Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 1

Kaunar da Ke Tsakaninmu da Allah Za Ta Kasance Har Abada

Kaunar da Ke Tsakaninmu da Allah Za Ta Kasance Har Abada

“Gama ƙaunarmu ga Allah ita ce, mu kiyaye umarnansa [ko dokokinsa], kuma umarnansa ba su da nauyi.”​—1 YOHANNA 5:3.

1, 2. Me ya sa kake ƙaunar Jehobah?

KANA ƙaunar Allah? Wataƙila kana ƙaunar sa sosai shi ya sa ka yi masa alkawari cewa za ka bauta masa. Kana iya ɗaukan sa a matsayin Amininka. Amma Jehobah yana ƙaunar ka tun kafin ka fara ƙaunar sa. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Muna ƙauna gama Allah ne ya fara ƙaunar mu.’​—1 Yohanna 4:19.

2 Ka yi tunanin abubuwa da yawa da Jehobah ya yi da suka nuna cewa yana ƙaunar mu. Ya ba mu duniya don mu yi rayuwa a cikinta da kuma abubuwan da za su sa mu ji daɗin rayuwa. (Matiyu 5:​43-48; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Yana son mu zama aminansa kuma ya yi tanadin da zai sa mu koya abubuwa game da shi. Ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki ne muke saurarar Jehobah. Shi kuma yana saurarar mu sa’ad da muka yi addu’a gare shi. (Zabura 65:2) Yana kāre mu da kuma ba mu ƙarfi ta wurin ruhunsa mai tsarki. (Luka 11:13) Fiye da haka ma, ya turo Ɗansa zuwa duniya don ya cece mu daga zunubi da kuma mutuwa.​—Karanta Yohanna 3:16; Romawa 5:8.

3. Ta yaya za mu ci gaba da zama abokan Jehobah?

3 Ka ɗan yi tunani game da wani amininka wanda bai bar ka ba ko cikin daɗi ko cikin wahala. Babu shakka, kun yi ƙoƙari sosai kafin abokantakarku ta yi ƙarfi. Haka abokantakarmu da Jehobah take, ta fi duk wani aminin da za mu iya samuwa. Zai yiwu mu ci gaba da zama aminan Allah har abada. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kiyaye kanku cikin ƙaunar Allah.” (Yahuda 21) Ta yaya za mu iya yin hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama ƙaunarmu ga Allah ita ce, mu kiyaye umarnansa, kuma umarnansa ba su da nauyi.”​—1 Yohanna 5:3.

“ƘAUNARMU GA ALLAH”

4, 5. Ta yaya ka soma ƙaunar Jehobah?

4 Manzo Yohanna ya rubuta game da ƙaunar da muke wa Allah. Shin ka tuna sa’ad da ka fara ƙaunar Allah?

Sa’ad da ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, ka nuna cewa kana ƙaunarsa kuma za ka riƙa yi masa biyayya har abada

5 Za ka iya tuna yadda ka ji sa’ad da ka koya cewa Jehobah yana son ka yi rayuwa har abada a sabuwar duniya? Ka riga ka san dukan abubuwan da Jehobah ya yi don ya cim ma hakan. Kuma ka san game da kyauta mafi daraja da Allah ya ba mu, wato Ɗansa da ya aiko duniya. (Matiyu 20:28; Yohanna 8:29; Romawa 5:​12, 18) Da ka fahimci yadda Jehobah yake ƙaunar ka, sai hakan ya sa ka soma ƙaunar sa.​—Karanta 1 Yohanna 4:​9, 10.

6. Idan kana ƙaunar abokinka, mene ne za ka yi? Waɗanne abubuwa ne ka yi domin kana ƙaunar Jehobah?

6 Amma ƙaunar da kake yi wa Allah yanzu, soma taɓi ne. Idan kana da abokin da kake so sosai, ba za ka riƙa ce masa kawai kana ƙaunar sa ba. Amma za ka riƙa yin abubuwan da za su faranta masa rai. Haka nan ma, ƙaunar da kake yi wa Jehobah ne ya sa kake so ka yi abubuwan da za su faranta masa rai. Kuma yayin da ƙaunar ta ci gaba da girma, mai yiwuwa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma. Ta yin hakan, ka yi wa Jehobah alkawari cewa za ka bauta masa har abada. (Karanta Romawa 14:​7, 8.) Mene ne zai taimaka maka ka cika wannan alkawarin?

“MU KIYAYE UMARNANSA”

7. Mene ne za mu yi idan muna ƙaunar Jehobah? Ka ambata wasu dokokin Jehobah.

7 Muna ƙaunar Jehobah, shi ya sa muke “kiyaye umarnansa.” Ta yaya muke yin hakan? Ta wurin yi masa biyayya. A cikin Littafi Mai Tsarki, mun koyi yadda Jehobah yake so mu yi rayuwa. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce mu guji buguwa, kuma ya ce kada mu yi sata ko ƙarya. Ƙari ga haka, ya ce kada mu yi jima’i da wanda ba mijinmu ko matarmu ba, kuma ya ce Jehobah ne kaɗai za mu bauta masa.​—1 Korintiyawa 5:11; 6:18; 10:14; Afisawa 4:28; Kolosiyawa 3:9.

8, 9. Ta yaya za mu san ra’ayin Jehobah a kan wani abin da Littafi Mai Tsarki bai ba da doka a kai ba? Ka ba da misali.

8 Amma don mu faranta ma Jehobah rai, muna bukatar mu yi wasu abubuwa ba bin umurninsa kawai ba. Bai kafa mana dokoki a kan kome da muke yi a rayuwa ba. Don haka, akwai wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki bai hana yin su kai tsaye ba. A irin wannan yanayin, mene ne za mu yi? (Afisawa 5:17) A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai ƙa’idodin da suke bayyana mana ra’ayin Jehobah game da wasu abubuwa. Idan muka ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki, za mu san Jehobah sosai. Za mu san ra’ayinsa, wato abin da yake so da kuma abin da ba ya so.​—Karanta Zabura 97:10; Karin Magana 6:​16-19; ka duba Ƙarin Bayani na 1.

9 Alal misali, ta yaya za mu san abubuwan da ya kamata mu kalla a talabijin ko kuma intane? Jehobah bai kafa mana doka a kan abin da za mu kalla ba. Amma ƙa’idodin da ke Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu san irin abubuwan da ya kamata mu kalla ko mu karanta. A yau, yawancin fina-finan da ake kallo game da mugunta ne da kuma lalata. A Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya gaya mana cewa “yakan ƙi mai son tā da hankali,” kuma “zai hukunta masu yin zina da masu yin lalata.” (Zabura 11:5; Ibraniyawa 13:4) Ta yaya waɗannan ƙa’idodin za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau? Ya kamata mu guji duk wani abin da muka san cewa Jehobah ba ya so.

10, 11. Me ya sa muke yi wa Jehobah biyayya?

10 Me ya sa muke wa Jehobah biyayya? Ba ma yin hakan don muna so mu guji matsalolin da rashin biyayya yake kawowa. (Galatiyawa 6:7) Amma muna ƙaunar Jehobah shi ya sa muke yi masa biyayya. Kamar yadda yara suke so su faranta wa babansu rai, haka mu ma muna so mu faranta ran Ubanmu na sama, wato Jehobah. Sanin cewa muna faranta ran Jehobah yana sa mu farin ciki sosai!​—Zabura 5:12; Karin Magana 12:2; ka duba Ƙarin Bayani na 2.

11 Ba ma bin dokokin Jehobah don suna da sauƙi ko kuma ya zama dole. Kuma ba ma bin wasu dokoki da ƙa’idodin Allah, amma mu ƙi bin wasu. (Maimaitawar Shari’a 12:32) Maimakon haka, muna masa biyayya da dukan zuciyarmu kamar yadda wani marubucin zabura ya ce: “Umurnanka suna faranta mini rai, gama ina ƙaunar su.” (Zabura 119:47; Romawa 6:17) Ƙari ga haka, muna so mu bi misalin Nuhu, wanda yake ƙaunar Jehobah kuma ya yi duk wani abin da Jehobah ya umurce shi ya yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nuhu kuwa ya yi kome daidai yadda Allah ya umarce shi.” (Farawa 6:22) Shin kana son Jehobah ya yaba maka kamar yadda ya yaba ma Nuhu?

12. Ta yaya za mu faranta ran Jehobah?

12 Yaya Jehobah yake ji sa’ad da muka yi masa biyayya? Muna sa ‘zuciyarsa ta ji daɗi.’ (Karin Magana 11:20; 27:11) Wannan abin ƙarfafa ne sosai cewa muna faranta ran Mahaliccinmu sa’ad da muka yi masa biyayya, ko ba haka ba? Amma ba ya sa mu dole mu yi hakan. A maimakon haka, ya ba mu ’yancin yin zaɓi. Hakan yana nufin cewa muna da ’yancin yin abin da ya dace ko wanda bai dace ba. Jehobah yana so mu riƙa yanke shawarwari masu kyau domin muna ƙaunar sa kuma hakan zai sa mu yi rayuwa mai kyau.​—Maimaitawar Shari’a 30:​15, 16, 19, 20; ka duba Ƙarin Bayani na 3.

“UMARNANSA BA SU DA NAUYI”

13, 14. Ta yaya muka san cewa dokokin Jehobah ba su da wuyar bi? Ka ba da misali.

13 Idan muna ganin cewa dokokin Jehobah suna da wuyar bi ko kuma za su iya hana mu yin amfani da ’yancinmu fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Umarnansa ba su da nauyi.” (1 Yohanna 5:3) A wasu wurare a Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da wannan kalmar nauyi wajen kwatanta dokoki masu wuya ko kuma mutanen da suke so su riƙa iko a kan wasu da kuma ɓata musu rai. (Matiyu 23:4; Ayyukan Manzanni 20:​29, 30) Wani juyin Littafi Mai Tsarki da ake kira New English Translation, ya ce: “Dokokinsa ba sa naƙasar da mu.” Hakika, dokokin Jehobah ba su da “nauyi”, ma’ana ba su da wuyar bi domin ba ya gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu.

14 Alal misali, a ce kana taya abokinka kwashe kaya zuwa sabon gidansa. Ya riga ya saka kayansa cikin akwatuna. Wasu akwatunan ba su da nauyi wasu kuma suna da nauyi da mutum ɗaya ba zai iya ɗauka ba. Shin kana ganin abokinka zai ce ka ɗauki babban akwatin kai kaɗai? A’a! Me ya sa? Domin ba ya son ka ji rauni. Haka Jehobah yake, ba zai sa aminansa su yi wani abin da ya fi ƙarfinsu ba. (Maimaitawar Shari’a 30:​11-14) Jehobah ya san yanayinmu sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya san abin da aka yi mu da shi, yana kuma tuna cewa mu ƙurar ƙasa ne.”​—Zabura 103:14.

15. Me ya sa muka tabbata cewa dokokin Jehobah don amfaninmu ne?

15 Musa ya gaya wa Isra’ilawa cewa idan suka bi dokokin Jehobah za su amfana kuma su yi zaman lafiya. (Maimaitawar Shari’a 5:​28-33; 6:24) Haka ma yake a yau, duk wani abin da Jehobah ya ce mu yi, abin zai amfane mu. (Karanta Ishaya 48:17.) Jehobah Ubanmu, ya san abin da ya dace da mu a koyaushe. (Romawa 11:33) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Hakan ya nuna cewa ƙauna ce take sa Jehobah ya yi kowane abu.

16. Ta yaya muka san cewa za mu iya yin biyayya ko da yake mu ajizai ne kuma muna rayuwa a duniyar Shaiɗan?

16 A wasu lokuta, dokokin Jehobah za su yi mana wuyar bi. Me ya sa? Domin muna rayuwa a muguwar duniya da Shaiɗan yake iko da ita. Yana yaudarar mutane su riƙa yin mugunta. (1 Yohanna 5:19) Kuma da yake mu ajizai ne muna ƙoƙarin daina tunanin banza domin zai iya sa mu taka dokar Allah. (Romawa 7:​21-25) Amma ƙaunar da muke yi wa Jehobah tana taimaka mana mu riƙa yin abin da ya dace. Yana ganin ƙoƙarin da muke yi don mu yi masa biyayya kuma yana taimaka mana da ruhu mai tsarki. (1 Sama’ila 15:​22, 23; Ayyukan Manzanni 5:32) Ruhun Jehobah yana taimaka mana mu koyi halayen da suke sa mu yi masa biyayya.​—Galatiyawa 5:​22, 23.

17, 18. (a) Mene ne za mu koya a wannan littafin? (b) Mene ne za mu tattauna a babi na gaba?

17 A wannan littafin, za mu koyi yadda za mu yi rayuwar da za ta faranta ran Jehobah. Ban da haka, za mu koyi yadda za mu yi amfani da ƙa’idodin Allah kuma mu bi ɗabi’u masu kyau. Kar mu manta cewa Jehobah ba ya sa mu dole mu bauta masa. Idan muka zaɓa mu yi biyayya, za mu yi rayuwa mai kyau yanzu da kuma a nan gaba. Abu mafi muhimmanci shi ne, yin biyayya ga Allah zai nuna irin zurfin ƙaunar da muke masa.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 4.

18 Jehobah ya ba mu zuciya don mu iya sanin abin da ya dace da wanda bai dace ba. Idan muka shirya zuciyarmu da kyau, za ta taimaka mana mu riƙa “kiyaye umurnansa.” To, mece ce zuciya kuma ta yaya za mu shirya ta? Za mu tattauna hakan a babi na gaba.