Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 12

Ku Rika Yin Maganganu Masu Dadin Ji

Ku Rika Yin Maganganu Masu Dadin Ji

“Kada wani ƙazamin zance ya fita daga bakinku, sai dai irin magana da take da amfani domin ƙarfafawar juna.”​—AFISAWA 4:29.

1-3. (a) Wane kyauta mai kyau ne Jehobah ya ba mu? Ta yaya za mu yi amfani da shi a hanyar da ba ta dace ba? (b) Yaya ya kamata mu yi amfani da kyautar yin magana?

WANI mutum ya saya wa ɗansa keke kuma ya yi farin cikin ba ma ɗansa keken. Amma kana ganin mutumin zai ji daɗi idan ɗansa ya riƙa gudu da keken har ya kaɗe wani da shi kuma ya ji masa rauni?

2 Jehobah shi ne Mai ba da “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yaƙub 1:17) Ɗaya daga cikin kyautar da ya ba mu ita ce kyauta ta yin magana. Wannan kyautar tana ba mu damar furta tunaninmu da kuma yadda muke ji. Muna iya gaya wa mutane abin da zai taimaka musu da kuma abin da zai ƙarfafa su. Amma, wasu abubuwan da muke furtawa za su iya sa mutane baƙin ciki sosai.

3 Harshenmu yana da iko, kuma Jehobah ya koya mana yadda za mu riƙa furta maganganu masu daɗi. Ya gaya mana cewa: “Kada wani ƙazamin zance ya fita daga bakinku, sai dai irin magana da take da amfani domin ƙarfafawar juna bisa ga bukatarku. Ta haka maganarku za ta zama da amfani ga masu jinta.” (Afisawa 4:29) Bari mu ga yadda za mu yi amfani da wannan kyautar da Allah ya ba mu a hanyar da za ta faranta masa rai da kuma ƙarfafa mutane.

KU YI HANKALI DA ABUBUWAN DA KUKE FAƊA

4, 5. Mene ne muka koya daga littafin Ƙarin Magana game da ikon da harshe yake da shi?

4 Harshe yana da iko. Don haka, muna bukatar mu yi hankali da abubuwan da muke faɗa da kuma yadda muke faɗan su. Littafin Karin Magana 15:4 ta ce: “Harshe mai maganar alheri itace mai ba da rai ne, amma munafuncin magana yana kashe ruhu.” Kamar yadda bishiya mai kyau takan ba da inuwa mai daɗi ga mutum, haka ma maganganu masu daɗi suke da daɗin ji. Amma maganganu marasa daɗi suna ɓata wa mutane rai kuma su sa su baƙin ciki.​—Karin Magana 18:21.

Kalmomi masu kyau suna da daɗin ji

5 Littafin Karin Magana 12:18 ta ce: “Maganar da an yi da rashin tunani tana sa rauni kamar sokin takobi.” Maganganu marasa daɗi suna jawo ɓacin rai kuma suna ɓata abokantaka. Mai yiwuwa ka tuna yadda ka ji sa’ad da wani ya yi maka magana marar daɗi. Amma ƙarin maganar ta ƙara da cewa: “Harshe mai hikima yakan kawo warkewa.” Magana mai daɗi tana sa mutum farin ciki, tana gyara dangantakar abokan da suka samu saɓani. (Karanta Karin Magana 16:24.) Idan muka tuna cewa abubuwan da muke faɗa suna iya shafan mutane, hakan zai sa mu mai da hankali sa’ad da muke magana.

6. Me ya sa ba shi da sauƙi mu yi magana yadda ya dace?

6 Wani dalili kuma da ya sa ya kamata mu mai da hankali sa’ad da muke magana shi ne, mu ajizai ne. ‘Tunanin zuciyar ɗan Adam yana cike da mugunta,’ kuma a yawancin lokaci, abin da ke zuciyarmu ne muke furtawa. (Farawa 8:21; Luka 6:45) Ba shi da sauƙi mu yi magana yadda ya dace. (Karanta Yaƙub 3:​2-4.) Muna bukatar mu ci gaba da kyautata yadda muke yi wa mutane magana.

7, 8. Ta yaya abubuwan da muke faɗa za su shafi dangantakarmu da Jehobah?

7 Ƙari ga haka, muna bukatar mu yi hankali da abubuwan da muke furtawa domin abubuwan da muke faɗa da kuma yadda muke faɗan su za su iya shafan ibadarmu. Yaƙub 1:26 ta ce: “Idan wani yana tsammani shi mai addini ne sosai, amma ba ya kame bakinsa, to, yana ruɗin kansa ne, addininsa kuma banza ne.” Don haka, idan muna furta abubuwan da ba su dace ba, hakan zai sa Jehobah ya ƙi amincewa da ibadarmu.​—Yaƙub 3:​8-10.

8 Hakika, muna da dalilai masu kyau da suka sa ya kamata mu riƙa hankali da abubuwan da muke faɗa da kuma yadda muke faɗan su. Don mu iya furta abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai, zai dace mu san irin maganganun da muke bukatar mu guje musu.

MAGANGANUN DA SUKE SA BAƘIN CIKI

9, 10. (a) Waɗanne irin maganganu ne mutane suke yawan yi a yau? (b) Me ya sa ya kamata mu guje wa maganganun rashin ɗa’a?

9 Mutane da yawa a yau suna yawan yin maganganu marasa kyau ko na iskanci. Suna ganin sai sun yi rantsuwa ko maganganun rashin da’a kafin a amince da abin da suke faɗa. Masu ba da dariya suna yawan amfani da maganganun iskanci don su sa mutane dariya. Amma manzo Bulus ya ce: “Dole ne ku rabu da dukan irin halayen nan. Ku bar yin fushi, da zafin rai, da ƙiyayyar zuciya, da ɓata suna, da maganar ƙazanta daga bakinku.” (Kolosiyawa 3:8) Ya kuma ce kada Kiristoci na gaskiya su riƙa yin maganganun iskanci.​—Afisawa 5:​3, 4.

10 Jehobah da kuma bayinsa ba sa ƙaunar maganganun rashin ɗa’a. Irin maganganun nan suna da ƙazanta. Littafi Mai Tsarki ya ce “ƙazanta” tana cikin “ayyukan jiki.” (Galatiyawa 5:​19-21, Tsohuwar Hausa A Sauƙaƙe) “Ƙazanta” ta ƙunshi abubuwa marasa kyau da yawa kuma da kaɗan-kaɗan mutum zai soma yin su. Idan mutum yana yawan yin maganganun iskanci ko na rashin da’a kuma ya ƙi dainawa, ba za a bar shi ya ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya ba.​—2 Korintiyawa 12:21; Afisawa 4:19; ka duba Ƙarin Bayani na 23.

11, 12. (a) Ta yaya hirarmu za ta iya juyawa ta zama gulma? (b) Me ya sa ya kamata mu guji yin ƙarya a kan mutane?

11 Ƙari ga haka, muna bukatar mu guje wa yin gulma. Ba laifi ba ne mu damu da mutane kuma mu yi hira game da su. Ko a ƙarni na farko ma, Kiristoci sun so su san irin yanayin da ’yan’uwansu suke ciki da kuma abin da za su yi don su taimaka musu. (Afisawa 6:​21, 22; Kolosiyawa 4:​8, 9) Amma yana da sauƙi mu soma gulman mutane yayin da muke hira game da su. Idan muka soma gulma, za mu iya faɗan abubuwan da ba gaskiya ba ko kuma abubuwan da bai kamata mu gaya ma wasu ba. Idan ba mu mai da hankali ba, za mu soma faɗan ƙarya game da mutanen ko kuma mu ɓata sunansu. Farisawa sun ɓata sunan Yesu sa’ad da suka yi ƙarya game da shi. (Matiyu 9:​32-34; 12:​22-24) Gulma tana ɓata sunan mutum, tana jawo jani-in-jaka da baƙin ciki kuma tana ɓata zumunci.​—Karin Magana 26:20.

12 Jehobah yana so mu riƙa maganganun da za su taimaka da kuma ƙarfafa mutane ba maganganun da za su jawo rigima tsakanin abokai ba. Jehobah ya tsani waɗanda suke “tā da faɗa tsakanin ’yan’uwa.” (Karin Magana 6:​16-19) Shaiɗan Iblis ne wanda ya fara yin ƙarya, ya yi ƙarya game da Allah kuma ya ɓata sunansa. (Ru’uyar da Aka Yi Wa Yohanna 12:​9, 10) A yau, mutane da yawa suna gulma. Amma bai kamata ’yan’uwa a ikilisiya su yi hakan ba. (Galatiyawa 5:​19-21) Don haka, mu yi hankali sosai da abin da muke faɗa, kuma mu yi tunani kafin mu furta wani abu. Kafin ka faɗin wani abu game da wani, ka tambayi kanka: ‘Shin abin da nake so na faɗa gaskiya ne? Abu mai kyau ne? Yin hakan zai taimaka kuwa? Zan so mutumin ya ji abin da nake faɗa game da shi? Yaya zan ji idan wani ya yi irin wannan maganar game da ni?’​—Karanta 1 Tasalonikawa 4:11.

13, 14. (a) Yaya mutane suke ji sa’ad da aka yi musu baƙar magana? (b) Mene ne zagi ya ƙunsa? Me ya sa ya kamata Kiristoci su guji zagin mutane?

13 A wasu lokuta, dukanmu mukan faɗi abubuwa kuma mu yi da-na-sani daga baya. Duk da haka, bai kamata mu riƙa yawan kushe mutane ko kuma mu yi musu maganganun banza ba. Bai kamata mu riƙa yi wa mutane baƙar magana ba. Baƙar magana tana rage mutuncin mutane kuma tana sa su ji kamar ba su da amfani. Baƙar magana tana sa yara baƙin ciki sosai, don haka, kada mu yi amfani da irin waɗannan kalmomin ga yara.​—Kolosiyawa 3:21.

14 Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu game da zage-zage. Bulus ya ce: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, . . . da zage-zage, su kawu daga gare ku, tare da dukan ƙeta.” (Afisawa 4:​31, Tsohuwar Hausa a Saukake) Zagi ya ƙunshi munanan maganganu game da mutane kuma akan yin hakan ne don a sa su baƙin ciki. Bai kamata ma’aurata su riƙa zagin juna ko yaransu ba. Ba za a ƙyale Kirista da ya ƙi daina zagin mutane ya ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya ba. (1 Korintiyawa 5:​11-13; 6:​9, 10) Kamar yadda muka koya, idan muna maganganun lalata ko ƙarya ko baƙar magana, za mu ɓata dangantakarmu da Jehobah da kuma mutane.

KALAMAI MASU DAƊIN JI

15. Wace irin magana ce take ƙara zumunci?

15 Ta yaya za mu yi amfani da kyautar yin magana da Allah ya ba mu yadda yake so? Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana ainihin abubuwan da za mu faɗa da waɗanda ba za mu faɗa ba, ya bayyana mana cewa mu riƙa maganganun da suke “da amfani domin ƙarfafawar juna.” (Afisawa 4:29) Maganar gaskiya mai daɗin ji ne take ƙarfafa mutane. Jehobah yana so mu riƙa gaya wa mutane abubuwan da za su ƙarfafa su da kuma taimaka musu. Yin hakan ba shi da sauƙi. Domin ya fi sauƙi a faɗi munanan abubuwa da a faɗi abubuwan da za su ƙarfafa mutane. (Titus 2:8) Bari mu ga wasu abubuwan da za mu faɗa don mu ƙarfafa mutane.

16, 17. (a) Me ya sa ya kamata mu riƙa yaba wa mutane? (b) Su waye ne za mu yaba wa?

16 Jehobah da Yesu sukan yaba wa mutane sosai. Mu ma muna bukatar mu kasance da wannan halin. (Matiyu 3:17; 25:​19-23; Yohanna 1:47) Muna bukatar mu ƙaunaci mutum kafin mu iya yaba masa a hanyar da za ta ƙarfafa shi. Littafin Karin Magana 15:23 ta ce, “abu mai kyau ne magana ta fita a daidai lokaci.” Muna farin ciki sosai idan mutane suka yaba mana don aikin da muke yi ko kuma wani abu mai kyau da muka yi.​—Karanta Matiyu 7:12; ka duba Ƙarin Bayani na 27.

17 Idan muna mai da hankali ga halaye masu kyau da mutane suke da su, zai mana sauƙi mu riƙa yaba musu. Alal misali, wataƙila ka lura cewa wani ɗan’uwa yana shirya jawabinsa da kyau ko kuma yana yin kalami a taro. Ko wani matashi yana kāre imaninsa a makaranta, ko kuma wani ɗan’uwa da ya tsufa yana iya ƙoƙarinsa wajen fita wa’azi. Za su ji daɗi sosai idan ka yaba musu. Yana da muhimmanci maigida ya riƙa yaba wa matarsa kuma ya gaya mata cewa yana ƙaunar ta. (Karin Magana 31:​10, 28) Kafin shuka ta yi girma, tana bukatar ruwa da kuma hasken rana. Haka ma, dukanmu muna so a riƙa yaba mana musamman ma yara. Mu riƙa yaba musu don halayensu masu kyau da kuma ƙoƙarin da suke yi. Idan ana yaba musu, hakan zai sa su ƙara ƙwazo wajen aikata abubuwan da suka dace.

Za mu iya ƙarfafa mutane ta abin da muke furtawa da kuma yadda muke furta su

18, 19. Me ya sa za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ƙarfafa mutane? Ta yaya za mu yi hakan?

18 Idan muna ƙarfafa mutane, muna koyi da halin Jehobah. Ya damu da masu sauƙin kai da kuma waɗanda suke baƙin ciki. (Ishaya 57:15) Jehobah yana so mu riƙa “ƙarfafa juna” kuma mu “ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya.” (1 Tasalonikawa 5:​11, 14) Idan muna hakan, yana gani kuma yana farin ciki da abin da muke yi.

19 Wataƙila ka lura da wani a cikin ikilisiya da yake baƙin ciki. Me za ka yi don ka taimaka masa? Mai yiwuwa ba za ka iya magance matsalarsa ba, amma za ka iya nuna masa cewa ka damu da shi sosai. Alal misali, kana iya keɓe lokaci don ka kasance tare da shi. Kana iya karanta wata aya a Littafi Mai Tsarki da za ta ƙarfafa shi ko kuma ka yi addu’a tare da shi. (Zabura 34:18; Matiyu 10:​29-31) Kana iya gaya ma waɗanda suke baƙin ciki cewa ’yan’uwa a ikilisiya suna ƙaunar su. (1 Korintiyawa 12:​12-26; Yaƙub 5:​14, 15) Ka yi musu magana a hanyar da za ta nuna cewa ka damu da su kuma abubuwan da kake faɗa gaskiya ne.​—Karanta Karin Magana 12:25.

20, 21. Me zai sa ya yi wa mutane sauƙi su amince da shawara?

20 Ƙari ga haka, muna ƙarfafa mutane sa’ad da muka ba su shawara mai kyau. Tun da dukanmu ajizai ne, muna bukatar shawara a kai a kai. Littafin Karin Magana 19:20 ta ce: “Kasa kunne ga shawara, ka karɓi koyarwa, domin wata rana za ka zama mai hikima.” Ba dattawa ne kawai ya kamata su riƙa ba da shawara ba. Iyaye suna bukatar su ba wa yaransu umurni. (Afisawa 6:4) ’Yan’uwa mata suna iya ba wa juna shawara. (Titus 2:​3-5) Muna ƙaunar ’yan’uwanmu, don haka, zai dace mu yi hankali kada mu ba su shawara a hanyar da za ta sa su baƙin ciki. Mene ne zai taimaka mana?

21 Mai yiwuwa wani ɗan’uwa ya taɓa ba ka shawara kuma ka ji daɗin shawarar. Me ya sa ya yi maka sauƙi ka amince da shawarar? Wataƙila domin ka fahimci cewa mutumin yana ƙaunar ka ne. Ko kuma ya yi maka magana a hanya mai kyau. (Kolosiyawa 4:6) Kuma mai yiwuwa shawarar daga Littafi Mai Tsarki ne. (2 Timoti 3:16) Ya kamata shawarar da muke bayarwa ta fito daga Littafi Mai Tsarki, za mu iya karanta shi ko kuma mu faɗa da baki. Kada mu tilasta wa mutane su bi ra’ayinmu kuma kada mu canja ma’anar wata aya don ta yi daidai da ra’ayinmu. Idan muka tuna yadda aka ba mu shawara, hakan zai taimaka mana sa’ad da muke so mu ba wa mutane shawara.

22. Yaya kake so ka yi amfani da kyautar yin magana?

22 Allah ne ya ba mu kyautar yin magana. Ya kamata ƙaunar da muke masa ta sa mu yi amfani da wannan kyauta yadda ya dace. Ku tuna cewa furucinmu suna da ikon ƙarfafa mutane ko sa su baƙin ciki. Don haka, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu wajen furta kalaman da za su ƙarfafa mutane.