Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 4

Me Ya Sa Ya Dace Mu Rika Yin Biyayya?

Me Ya Sa Ya Dace Mu Rika Yin Biyayya?

“Ku ba da girma ga kowa, ku ƙaunaci ’yan’uwa masu bin Yesu. Ku ji tsoron Allah. Ku ba da girma ga babban sarki.”​—1 BITRUS 2:17.

1, 2. (a) Umurnin waye ne ya kamata mu bi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan babin?

WATAƘILA lokacin da kake yaro, akwai lokutan da iyayenka suka gaya maka ka yi wani abin da ba ka so. Kana ƙaunar iyayenka sosai kuma ka san cewa ya kamata ka yi musu biyayya. Duk da haka, mai yiwuwa ba a kowane lokaci kake so ka yi musu biyayya ba.

2 Mun san cewa Jehobah, Ubanmu na sama yana ƙaunar mu. Ya damu da mu kuma yana ba mu abubuwan da za su sa mu ji daɗin rayuwa. Yana ba mu shawarwarin da za su taimaka mana mu yi nasara. A wasu lokuta ma, yana amfani da mutane don su yi mana ja-goranci. Don haka, muna bukatar mu yi biyayya da dokokin Jehobah. (Karin Magana 24:21) Amma me ya sa yin biyayya yake mana wuya a wasu lokuta? Me ya sa Jehobah ya ce mu riƙa yin biyayya? Kuma ta yaya za mu nuna cewa muna daraja da kuma bin umurninsa?​—Ka duba Ƙarin Bayani na 9.

ME YA SA YIN BIYAYYA YAKE DA WUYA?

3, 4. Ta yaya ’yan Adam suka zama masu zunubi? Me ya sa yake mana wuya mu amince da ja-gorancin mutane?

3 Mu ’yan Adam mukan yi rashin biyayya. Mun gāji wannan halin tun daga lokacin da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi. Ko da yake su kamiltattu ne, sun bijire wa umurnin Allah. Hakan ne ya sa dukanmu muka zama masu zunubi. Shi ya sa yake mana wuya mu amince da ja-gorancin Jehobah da na ’yan Adam. Wani dalili kuma da ya sa yake mana wuya mu yi biyayya shi ne, mutanen da Jehobah yake amfani da su don ya ja-gorance mu ajizai ne kamar mu.​—Farawa 2:​15-17; 3:​1-7; Zabura 51:5; Romawa 5:12.

4 Saboda mu masu zunubi ne, mukan zama masu girman kai. Idan muna da girman kai, ba za mu iya amincewa da ja-gorancin mutane ba. Alal misali, Jehobah ya zaɓi Musa ya ja-goranci mutanensa Isra’ilawa. Sai wani mutum mai suna Kora wanda ya daɗe yana bauta wa Jehobah ya soma girman kai kuma ya ƙi daraja Musa. Duk da cewa Musa ne yake ja-gorantar mutanen Allah, shi ba mai girman kai ba ne. Littafi Mai Tsarki ya ce Musa ya fi kowa a zamaninsa sauƙin kai. Amma Kora ya ƙi bin ja-gorancin Musa. Har ma ya sa wasu cikin Isra’ilawan suka ƙi bin ja-gorancin Musa. Mene ne ya faru da Kora da kuma mutanen? An halaka su. (Littafin Ƙidaya 12:3; 16:​1-3, 31-35) Akwai labaran mutane da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna mana cewa girman kai yana da haɗari sosai.​—2 Tarihi 26:​16-21; ka duba Ƙarin Bayani na 10.

5. Ta yaya wasu mutane suka yi amfani da ikonsu a hanyar da ba ta dace ba?

5 Wataƙila ka lura cewa iko yakan canja halin mutum. Tun daga farkon tarihin ’yan Adam, mutane da yawa sun yi amfani da ikonsu a hanyar da ba ta dace ba. (Karanta Mai-Wa’azi 8:9.) Alal misali, Saul mutumin kirki ne kuma yana da sauƙin kai a lokacin da Jehobah ya zaɓe shi ya zama sarkin Isra’ila. Amma da shigewar lokaci, ya soma girman kai da kuma kishin Dauda. Hakan ya sa ya tsananta wa Dauda duk da cewa bai yi wani laifi ba. (1 Sama’ila 9:​20, 21; 10:​20-22; 18:​7-11) Daga baya, Dauda ya zama sarkin Isra’ila, kuma yana ɗaya daga cikin sarakunan Isra’ila masu kirki. Bayan wasu lokuta, shi ma Dauda ya yi amfani da ikonsa a hanyar da ba ta dace ba. Ya kwana da Batsheba matar Uriya. Ya san abin da ya yi bai da kyau, sai ya yi ƙoƙarin ɓoye zunubinsa ta wajen aika Uriya yaƙi don a kashe shi.​—2 Sama’ila 11:​1-17.

ME YA SA MUKE YI WA JEHOBAH BIYAYYA?

6, 7. (a) Mene ne za mu yi idan muna ƙaunar Jehobah? (b) Mene ne zai taimaka mana mu yi biyayya ko a lokacin da hakan bai da sauƙi?

6 Ƙaunar da muke wa Jehobah ce take sa muke bin umurninsa. Idan muna ƙaunar Jehobah fiye da kome, za mu so mu riƙa faranta masa rai. (Karanta Karin Magana 27:11; Markus 12:​29, 30.) Tun daga lokacin da Adamu da Hauwa’u suke zama a lambun Adnin, Shaiɗan ya so mutane su ƙi ja-gorancin Jehobah. Shaiɗan yana so mu gaskata cewa Jehobah ba shi da iko ya gaya mana abin da za mu yi. Amma mun san cewa hakan ƙarya ne. Mun yarda da kalaman nan cewa: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cancanci ka karɓi ɗaukaka, da girma, da iko. Gama ka halicci kome da kome, kuma ta wurin nufinka suka kasance aka kuma halicce su.”​—Ru’uyar da aka yi wa Yohanna 4:11.

7 Wataƙila a lokacin da kake yaro, an gaya maka cewa wajibi ne ka yi wa iyayenka biyayya ko da hakan bai da sauƙi. Haka nan ma, yin biyayya yakan yi wa bayin Jehobah wuya a wasu lokuta. Amma idan muna ƙaunar Jehobah kuma muna daraja shi, za mu iya yi masa biyayya a kowane lokaci. Yesu ya kafa mana misali mai kyau game da hakan. Ya yi wa Jehobah biyayya ko a lokacin da hakan bai da sauƙi. Shi ya sa ya gaya wa Ubansa cewa: “Ba nufina ba, sai dai nufinka za a bi.”​—Luka 22:42; ka duba Ƙarin Bayani na 11.

8. Ta yaya Jehobah yake mana ja-goranci? (Ka duba akwatin nan “ Ka Riƙa Jin Shawara.”)

8 A zamaninmu, Jehobah yana amfani da hanyoyi da yawa don ya ja-gorance mu. Alal misali, ya ba mu Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki. Ya naɗa dattawa a cikin ikilisiya. Idan muna daraja waɗanda Jehobah yake amfani da su wajen yi mana ja-goranci, kamar muna daraja Jehobah ne. Idan kuma muka ƙi mu yi musu biyayya, muna ƙin Jehobah ke nan. Sa’ad da Isra’ilawa suka ƙi yi wa Musa biyayya, Jehobah bai ji daɗi ba. Kuma a gun Jehobah, shi suka yi wa rashin biyayya.​—Littafin Ƙidaya 14:​26, 27; ka duba Ƙarin Bayani na 12.

9. Ta yaya ƙauna za ta sa mu riƙa bin umurni?

9 Idan muna bin umurni, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Bari mu ba da misali, idan bala’i ya abko a wani wuri, ƙungiyoyin agaji sukan yi aiki tare don su ceci mutanen da bala’in ya shafa. Amma kafin su yi aiki mai kyau, wajibi ne a samu wanda zai ja-gorance su kuma kowanne mutum a cikin masu ba da agajin yana bukatar ya bi umurninsa. Amma idan wani ya ƙi bin ja-gorancin kuma ya yi abin da ya ga dama fa, me kake ganin zai faru? Ko da ya yi hakan da manufa mai kyau, ƙin bin ja-gorancin nan zai iya jefa su cikin haɗari sosai. Haka nan ma, idan ba ma bin ja-gorancin Jehobah da na waɗanda ya naɗa, za mu iya sa ’yan’uwanmu cikin damuwa. Amma idan muna yi wa Jehobah biyayya, hakan na nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwa kuma muna daraja tsarin da Jehobah ya kafa.​—1 Korintiyawa 12:​14, 25, 26.

10, 11. Mene ne za mu tattauna yanzu?

10 Mu ne za mu amfana idan muka bi dokokin Allah. Idan muna daraja magidanta da dattawa a ikilisiyarmu har ma da gwamnatocin ’yan Adam, za mu amfana sosai.​—Maimaitawar Shari’a 5:16; Romawa 13:4; Afisawa 6:​2, 3; Ibraniyawa 13:17.

11 Idan muka san dalilan da suka sa Jehobah yake so mu riƙa daraja mutane kuma mu bi ja-gorancinsu, hakan zai taimaka mana. Bari mu tattauna hanyoyi uku da za mu nuna cewa muna daraja tsarin da Jehobah ya kafa.

YIN BIYAYYA A IYALI

12. Ta yaya maigida zai nuna cewa yana yi wa Jehobah biyayya?

12 Jehobah ne ya kafa iyali kuma ya ba wa kowa a cikin iyali aikin da zai yi. Idan kowa a iyali yana yin abin da Jehobah ya bukace shi ya yi, iyalin za ta zauna lafiya. (1 Korintiyawa 14:33) Jehobah ya naɗa namiji ya zama magidancin iyali. Don haka, Jehobah yana son maigidan ya kula da matarsa da yaransa kuma ya ja-gorance su a hanya mai kyau. Maigidan zai ba da lissafin yadda ya kula da iyalinsa ga Jehobah. Kiristoci magidanta suna ƙaunar iyalinsu kuma suna sha’ani da su cikin ƙauna kamar yadda Yesu yake yi wa ikilisiya. Idan maigida yana yin waɗannan abubuwan, yana daraja Jehobah.​—Afisawa 5:23; ka duba Ƙarin Bayani na 13.

Kirista da yake kula da iyalinsa da kyau yana koyi da halayin Kristi

13. Ta yaya mata za ta nuna cewa tana yi wa Jehobah biyayya?

13 Mata Kiristoci ma suna da aiki mai muhimmanci a cikin iyali. Mata tana taimaka wa maigidanta don ya kula da iyalin da kyau. Su biyun suna da hakkin koya wa yaransu halaye masu kyau. Idan tana so yaranta su riƙa daraja mutane, dole ne ita ma ta riƙa daraja maigidanta. Kuma ta riƙa bin umurninsa. (Karin Magana 1:8) Ko da yana so ya yi wani abin da ba ta so, ya kamata ta gaya masa ra’ayinta cikin ladabi. Idan Mashaidiya ta auri wanda ba Mashaidi ba, hakan yana iya jawo damuwa da yawa. Amma idan ta ci gaba da ƙaunar mijinta kuma tana daraja shi, hakan zai iya sa ya soma bauta wa Jehobah.​—Karanta 1 Bitrus 3:1.

14. Ta yaya yara za su nuna cewa suna yi wa Jehobah biyayya?

14 Yara suna da daraja a wajen Jehobah kuma suna bukatar kāriya da kuma ja-goranci. Iyaye suna farin ciki idan yaransu suna musu biyayya. Mafi muhimmanci ma, yara suna faranta wa Jehobah rai kuma suna nuna cewa suna daraja shi idan suna wa iyayensu biyayya. (Karin Magana 10:1) A wasu lokuta, mahaifi ko mahaifiya ce kaɗai take renon yaranta. Irin wannan yanayin ba ya yi wa mahaifiyar ko mahaifin da kuma yaran sauƙi. Amma za su zauna lafiya idan yaran suna taimaka da kuma yi wa mahaifinsu ko mahaifiyarsu biyayya. Ko da yaya yanayin yake, akwai damuwa a kowace iyali. Amma idan kowa a iyalin yana yin abin da ya kamata, iyalin za ta yi farin ciki. Kuma hakan yana ɗaukaka Jehobah, wanda ya kafa iyali.​—Afisawa 3:​14, 15.

YIN BIYAYYA A IKILISIYA

15. Ta yaya zan yi biyayya ga ’yan’uwa da suke ja-goranci a ikilisiya?

15 Jehobah yana amfani da dattawa a cikin ikilisiya don ya yi mana ja-goranci kuma ya ba Yesu shugabancin ikilisiyar Kirista. (Kolosiyawa 1:18) Yesu kuma ya ba wa “bawan nan mai aminci, mai hikima” gatan kula da bayin Allah a nan duniya. (Matiyu 24:​45-47) A yau, “bawan nan mai aminci, mai hikima” shi ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Hukumar tana tanadar mana da abubuwan da za su ƙarfafa bangaskiyarmu. Dattawa da bayi masu hidima da masu kula da da’ira suna taimaka ma ikilisiyoyi a duk faɗin duniya. Suna yin hakan ta wurin ja-gorancin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. Hakkin ’yan’uwan ne su riƙa kula da mu. Idan muna yin biyayya ga ’yan’uwan nan, muna yin biyayya ga Jehobah ke nan.​—Karanta 1 Tasalonikawa 5:12; Ibraniyawa 13:17; ka duba Ƙarin Bayani na 14.

16. Me ya sa muka ce ruhu mai tsarki ne yake naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima?

16 Dattawa da kuma bayi masu hidima suna taimaka wa ikilisiya ta kasance da haɗin kai da kuma bangaskiya. Ta yaya ake naɗa su tun da yake su ma masu kasawa ne kamar mu? Kafin a naɗa su, sai an tabbata suna da irin halayen da Littafi Mai Tsarki ya ambata. (1 Timoti 3:​1-7, 12; Titus 1:​5-9) Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya gaya wa marubutan Littafi Mai Tsarki abin da ya kamata mutum ya yi kafin a naɗa shi. Dattawa sukan roƙi Jehobah ya ba su ruhu mai tsarki a lokacin da suke tattaunawa game da wanda za a naɗa shi dattijo ko kuma bawa mai hidima. Hakan ya nuna cewa Yesu da Jehobah ne suke ja-gorantar ikilisiyoyinmu. (Ayyukan Manzanni 20:28) Allah ne ya yi tanadin ’yan’uwa da ake naɗawa don su kula da mu.​—Afisawa 4:8.

17. Me ya kamata ’yan’uwa mata su yi a wasu lokuta don su nuna biyayya?

17 A wasu lokuta, zai iya kasance babu dattijo ko bawa mai hidima da zai yi wasu ayyuka a ikilisiya. A irin wannan yanayi, ɗan’uwan da ya yi baftisma zai iya yin ayyukan. Idan har ila babu wani ɗan’uwa da ya yi baftisma, ’yar’uwa da ta yi baftisma za ta iya yin aikin da ya kamata ɗan’uwa mai baftisma ya yi. Amma kafin ta yi hakan, ta ɗaura ɗankwali ko kuma ta saka hula. (1 Korintiyawa 11:​3-10) Yin hakan zai nuna cewa tana daraja yadda Jehobah ya tsara shugabanci a gida da kuma ikilisiya.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 15.

BIYAYYA GA HUKUMOMIN GWAMNATI

18, 19. (a) Me muka koya daga Romawa 13:​1-7? (b) Ta yaya za mu yi biyayya ga hukumomin gwamnati?

18 Da yake Jehobah ya ƙyale gwamnatocin ’yan Adam su ci gaba da mulki, ya kamata mu yi musu biyayya. Su ne suke mulkan ƙasashe da yankuna kuma suna yin wasu ayyukan da mu ma muke mora. Kiristoci suna bin abin da ke littafin Romawa 13:​1-7. (Karanta.) Muna daraja “shugabannin gwamnati,” kuma muna bin dokar kowace ƙasa ko yankin da muke zama. Wataƙila dokar za ta iya shafan iyalinmu ko sana’armu ko kuma dukiyarmu. Alal misali, hukumomin gwamnati suna iya ce mu biya haraji ko kuma su bukaci wani bayani daga wurinmu. Amma me ya kamata mu yi idan gwamnati ta ce mu yi wani abin da ya taka dokar Allah? Manzo Bitrus ya ce: “Dole ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mu yi wa mutum.” ​—Ayyukan Manzanni 5:​28, 29.

19 A kowane irin sha’ani da muke yi da hukumomin gwamnati kamar su alƙali ko ɗan sanda, mu yi musu biyayya. Kiristoci matasa suna yin biyayya ga malaman makarantarsu da kuma wasu ma’aikatan makarantar. Muna daraja shugabanninmu a wurin aiki ko da wasu ba sa yin hakan. Idan muka yi biyayya, muna koyi da manzo Bulus ne domin ya yi biyayya ga hukumomi, ko da yin hakan ya masa wuya a wasu lokuta. (Ayyukan Manzanni 26:​2, 25) Ko da wasu sun yi mana rashin mutunci, mu ci gaba da yi musu biyayya.​—Karanta Romawa 12:​17, 18; 1 Bitrus 3:15.

20, 21. Wane sakamako mai kyau ne za a samu idan muna daraja mutane?

20 A ko’ina a duniya mutane ba sa yawan daraja juna. Amma ba haka bayin Jehobah suke ba. Niyyarmu ita ce mu daraja kowa da kowa. Muna bin gargaɗin manzo Bitrus cewa: “Ku ba da girma ga kowa.” (1 Bitrus 2:17) Mutane sukan lura da yadda muke daraja su. Shi ya sa Yesu ya ce: “Bari ku zama masu haske ga mutane, domin idan suka ga ayyuka masu kyau da kuke yi, za su ɗaukaka Ubanku wanda yake cikin sama.”​—Matiyu 5:16.

21 Idan muna yin biyayya a iyalinmu da ikilisiya da kuma wasu ɓangarori na rayuwa, hakan zai sa mutane su yi marmarin sanin Jehobah. Kuma idan muka daraja mutane muna yin hakan ne ga Jehobah. Hakan zai sa shi farin ciki kuma zai gane cewa muna ƙaunar sa.