20.

6, 7. Ta yaya Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta nuna cewa dole ne bayin Jehobah su zama da tsabta?

6 Ban da haka ma, mun fahimci muhimmancin kasancewa da tsabta daga Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa. Alal misali, idan suna so Jehobah ya amince da ibadarsu, dole ne su kasance da tsabta. An gaya wa babban firist ya yi wanka sau biyu a Ranar Yin Gafara. (Littafin Firistoci 16:​4, 23, 24) Kuma kafin sauran firistocin su ba da hadayu, dole ne su wanke hannayensu da kuma ƙafafunsu. (Fitowa 30:​17-21; 2 Tarihi 4:6) A wasu yanayi, ana iya kashe wanda ya ƙi bin dokokin nan.​—Littafin Firistoci 15:31; Littafin Ƙidaya 19:​17-20.

7 Mu kuma fa? Za mu iya gane ƙa’idodin Jehobah daga wannan Dokar. (Malakai 3:6) Dokar ta nuna mana dalla-dalla cewa ya kamata bayin Jehobah su kasance da tsabta. Ƙa’idodin Jehobah ba su canja ba. Har ila, yana so bayinsa su kasance da tsabta ko kuma tsarki.​—Yaƙub 1:27.

ME ZAMA DA TSABTA YAKE NUFI?

8. A waɗanne hanyoyi ne za mu kasance da tsabta?

8 Ra’ayin Jehobah game da tsabta ya wuce yin wanka da wanke tufafi da kuma tsabtace gidajenmu kawai. Hakan ya ƙunshi kasancewa da tsabta a rayuwarmu gabaki ɗaya, wato a ibadarmu da halinmu da kuma tunaninmu. Babu shakka, idan muna so mu kasance da tsabta a gaban Jehobah, dole ne mu kasance da tsabta a kowane fannin rayuwarmu.

9, 10. Ta yaya za mu kasance da tsarki a ibadarmu?

9 Ibada mai tsarki. Bai kamata wani abu ya haɗa mu da addinin ƙarya ba. A lokacin da Isra’ilawa suke bauta a Babila, suna zama da mutanen da suke bauta wa allolin ƙarya. Shi ya sa Ishaya ya yi annabci cewa Isra’ilawa za su koma ƙasarsu don su soma ibada ta gaskiya. Jehobah ya gaya musu cewa: “Ku bar Babila! Kada ku taɓa wani abin ƙyama! Ku fita daga birnin, ku tsabtace kanku.” Bai kamata su haɗa ibadarsu da koyarwa ko halaye ko kuma al’adun addinin ƙarya na Babila ba.​—Ishaya 52:11.

10 Kiristoci na gaskiya ma a yau suna ƙin addinin ƙarya. (Karanta 1 Korintiyawa 10:21.) Al’adu da koyarwa da yawa na mutane a faɗin duniya sun samo asali ne daga addinan ƙarya. Alal misali, mutane da yawa sun gaskata cewa idan mutum ya mutu, akwai wani abu da yake fita daga jikinsa ya ci gaba da rayuwa. Kuma al’adu da yawa suna da alaƙa da wannan koyarwar. (Mai-Wa’azi 9:​5, 6, 10) Amma ya kamata Kiristoci su guji irin al’adun nan. Iyalanmu za su iya matsa mana mu bi irin waɗannan al’adun. Amma da yake muna so mu kasance da tsabta a gaban Jehobah, ba za mu amince da hakan ba.​—Ayyukan Manzanni 5:29.

11. Ta yaya za mu kasance da tsabta a halinmu?

11 Hali mai kyau. Idan muna so mu kasance da tsabta a gaban Jehobah, dole ne mu guji kowane irin halin lalata. (Karanta Afisawa 5:5.) Jehobah ya gaya mana a Littafi Mai Tsarki cewa mu “guje wa halin lalata.” Kuma ya bayyana mana dalla-dalla cewa masu lalata da suka ƙi tuba ba za su “shiga mulkin Allah” ba.​—1 Korintiyawa 6:​9, 10, 18, ka duba Ƙarin Bayani na 22.

12, 13. Me ya sa muke so mu kasance da tsabta a tunaninmu?

12 Tunani mai kyau. Mukan aikata abin da muke tunaninsa. (Matiyu 5:28; 15:​18, 19) Idan muna tunanin abubuwa masu kyau, za mu riƙa yin abin da ya dace. Da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta mukan yi tunanin da bai dace ba. Kuma idan hakan ya faru, zai dace mu daina nan da nan. Me ya sa? Domin idan ba mu yi hakan ba, za mu daina yin tunanin abubuwa masu kyau. Kuma za mu iya soma yin abubuwa marar kyau da muke tunaninsu. Amma a maimakon mu riƙa yin hakan, zai dace mu riƙa yin tunani a kan abubuwa masu kyau. (Karanta Filibiyawa 4:8.) Don haka, zai dace mu guji nishaɗin da ake lalata ko faɗa. Abin da zai taimaka mana shi ne mu mai da hankali sa’ad da muke zaɓan abubuwan da za mu karanta ko kalla ko kuma mu yi hira a kai.​—Zabura 19:​8, 9.

13 Dole ne mu zama masu tsabta a ibadarmu da halinmu da kuma tunaninmu idan muna so mu ci gaba da ƙaunar Allah. Ban da haka, Jehobah yana so mu kasance da tsabta a jikinmu ma.

TA YAYA ZA MU KASANCE DA TSABTA A JIKI?

14. Me ya sa kasancewa da tsabta a jiki yake da muhimmanci?

14 Idan muka tsabtace jikinmu da gidajenmu, za mu amfana kuma mutanen da muke zama tare da su ma, za su amfana. Za mu ji daɗi kuma mutane za su so tarayya da mu. Amma akwai babban dalilin da ya sa ya kamata mu kasance da tsabta a jiki. Idan muka kasance da tsabta, hakan yana girmama Jehobah. Ka yi la’akari da wannan misalin: Idan ka ga yaro mai datti, za ka iya cewa iyayensa ma marasa tsabta ne. Haka nan ma, idan ba mu kasance da tsabta ba, mutane ba za su girmama Jehobah ba. Manzo Bulus ya ce: ‘Kada mu zama dalilin tuntuɓe ga kowa, domin kada a sami dalili a zargi hidimarmu. A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi domin mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne.’​—2 Korintiyawa 6:​3, 4.

Mu bayin Jehobah muna so mu riƙa tsabtace kanmu da kuma mahallinmu

15, 16. Me za mu yi don mu kasance da tsabta?

15 Jikinmu da tufafinmu. Ya kamata mu riƙa tsabtace jikinmu a kullum. Alal misali, zai dace mu riƙa wanka kowace rana idan zai yiwu. Zai dace mu wanke hannayenmu da sabulu kafin mu dafa abinci ko bayan mun fito daga gidan wanka ko wurin ba-haya. Ban da haka ma, zai dace mu wanke hannayenmu bayan mun taɓa wani abu mai datti. Muna iya ɗauka cewa wanke hannu bai da wani muhimmanci, amma idan ba ma so mu yaɗa cuta ko ƙwayoyin cuta, zai dace mu riƙa wanke hannayenmu. Ƙari ga haka, wanke hannu zai iya kāre rayukan mutane. Idan ba mu da wurin ba-haya, za mu iya amfani da wasu hanyoyi dabam. Isra’ilawa a zamanin dā ba su da wurin ba-haya, don haka, sukan binne bayan gida da suka yi a ƙasa. Kuma wurin da suke binne bayan gidan yana da nisa da gidajensu da kuma ruwan da suke sha.​—Maimaitawar Shari’a 23:​12, 13.

16 Ba sai tufafi masu tsada ko kuma waɗanda ake yayin su ne za mu riƙa sakawa ba. Amma abin da ake so shi ne su kasance da tsabta da kuma daraja. (Karanta 1 Timoti 2:​9, 10.) A kullum muna so tufafin da muke sakawa su sa a girmama Jehobah.​—Titus 2:10.

17. Me ya sa muke bukatar mu tsabtace gidajenmu da kewayenmu?

17 Gidajenmu da mahallinmu. Ya kamata gidajenmu su zama da tsabta ko da yaya yanayin gidanmu yake. Kuma ya kamata mu tabbata cewa motocinmu ko baburanmu ko kekunanmu da dai sauransu su kasance da tsabta, musamman ma idan muna zuwa taro ko wa’azi da su. Me ya sa? Domin idan muka je wa’azi, muna gaya wa mutane game da yadda aljanna a duniya za ta kasance da tsabta. (Luka 23:43; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18) Yadda muke tsabtace gidajenmu da kewayenmu zai nuna cewa muna shirin yin rayuwa a sabuwar duniya mai tsabta da aka yi mana alkawarinta.

18. Me ya sa muke so wurin da muke ibada ya kasance da tsabta?

18 Wurin da muke ibada. Muna nuna cewa mun san muhimmancin tsabta idan muna tsabtacce wuraren da muke yin taro, wato Majami’ar Mulki ko wuraren da muke manyan taro. Idan baƙi suka zo Majami’ar Mulki, sukan ce wurin yana da tsabta sosai. Hakan yana ɗaukaka Jehobah. Dukan ’yan’uwa a ikilisiya suna da hakkin tsabtacce Majami’ar Mulki kuma su kula da ita.​—2 Tarihi 34:10.

YADDA ZA MU DAINA HALAYEN BANZA

19. Waɗanne halaye ne muke bukata mu guje musu?

19 Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana jerin halayen banza da ya kamata mu guje musu ba, amma ya nuna mana ƙa’idodin da za su taimaka mana mu fahimci ra’ayin Jehobah game da halayen. Ba ya so mu sha taba ko mugayen ƙwayoyi ko kuma mu bugu da giya. Idan muna so mu zama aminan Allah, dole ne mu guji waɗannan abubuwan. Me ya sa? Domin muna daraja ran da Allah ya ba mu kyauta. Irin waɗannan halayen suna iya gajartar da rayuwarmu ko su sa mu rashin lafiya ko kuma su cutar da mutanen da muke zama da su. Mutane da yawa sun yi ƙoƙarin daina irin waɗannan halayen don suna so su kasance da ƙoshin lafiya. Amma, mu aminan Jehobah, muna ƙaunar sa shi ya sa muke ƙin waɗannan halayen. Wata mata ta ce: “Da taimakon Jehobah, na iya gyara rayuwata kuma na daina shaye-shayen da nake yi. . . . Na san cewa ba da ƙarfina na canja halayena ba.” Bari mu tattauna dalilai biyar da za su taimaka mana mu daina halayen banza.

20, 21. Waɗanne halaye ne Jehobah yake so mu guje wa?

20 ‘’Yan’uwa waɗanda nake ƙauna, da yake an yi mana waɗannan alkawarai, bari mu tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu su ƙazantu. Bari kuma mu zama da cikakken tsarki cikin tsoron Allah.’ (2 Korintiyawa 7:1) Jehobah ba ya so mu kasance da halaye marasa kyau da za su iya lalata zukatanmu da kuma jikinmu.

21 Littafin 2 Korintiyawa 6:​17, 18 sun nuna babban dalilin da ya sa ya kamata mu ‘tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu su ƙazantu.’ Jehobah ya ce: “Kada ku haɗa kanku da wani abu mai ƙazanta.” Sai ya yi mana wannan alkawarin: “Zan zama uba a gare ku. Ku kuma ku zama ’ya’yana maza da mata.” Babu shakka, idan muka guji duk wani abin da zai sa mu kasance mara tsabta a gabansa, Jehobah zai ƙaunace mu kamar yadda kowane uba yake ƙaunar ’ya’yansa.

22-25. Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka mana mu guji halayen banza?

22 “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka.” (Matiyu 22:37) Wannan dokar ce ta fi muhimmanci a kan sauran. (Matiyu 22:38) Jehobah yana so mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu. Ta yaya za mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu idan muna yin abubuwan da za su gajartar da rayukanmu ko juya ƙwaƙwalwarmu? Hakan ba zai yiwu ba, don haka, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu nuna cewa muna daraja rai da Allah ya ba mu kyauta.

23 “[Jehobah] ne yake ba dukan mutane rai, da numfashi da dukan abubuwan da suke bukata.” (Ayyukan Manzanni 17:​24, 25) Idan abokinka ya ba ka wani kyauta mai daraja, za ka yar da kyautar ne ko kuma za ka ƙona? A’a, ba za ka yi hakan ba. Rai babban kyauta ne daga wurin Jehobah. Muna son wannan kyautan sosai. Don haka, muna so mu yi amfani da rayuwarmu a hanyar da za ta ɗaukaka shi.​—Zabura 36:9.

24 “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.” (Matiyu 22:39) Idan muna halayen banza, za mu cutar da kanmu har da mutanen da muke zama da su, wato ’yan’uwanmu da aminanmu. Alal misali, mutumin da yake zama a gida ɗaya da mai shan taba zai iya kamuwa da cuta domin hayakin da yake shaƙa daga mai shan tabar. Amma idan muka daina halayen banza, muna nuna cewa muna ƙaunar mutanen da muke zama da su.​—1 Yohanna 4:​20, 21.

25 “Ka tuna wa mutanenka su miƙa kansu ga shugabanni da kuma masu mulki, su yi musu biyayya.” (Titus 3:1) A ƙasashe da yawa, an haramta saya ko shan wasu ƙwayoyi. Muna biyayya ga waɗannan dokokin domin Jehobah ya ce mu riƙa biyayya ga shugabanni da masu mulki.​—Romawa 13:1.

Idan muka kasance da tsabta, muna ɗaukaka Jehobah

26. (a) Me muke bukatar mu yi idan muna so Jehobah ya karɓi ibadarmu? (b) Me ya sa kasancewa da tsabta a gaban Allah zai sa mu yi rayuwa mai kyau?

26 Mun ga cewa idan muna so mu zama aminan Jehobah, muna bukatar mu yi wasu gyara kuma zai dace mu soma yin hakan yanzu. Bai da sauƙi mutum ya daina halin banza, amma za mu yi nasara domin Jehobah ya ce zai taimaka mana! Ya ce: ‘Ni ne Yahweh Allahnku, wanda yake koya muku domin amfanin kanku, wanda yake nuna muku hanyar da za ku bi.’ (Ishaya 48:17) Idan muka kasance masu tsabta, za mu ɗaukaka Allahnmu.