Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 13

Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake So?

Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake So?

“Ku tabbata cewa kun koyi abin da zai gamshi Ubangiji.”​—AFISAWA 5:10.

1. Mene ne za mu yi don Jehobah ya amince da ibadarmu, kuma me ya sa?

YESU ya ce: “Masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin ruhu, da kuma gaskiya, gama Uba yana neman irin waɗannan ne su yi masa sujada.” (Yohanna 4:23; 6:44) Dole ne kowannenmu ya riƙa yin “abin da zai gamshi Ubangiji.” (Afisawa 5:10) Hakan bai da sauƙi a wasu lokuta domin Shaiɗan yana so ya rinjaye mu mu yi ma Jehobah rashin biyayya.​​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9.

2. Ka bayyana abin da ya faru kusa da Dutsen Sinai.

2 Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya rinjaye mu? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta wurin rikitar da mu don kar mu fahimci abin da ke da kyau da marar kyau. Ka lura da abin da ya faru da Isra’ilawa sa’ad da suka kafa sansani kusa da Dutsen Sinai. Musa ya hau kan Dutsen Sinai, Isra’ilawan kuma suna jiran sa a sansanin. Daga baya, Isra’ilawan sun gaji da jiran Musa, sai suka ce wa Haruna ya ƙera musu allah. Haruna ya ƙera musu gunki da ke kama da ƙaramin bijimi. Sai Isra’ilawan suka yi biki da rawa suna kewaye gunkin kuma suka bauta masa. Sun ɗauka cewa idan sun bauta ma gunkin kamar sun bauta ma Jehobah ne. Abin da suka yi zunubi ne duk da cewa a ganinsu “ga Yahweh,” suka yi bikin. A gun Jehobah, abin da suka yi bautar gumaka ne kuma da yawa daga cikinsu sun mutu. (Fitowa 32:​1-6, 10, 28) Wane darasi muka koya daga labarin? Mun koyi cewa bai kamata mu yaudari kanmu ba domin Kalmar Allah ta ce, “kada ku taɓa wani abin ƙyama!” Saboda haka, mu bar Jehobah ya nuna mana abin da ke da kyau da wanda bai da kyau.​—Ishaya 52:11; Ezekiyel 44:23; Galatiyawa 5:9.

3, 4. Me ya sa yake da kyau mu bincika tushen yawancin bukukuwan da ake yi a yau?

3 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya koyar da mabiyansa yadda za su riƙa kafa misali a kan yadda za a yi bauta mai tsabta. Har bayan mutuwarsa, manzanninsa sun ci gaba da koya wa sabbin Kiristoci ƙa’idodin Jehobah. Amma bayan manzanninsa sun mutu, malaman ƙarya sun shigo da koyarwar ƙarya da al’adu da kuma bukukuwan arna cikin ikilisiya. Sun yi ma bukukuwan arnan gyarar fuska don a ga kamar sun dace da Kiristoci. (2 Tasalonikawa 2:​7, 10; 2 Yohanna 6, 7) Har yanzu ana yin irin waɗannan bukukuwa kuma bukukuwan suna ɗaukaka koyarwar ƙarya da kuma sihiri. *​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​2-4, 23.

4 A duk duniya, mutane suna ɗaukan bukukuwa da muhimmanci sosai. Amma yayin da ka ci gaba da koyan ra’ayin Jehobah game da bukukuwan nan, mai yiwuwa za ka canja ra’ayinka game da wasu bukukuwan. Hakan zai iya kasance maka da wuya, amma ka san cewa Jehobah zai taimaka maka. Bari mu tattauna game da tushen wasu bukukuwa da ake yi a yau don mu san ko suna faranta ma Jehobah rai ko suna sa shi baƙin ciki.

TA YAYA AKA SOMA YIN KIRSIMATI?

5. Wane tabbaci ne ya nuna cewa ba a haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba ba?

5 Akan yi bikin Kirsimati a ranar 25 ga Disamba a wurare da dama a faɗin duniya, kuma masu yin bikin suna tsammanin cewa ranar ce aka haifi Yesu. Amma Littafi Mai Tsarki bai gaya mana rana ko watan da aka haifi Yesu ba, amma ya gaya mana yadda yanayi yake a lokacin. Littafin Luka ya gaya mana cewa lokacin da aka haifi Yesu a Baitalami, “makiyaya suna kwana a fili, suna lura da dabbobinsu da dare.” (Luka 2:​8-11) A watan Disamba, akan yi sanyi da ruwan sama da ma ƙanƙara a Baitalami. Saboda haka, ba zai yiwu makiyaya su kwana da dabbobinsu a waje ba. Me hakan ya koya mana? Mun koya cewa a lokacin zafi ne aka haifi Yesu ba a watan Disamba ba. Littafi Mai Tsarki da ma kayan tarihi da aka tono sun nuna cewa a tsakanin watan Satumba da Oktoba ne aka haifi Yesu.

6, 7. (a) Daga ina aka kwaikwayo wasu abubuwan da ake yi a lokacin Kirsimati? (b) Me ya kamata ya sa mu ba da kyauta?

6 To, ta yaya aka soma yin Kirsimati? An kwaikwayo shi ne daga bukukuwan arna, kamar bikin Saturnalia na Romawa. Romawa sukan yi bikin ne ga allahnsu na noma mai suna Sartun. Littafin nan The Encyclopedia Americana ya ce: “Yawancin abubuwan da ake yi a lokacin Kirsimati, an kwaikwayo su ne daga bikin Saturnalia na Romawa da ake yi a tsakiyar watan Disamba. Alal misali, daga wannan bikin ne aka kwaikwayo yin manyan bukukuwa da ba da kyaututtuka da kuma kunna kyandir a lokacin Kirsimati.” Ban da haka, a ranar 25 ga Disamba ne ake yin bikin haifuwar allahn rana na mutanen Fasiya mai suna Mithra.

7 Amma yawancin mutanen da suke bikin Kirsimati a yau, ba sa damuwa da tushensa. Sukan yi marmarin zuwan ranar don su kasance da iyalinsu, su ci abinci mai daɗi kuma su ba da kyaututtuka. Hakika, mu ma muna ƙaunar iyalanmu da abokanmu, kuma Jehobah yana so bayinsa su riƙa ba da kyauta. Shi ya sa littafin 2 Korintiyawa 9:7 ta gaya mana cewa “Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.” Jehobah ba ya so mu jira har sai rana ta musamman kafin mu ba da kyauta. Bayin Jehobah suna jin daɗin ba da kyauta da kuma yin liyafa tare da ’yan’uwa da abokan arziki, kuma ba sa tsammanin cewa za a biya su abin da suka yi. Ƙauna ce take sa su ba da kyauta.​—Luka 14:​12-14.

Idan mun san tushen bukukuwan da ake yi, zai taimaka mana mu san waɗanda za mu guje musu

8. A lokacin da Yesu yake jariri ne masu dūban suka ba shi kyauta? Ka bayyana.

8 Wasu sun ce ba da kyaututtuka da ake yi a lokacin Kirsimati ya dace, domin sa’ad da Yesu yake ɗan jariri, wasu mutane uku masu ilimi sun kawo masa kyaututtuka. Gaskiya ne cewa wasu mutane sun ziyarci Yesu kuma suka kawo masa kyaututtuka. A lokacin, al’adarsu ce su kai kyaututtuka ga mutumin da ke da daraja. (1 Sarakuna 10:​1, 2, 10, 13) Amma ka san cewa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mutanen masu dūba ne kuma ba sa bauta ma Jehobah? Ban da haka, ba su ziyarci Yesu sa’ad da yake jariri yana kwance a inda ake sa ma dabbobi abinci ba, amma sun ziyarce shi bayan ya ɗan girma kuma suna zama a wani gida.​—Matiyu 2:​1, 2, 11.

ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA BIKIN RANAR HAIFUWA?

9. Su waye ne aka ba da labarin bikin ranar haifuwarsu a Littafi Mai Tsarki?

9 Akan yi farin ciki a ranar da aka haifi yaro. (Zabura 127:3) Amma hakan bai nuna cewa za mu riƙa yin biki in ranar ta zagayo ba. Ga wani abin lura: A Littafi Mai Tsarki, mutane biyu ne kawai aka ba da labarin bikin ranar haifuwarsu, wato Sarki Fir’auna na Masar da kuma Sarki Hiridus Antibas. (Karanta Farawa 40:​20-22; Markus 6:​21-29.) Dukansu ba sa bauta ma Jehobah. Littafi Mai Tsarki bai ba da labarin wani bawan Jehobah da ya yi bikin ranar haifuwarsa ba.

10. Ta yaya Kiristocin ƙarni na farko suka ɗauki bikin ranar haifuwa?

10 Littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce a gun Kiristocin ƙarni na farko, “bikin ranar haifuwa, bikin arna ne.” Daga koyarwar ƙarya ne aka samo bukukuwan nan. Alal misali, Helenawa a dā sun yi imani cewa akan haifi kowanne mutum rana ɗaya da allahn da zai riƙa kiyaye shi. Shi ya sa sukan yi bikin ranar haifuwa domin a ganinsu, bikin zai sa allahn da aka haifa rana ɗaya da mutumin ya riƙa kiyaye shi. Ban da haka ma, akan haɗa bikin ranar haifuwa da dūba.

11. Yaya Jehobah yake ji idan muka ba da kyauta?

11 Mutane da yawa a yau suna ganin cewa ranar da aka haife su, rana ce da ya kamata a nuna musu ƙauna da kuma yi musu fatan alheri. Amma za mu iya nuna ƙauna ga iyalanmu da abokanmu a koyaushe, ba kawai sau ɗaya a shekara ba. Jehobah yana so mu riƙa yin alheri kuma mu zama masu kirki ko da yaushe. (Karanta Ayyukan Manzanni 20:35.) A kullum muna gode masa da kyautan rai da ya ba mu, ba sai ranar haifuwarmu ba.​—Zabura 8:​3, 4; 36:9.

Ƙauna ce take sa Kiristoci na gaskiya su ba da kyauta

12. Me ya sa ranar mutuwarmu ta fi ranar haifuwarmu?

12 Littafin Mai-Wa’azi 7:1 ta ce: “Suna mai kyau ya fi man ƙashi mai tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haifuwa.” Me ya sa ranar mutuwar mutum ta fi ranar haifuwarsa? Ranar da aka haife mu, ba mu yi kome da rayuwarmu ba tukuna, ko mai kyau ko mara kyau. Amma idan muka bauta ma Jehobah har iya rayuwarmu kuma muka yi wa mutane alheri, za mu yi “suna mai kyau” kuma Jehobah zai tuna da mu in mun mutu. (Ayuba 14:​14, 15) Bayin Jehobah ba sa yin bikin ranar haifuwarsu ko na Yesu. Abin da Yesu ya ce mu riƙa yi shi ne Tunawa da mutuwarsa.​—Luka 22:​17-20; Ibraniyawa 1:​3, 4.

YADDA AKA SOMA YIN ISTA

13, 14. Wane abu ne bikin Ista yake da alaƙa da shi?

13 Mutane da yawa suna ganin cewa Ista shi ne bikin tashin Yesu daga mutuwa. Amma gaskiyar ita ce, bikin Ista yana da alaƙa da allahiyar asuba da lokacin zafi na Anglo-Saxon mai suna Eostre. Littafin nan The Dictionary of Mythology ya bayyana cewa ban da allahiyar asuba da na lokacin zafi, har ila ita allahiyar amfanin gona ce. Wasu abubuwan da ake yi a lokacin Ista suna da alaƙa da allahiyar. Alal misali, littafin nan Encyclopædia Britannica ya ce, kwai “yana nuna alamar sabuwar rayuwa da kuma tashin matattu.” Ban da haka ma, arna sun daɗe suna amfani da zomaye a matsayin alama ta amfanin gona. Babu shakka, bikin Ista ba shi da wani alaƙa da tashin Yesu daga matattu.

14 Jehobah ba ya jin daɗin yadda mutane suke haɗa bautar ƙarya da tashin Ɗansa daga mutuwa. (2 Korintiyawa 6:​17, 18) Ban da haka ma, bai ce mana mu yi bikin tashin Ɗansa daga matattu ba.

BIKIN CIKA SABUWAR SHEKARA DA HALLOWEEN

15. Ta yaya aka soma yin bikin Sabuwar Shekara da Halloween?

15 Ranar da ake yin bikin cika Sabuwar Shekara da ma abubuwan da ake yi a lokacin bikin ya bambanta a ƙasashe da dama. Ga abin da littafin nan The World Book Encyclopedia ya faɗa game da bikin cika Sabuwar Shekara: “A shekara ta 46 kafin haifuwar Yesu, Julius Caesar, Shugaban Romawa, ya mai da ranar 1 ga Janairu, ranar bikin cika Sabuwar Shekara. Romawan sun keɓe ranar ga Janus, allahn kofofi da farkon shekara. An kirkiro watan Janairu daga Janus ne allahn da ke da fuska biyu, ɗayan ya fuskanci gaba, ɗayan kuma ya fuskanci baya.” Saboda haka, arna ne suka soma bikin cika Sabuwar Shekara. Bikin Halloween yana da alaƙa da maitanci da aljanu. Ba yau aka soma wannan bikin ba. Tun a zamanin dā idan wata ya yi girma, kusan 1 ga watan Nuwamba, ƙabilun Birtaniya da Ireland suna yin bikin Samhain. Sun yi imani cewa ruhohin mutanen da suka mutu sukan dawo duniya a lokacin bikin. Mutane sukan ajiye abinci da abin sha a waje don kar ruhohin su yi musu illa.

IRIN BIKIN AURE DA ALLAH YAKE SO

16, 17. Me ya kamata mu yi tunani a kai sa’ad da muke shirin yin aure?

16 Ranar aure, ranar murna ce. Akan yi bikin aure a hanyoyi dabam-dabam a faɗin duniya. Mutane ba sa damuwa a kan tushen wasu abubuwa da ake yi a bikin aure. Saboda haka, ba su san cewa wasu abubuwa da ake yi a bikin aure suna da alaƙa da bautar gumaka ba. Amma Kiristoci da suke shirin yin aure, suna so bikin aurensu ya faranta ma Allah rai. Idan sun san tushen wasu abubuwa da ake yi a bikin aure, zai taimaka musu su yi abin da ya dace.​—Markus 10:​6-9.

17 Akwai wasu abubuwa da mutane suke yi a bikin aure kuma sun gaskata cewa yin hakan zai kawo ‘sa’a’ ga ma’auratan. (Ishaya 65:11) Alal misali, a wasu wurare, mutane sukan wasa wa ma’auratan shinkafa ko wani abu da ya yi kama da hakan. Sun yi imani cewa hakan zai sa ma’auratan su haifi ’ya’ya, su yi farin ciki kuma zai sa su yi dogon kwana da kuma kāre su daga lahani. Ya kamata Kiristoci su yi hankali don kada su yi wani abin da yake da alaƙa da bautar ƙarya.​​—Karanta 2 Korintiyawa 6:​14-18.

18. Waɗanne ƙa’idodi ne kuma suka shafi aure?

18 Kiristoci da suke so su yi aure suna so aurensu ya kasance da daraja da kuma daɗi ga waɗanda za su halarci bikin. Waɗanda suka halarci bikin ba za su yi furuci mara daɗi ko na iskanci ko kuma na reni ga ma’auratan ko sauran mutanen ba. (Karin Magana 26:​18, 19; Luka 6:31; 10:27) Kiristoci ba sa “taƙama da abubuwan” duniya a lokacin aurensu. (1 Yohanna 2:16) Idan kuna shirin yin aure, ku tabbata cewa kun yi zaɓi mai kyau domin ku yi farin ciki a duk lokacin da kuka tuna da bikin aurenku.​—Ka Duba Ƙarin Bayani na 28.

YA DACE MU YI TOASTING NE?

19, 20. Mene ne tushen toasting?

19 Ana yawan yin toasting, wato mutum ya ɗaga kofi kuma ya kaɗa shi da na wasu a bikin aure ko wasu bukukuwa. A lokacin da suke yin hakan, wani yakan yi fatan alheri sai sauran kuma su haɗa kofinsu da nasa. Shin ya dace Kirista ya yi hakan?

20 Littafin nan International Handbook on Alcohol and Culture ya ce wataƙila hakan ya samo asali ne daga “yadda arna a dā suke ba allolinsu jini ko kuma giya.” Suna yin hakan ne don allolin su amince da “bukatunsu na ‘dogon kwana’ ko kuma ‘ƙoshin lafiya!’ ” A dā mutane sukan daga kofinsu don su roƙi allolinsu su yi musu albarka. Amma ba ta wannan hanyar ce Jehobah yake yi wa mutane albarka ba.​—Yohanna 14:6; 16:23.

“KU DA KUKE ƘAUNAR YAHWEH, KU ƘI MUGUNTA”

21. Waɗanne irin bukukuwa ne ya kamata Kiristoci su guje musu?

21 Kafin ka tsai da shawara ko za ka yi wasu bukukuwa ko a’a, zai dace ka yi tunani sosai a kan tushensu. Alal misali, a wasu bukukuwa ana yin rawar banza da shaye-shaye da kuma lalata. Irin waɗannan bukukuwa suna ɗaukaka yin luwaɗi ko kuma ƙishin ƙasa. Idan muna yin irin waɗannan bukukuwan, shin muna ƙin abin da Jehobah ya tsana?​—Zabura 1:​1, 2; 97:10; 119:37.

22. Me zai iya taimakon Kirista ya tsai da shawara ko zai iya yin wasu bukukuwa ko a’a?

22 Kiristoci suna bukata su mai da hankali sosai don kada su saka hannu a bukukuwan da suke ɓata ma Allah rai. Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Duk abin da kuke yi, ko kuke ci, ko kuke sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.” (1 Korintiyawa 10:31; ka duba Ƙarin Bayani na 29.) Hakika, ba a dukan bukukuwa ne ake lalata da koyarwar addinin ƙarya ko kuma ƙishin ƙasa ba. Don haka, idan akwai wani biki da bai saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, mu ne muke da hakkin tsai da shawara ko za mu je bikin ko a’a. Zai dace mu yi tunani a kan yadda zaɓin da muke yi yake shafan mutane.

KA GIRMAMA JEHOBAH A FURUCINKA DA AYYUKANKA

23, 24. Ta yaya za mu bayyana ma danginmu da ba Shaidu ba dalilin da ya sa ba ma yin wasu bukukuwa?

23 Wataƙila ka daina yin wasu bukukuwa da suke ɓata wa Jehobah rai. Amma idan ’yan’uwanka da ba Shaidu ba suka ga ba ka yin bukukuwan tare da su, za su iya ganin kamar ba ka son su ko kuma ba ka son yin tarayya da su. Suna iya ganin cewa a lokutan bukukuwa ne dangi sukan ga juna. Me za ka yi? Akwai hanyoyi da yawa da za ka nuna musu cewa kana ƙaunar su kuma kana daraja su. (Karin Magana 11:25; Mai-Wa’azi 3:​12, 13) Za ka iya gayyatar su a wasu lokuta dabam don ku yi liyafa.

24 Idan danginka ko iyalinka suka tambaye ka dalilin da ya sa ba ka yin wasu bukukuwa, za ka iya neman bayani a littattafanmu ko kuma ka shiga dandalinmu na jw.org/ha don ka iya bayyana musu dalilin da ya sa ba ka yin hakan. Kar ka yi abin da zai sa su ga kamar kana nuna musu cewa ka fi su ilimi ko kana sa su dole su bi ra’ayinka. Ka taimaka musu su gane cewa ka yi la’akari da wasu abubuwa da yawa kafin ka yanke shawarar yin hakan. Ka kame kanka kuma ‘maganarka ta kasance da alheri da kuma daɗin ji.’​—Kolosiyawa 4:6.

25, 26. Ta yaya iyaye za su taimaka ma yaransu su so ƙa’idodin Jehobah?

25 Zai dace dukanmu mu fahimci dalilin da ya sa ba ma wasu bukukuwa. (Ibraniyawa 5:14) Burinmu shi ne mu faranta ma Jehobah rai. Idan kuma muna da yara, zai dace mu taimaka wa yaranmu su fahimci ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma su riƙa bi. Idan suka san Jehobah da kyau, za su ƙaunace shi kuma su so faranta masa rai.​—Ishaya 48:​17, 18; 1 Bitrus 3:15.

26 Jehobah yana farin ciki domin yadda muke iya ƙoƙarinmu don mu bauta masa cikin ruhu da gaskiya. (Yohanna 4:23) Amma wasu suna ganin cewa ba zai yiwu mutum ya bauta ma Allah cikin gaskiya a wannan duniyar da ke cike da rashin gaskiya ba. Hakan gaskiya ne? Za mu tattauna hakan a babi na gaba.

^ sakin layi na 3 Don ka san irin waɗannan bukukuwan, ka bincika littafin nan Littafin Bincike don Shaidun Jehobah ko kuma ka shiga dandalin jw.org/ha.