Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 3

Ka Yi Abokantaka da Masu Kaunar Allah

Ka Yi Abokantaka da Masu Kaunar Allah

“Wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima.”​—KARIN MAGANA 13:20.

1-3. (a) Me muka koya a Karin Magana 13:20? (b) Me ya sa ya kamata mu zaɓi abokan kirki?

KA TAƁA ganin yadda jariri yake kallon iyayensa? Tun kafin ya fara magana, yakan koyi duk wani abin da yake ji ko gani. Idan ya soma girma, sai ya yi kwaikwayon iyayensa. Shi ya sa ko manya ma sukan yi kwaikwayon mutanen da suke yawan zama da su.

2 Littafin Karin Magana 13:20 ta ce: “Wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima.” Furucin nan “tafiya tare” da wani yana nufin abokin tarayyarka. Hakan ya wuce kasancewa tare da mutumin kawai. Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce tafiya tare da mutum ya ƙunshi ƙaunar mutumin da kuma jin daɗin zama da mutumin. Mutanen da muke jin daɗin zama da su za su iya sa mu yi abu mai kyau ko mara kyau.

Abokanmu za su iya sa mu yi abu mai kyau ko mara kyau. Littafin Karin Magana 13:20 ta ci gaba da cewa: “Amma abokin tafiyar wawaye zai lalace.” Furucin nan ‘abokin tafiya’ a Helenanci yana nufin yin “abokantaka” da mutum. (Karin Magana 22:24; Alkalai 14:20) Abokin da yake ƙaunar Allah zai taimaka mana mu ci gaba da bauta ma Allah. Bari mu ga irin mutanen da Jehobah ya yi abokantaka da su don mu san irin mutanen da mu ma za mu yi abokantaka da su.

SU WAYE NE AMINAN ALLAH?

4. Me ya sa zama aminin Allah babban gata ne? Me ya sa Jehobah ya kira Ibrahim ‘amininsa’?

4 Jehobah wanda shi ne mai iko duka a sama da ƙasa, ya ba mu gatan zama aminansa. Hakika muna murna don wannan gatan da Allah ya ba mu. Jehobah yana mai da hankali sa’ad da yake zaɓan aminansa. Yana zaɓan mutanen da suke ƙaunarsa kuma suke ba da gaskiya a gare shi. Ka tuna da Ibrahim wanda yake a shirye ya yi abin da Allah yake so. Sau da dama Ibrahim ya yi biyayya kuma ya nuna bangaskiya sosai. Ya ma yarda ya yi hadaya da ɗansa Ishaku. Ibrahim ya gaskata cewa ‘Allah yana iya tā da matattu.’ (Ibraniyawa 11:​17-19; Farawa 22:​1, 2, 9-13) Ibrahim mutum ne mai biyayya da kuma bangaskiya, shi ya sa Jehobah ya kira shi ‘amininsa.’​—Ishaya 41:​8, Littafi Mai Tsarki; Yaƙub 2:​21-23.

5. Yaya Jehobah yake ɗaukan masu yi masa biyayya?

5 Jehobah yana ɗaukan aminansa da daraja. Abokansa suna ƙaunarsa fiye da kome. (Karanta 2 Sama’ila 22:26.) Su masu aminci ne kuma suna masa biyayya domin suna ƙaunarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “yana amincewa da mai gaskiya a zuci,” wato masu yi masa biyayya. (Karin Magana 3:32) Jehobah yana kiran abokansa su zo su bauta masa. Yana so su yi masa ibada da kuma addu’a a kowane lokaci.​—Zabura 15:​1-5.

6. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Yesu?

6 Yesu ya ce: “Duk wanda yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi.” (Yohanna 14:23) Don haka, idan muna son mu zama abokan Jehobah, muna bukatar mu ƙaunaci Yesu kuma mu yi abin da ya gaya mana mu yi. Alal misali, muna bin umurnin da ya ba mu cewa mu yi wa’azin bishara kuma mu koyar da mutane. (Matiyu 28:​19, 20; Yohanna 14:​15, 21) Da yake muna ƙaunar Yesu, muna bin misalinsa. (1 Bitrus 2:21) Jehobah yana farin ciki sosai idan ya ga muna yin abin da Ɗansa ya gaya mana mu yi.

7. Me ya sa ya kamata mu yi abokantaka da waɗanda suke ƙaunar Jehobah?

Abokan Jehobah suna da aminci da gaskiya kuma suna biyayya. Ban da haka ma, suna ƙaunar Ɗansa, Yesu. Shin muna zaɓan abokan da Jehobah yake so? Idan abokanka suna bin gurbin Yesu kuma suna wa mutane wa’azin Mulkin Allah, za su iya taimaka maka ka zama mutumin kirki kuma ka ci gaba da bauta wa Jehobah.

MISALAI MASU KYAU A LITTAFI MAI TSARKI

8. Me ya burge ka game da abokantakar Rut da Naomi?

8 Akwai labaran abokai da yawa a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Rut da surkuwarta Naomi abokai ne. Waɗannan matan ba daga ƙasa ɗaya suka fito ba kuma Naomi ta girmi Rut sosai. Duk da haka, sun zama abokai domin dukansu suna ƙaunar Jehobah. A lokacin da Naomi take son ta bar ƙasar Mowab don ta koma Isra’ila, “Rut ta manne mata.” Ta gaya wa Naomi cewa: “Mutanenki za su zama mutanena; kuma Allahnki zai zama Allahna.” (Rut 1:​14, 16) Rut ta yi wa Naomi alheri ta wurin yin aiki sosai don ta taimaka mata. Naomi ta so Rut sosai kuma ta riƙa ba ta shawara mai kyau. Rut ta bi shawarar kuma dukansu sun sami albarka ba kaɗan ba.​—Rut 3:6.

9. Me ya burge ka game da abokantakar Dauda da Jonathan?

9 Dauda da Jonathan masu aminci ga Jehobah ne da suka zama abokai. Jonathan ya girmi Dauda da shekaru wajen 30 kuma shi ne ya kamata ya gāji sarautar mahaifinsa a ƙasar Isra’ila. (1 Sama’ila 17:33; 31:2; 2 Sama’ila 5:4) Amma, da ya ji cewa Jehobah ya zaɓi Dauda ya zama sarki, bai yi ƙishin Dauda ko kuma ya yi gasa da shi ba. A maimakon haka, Jonathan ya yi iya ƙoƙarinsa domin ya taimaka wa Dauda. Alal misali, a lokacin da ake so a kashe Dauda, Jonathan ya “ƙarfafa shi ya tsaya ga Allah.” Jonathan ya ma sadaukar da ransa domin Dauda. (1 Sama’ila 23:​16, 17) Dauda ma mai aminci ne. Ya ɗauki nauyin kula da iyalin Jonathan kuma ya cika alkawarinsa har ma a lokacin da Jonathan ya rasu.​—1 Sama’ila 18:1; 20:​15-17, 30-34; 2 Sama’ila 9:​1-7.

10. Me labarin Ibraniyawa ukun ya koya mana a kan abokantaka?

10 Shadrak da Meshak da Abednego matasan Ibraniyawa ne da aka kai su wata ƙasa tun suna yara. Kuma dukansu abokai ne. Ko da yake ba sa tare da iyayensu, sun taimaka wa juna don su ci gaba da bauta wa Jehobah. Bayan sun girma, an gwada bangaskiyarsu a lokacin da Sarki Nebuchadnezzar ya ce kowa ya bauta wa gunkin zinariya da ya yi. Amma Shadrak da Meshak da Abednego sun ƙi su bauta wa gunkin. Sun gaya wa sarkin cewa: “Ba za mu bauta wa allolinka ba, ko mu yi wa gunkin zinariyar nan wanda ka kafa sujada ba.” Da aka gwada bangaskiyarsu, abokan nan uku sun ƙi su ɓata dangantakarsu da Allah.​—Daniyel 1:​1-17; 3:​12, 16-28.

11. Ta yaya muka san cewa Bulus da Timoti abokai ne sosai?

11 A lokacin da Bulus ya haɗu da matashin nan Timoti, ya gane cewa Timoti yana ƙaunar Jehobah kuma yana kula da ikilisiyarsu. Don haka, Bulus ya koyar da Timoti don ya iya taimaka wa ’yan’uwa maza da mata a wurare dabam-dabam. (Ayyukan Manzanni 16:​1-8; 17:​10-14) Timoti ya yi aiki sosai shi ya sa Bulus ya gaya masa cewa: Mun yi “aikin shelar labari mai daɗi tare.” Bulus ya san cewa Timoti “ya damu” da ’yan’uwa sosai. Aiki sosai da Bulus da Timoti suka yi a bautarsu ga Jehobah ne ya sa suka zama aminai.​—Filibiyawa 2:​20-22; 1 Korintiyawa 4:17.

YADDA ZA MU ZAƁI ABOKAI

12, 13. (a) Me ya sa muke bukata mu zaɓi abokanmu da kyau ko ma a ikilisiya ne? (b) Me ya sa manzo Bulus ya ja kunnen ’yan’uwa a 1 Korintiyawa 15:33?

12 Za mu iya koyan abubuwa daga ’yan’uwanmu maza da mata, kuma mu taimaka musu su ci gaba da bauta wa Jehobah. (Karanta Romawa 1:​11, 12.) Amma ya kamata mu mai da hankali game da abokan da muke zaɓa ko a ikilisiya ma. Muna da ’yan’uwa maza da mata da yawa daga kabilu da wurare dabam-dabam. Wasu ba su daɗe da soma bauta wa Jehobah ba, wasu kuma sun daɗe suna yin hakan. Yakan ɗauki lokaci sosai kafin mutum ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah kamar yadda yake ɗaukan lokaci kafin ’ya’yan itace su nuna. Don haka, ya kamata mu riƙa haƙuri da juna, mu ƙaunaci juna kuma mu zaɓi abokan kirki.​—Romawa 14:1; 15:1; Ibraniyawa 5:12–6:3.

13 A wasu lokuta, wani abu zai iya faruwa a ikilisiya da zai iya sa mu mai da hankali sosai. Wataƙila wata ko wani yana yin abin da Littafi Mai Tsarki ya hana. Ko kuma wani yakan yi maganganun da za su iya ɓata haɗin kan ikilisiya. Hakan ba abin mamaki ba ne domin ko a ikilisiyar ƙarni na farko ma, an sami matsaloli a wasu lokuta. Shi ya sa Bulus ya ja kunnen Kiristoci a lokacin ya ce: “Kada fa a ruɗe ku! Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.” (1 Korintiyawa 15:​12, 33) Bulus ya sake jan kunnen Timoti cewa kada ya yi tarayya da abokan banza. Mu ma a yau ya kamata mu zaɓi abokanmu da kyau.​—Karanta 2 Timoti 2:​20-22.

14. Ta yaya abokanmu za su iya shafan dangantakarmu da Jehobah?

14 Wajibi ne mu yi ƙoƙari don kada wani abu ya shiga tsakaninmu da Jehobah. Dangantakarmu da Jehobah ta fi muhimmanci. Don haka, bai kamata mu yi zama da waɗanda za su sa bangaskiyarmu ta yi sanyi ko kuma waɗanda za su ɓata dangantakarmu da Jehobah ba. Ba zai yiwu mu saka soso a cikin ruwan datti kuma mu yi tsammanin cewa ruwa mai tsabta zai fito daga ciki ba. Haka ma yake da mu, ba za mu yi zama da abokan banza kuma mu yi tsammanin cewa za mu riƙa yin abin da ya dace ba. Muna bukatar mu zaɓi abokan kirki.​—1 Korintiyawa 5:6; 2 Tasalonikawa 3:​6, 7, 14.

Za ka iya samun abokan kirki waɗanda suke ƙaunar Jehobah

15. Me za ka yi don ka sami abokan kirki a ikilisiya?

15 Za ka sami mutanen da suke bauta wa Jehobah da gaske a ikilisiya. Za su iya zama abokanka na ƙwarai. (Zabura 133:1) Kar ka yi abokantaka da tsaranka kawai. Ka tuna cewa Jonathan ya girme Dauda sosai kuma Naomi ma ta girme Rut ba kaɗan ba. Zai dace mu bi shawarar Littafi Mai Tsarki cewa: “Ku ƙaunaci ’yan’uwa.” (2 Korintiyawa 6:13; karanta 1 Bitrus 2:17.) Kuma idan kana ƙoƙarin bin misalin Jehobah, mutane za su so su zama abokanka.

IDAN AKA SAMU SAƁANI

16, 17. Me ya kamata mu guji yi idan wani ya ɓata mana rai?

16 A cikin kowace iyali, akan samu bambancin ra’ayi da bambancin hali da kuma yadda suke yin abubuwa. Haka yake a kowace ikilisiya. Bambancinmu yana sa rayuwa ta yi daɗi kuma za mu iya koyan abubuwa daga juna. Amma don bambancinmu, mukan kasa gane dalilin da ya sa wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi wani abu da ya sa mu fushi. A wasu lokuta za mu iya ɓata rai. (Karin Magana 12:18) Amma ya kamata mu bar ikilisiya domin irin wannan saɓanin?

17 A’a. Ko da wani ya ɓata mana rai ko ya yi abin da ba mu ji daɗinsa ba, ba za mu bar ikilisiya domin hakan ba. Domin ba Jehobah ba ne ya ɓata mana rai. Shi ya ba mu rai da duk abin da muke so. Shi ya sa ya kamata mu ƙaunaci Allah kuma mu yi masa biyayya. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Jehobah ne ya tanada mana ikilisiya don mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. (Ibraniyawa 13:17) Ba za mu taɓa ƙin wannan tanadin da ya yi mana don wani ya ɓata mana rai ba.​—Karanta Zabura 119:165.

18. (a) Mene ne zai taimaka mana mu zauna lafiya da ’yan’uwanmu? (b) Me ya sa ya kamata mu gafarta ma ’yan’uwanmu?

18 Muna ƙaunar ’yan’uwanmu Kiristoci sosai kuma muna son kasancewa tare da su. Tun da Jehobah bai ce dole sai mun zama kamilai ba, mu ma bai kamata mu bukaci ’yan’uwanmu su zama kamilai ba. (Karin Magana 17:9; 1 Bitrus 4:8) Dukanmu mukan yi kuskure, amma ƙauna za ta sa mu riƙa “gafarta wa juna.” (Kolosiyawa 3:13) Idan muna ƙaunar juna, ba za mu bar ƙaramin abu ya zama babbar matsala ba. Gaskiya ne cewa idan wani ya ɓata mana rai, zai yi wuya mu daina tunani a kai. Yana da sauƙi mu yi fushi kuma mu riƙe mutumin a zuciya. Amma hakan zai ƙara sa mu baƙin ciki. Amma idan muka gafarta wa mutumin da ya yi mana laifi, za mu sami kwanciyar hankali da haɗin kai a cikin ikilisiya. Ban da haka, Jehobah zai yi farin ciki don abin da muka yi.​—Matiyu 6:​14, 15; Luka 17:​3, 4; Romawa 14:19.

IDAN AN YI MA WANI YANKAN ZUMUNCI

19. Me zai sa mu daina tarayya da wani a cikin ikilisiya?

19 A iyalin da ake zaman lafiya, kowa yakan yi ƙoƙari don ya sa sauran farin ciki. Amma a ce ɗaya daga cikin yaran ya soma taurin kai kuma kowa a cikin iyalin ya yi ƙoƙarin taimaka masa, amma ya ƙi ji. A ƙarshe, yana iya barin gidan da kansa ko kuma baban ya ce masa ya bar gidan. Hakan zai iya faruwa a cikin ikilisiya. Wani zai iya soma yin abubuwan da Jehobah ba ya so kuma suna da haɗari ga ikilisiya. Ya ƙi jin gargaɗin da aka yi masa kuma halinsa ya nuna cewa ba ya son ya ci gaba da zama a cikin ikilisiyar. Yana iya zaɓa ya bar ikilisiyar da kansa ko kuma a yi masa yankan zumunci. Idan aka yi masa yankan zumunci, Littafi Mai Tsarki ya ce ‘kada mu haɗa kai’ da shi. (Karanta 1 Korintiyawa 5:​11-13; 2 Yohanna 9-11) Idan shi abokinmu ne ko kuma danginmu, yin hakan ba zai kasance mana da sauƙi ba. Amma a irin wannan yanayi, ya kamata ƙaunar da muke nuna wa Allah ta fi wanda muke nuna wa kowa.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 8.

20, 21. (a) Ta yaya Jehobah ya nuna ƙauna a umurnin da ya ba mu cewa kada mu yi tarayya da wanda aka masa yankan zumunci? (b) Me ya sa ya dace mu zaɓi abokan kirki?

20 Jehobah yana ƙaunar mu, shi ya sa ya ce mu daina haɗa kai da mai zunubin da ya ƙi tuba. Hakan yana kāre ikilisiya daga mutanen da ba sa so su yi biyayya ga Allah. (1 Korintiyawa 5:7; Ibraniyawa 12:​15, 16) Hakan yana sa mu ƙaunaci sunan Allah mai tsarki, mu ƙaunaci ƙa’idodinsa, mu kuma ƙaunace shi. (1 Bitrus 1:​15, 16) Ban da haka ma, Jehobah yana nuna ƙauna ga mutumin da aka yi masa yankan zumunci ta wurin umurtarmu cewa mu daina tarayya da mutumin. Horon da aka yi masa zai sa ya gane cewa abubuwan da yake yi ba su dace ba kuma ya daina yin su. Mutane da yawa da aka yi musu yankan zumunci a dā, sun sake komo cikin ikilisiya kuma an marabce su da farin ciki.​—Ibraniyawa 12:11.

21 Abokanmu suna da tasiri a kanmu a hanyoyi da dama. Shi ya sa ya dace mu zaɓi abokan kirki. Idan muna ƙaunar mutanen da Jehobah yake ƙaunar su, za mu kasance da mutanen da za su taimaka mana mu riƙa bauta masa har abada.