Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Karin Bayani

Karin Bayani

 1 ƘA’IDODI

Dokokin Allah sun samo asali ne daga ƙa’idodinsa. Ƙa’idodin su ne muhimman gaskiya da ke Littafi Mai Tsarki. Suna taimaka mana mu san tunanin Allah da kuma ra’ayinsa game da abubuwa. Suna kuma taimaka mana mu yanke shawara mai kyau kuma mu yi abin da ya dace. Ƙari ga haka, suna taimaka mana mu san abin da za mu yi a yanayin da Littafi Mai Tsarki bai ba da doka kai tsaye ba.

Babi na 1, sakin layi na 8

 2 BIYAYYA

Yin biyayya ga Jehobah yana nufin mu yi duk abin da ya ce mu yi. Jehobah yana so mu yi masa biyayya domin muna ƙaunar sa. (1 Yohanna 5:3) Idan muna ƙaunar Allah kuma muna dogara gare shi, za mu bi shawararsa a koyaushe. Za mu yi masa biyayya ko a lokacin da yin hakan yake da wuya. Yana da kyau mu yi biyayya ga Allah domin yana koya mana yadda za mu yi rayuwa mai kyau kuma ya yi mana alkawari cewa za mu sami albarka masu yawa a nan gaba.​—Ishaya 48:17.

Babi na 1, sakin layi na 10

 3 ‘YANCIN YIN ZAƁI

Jehobah ya ba wa kowa ’yanci ya zaɓi abin da yake so. Bai yi mu kamar bebin roba ba. (Maimaitawar Shari’a 30:19; Yoshuwa 24:15) Za mu iya yin amfani da ’yancinmu mu yi abu mai kyau. Amma idan ba mu yi hankali ba, za mu yanke shawarar da ba ta dace ba. Da yake muna da ’yancin yin abin da muke so, mu ne za mu zaɓa mu yi wa Jehobah biyayya don mu nuna cewa muna ƙaunar sa.

Babi na 1, sakin layi na 12

 4 HALAYEN DA JEHOBAH YAKE SO

Jehobah ya nuna irin halayen da yake so mu kasance da su. Za mu iya koyan halayen a Littafi Mai Tsarki kuma mu san yadda za su amfane mu. (Karin Magana 6:​16-19; 1 Korintiyawa 6:​9-11) Halayen suna taimaka mana mu san abin da Jehobah yake so da wanda ba ya so. Suna kuma taimaka mana mu san yadda za mu nuna ƙauna da yadda za mu yanke shawara mai kyau da kuma yadda za mu yi wa mutane alheri. Ko da yake halayen mutanen duniya suna ci gaba da lalacewa, Jehobah bai canja ra’ayinsa a kan irin halayen da yake so mu kasance da su ba. (Maimaitawar Shari’a 32:​4-6; Malakai 3:6) Idan muka kasance da halayen, za mu zauna lafiya da mutane kuma za mu sami kwanciyar hankali.

Babi na 1, sakin layi na 17

 5 TUNANIN ZUCIYA

Jehobah ya halicce mu yadda za mu iya yin tunani don mu iya bambanta abu mai kyau da mara kyau. (Romawa 2:​14, 15) Don mu iya bambanta abu mai kyau da mara kyau, muna bukatar mu shirya zuciyarmu bisa ƙa’idodin Jehobah. Hakan zai sa mu riƙa yanke shawarar da za ta sa Jehobah farin ciki. (1 Bitrus 3:16) Zuciyarmu za ta iya gaya mana ko shawarar da muke so mu yanke ta dace ko ba ta dace ba. Idan muka yanke shawarar da ba ta dace ba, zuciyarmu za ta dame mu. Mu roƙi Jehobah ya taimaka mana don mu kasance da zuciya mai tsabta. Zuciya mai tsabta za ta sa mu kasance da kwanciyar hankali kuma mu mutunta kanmu.

Babi na 2, sakin layi na 3

 6 TSORON ALLAH

Tsoron Allah yana nufin mu ƙaunace shi da daraja shi kuma mu guji yin duk wani abin da zai ɓata masa rai. Tsoron Allah yana taimaka mana mu yi abin da yake da kyau kuma mu ƙi yin abin da bai da kyau. (Zabura 111:10) Yana sa mu yi biyayya ga duk abin da Jehobah ya ce. Yana kuma sa mu cika duk wani alkawarin da muka yi masa domin muna daraja shi. Tsoron Allah yana kyautata tunaninmu da yadda muke sha’ani da mutane da kuma shawarar da muke yankewa kullum.

Babi na 2, sakin layi na 9

 7 TUBA

Tuba yana nufin baƙin cikin da mutum yakan yi idan ya yi zunubi. Waɗanda suke ƙaunar Allah sukan yi baƙin ciki sosai sa’ad da suka yi abin da ba ya so. Idan muka yi zunubi, mu roƙi Jehobah ya gafarta mana ta fansar Yesu Kristi. (Matiyu 26:28; 1 Yohanna 2:​1, 2) Idan muka tuba kuma muka daina yin zunubin, mu tabbata cewa Jehobah zai gafarta mana. Bai kamata mu riƙa damuwa saboda zunubin da muka yi a dā ba. (Zabura 103:​10-14; 1 Yohanna 1:9; 3:​19-22) Dole ne mu koyi darasi daga kuskuren da muka yi, mu yi ƙoƙari mu daina tunanin banza kuma mu kasance da irin halayen da Jehobah yake so.

Babi na 2, sakin layi na 18

 8 YANKAN ZUMUNCI

Idan wani ya yi zunubi mai tsanani kuma ya ƙi ya tuba, amma ya ci gaba da aikata abin da Jehobah ba ya so, ba zai ci gaba da zama memban ikilisiya kuma ba. Dole ne a yi masa yankan zumunci. Idan an yi wa mutum yankan zumunci, ba abin da zai sake haɗa mu da shi kuma za mu daina magana da shi. (1 Korintiyawa 5:11; 2 Yohanna 9-11) Yankan zumunci yana taimaka wajen kāre sunan Jehobah da ikilisiya. (1 Korintiyawa 5:6) Yankan zumunci horo ne da zai taimaka wa mai zunubin ya tuba don ya komo ga Jehobah.​—Luka 15:17.

Babi na 3, sakin layi na 19

 9 JA-GORANCI DA UMURNI DA KUMA GARGAƊI

Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana so ya taimaka mana. Shi ya sa yake amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma mutane da suke ƙaunar sa don ya mana ja-goranci da ba mu umurni da kuma gargaɗi. Tun da yake mu ajizai ne, muna bukatar taimakon nan sosai. (Irmiya 17:9) Idan muka saurari waɗanda Jehobah yake amfani da su don ya ba mu gargaɗi, hakan zai nuna cewa muna daraja shi kuma muna so mu yi masa biyayya.​—Ibraniyawa 13:7.

Babi na 4, sakin layi na 2

 10 GIRMAN KAI DA SAUƘIN KAI

Da yake mu masu kasawa ne, yana da sauƙi mu zama masu son kai ko kuma girman kai. Amma Jehobah yana so mu zama masu sauƙin kai. Idan muka yi la’akari cewa mu ba kome ba ne idan aka kwatanta mu da Allah, hakan zai sa mu kasance da sauƙin kai. (Ayuba 38:​1-4) Wani abu kuma da zai sa mu zama da sauƙin kai shi ne, mu mai da hankali ga mutane da kuma abin da zai amfane su, ba kanmu ba. Girman kai yakan sa mutum ya ɗauki kansa fiye da kowa. Mutumin da yake da sauƙin kai yakan bincika kansa don ya san iyawarsa da kasawarsa. Ba ya jin tsoron amincewa da kuskurensa. Ba ya jin kunyar neman gafara kuma yakan amince da shawara ko gargaɗin da aka ba shi. Mutum mai sauƙin kai yakan dogara ga Jehobah kuma yakan bi umurninsa.​—1 Bitrus 5:5.

Babi na 4, sakin layi na 4

 11 IKO

Wanda yake da iko shi yake ba da umurni kuma shi yake yanke shawara. Jehobah ne yake da iko fiye da kowa a sama da ƙasa domin shi ne ya halicci kome da kome. A kullum yana yin amfani da ikonsa don mutane su amfana. Jehobah ya ba wasu hakkin kula da mu. Alal misali, iyaye da dattawan ikilisiya da kuma hukumomin gwamnati suna da iko kuma Jehobah yana so mu yi musu biyayya. (Romawa 13:​1-5; 1 Timoti 5:17) Amma, idan ’yan Adam suka ce mu yi abin da Jehobah ba ya so, ba za mu yarda mu yi hakan ba. (Ayyukan Manzanni 5:29) Idan muka yi biyayya ga waɗanda Jehobah ya ba su hakkin kula da mu, muna yin biyayya ga Jehobah ke nan.

Babi na 4, sakin layi na 7

 12 DATTAWA

Dattawa ’yan’uwa maza ne da suka ƙware, kuma Jehobah ya ba su hakkin kula da ikilisiya. (Maimaitawar Shari’a 1:13; Ayyukan Manzanni 20:28) Waɗannan ’yan’uwan suna taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma mu riƙa bauta masa a hanyar da ta dace. (1 Korintiyawa 14:​33, 40) Kafin ɗan’uwa ya cancanci yin hidima a matsayin dattijo, dole ya nuna wasu halaye da ke Littafi Mai Tsarki. (1 Timoti 3:​1-7; Titus 1:​5-9; 1 Bitrus 5:​2, 3) Mun yarda da ƙungiyar Jehobah kuma muna goyon bayanta, shi ya sa muke yi wa dattawa biyayya.​—Zabura 138:6; Ibraniyawa 13:17.

Babi na 4, sakin layi na 8

 13 MAIGIDA

Jehobah ya ba wa iyaye hakkin kula da yaransu har da iyalin gabaki ɗaya. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce miji shi ne wanda zai riƙa yi wa iyalinsa ja-gora. Idan ba uba, uwa za ta zama mai ja-gora a iyalin. Hakkin mai kula da iyalin shi ne ya tanadar da abinci da sutura da kuma gida wa iyalin. Ban da haka ma, maigidan shi ne zai ja-goranci iyalinsa a ibadarsu ga Jehobah. Alal misali, maigidan zai yi ƙoƙari ya ga cewa suna halartan taro a kullum da zuwa wa’azi da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Ƙari ga haka, maigidan shi yake da hakkin yanke shawara. A kullum yana koyi da Yesu ta yin alheri da nuna sanin-ya-kamata, ba ya ma iyalinsa tsawa ko ya wulaƙanta su. Hakan yana sa iyalin su ji daɗi kuma su ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah.

Babi na 4 sakin layi na 12

 14 HUKUMAR DA KE KULA DA AYYUKAN SHAIDUN JEHOBAH

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah shafaffun Kiristoci ne da Allah yake amfani da su don su ja-goranci aikin da mutanensa suke yi. A ƙarni na farko, Jehobah ya yi amfani da shafaffun Kiristoci don su ja-goranci ibada da wa’azi a lokacin. (Ayyukan Manzanni 15:2) A yau, Jehobah yana amfani da Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah don ya ja-goranci mutanensa, ya ba su umurni kuma ya kāre su. Idan hukumar tana so ta yanke wata shawara, tana bin ja-gorancin Littafi Mai Tsarki da kuma ruhu mai tsarki. Yesu ya kira wannan rukunin shafaffun Kiristocin “bawan nan mai aminci, mai hikima.”​—Matiyu 24:​45-47.

Babi na 4, sakin layi na 15

 15 ƊAURA ƊANKWALI

A wasu lokuta, ’yar’uwa takan iya yin wasu ayyukan da ya kamata ’yan’uwa maza su yi. Sa’ad da take waɗannan ayyukan, zai dace ta ɗaura ɗankwali don ta nuna cewa tana daraja tsarin Allah. Amma ba a kowane yanayi ba ne za ta riƙa ɗaura ɗankwali. Alal misali, za ta ɗaura ɗankwali idan tana nazari kuma maigidanta ko wani ɗan’uwa da ya yi baftisma yana wurin.​—1 Korintiyawa 11:​11-15.

Babi na 4, sakin layi na 17

 16 ƘIN SAKA HANNU A HARKOKIN DUNIYA

Tun da ba ruwanmu da harkokin duniya, ba za mu saka hannu a siyasa ba. (Yohanna 17:16) Bayin Jehobah suna goyon bayan Mulkinsa ne kaɗai. Kamar Yesu, ba ma saka hannu a harkokin duniya.

Duk da haka, Jehobah ya umurce mu mu ‘miƙa kanmu ga shugabanni da kuma masu mulki.’ (Titus 3:​1, 2; Romawa 13:​1-7) Amma dokar Allah ta kuma ce kada mu kashe mutum. Don haka, zuciyar Kirista ba za ta bar shi ya je yaƙi ba. Amma idan aka ce wa Kirista ya yi wani aikin da bai shafi yaƙi kai tsaye ba, dole ne ya yi tunani ko zuciyarsa ba za ta dame shi ba idan ya yi hakan.

Jehobah ne kaɗai muke bauta wa domin shi ya halicce mu. Ko da yake muna daraja tutar ƙasa da tambarin ƙasa da dai sauran su, ba ma tsara wa tutar ƙasa ko rera taken ƙasa. (Ishaya 43:11; Daniyel 3:​1-30; 1 Korintiyawa 10:14) Ƙari ga haka, kowane bawan Jehobah ne yake yanke shawarar ƙin zaɓe. Domin sun riga sun zaɓi Mulkin Allah.​—Matiyu 22:21; Yohanna 15:19; 18:36.

Babi na 5, sakin layi na 2

 17 HALAYEN MUTANEN DUNIYA

Mutanen duniya suna ɗaukaka tunani da kuma halayen Shaiɗan. Waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah da dokokinsa ne suke yin irin wannan tunani da halayen. (1 Yohanna 5:19) Ana kiran wannan tunanin da kuma halayen ruhun duniya. (Afisawa 2:2) Bayin Jehobah suna iya ƙoƙarinsu don kada su kasance da waɗannan halayen. (Afisawa 6:​10-18) Suna son irin rayuwar da Jehobah yake so kuma suna iya ƙoƙarinsu don su yi koyi da shi.

Babi na 5, sakin layi na 7

 18 RIDDA

Ridda tana nufin yin gāba da ainihin koyarwar Littafi Mai Tsarki. ’Yan ridda suna daina yin biyayya ga Jehobah da kuma Yesu, Sarkin Mulkin Allah, kuma suna rinjayar mutane su yi hakan. (Romawa 1:25) Niyyar su ita ce su sa waɗanda suke bauta wa Jehobah su soma shakka a zuciyarsu. A ƙarni na farko, wasu Kiristoci sun zama ’yan ridda, haka ma a yau. (2 Tasalonikawa 2:3) Waɗanda suke ƙaunar Jehobah ba sa tarayya da ’yan ridda. Kada mu bar son jin ƙwaƙwaf ko kuma matsi daga mutane su sa mu karanta ko mu saurari abin da ’yan ridda suke yaɗawa. Mu riƙe amincinmu ga Jehobah kuma mu bauta masa shi kaɗai.

Babi na 5, sakin layi na 9

 19 ƊAUKAR ALHAKIN ZUNUBI

Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta dokaci Isra’ilawa su nemi gafarar Jehobah don zunubansu. Suna kawo hadayar dabbobi ko hatsi ko māi zuwa haikali. Hakan yana tuna wa Isra’ilawan cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta musu zunubansu. Amma bayan Yesu ya ba da hadayar ransa don zunubanmu, an daina hadayar dabbobi kuma. Yesu ya ba da hadayar “sau ɗaya tak ba ƙari.”​—Ibraniyawa 10:​1, 4, 10.

Babi na 7, sakin layi na 6

 20 DARAJA DABBOBI

Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta amince mutane su ci nama. Ƙari ga haka, ta dokaci mutane su yi amfani da dabbobi wajen miƙa hadaya. (Littafin Firistoci 1:​5, 6) Amma Jehobah ba ya so mutane su riƙa cin zalin dabbobi. (Karin Magana 12:10) A cikin Dokar, akwai umurnin da aka bayar da ya kāre dabbobi. An dokaci Isra’ilawan da su riƙa kula da dabbobinsu.​—Maimaitawar Shari’a 22:​6, 7.

Babi na 7, sakin layi na 6

 21 ƘANANAN SASSAN JINI DA KUMA HANYOYIN JINYA

Ƙananan sassan jini. Jini yana da sashe guda huɗu, wato jajayen jini da fararen jini da kamewar jini da kuma ruwan jini (red cells da white cells da platelets da kuma plasma). Ana rarraba waɗannan sashe huɗu na jini zuwa ƙananan sassa. *

Kiristoci ba sa karɓan jini gabaki ɗaya ko kuma waɗannan sashe guda huɗu. Amma za su iya amincewa da ƙananan sassa na jini? Littafi Mai Tsarki bai ba da takamaiman doka game da hakan ba. Don haka, kowane Kirista ne yake da hakkin yanke shawara ko zai amince da hakan ko a’a.

Zuciyar wasu Kiristoci ba za ta amince musu su yi jinyar da ta ƙunshi jini ba ko da ƙananan sassan jinin ne. Mai yiwuwa dalilinsu shi ne, Dokar Allah ta bukaci Isra’ilawa da su “zubar” da jinin dabba “a ƙasa.”​—Maimaitawar Shari’a 12:​22-24.

Amma zuciyar wasu za ta amince musu su yi jinyar da ta ƙunshi ƙananan sassa na jini. Suna iya cewa ƙananan sassan jinin ba sa wakiltar ran mutumin.

Sa’ad da kake tunani a kan shawarar da za ka yanke game da ƙananan sassa na jini, ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  • Na san cewa idan nan ƙi dukan sassa na jini hakan na nufin cewa ba zan amince da wasu magunguna da suke yaƙar cuta ko kuma suke hana jini zuba?

  • Ta yaya zan bayyana ma likita dalilin da ya sa na amince da ɗaya ko biyu daga cikin ƙananan sassa na jini, ko kuma dalilin da ya sa na ƙi amincewa da dukansu?

Hanyoyin jinya. Mu Kiristoci ba ma ba da jininmu ko kuma mu adana jininmu na ’yan makonni kafin a mana tiyata, a kuma mayar da shi bayan an gama. Amma, akwai wasu jinya da ake yi da jinin mara lafiya. Kowane Kirista ne zai zaɓi yadda za a yi amfani da jininsa sa’ad da ake masa tiyata ko sa’ad da ake masa gwaje-gwaje ko sa’ad da ake masa wata jinya. Sa’ad da ake irin wannan jinyar, akan cire jinin mara lafiyar gabaki ɗaya a ajiye a gefe.​—Don ƙarin bayani, ka bincika Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2000, shafi na 30-31.

Alal misali, akwai wata jinya da ake kira hemodilution. A irin wannan jinyar, kafin a yi wa mutum tiyata, za a cire dukan jininsa nan da nan a ajiye a wani waje, sai a sa masa wani abu da zai maye gurbin jinin a jikinsa. Kafin a gama tiyatar ko bayan an gama tiyatar, sai a maido masa da jininsa.

Wata jinya kuma ita ce cell salvage. A wannan jinyar, za a tsabtace jinin da ya fita daga jikin mara lafiya sa’ad da ake masa tiyata kuma a maida shi jikinsa sa’ad da ake tiyatar ko kuma bayan an gama tiyatar.

Likitoci suna iya yin wannan jinyar ta hanyoyi dabam-dabam. Don haka, kafin ka amince da wata tiyata ko gwaji ko jinya, ka tabbata cewa ka san yadda likitan yake so ya yi amfani da jininka.

Sa’ad da kake so ka yanke shawara a kan wata jinya da za a yi amfani da jininka, ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  • Idan aka janye jinina kuma aka adana shi na ɗan lokaci, shin zuciyata za ta amince na sake karɓa maimakon a “zubar a ƙasa”?​—Maimaitawar Shari’a 12:​23, 24.

  • Shin zuciyata za ta dame ni idan na amince da wata irin jinya da za a janye jinina, a tsabtace shi kuma a sake mayar min?

  • Shin na san cewa idan na ƙi amincewa da kowace irin jinyar da ta ƙunshi jinina, hakan yana nufin cewa ba zan amince a min gwajin jini ko hemodialysis kuma ba za a saka min mashin da yake aiki a madadin zuciya da huhu ba?

Zai dace mu yi addu’a da bincike sosai kafin mu tsai da shawarar irin ƙananan sassan jini da za mu amince da su da kuma irin jinyar da ta ƙunshi jininmu da za a mana. (Yaƙub 1:​5, 6) Bayan haka, wajibi ne mu yi amfani da zuciyarmu da muka shirya da Kalmar Allah wajen yanke shawarar. Kada mu tambayi mutane abin da za su yi idan suna cikin yanayinmu kuma kada mu bar mutane su gaya mana abin da za mu yi.​—Romawa 14:12; Galatiyawa 6:5.

Babi na 7, sakin layi na 11

 22 HALAYE MASU KYAU

Kasancewa da halaye masu kyau yana nufin mu kasance da halayen da Jehobah yake so. Kuma hakan yana nufin mu riƙa tunani da magana da kuma abubuwa yadda Jehobah yake so. Jehobah ya ce mu guji duk wani irin halin da ya ƙunshi lalata. (Karin Magana 1:10; 3:1) Wajibi ne mu kuɗiri niyyar yi wa Jehobah biyayya kafin mu sami kanmu a yanayin da zai sa mu yi abin da bai dace ba. Mu riƙa yin addu’a ga Jehobah ya taimaka mana mu riƙa tunanin da ya dace. Kuma dole ne mu guji duk wani abin da zai sa mu yi lalata.​—1 Korintiyawa 6:​9, 10, 18; Afisawa 5:5.

Babi na 8, sakin layi na 11

 23 RASHIN ƊA’A DA ƘAZANTA

Rashin ɗa’a ya ƙunshi yin magana ko abubuwan da suka taka dokar Allah ba tare da jin kunya ba. Mutumin da yake yin hakan ba ya daraja dokokin Allah. Idan Kirista ya kasance da rashin ɗa’a, za a kafa masa kwamitin shari’a. Ƙazanta ta ƙunshi abubuwa da yawa marasa kyau. Idan wani ya soma nuna halin ƙazanta, za a iya kafa masa kwamitin shari’a, amma ya dangana ga yanayin da hakan ya faru.​—Galatiyawa 5:​19-21; Afisawa 4:19; don samun ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga watan Yuli, 2006.

Babi na 9, sakin layi na 7; Babi na 12, sakin layi na 10

 24 TATTAƁA AL’AURA

Jima’i abu mai tsabta ne da Jehobah ya tsara don ma’aurata kaɗai su nuna yadda suke son juna. Amma idan mutum yana tattaɓa al’aurarsa don ya gamsar da sha’awarsa ta jima’i, hakan yana nuna cewa bai da ra’ayin Jehobah game da jima’i. Wannan halin zai ɓata dangantakarsa da Jehobah. Hakan zai sa mutumin yawan sha’awa kuma ya kasance da ra’ayin da bai dace ba game da jima’i. (Kolosiyawa 3:5) Idan wani yana da irin wannan halin kuma ya kasa dainawa, kar ya fid da rai. (Zabura 86:5; 1 Yohanna 3:20) Me za ka yi idan kana fama da hakan? Ka yi addu’a kuma ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Zai dace ka guji kallon batsa tun da yake batsar ce take sa ka soma tunanin lalata. Ƙari ga haka, zai dace ka gaya ma iyayenka ko wani abokinka da ya manyanta wanda yake ƙaunar Jehobah matsalar da kake da ita. (Karin Magana 1:​8, 9; 1 Tasalonikawa 5:14; Titus 2:​3-5) Babu shakka, Jehobah yana ganin bangaskiyarka da ƙoƙarin da kake yi don ka kasance da hali mai kyau.​—Zabura 51:17; Ishaya 1:18.

Babi na 9, sakin layi na 9

 25 AUREN MATA DA YAWA

Jehobah ya tsara aure tsakanin miji ɗaya da mace ɗaya. A zamanin Isra’ilawa, Allah ya ƙyale mutane su auri fiye da mace ɗaya, amma ba haka ba ne Allah ya tsara aure tun farko. A yau, Jehobah ba ya so bayinsa su auri mata da yawa. Ya kamata miji ya kasance da mata ɗaya, mata kuma ta kasance da miji ɗaya.​—Matiyu 19:9; 1 Timoti 3:2.

Babi na 10, sakin layi na 12

 26 RABUWA DA KASHE AURE

Nufin Jehobah shi ne mata da miji su zauna tare ba rabuwa har iya rayuwarsu. (Farawa 2:24; Malakai 2:​15, 16; Matiyu 19:​3-6; 1 Korintiyawa 7:39) Amma za su iya kashe aurensu idan ɗaya a cikinsu ya yi zina. A wannan yanayin, Jehobah ya ba wa mara laifin damar kashe auren.​—Matiyu 19:9.

Amma a wasu lokuta, wasu za su iya rabu da juna ko da yake ba wani cikinsu da ya yi zina. (1 Korintiyawa 7:11) Ga wasu dalilai a gaba da za su iya sa ma’aurata su rabu da juna.

  • Idan maigida ya ƙi kula da iyalinsa da gangan, yana barin su ba kuɗi ko abinci.​—1 Timoti 5:8.

  • Idan mijin yana cin zalin matarsa ko matar tana cin zalin mijinta kuma hakan ya sa ran mijin ko matar cikin hadari.​—Galatiyawa 5:​19-21.

  • Idan mace tana hana mijinta ko mijin yana hana matarsa bauta wa Jehobah.​—Ayyukan Manzanni 5:29.

Babi na 11, sakin layi na 19

 27 YABO DA KUMA ƘARFAFA

Dukanmu muna so a yaba mana kuma a ƙarfafa mu. (Karin Magana 12:25; 16:24) Muna iya ƙarfafa da kuma ta’azantar da juna da kalmomi masu daɗi. Irin waɗannan kalaman za su taimaka wa ’yan’uwanmu su jimre kuma su ci gaba da bauta ma Jehobah duk da matsalolin rayuwa. (Karin Magana 12:18; Filibiyawa 2:​1-4) Idan wani yana sanyin gwiwa, zai dace mu saurare shi sosai kuma mu yi ƙoƙari mu fahimci yadda yake ji. Hakan zai taimaka mana mu san abin da za mu faɗa ko yadda za mu iya taimaka masa. (Yaƙub 1:19) Mu yi ƙoƙari mu san ’yan’uwanmu da kyau don mu san bukatunsu. Idan muka san wuraren da suke bukatar taimako, za mu nuna musu inda za su sami ta’aziya da ƙarfafa daga Allah.​—2 Korintiyawa 1:​3, 4; 1 Tasalonikawa 5:11.

Babi na 12, sakin layi na 16

 28 ƊAURIN AURE

Littafi Mai Tsarki bai ba da takamammun dokoki game da yadda ɗaurin aure zai kasance ba. Yadda mutane suke ɗaura aure da kuma abubuwan da hukuma take bukata su yi sun bambanta. (Farawa 24:67; Matiyu 1:24; 25:10; Luka 14:8) Amma abin da ya fi muhimmanci a ɗaurin aure shi ne alkawarin da ma’auratan za su yi a gaban Jehobah. Wasu ma’aurata suna so iyayensu da kuma abokansu su zo su shaida sa’ad da suke yin alkawari, kuma su gaya wa wani dattijo ya ba da jawabi ranar auren. Ma’auratan ne za su zaɓi irin liyafar da za su yi bayan an ɗaura auren. (Luka 14:28; Yohanna 2:​1-11) Duk shawarar da ma’auratan za su yanke game da ranar aurensu, su tabbata cewa hakan zai ɗaukaka Jehobah. (Farawa 2:​18-24; Matiyu 19:​5, 6) Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka musu su yanke shawarar da ta dace. (1 Yohanna 2:​16, 17) Idan za a ba da giya a wurin liyafar, su tabbata cewa akwai wanda zai riƙa lura da hakan. (Karin Magana 20:1; Afisawa 5:18) Idan za a saka waƙa ko za a yi wani nishaɗi, su tabbata cewa abubuwan za su ɗaukaka Jehobah. Zai dace ma’aurata su fi mai da hankali ga dangantakarsu da Jehobah da kuma junansu, maimakon ranar auren kawai.​—Karin Magana 18:22; don samun ƙarin bayani, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga watan Oktoba, 2006, shafi na 18-31.

Babi na 13, sakin layi na 18

 29 YANKE SHAWARA MAI KYAU

Muna so mu riƙa yanke shawarar da ta dace bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, mijin wata Kirista ko matar wani Kirista da ba Mashaidiya ba za ta iya gayyatar sa zuwa wata liyafa da iyalinta suka shirya a lokacin wani bikin da Kiristoci ba sa yi. Idan kai ne, me za ka yi? Za ka iya zuwa idan zuciyarka ba za ta dame ka ba, kuma za ka gaya wa matarka cewa idan za a yi wani abu a liyafar da ke da alaƙa da bautar ƙarya, ba za ka yi abin ba. Ƙari ga haka, ya kamata ka yi tunani a kan ko zuwa liyafar zai sa ’yan’uwa su yi tuntuɓe.​—1 Korintiyawa 8:9; 10:​23, 24.

Ko kuma, a ce wanda kake wa aiki ya ba ka kyautar kuɗi a lokacin wani biki da ke da alaƙa da bautar ƙarya. Za ka amince da kuɗin? Wataƙila. Abin da zai taimaka maka ka san ko ya dace ka karɓi kuɗin ko a’a shi ne dalilin da ya sa ya ba ka kyautar. Shin ya ba ka kuɗin ne don bikin da ake yi? Ko kuwa don ya nuna godiyarsa? Yin tunani game da hakan da kuma wasu abubuwa za su taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace.

Ga wani misali kuma, a ce wani ya ba ka kyauta a ranar wani biki kuma ya ce: “Na san cewa ba ka yin bikin nan, amma ina so in ba ka kyautar nan.” Wataƙila mutumin yana so ya yi maka alheri ne kawai. Amma kana ganin mutumin yana so ya jarraba ka ne ko kuma ya sa ka yin bikin? Bayan ka yi tunani a kan hakan, za ka iya zaɓan ko ka karɓi kyautar ko a’a. Muna so mu kasance da zuciya mai kyau da kuma aminci ga Jehobah sa’ad da muke yanke kowace irin shawara.​—Ayyukan Manzanni 23:1.

Babi na 13, sakin layi na 22

 30 KASUWANCI DA BATUN DA YA SHAFI KOTU

A yawancin lokaci, idan aka sasanta matsala da wuri kuma cikin lumana, matsalar ba za ta zama babba ba. (Matiyu 5:​23-26) Abin da ya kamata ya fi muhimmanci ga dukan Kiristoci shi ne ɗaukaka Jehobah kuma su sa a kasance da haɗin kai a ikilisiya.​—Yohanna 13:​34, 35; 1 Korintiyawa 13:​4, 5.

Idan ’yan’uwa suna kasuwanci tare kuma suka samu saɓani, su yi ƙoƙari su sasanta hakan ba tare da sun je kotu ba. Manzo Bulus ya gargaɗe mu game da kai ’yan’uwanmu kotu a 1 Korintiyawa 6:​1-8. Idan muka kai ’yan’uwanmu kotu, hakan zai ɓata sunan Jehobah da kuma ikilisiya. Littafin Matiyu 18:​15-17 suna ɗauke da matakai guda uku da Kiristoci za su ɗauka don su sasanta matsala kamar ɓata suna ko cuci. (1) Da farko, su sasanta matsalar da kansu. (2) Idan sun gagara yin hakan, su gaya ma Kirista da ya manyanta guda ɗaya ko biyu su sasanta su. (3) Idan an gagara sasanta su, su gaya wa dattawa su sasanta matsalar. Dattawa za su yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su taimaka wa ’yan’uwan su sasanta matsalar da ke tsakaninsu. Idan wani a cikinsu ya ƙi bin taimakon dattawan, dattawan za su iya kafa wa mutumin kwamitin shari’a.

Abubuwan da za su iya sa Kirista ya je kotu su ne, kashe aure, ɗaukan hakkin renon yaro, ba da kuɗin tallafi don kula da yara, biyan kuɗin inshora, ko in wani ya cinye masa kuɗin jari da kuma batun wasiyya. Idan mutum ya je kotu don ya sasanta irin matsalar nan cikin lumana, bai taka gargaɗin da Bulus ya bayar ba.

Idan wani mummunar abu ne ya faru kamar fyaɗe ko cin zarafin yara, ko babban sata ko kisa, Kirista zai iya kai ƙara ga hukuma. Idan ya yi hakan, bai taka umurnin da Bulus ya bayar ba.

Babi na 14, sakin layi na 14

 31 DABARUN SHAIƊAN

Tun daga lambun Adnin, Shaiɗan ya ci gaba da yaudarar mutane. (Farawa 3:​1-6; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9) Ya san cewa idan ya lalata tunaninmu, hakan zai iya sa mu yi abu mara kyau. (2 Korintiyawa 4:4; Yaƙub 1:​14, 15) Yana amfani da siyasa da addini da kuɗi da nishaɗi da ilimi da kuma abubuwa da yawa don ya sa mu kasance da halaye marasa kyau irin nasa.​—Yohanna 14:30; 1 Yohanna 5:19.

Shaiɗan ya san cewa lokacinsa ya kusan ƙarewa. Don haka, yana yin iya ƙoƙarinsa don ya yaudari mutane da yawa. Amma ya fi mai da hankali ga waɗanda suke bauta wa Jehobah. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:12) Idan ba mu mai da hankali ba, Iblis zai lalata tunaninmu. (1 Korintiyawa 10:12) Alal misali, Jehobah yana so ma’aurata su kasance tare har iya rayuwarsu. (Matiyu 19:​5, 6, 9) Amma mutane a yau ba sa ɗaukan aure da daraja, suna ganin za su iya raba aure a kowane lokaci. Fina-finai da yawa da kuma shirin talabijin ma suna ɗaukaka wannan ra’ayin. Muna bukatar mu guji wannan ra’ayin.

Wata hanya kuma da Shaiɗan yake amfani da ita, ita ce, son cin gashin kanmu. (2 Timoti 3:4) Idan ba mu yi hankali ba, za mu soma ƙin bin ja-gorancin mutane da Jehobah ya naɗa. Alal misali, wani ɗan’uwa zai iya soma ƙin amincewa da shawarar dattawa. (Ibraniyawa 12:5) Ko kuma ’yar’uwa ta soma ƙin amincewa da tsarin da Jehobah ya kafa na shugabanci a cikin iyali.​—1 Korintiyawa 11:3.

Muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don kada Shaiɗan ya lalata tunaninmu. Maimakon haka, mu kasance da ra’ayi irin na Jehobah kuma mu mai da hankali ga “abubuwan da suke na sama.”​—Kolosiyawa 3:2; 2 Korintiyawa 2:11.

Babi na 16, sakin layi na 9

 32 JINYA

Dukanmu muna so mu kasance da ƙoshin lafiya, kuma idan ba mu da lafiya, muna so a mana jinya mai kyau. (Ishaya 38:21; Markus 5:​25, 26; Luka 10:34) A yau, akwai jinya dabam-dabam da likitoci suke yi wa mutane. Don haka, yana da muhimmanci mu bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke tunani a kan jinyar da za mu yi. Mu tuna cewa a Mulkin Allah ne kawai za a iya warkar da mu gabaki ɗaya. Bai kamata mu mai da hankali ga lafiyar jikinmu fiye da ibadarmu ga Jehobah ba.​—Ishaya 33:24; 1 Timoti 4:16.

Wajibi ne mu guji duk wata jinya da take da alaƙa da aljanu. (Maimaitawar Shari’a 18:​10-12; Ishaya 1:13) Don haka, kafin mu amince da wata jinya, muna bukatar mu nemi isashen bayani game da jinyar. (Karin Magana 14:15) Kada mu manta cewa Shaiɗan yana so ya yaudare mu don mu soma sha’ani da aljanu. Idan muna ganin cewa wata jinya tana da alaƙa da aljanu, zai fi kyau mu ƙi amincewa da jinyar.​—1 Bitrus 5:8.

Babi na 16, sakin layi na 18

^ sakin layi na 98 A ganin wasu likitoci sashe huɗu na jini ɗaya ne da ƙananan sassan jini. Saboda haka, idan ka tsai da shawara cewa ba za ka karɓi jini gabaki ɗaya ko kuma sashe huɗu na jini ba, wato jajayen jini da fararen jini da kamewar jini da kuma ruwan jini, ka bayyana hakan ga likitan.