Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 6

Yadda Za Mu Zabi Nishadin da Ya Dace

Yadda Za Mu Zabi Nishadin da Ya Dace

“Ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.”​—1 KORINTIYAWA 10:31.

1, 2. Me ya sa muke bukatar mu yi hankali sosai idan muna zaɓan nishaɗi?

A CE kana so ka ci wani ’ya’yan itace, sai ka ga cewa akwai inda ya ruɓe a jikinsa. Mene ne za ka yi? Za ka ci shi haka? Ko za ka yar da shi? Ko kuma za ka yanke gefen da ya ruɓe, sai ka ci gefen da bai ruɓe ba?

2 Fina-finai da waƙoƙi da kuma littattafai suna kama da ’ya’yan itacen nan. Wasu suna da kyau, amma mafi yawa ba su da kyau domin akan yi lalata da mugunta da kuma sihiri a cikinsu. Saboda haka, yaya kake zaɓan abin da za ka kalla ko za ka saurara? Shin kana ganin kana da ’yancin kallon kowanne irin bidiyo ko waƙar da kake so ne? Ko kana ganin dukansu suna da haɗari? Ko kuma kakan kalli masu kyau kuma ka ƙi marasa kyau?

3. Mene ne ya kamata mu tuna yayin da muke zaɓan irin nishaɗin da za mu yi?

3 Dukanmu muna jin daɗin yin nishaɗi. Don haka, muna so mu yi zaɓi mai kyau. Shi ya sa ya dace mu riƙa tunani sosai a kan yadda nishaɗin zai shafi bautarmu ga Jehobah.

“KU YI KOME SABODA ƊAUKAKAR ALLAH”

4. Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce za ta taimaka mana mu san irin nishaɗin da ya dace?

4 A lokacin da muka yi baftisma, mun yi wa Jehobah alkawari cewa za mu bauta masa da dukan zuciyarmu. (Karanta Mai-Wa’azi 5:4.) Mun yi alkawari cewa za mu “yi kome saboda ɗaukakar Allah.” (1 Korintiyawa 10:31) Hakan yana nufin cewa za mu riƙa yin nufin Allah ko a lokacin da muke yin nishaɗi, ba sai a taro ko a wa’azi kawai ba.

5. Wace irin bauta ce Jehobah yake bukata a gare mu?

5 Duk wani abin da muke yi a rayuwarmu yana da alaƙa da bautarmu ga Jehobah. Shi ya sa Bulus ya ce: “Ku miƙa kanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki, da kuma abin karɓa ga Allah.” (Romawa 12:1) Yesu ya ce: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.” (Markus 12:30) Muna son mu riƙa bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. A zamanin Isra’ilawa na dā, an gaya musu cewa idan za su ba da hadaya, su yi hakan da dabbar da take da ƙoshin lafiya. Idan dabbar tana da wata illa, Allah ba zai karɓi hadayar ba. (Littafin Firistoci 22:​18-20) Haka ma, Jehobah zai iya ƙin amincewa da bautarmu. Ta yaya?

6, 7. Ta yaya abubuwan da muke kalla ko saurara za su iya shafan bautarmu ga Jehobah?

6 Jehobah ya ce mana: “Ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne.” (1 Bitrus 1:​14-16; 2 Bitrus 3:11) Idan bautarmu ba ta kasance da tsabta ba, Jehobah ba zai amince da ita ba. (Maimaitawar Shari’a 15:21) Idan muna yin abubuwan da Jehobah ba ya so, kamar kallon fina-finai ko waƙoƙin da ake lalata da mugunta da kuma sihiri a ciki, bautarmu za ta kasance marar tsabta. (Romawa 6:​12-14; 8:13) Har ila, idan muna jin daɗin kallo ko saurarar su, hakan zai ɓata wa Jehobah rai. Hakan zai ƙazantar da bautarmu kuma Jehobah ba zai amince da ita ba. Ban da haka, dangantakarmu da shi za ta lalace.

7 Saboda haka, ta yaya za mu zaɓi fina-finai da waƙoƙin da suka dace? Waɗanne ƙa’idodi ne za su taimaka mana mu san waɗanda suke da kyau da waɗanda ba su da kyau?

KA ƘI MUGUNTA

8, 9. Wane irin nishaɗi ne ya kamata mu guje wa? Me ya sa?

8 A yau, akwai fina-finai da waƙoƙi da yawa. Wasu suna da kyau, amma mafi yawa daga cikinsu ba su dace da Kiristoci ba. Bari mu fara tattauna waɗanda ya kamata mu guje musu.

9 Yawancin fina-finai da shafuffukan intane da waƙoƙi da kuma wasannin bidiyo suna cike da lalata da mugunta da kuma sihiri. Abubuwan nan suna da haɗari, amma akan nuna su kamar ba su da haɗari kuma suna sa mutane dariya. Amma ya kamata Kiristoci su guji yin nishaɗi da irin waɗannan abubuwan domin sun saɓa wa ƙa’idodin Allah. (Ayyukan Manzanni 15:​28, 29; 1 Korintiyawa 6:​9, 10) Idan mun guje su, hakan zai nuna wa Jehobah cewa muna ƙin mugunta.​—Zabura 34:14; Romawa 12:9.

10. Me zai iya faruwa idan muna kallon abubuwan da ba su da kyau?

10 Amma wasu mutane suna ganin ba laifi ba ne a kalli fina-finai ko sauti ko kuma wasannin bidiyo da ke nuna lalata da mugunta da kuma sihiri. Sukan ce: ‘Ina laifin kallon su? Ba zan taɓa aikata abubuwan ba.’ Idan muna irin wannan tunanin, ruɗin kanmu kawai muke yi. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyar mutum ta fi kome ruɗu, cike take kuma da mugunta.” (Irmiya 17:9) Idan muna jin daɗin kallon abubuwan da Jehobah ba ya so, ta yaya za mu ce muna ƙin su? Da zarar mun ci gaba da kallon su, za mu ci gaba da ƙaunar su. A sannu a hankali, zuciyarmu za ta daina aiki. Ba za ta kāre mu ba idan muna son mu yi abin da bai dace ba.​—Zabura 119:70; 1 Timoti 4:​1, 2.

11. Ta yaya Galatiyawa 6:7 za ta taimaka mana mu yi zaɓin da ya dace?

11 Kalmar Allah ta ce: “Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.” (Galatiyawa 6:7) Hakika, idan muna jin daɗin kallon abubuwa marasa kyau, a-kwana-a-tashi, za mu soma yin su. Alal misali, wasu Kiristoci sun shaƙu da fina-finai da littattafan batsa kuma hakan ya sa sun yi lalata. Amma Jehobah yana taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace.

KA YI ZAƁIN DA YA YI DAIDAI DA ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI

12. Mene ne zai taimaka mana mu zaɓi abin kallo ko waƙoƙin da suka dace?

12 Akwai wasu nishaɗi da za mu iya ganewa kai tsaye cewa Jehobah ba ya so kuma dole ne mu guje musu. Amma in muna shakka kuma fa? Jehobah bai gaya mana abubuwan da za mu kalla ko saurara ko kuma karanta ba. A maimakon haka, yana son mu yi amfani da tunanin zuciyarmu wanda muka horar da Littafi Mai Tsarki. (Karanta Galatiyawa 6:5.) Jehobah ya ba mu ƙa’idodinsa kuma su ne suke sa mu san ra’ayinsa game da kowane abu. Ƙa’idodin ne suke shirya zuciyarmu. Suna taimaka mana mu san “nufin Ubangiji” kuma mu yi abin da yake so.​—Afisawa 5:17.

Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau

13. Me ya sa zaɓin da Kiristoci suke yi a kan nishaɗi ya bambanta? Amma mene ne kowanne Kirista yake bukatar ya yi?

13 Zaɓin da Kiristoci suke yi a kan fina-finai da waƙoƙi ba zai zama iri ɗaya ba. Me ya sa? Domin ra’ayinmu ba ɗaya ba ne, abin da wani yake so ba shi ne wani yake so ba. Amma duk da haka, kowane Kirista yana bukatar ya bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don ya yi zaɓin da ya dace. (Filibiyawa 1:9) Ƙa’idodin za su taimaka mana mu yi zaɓin da za su faranta ma Allah rai.​—Zabura 119:​11, 129; 1 Bitrus 2:16.

14. (a) Me ya sa ya kamata mu yi la’akari da yadda muke amfani da lokacinmu? (b) Wane gargaɗi ne Bulus ya ba Kiristoci?

14 Mu kuma yi la’akari da lokacin da muke amfani da shi don yin nishaɗi. Hakan zai nuna muhimmancin nishaɗi a gare mu. Ya kamata bautarmu ga Jehobah ta fi kome muhimmanci a rayuwarmu. (Karanta Matiyu 6:33.) Amma in ba mu yi hankali ba, nishaɗi zai fi ci mana lokaci. Ga gargaɗin da Bulus ya ba Kiristoci: “Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, sai dai kamar masu hikima. Ku yi amfani da kowane zarafi na yin kirki.” (Afisawa 5:​15, 16) Don haka, ya kamata mu rage yawan lokacin da muke amfani da shi wajen yin nishaɗi, kuma mu fi mai da hankali ga ayyukan ibadarmu.​—Filibiyawa 1:10.

15. Ta yaya za mu kāre kanmu daga nishaɗin da zai iya ɓata dangantakarmu da Allah?

15 Dole ne mu guji duk wani nishaɗin da muka san cewa Jehobah ba ya so. Amma, waɗanda muke shakka ko sun dace ko ba su dace ba fa? Shin su ma ya kamata mu yi hankali da su? E. Alal misali, idan ka hau dutse kana tafiya, ba za ka bi inda za ka faɗi ba in kana son ranka. A maimakon haka, za ka mai da hankali sosai don kar ka faɗi ka rasa ranka. Wannan kwatancin ya yi daidai da yadda muke zaɓan nishaɗi. Kalmar Allah ta ce: “Cire ƙafarka daga hanyar mugunta.” (Karin Magana 4:​25-27) Don haka, ba sai nishaɗin da muka san bai dace ba ne za mu guje wa. Amma har da wanda muke ganin zai iya ɓata dangantakarmu da Allah.

ABIN DA JEHOBAH YAKE SO

16. (a) Waɗanne abubuwa ne Jehobah ba ya so? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙin abubuwan da Jehobah ba ya so?

16 Mai zabura ya ce: “Ku da kuke ƙaunar Yahweh, ku ƙi mugunta!” (Zabura 97:10) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abubuwan da Jehobah yake so da kuma ra’ayinsa. Ka yi tunani a kan yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka so abubuwan da Jehobah yake so. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ba ya son “harshe mai faɗin ƙarya, da hannuwa masu zub da jinin marasa laifi, da zuciya mai ƙulle-ƙullen mugunta, da ƙafa mai saurin aikata mugunta.” (Karin Magana 6:​16-19) Mun kuma koya cewa dole ne mu guji “lalata, da . . . bautar gumaka, da maitanci, . . . da kishin juna, da fushi, . . . da buguwa, da bukukuwan shaye-shaye, da kuma sauran irin abubuwa kamar haka.” (Galatiyawa 5:​19-21) Shin ka lura da yadda waɗannan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka ka yi zaɓin da ya dace? Ko muna cikin jama’a ko kuma inda babu kowa, mu riƙa yin abubuwan da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (2 Korintiyawa 3:18) Abubuwan da muke yi a inda ba kowa ne suke nuna ainihin halinmu.​—Zabura 11:4; 16:8.

17. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu kafin mu zaɓi nishaɗi?

17 Saboda haka, kafin ka zaɓi fina-finan da za ka kalla ko waƙoƙi da dai sauransu, ka tambayi kanka: ‘Ta yaya zaɓin da na yi zai shafi dangantakata da Jehobah? Yaya zai shafi zuciyata?’ Bari mu tattauna wasu ƙarin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu yi zaɓin da ya dace.

18, 19. (a) Wace shawara ce Bulus ya ba Kiristoci? (b) Wace ƙa’ida ce za ta taimaka mana mu zaɓi fina-finan da suka dace?

18 Abin da muke kalla ko saurara ko kuma karantawa su ne abubuwan da za su mamaye zukatanmu. Manzo Bulus ya ce: “Iyakar abin da yake na gaskiya, da iyakar abin da ya isa bangirma, da iyakar abin da yake daidai, da iyakar abin da yake jawo ƙauna, da iyakar abin da yake na kirki, wato a kan dukan abin da yake mafi kyau, ko abin da ya isa yabo, a kan waɗannan sai ku yi tunani.” (Filibiyawa 4:8) Idan muka cika zukatanmu da waɗannan abubuwa masu kyau, mu ma za mu iya ce: “Bari maganar bakina da tunanin zuciyata su zama abin karɓa a gare ka, ya Yahweh.”​—Zabura 19:14.

19 Ka tambayi kanka: ‘Mene ne ya fi mamaye zuciyata? Wani irin tunani nake yi bayan na kalli wani bidiyo? Zuciyata takan dame ni ne? (Afisawa 5:5; 1 Timoti 1:​5, 19) Zan iya yin addu’a ga Jehobah da zuciya ɗaya ko kuma hankalina yakan tashi? Bidiyon yana sa ni tunanin yin lalata ko kuma mugunta? (Matiyu 12:33; Markus 7:​20-23) Shin irin bidiyon da nake kalla yana sa in yi rayuwa ko “tunani irin na zamanin nan” ne?’ (Romawa 12:2) Idan muka gaya wa kanmu gaskiya game da tambayoyin nan, hakan zai taimaka mana mu san abin da za mu yi don mu ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah. Mu ma muna son mu yi addu’a kamar yadda mai zabura ya yi cewa, ka “kawar da idanuna daga abubuwan banza.” *​—Zabura 119:37.

SHAWARAR DA MUKA TSAI DA TAKAN SHAFI MUTANE

20, 21. Me ya sa ya kamata mu yi la’akari da mutane yayin da muke zaɓan nishaɗin da za mu yi?

20 Wata ƙa’ida kuma da ya kamata mu tuna ita ce: “Dukan abubuwa an yarda mana, amma ba dukan abubuwa ne suke ginawa ba. Kada ka yi wa kanka kaɗai abu mai kyau, amma ka yi wa ɗan’uwanka kuma.” (1 Korintiyawa 10:​23, 24) Za mu iya zama da ’yancin yin wani abu, amma idan yin hakan zai dami zuciyar ’yan’uwanmu, ba dole sai mun yi abin ba. Zai dace mu riƙa yin la’akari da yadda abubuwan da muke yi za su iya shafan ’yan’uwanmu maza da mata.

21 Tunanin zuciyarmu da na ’yan’uwanmu ba ɗaya ba ne. Alal misali, za ka iya kallon wani shirin talabijin kuma zuciyarka ba za ta dame ka ba. Amma me za ka yi idan ka lura cewa wannan shirin talabijin yana damun zuciyar wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa? Za ka iya daina kallon shirin ko da yake kana da ’yancin kallo. Me ya sa? Domin ba ka son ka ‘yi wa ’yan’uwanka laifi,’ ko ka “yi wa Almasihu laifi.” (1 Korintiyawa 8:12) Ba ma so mu yi kome da zai sa ’yan’uwanmu tuntuɓe.​—Romawa 14:1; 15:1; 1 Korintiyawa 10:32.

22. Ta yaya za mu nuna sanin-ya-kamata idan wani Kirista ya yi zaɓin da bai yi daidai da namu ba?

22 Idan kuma lamirinka bai bar ka ka kalli wani bidiyo ko ka yi abin da wani ɗan’uwanka yake yi ba fa? Don kana ƙaunar ɗan’uwanka, kuma kana daraja shi, ba za ka nace sai ya yi abin da ka fi so ba. Matukin mota ya san cewa akwai wasu direbobin da suka fi shi gudu, wasu kuma ba su kai shi gudu ba, amma dukansu sun iya tuki. Haka nan ma, zai yiwu cewa kai da wani Kirista kuna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, amma ba a kowane lokaci ne zaɓinku zai zama ɗaya ba.​—Mai-Wa’azi 7:16; Filibiyawa 4:5

23. Me zai taimaka mana mu yi zaɓin da ya dace?

23 Me zai taimaka mana mu zaɓi fina-finai da waƙoƙin da suka dace? Idan muna amfani da lamirinmu da muka horar da shi da Littafi Mai Tsarki kuma muna ƙaunar ’yan’uwanmu, za mu yi zaɓin da ya dace. Kuma za mu yi farin ciki domin muna “yin kome saboda ɗaukakar Allah.”

^ sakin layi na 19 Akwai wasu ƙa’idodin da za su taimaka mana mu zaɓi fina-finai da waƙoƙin da suka dace a Karin Magana 3:31; 13:20; da kuma Kolosiyawa 3:​5, 8, 20.