Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 9

“Ku Guje Wa Halin Lalata!”

“Ku Guje Wa Halin Lalata!”

“Saboda haka, sai ku kashe halin sha’awace-sha’awacen duniya a zuciyarku, wato iskanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa, da mugun hali, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.”​—KOLOSIYAWA 3:5

1, 2. Mene ne Bala’am ya yi don ya yaudari mutanen Jehobah?

WANI mai kamun kifi ya je inda zai iya kama kifin da yake so. Ya saka tāna a ƙugiyarsa kuma ya jefa ta cikin ruwa. Sai ya tsaya yana jira. Da kifin ya soma cin tānar, sai ƙugiyar ta kama shi. Sai mai kamun kifin ya cire ƙugiyar tare da kifin da wuri.

2 Haka ma da mutane, ana iya kama su. Alal misali, da Isra’ilawa suka kai kusa da Ƙasar Alkawari, sun kafa zango a Filayen Mowab. Sai sarkin Mowab ya yi wa Bala’am alkawari cewa zai ba shi kuɗi mai yawa idan ya je ya tsine wa Isra’ilawan. Bala’am ya yi amfani da wata hanyar da za ta sa Isra’ilawan su jawo wa kansu bala’i. Ya sa tarkonsa da kyau don ya kama su. Ya tura matan Mowab su je inda mazajen Isra’ilawa suke don su yaudare su.​—Littafin Ƙidaya 22:​1-7; 31:​15, 16; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:14.

3. Ta yaya tarkon Bala’am ya kama Isra’ilawan?

3 Tarkon Bala’am ya yi aiki kuwa? Ƙwarai kuwa. Dubban Isra’ilawa sun yi ‘lalata da matan Mowab.’ Ban da haka, sun soma bauta wa allolin ƙarya har da allah na lalata da ake kira Ba’al na Feyor. Duk da cewa suna gab da shiga Ƙasar Alkawari, abin da suka aikata ya sa mutane 24,000 suka mutu.​—Littafin Ƙidaya 25:​1-9.

4. Me ya sa dubban Isra’ilawa suka yi lalata?

4 Me ya sa tarkon Bala’am ya kama Isra’ilawan? Domin sun mai da hankali ga sha’awar jikinsu kuma suka manta da dukan abubuwan da Jehobah ya yi musu. Akwai dalilai da yawa da ya kamata ya sa Isra’ilawan su riƙe amincinsu ga Jehobah. Ya ’yantar da su daga bauta a Masar, ya ciyar da su sa’ad da suke cikin jeji kuma ya kāre su har suka iso kusa da Ƙasar Alkawari. (Ibraniyawa 3:12) Duk da haka, sun yi lalata. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: “Kada fa mu shiga halin lalata yadda waɗansu suka yi, har . . . suka mutu.”​—1 Korintiyawa 10:8.

5, 6. Mene ne za mu koya daga abin da ya faru a Filayen Mowab?

5 Nan ba da daɗewa ba, duniya za ta zama aljanna. Don haka, kamar Isra’ilawan, muna gab da shiga Ƙasar Alkawari. (1 Korintiyawa 10:11) Mutane a zamaninmu suna son yin lalata fiye da mutanen Mowab. Kuma wannan halin zai iya shafan bayin Jehobah. Ban da haka ma, wannan tarkon ne Iblis ya fi amfani da shi.​—Littafin Ƙidaya 25:​6, 14; 2 Korintiyawa 2:11; Yahuda 4.

6 Ka tambayi kanka, ‘Shin zan so in ji daɗin rayuwa na ɗan lokaci maimakon in more rayuwa har abada a sabuwar duniya?’ Gwamma ka bi umurnin Jehobah da ya ce: “Ku guje wa halin lalata!”​—1 Korintiyawa 6:18.

MECE CE LALATA?

7, 8. Mece ce lalata? Me ya sa wannan halin ba shi da kyau?

7 Mutane da yawa a yau ba su da kunya kuma suna taka dokar Allah game da jima’i. A Littafi Mai Tsarki, lalata tana nufin jima’i tsakanin mutane biyu da ba su yi aure bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. Kuma hakan ya haɗa da jima’i tsakanin namiji da namiji ko ta mace da tamace ko kuma mutum da dabba. Ƙari ga haka, ta ƙunshi yin zina da tsotsan al’aura da jima’i ta ɗuwawu da kuma tattaɓa al’aurar wani a hanyar da ba ta dace ba. Za mu iya jin kunyar tattauna wannan batun, amma muna bukatar mu fahimci wannan batun dalla-dalla don mu guji yin abin da Jehobah ba ya so.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 23.

8 Littafi Mai Tsarki ya ce idan mutum ya yi lalata kuma ya ƙi ya tuba, za a fitar da shi daga cikin ikilisiya. (1 Korintiyawa 6:9; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 22:15) Ƙari ga haka, mutane ba za su yarda ko daraja wanda yake yin lalata ba. Lalata tana jawo matsaloli da yawa. Tana sa zuciyar mutum ta riƙa damun sa. Tana kuma jawo cikin shege da matsaloli a aure da cututtuka ko kuma mutuwa. (Karanta Galatiyawa 6:​7, 8.) Idan mutum ya yi tunani a kan damuwa da lalata take jawowa, ba zai so ya yi ta ba. Amma a yawancin lokaci, abin da yake sa mutum ya yi lalata shi ne idan yana tunani kawai a kan yadda zai gamsar da sha’awarsa. Abu na farko da ke kai ga yin lalata shi ne batsa.

BATSA CE ABU TA FARKO DA KE KAI GA YIN LALATA

9. Me ya sa batsa take da haɗari sosai?

9 Abin da ya sa ake shirya batsa shi ne don a sa mutane shawarar jima’i. A zamaninmu, ana iya samun batsa a ko’ina, a mujallu da littattafai da waƙoƙi da shirin telibijin da kuma Intane. Mutane da yawa suna cewa batsa ba ta da haɗari, amma gaskiyar ita ce tana da haɗari sosai. Za ta sa mutum ya kasance da jarabar yin jima’i kuma ya soma sha’awoyin da ba su dace ba. Kallon hotuna da bidiyon batsa yakan jawo matsaloli da yawa. Alal misali, zai iya sa mutum ya riƙa tattaɓa al’aurarsa ko ya sami matsala a aurensa ko kuma ya kashe aurensa.​—Romawa 1:​24-27; Afisawa 4:19; ka duba Ƙarin Bayani na 24.

Ya kamata mu yi hankali sa’ad da muke amfani da Intane

10. Ta yaya ƙa’idar da ke Yaƙub 1:​14, 15 za ta taimaka mana mu guje wa lalata?

10 Yana da muhimmanci mu san yadda tarkon yin lalata zai iya kama mu. Ka yi la’akari da gargaɗin da ke littafin Yaƙub 1:​14, 15. Wurin ya ce: “Kowane mutum dai yakan sami jarraba sa’ad da mugun kwaɗayinsa ya ruɗe shi, ya kuma sha kansa. Mugun kwaɗayi kuwa in ya yi ciki yakan haifi zunubi. Zunubi in ya yi girma yakan haifi mutuwa.” Idan ka soma tunanin da bai dace ba, ya kamata ka daina hakan da sauri. Idan ka ga hotuna marasa kyau ba da saninka ba, ka ɗauke fuskarka nan da nan ko ka kashe kwamfutar ko kuma ka canja tashar talabijin ɗin! Kada ka bar sha’awoyin da ba su dace ba su mamaye tunaninka. In ba haka ba, waɗannan sha’awoyin za su yi ƙarfi sosai har ka kasa kame kanka.​—Karanta Matiyu 5:​29, 30, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

11. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana sa’ad da muke fama da tunanin da bai dace ba?

11 Jehobah ya san mu fiye da yadda muke tsammani. Ya san cewa mu ajizai ne. Duk da haka, ya san za mu iya guje wa sha’awoyin da ba su dace ba. Jehobah ya gaya mana: “Saboda haka, sai ku kashe halin sha’awace-sha’awacen duniya a zuciyarku, wato iskanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa, da mugun hali, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.” (Kolosiyawa 3:5) Ko da yake yin hakan ba shi da sauƙi, Jehobah yana haƙuri da mu kuma yana taimaka mana. (Zabura 68:19) Akwai wani ɗan’uwa da ya shaƙu da kallon batsa da kuma tattaɓa al’aurarsa. Abokansa a makaranta suna ganin hakan ba laifi ba ne, amma ya ce: “Waɗannan abubuwan sun lalata tunanin zuciyata kuma suka sa na soma yin lalata.” Ya gano cewa yana bukatar ya riƙa kame kansa, kuma da taimakon Jehobah, ya daina wannan halin. Idan kana yin tunanin da bai dace ba, ka roƙi Jehobah ya ba ka ‘cikakken iko’ don ka daina irin wannan tunanin.​—2 Korintiyawa 4:7; 1 Korintiyawa 9:27.

12. Me ya sa muke bukatar mu ‘kiyaye zuciyarmu’?

12 Sulemanu ya rubuta cewa: “Kiyaye zuciyarka da dukan iyakacin ƙoƙari, gama daga cikinta rai yake fitowa kamar ruwa.” (Karin Magana 4:23) ‘Zuciyarmu’ ce take nuna ainihin halinmu kuma ita ce Jehobah yake gani. Abin da muke gani ko kalla yana shafan mu sosai. Shi ya sa mutum mai amincin nan Ayuba ya ce: “Na yi yarjejeniya da idanuna, to, me zai sa in yi sha’awar budurwa?” (Ayuba 31:1) Kamar Ayuba, muna bukatar mu yi hankali da abubuwan da muke kalla da kuma tunanin su. Mu yi addu’a kamar na mai zabura da ya ce: “Kawar da idanuna daga abubuwan banza.”​—Zabura 119:37.

ZAƁI MARAR KYAU DA DINA TA YI

13. Waɗanne irin ƙawaye ne Dina take tarayya da su?

13 Abokanmu suna iya shafan mu. Suna iya sa mu yi abubuwa masu kyau ko marasa kyau. Idan ka zaɓi abokan da suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, za su taimaka maka ka yi hakan. (Karin Magana 13:20; karanta 1 Korintiyawa 15:33.) Labarin Dina ya nuna mana muhimmancin yin abokan kirki. Ita ’yar Yakubu ce. Don haka, iyayenta da dukan ’yan’uwanta suna bauta wa Jehobah. Dina ba ’yar iska ba ce, amma ta yi tarayya da ’yan matan Kan’ana waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. Ra’ayin mutanen Kan’ana da na Isra’ilawa game da jima’i ba ɗaya ba ne kuma an san mutanen Kan’ana da yin lalata sosai. (Littafin Firistoci 18:​6-25) A lokacin da Dina take tare da ƙawayenta, ta haɗu da wani ɗan Kan’ana mai suna Shekem kuma yana son ta sosai. Shekem saurayi ne da aka “fi girmamawa” a gidansu. Amma ba ya bauta wa Jehobah.​—Farawa 34:​18, 19.

14. Mene ne ya faru da Dina?

14 Abin da Shekem ya yi a ganinsa ba laifi ba ne. Da yake yana son Dina sosai, hakan ya sa “ya cafke ta” kuma “ya kwana da ita.” (Karanta Farawa 34:​1-4.) Wannan abin da ya aikata ya janyo bala’i da masifa ga Dina da kuma dukan iyalinta.​—Farawa 34:​7, 25-31; Galatiyawa 6:​7, 8.

15, 16. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da hikima?

15 Ba sai abin da ya faru da Dina ya faru da mu kafin mu san cewa ƙa’idodin Jehobah suna taimaka mana ba. “Wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima, amma abokin tafiyar wawaye zai lalace.” (Karin Magana 13:20) Ka yi iya ƙoƙarinka ka fahimci “kowace hanya mai kyau,” domin hakan zai hana ka shiga cikin matsala.​—Karin Magana 2:​6-9; Zabura 1:​1-3.

16 Za mu kasance da hikima idan muna nazarin Kalmar Allah, da yin addu’a kafin mu yanke shawara da kuma bin gargaɗin bawan nan mai aminci. (Matiyu 24:45; Yaƙub 1:5) Babu shakka, dukanmu ajizai ne kuma muna da kasawarmu. (Irmiya 17:9) Amma mene ne za ka yi idan wani ya ja kunnenka domin ya ga kana yin abubuwan da za su kai ka ga yin lalata? Za ka yi fushi ne, ko kuma ka yarda da abin da mutumin ya faɗa?​—2 Sarakuna 22:​18, 19.

17. Ka ba da misalin da ya nuna cewa gargaɗi daga ’yan’uwa yana iya taimaka mana.

17 Ka yi la’akari da wannan misalin. Abokin aikin wata ’yar’uwa yana yawan tarayya da ita kuma ya gaya mata cewa yana son ta. Mutumin ba ya bauta wa Jehobah amma yana da kirki. Sai wata rana wata ’yar’uwa ta gan su tare kuma ta ja mata kunne game da hakan. Me wannan ’yar’uwa za ta yi? Za ta kāre kanta ne ko kuma ta amince da gargaɗin da ’yar’uwar ta yi mata? Mai yiwuwa ’yar’uwar tana ƙaunar Jehobah kuma tana so ta yi abin da ya dace. Amma idan ta ci gaba da soyayya da wannan mutumin, kana ganin tana “guje wa halin lalata” ne, ko kuwa tana ‘dogara ga kanta’?​—Karin Magana 22:3; 28:26; Matiyu 6:13; 26:41.

KA KOYI DARASI DAGA YUSUFU

18, 19. Ka ba da labarin yadda Yusufu ya guje wa yin lalata.

18 Yusufu matashi ne sa’ad da ya zama bawa a ƙasar Masar. Kowace rana, matar maigidansa tana gaya masa cewa ya yi lalata da ita, amma Yusufu ya san cewa hakan babban laifi ne. Yusufu yana ƙaunar Jehobah sosai kuma yana so ya faranta masa rai. Don haka, a duk lokacin da matar ta zo don ta yaudare shi, Yusufu yana ƙin yin hakan. Tun da shi bawa ne, ba zai iya guduwa ya bar maigidansa ba. Wata rana matar ta so ta sa shi dole ya kwana da ita, sai Yusufu “ya gudu waje.”​—Karanta Farawa 39:​7-12.

19 Da a ce Yusufu yana tunanin yin lalata da matar, da ba zai iya guduwa sa’ad da matar ta so ya kwana da ita ba. A gun Yusufu, dangantakarsa da Jehobah ta fi kome muhimmanci. Shi ya sa ya gaya wa matar cewa: “Maigidana . . . bai kuma hana mini kome ba sai ke, da yake ke ce matarsa. Don me zan yi wannan . . . mugunta, in yi wa Allah zunubi?”​—Farawa 39:​8, 9.

20. Ta yaya muka san cewa Jehobah ya yi farin ciki don abin da Yusufu ya yi?

20 Duk da cewa Yusufu yana nesa da gida da kuma iyalinsa, ya riƙe amincinsa ga Allah kuma Jehobah ya masa albarka. (Farawa 41:​39-49) Jehobah ya yi farin ciki sosai domin amincin Yusufu. (Karin Magana 27:11) Ba shi da sauƙi mutum ya guje wa yin lalata. Amma ka tuna da kalmomin nan: “Ku da kuke ƙaunar Yahweh, ku ƙi mugunta! Gama yana kiyaye rayukan masu ƙaunarsa, yana kuɓutar da su daga hannun mugaye.”​—Zabura 97:10.

21. Ta yaya wani ɗan’uwa ya bi misalin Yusufu?

21 A kowace rana, mutanen Jehobah suna nuna cewa suna ‘ƙin mugunta’ kuma suna ‘son abu mai kyau.’ (Amos 5:15) Dukanmu yara da manya za mu iya riƙe aminci ga Jehobah. Akwai wani ɗan’uwa matashi da aka jaraba bangaskiyarsa a makarantarsu. Wata yarinya ta gaya masa cewa idan ya taimaka mata ta ci jarabawa, za ta yarda ya kwana da ita. Mene ne wannan ɗan’uwan ya yi? Ya yi abin da Yusufu ya yi. Ya ce: “Nan da nan na gaya mata cewa ba zan iya yin hakan ba. Ƙin yin lalata da ita ya sa ban rasa darajata ba.” Duk wani ‘daɗi . . . na ɗan lokaci’ da lalata yake kawowa yana jawo masifa da ɓacin rai. (Ibraniyawa 11:25) Amma yin biyayya ga Jehobah yana sa mutum ya yi farin ciki.​—Karin Magana 10:22.

KA AMINCE DA TAIMAKON JEHOBAH

22, 23. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana ko da mun yi zunubi mai tsanani?

22 Shaiɗan zai yi ƙoƙarin sa mu yi lalata kuma guje ma wannan tarkon ba zai kasance mana da sauƙi ba. Wataƙila dukanmu mukan yi tunanin da bai dace ba a wasu lokuta. (Romawa 7:​21-25) Jehobah ya san cewa “mu ƙurar ƙasa ne.” (Zabura 103:14) Amma idan wani Kirista ya yi lalata fa? Na shi ya ƙare ke nan? A’a. Idan mutumin ya tuba da gaske, Jehobah zai taimaka masa. Allah “mai yin gafara” ne.​—Zabura 86:5; Yaƙub 5:16; karanta Karin Magana 28:13.

23 Ƙari ga haka, Jehobah ya ba mu dattawa da suke ƙaunar mu da kuma kula da mu. (Afisawa 4:​8, 12; Yaƙub 5:​14, 15) Ya yi mana tanadin dattawa don su taimaka mana mu gyara dangantakarmu da shi.​—Karin Magana 15:32.

KA ZAMA DA BASIRA

24, 25. Ta yaya “hankali” ko basira za ta taimaka mana mu guji yin lalata?

24 Idan muna so mu yanke shawara mai kyau, muna bukatar mu fahimci yadda dokokin Jehobah suke taimaka mana. Ba ma so mu zama kamar matashin da aka ambata a Karin Magana 7:​6-23. Matashin ba shi da “hankali” ko basira kuma hakan ya sa tarkon yin lalata ya kama shi. Kasancewa da basira ya wuce mutum ya zama da ilimi kawai. Idan muna da basira, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu fahimci ƙa’idodin Allah kuma mu yi amfani da su a rayuwarmu. Ka tuna da kalaman nan: “Mai samun hikima, ƙaunar ransa yake yi, mai kiyaye fahimta kuma, zai yalwata.”​—Karin Magana 19:8.

25 Shin ka gaskata cewa ƙa’idodin Allah suna da amfani? Ka gaskata cewa bin ƙa’idodin za su sa ka farin ciki a rayuwarka? (Zabura 19:​7-10; Ishaya 48:​17, 18) Idan kana shakkar hakan, ka tuna da dukan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi maka. Littafi Mai Tsarki ya ce, “ku ɗanɗana ku ga Yahweh mai alheri ne.” (Zabura 34:8) Idan kana tuna abubuwan nan, za ka ƙaunaci Allah sosai. Za ka so abin da yake so kuma ka ƙi abin da ya tsana. Za ka riƙa yin tunani a kan abin da yake na gaskiya da ban girma da abin da yake daidai da wanda ke jawo ƙauna da kuma kirki. (Filibiyawa 4:​8, 9) Kamar Yusufu, za mu amfana daga hikimar Jehobah.​—Ishaya 64:8.

26. Mene ne za mu koya a babi biyu na gaba?

26 Ko da ka yi aure ko ba ka yi ba, Jehobah yana so ka ji daɗin rayuwarka kuma ka riƙa yin farin ciki. A babi biyu na gaba, za mu koya yadda za mu yi farin ciki a aurenmu.