Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 11

Zaman Aure

Zaman Aure

“Ƙauna ba ta ƙārewa har abada.”​—1 KORINTIYAWA 13:8.

1, 2. Matsalolin da ma’aurata suke fuskanta ya nuna cewa ba za su ji daɗin aurensu ba ne? Ka bayyana.

AURE kyauta ne da Jehobah ya ba mu. Ko da yake aure yakan sa mutum ya yi farin ciki a rayuwa, duk da haka, ma’aurata suna iya fuskantar matsaloli. A wasu lokuta za a ga kamar ba za a iya magance matsalolin ba. Kuma ma’auratan ba za su ƙaunaci juna kamar yadda suka yi da farko ba.

2 Bai kamata mu yi mamaki ba idan a wasu lokuta muna fuskantar matsaloli a aurenmu. Matsalolin da muke fuskanta ba za su hana mu jin daɗin aurenmu ba. Ko ma’auratan da suka fuskanci matsaloli masu tsanani ma sun iya magance su kuma suna zaman lafiya. Ta yaya suka yi hakan?

KU KUSACI ALLAH DA KUMA JUNA

3, 4. Me zai iya faruwa da ma’aurata a wasu lokuta?

3 Aure yana haɗa kan mutane biyu waɗanda halinsu da ra’ayinsu da kuma yadda suke yin abubuwa ya bambanta. Ban da haka ma, mata da miji za su iya fitowa daga ƙabilu dabam-dabam. Don haka, yana ɗaukan lokaci sosai kafin ma’aurata su fahimci juna da kyau.

4 Amma bayan wani lokaci, ma’aurata za su iya shaƙuwa da ayyukansu kuma su daina ƙaunar juna kamar yadda suka saba. Yanayin zai iya zama kamar kowa ta kansa yake yi. Amma me zai taimaka musu su ƙaunaci juna sosai?

Shawarar Littafi Mai Tsarki tana ƙarfafa aure sosai

5. (a) Me zai taimaka wa ma’aurata su ƙaunaci juna sosai? (b) Yaya Ibraniyawa 13:4 ta ce mu riƙa ɗaukan aure?

5 Jehobah ya ba ma’aurata shawarar da za ta taimaka musu su ƙaunaci juna sosai. (Zabura 25:4; Ishaya 48:​17, 18) Jehobah ya ce: “Zaman aure ya zama abin daraja a gare ku duka.” (Ibraniyawa 13:4) Babu shakka, ba za ka yi wasa da abin da yake da daraja a gare ka ba. Za ka kula da abin kuma ka kāre shi. Haka Jehobah yake so mu riƙa ɗaukan aure.

AURE ZAI YI DAƊI IDAN MA’AURATA SUNA ƘAUNAR JEHOBAH

6. Yaya Jehobah yake ɗaukan aure bisa Matiyu 19:​4-6?

6 Jehobah ne ya haɗa aure na farko. Ɗansa Yesu ya ce: “Ashe, ba ku karanta ba cewa, shi Mahaliccin da ya yi su tun farko ‘ya yi su ne namiji da ta mace?’ Ya kuma ce, ‘Domin haka fa, mutum zai bar babansa da mamarsa ya manne wa matarsa, su biyun kuma su zama ɗaya.’ Har nan gaba ba za su zama mutum biyu ba, sai dai su zama kamar mutum ɗaya. Saboda haka, abin da Allah ya haɗa, kada wani ya raba.” (Matiyu 19:​4-6) Tun da farko Jehobah bai so ma’aurata su riƙa kashe aure ba. Ya so iyalai su ƙaunaci juna, su yi farin ciki kuma su ji daɗin rayuwa.

7. Ta yaya ma’aurata za su iya ƙarfafa aurensu?

7 Amma ma’aurata na yanzu suna fuskantar matsaloli sosai fiye da na dā. A wasu lokuta sukan ɗauka cewa matsalolinsu sun fi ƙarfinsu kuma mafitar ita ce su kashe auren. Amma sanin yadda Jehobah yake ɗaukan aure zai taimaka wa ma’aurata sosai.​—1 Yohanna 5:3.

8, 9. (a) A wane lokaci ne ya kamata mu bi shawarar Jehobah game da aure? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja aurenmu?

8 Jehobah yana ba mu shawara don mu amfana a koyaushe. Kamar yadda muka karanta, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada gadon aurenku ya ƙazantu.” (Ibraniyawa 13:4; Mai-Wa’azi 5:4) Zai dace mu bi ja-gorancin Jehobah ko cikin daɗi ko cikin wahala don yin hakan zai amfane mu sosai.​—1 Tasalonikawa 1:3; Ibraniyawa 6:10.

9 Da yake muna daraja aurenmu, ba za mu so mu yi ko mu faɗi wani abin da zai ɓata aurenmu ba. A maimakon haka, muna so mu ƙarfafa aurenmu sosai. Ta yaya za mu yi hakan?

KU DARAJA JUNA TA FURUCINKU DA AYYUKANKU

10, 11. (a) Waɗanne matsaloli ne wasu ma’aurata suke fuskanta? (b) Me ya sa zai dace mu yi hankali da irin maganar da muke gaya wa mazajenmu ko matanmu?

10 Akwai hanyoyi da yawa da ma’aurata za su iya sa juna baƙin ciki. Mun san cewa Kalmar Allah ba ta amince ma’aurata su yi faɗa ko kuma su ji wa ɗayansu rauni ba. Duk da haka, zai yiwu mu sa juna baƙin ciki ta furucinmu. Kalamanmu za su iya zama kamar kibiyoyi masu sūka. Wata mata ta ce: “Maigidana yakan min sūka da kalamansa. Ko da yake kalamansa ba sa saka min tabo a jikina, amma furucin da yake yi kamar, ‘Ke damuwa ce!’ da ‘Ba ki da amfani a gare ni!’ suna ɓata min rai sosai.” Wani mutum ya ce matarsa takan zazzage shi kuma hakan yana ƙaskantar da shi sosai. Ya ce: “Da yake ba na so in yi cacar baki da ita, ba na tanka mata kuma nakan yi dare a wurin aiki don in guji masifa.” Ma’aurata a yau suna zage-zage da faɗin abubuwan da ba su dace wa juna ba, kuma hakan yakan jawo baƙin ciki sosai.

11 Idan ma’aurata suka yi wa juna baƙar magana, hakan na sa baƙin ciki kuma yakan ɗauki lokaci kafin su manta. Amma ba haka Jehobah yake so ma’aurata su bi da juna ba. Ma’aurata za su iya ɓata wa juna rai ba tare da saninsu ba. Maigida zai iya ganin cewa yana daraja matarsa amma macen kuma fa, haka take ji? Idan akwai furucin da kuka yi da ya ɓata ma junanku rai, za ku iya roƙan gafara kuma ku daina faɗin hakan?​—Galatiyawa 5:15; karanta Afisawa 4:31.

12. Me zai iya shafan dangantakar ma’aurata da Jehobah?

12 Yadda muke magana da juna a gida ko a cikin jama’a yana da muhimmanci a gaban Jehobah. (Karanta 1 Bitrus 3:7.) Yaƙub 1:26 ta ce: “Idan wani yana tsammani shi mai addini ne sosai, amma ba ya kame bakinsa, to, yana ruɗin kansa ne, addininsa kuma banza ne.”

13. A wace hanya ce kuma ma’aurata za su iya ɓata wa juna rai?

13 Akwai wasu hanyoyi ma da ya kamata ma’aurata su mai da hankali sa’ad da suke sha’ani da juna. Alal misali, yaya ma’aurata za su ji idan ɗayansu ya soma kusantar wani da ba mijinta ko matarsa ba? Matarka tana ɓata rai idan ta gan ka da wata ko da wa’azi kuke yi tare ko kuma kana taimaka mata? Wata mata ta ce: “Idan na ga maigidana yana mai da hankali sosai ga wata ’yar’uwa a ikilisiya, hakan yakan ɓata min rai. Sai in ji kamar ba ni da wani muhimmanci a wurinsa.”

14. (a) Me muka koya a littafin Farawa 2:24? (b) Me ya kamata mu tambayi kanmu?

14 Mu Kiristoci muna da hakkin kula da iyayenmu da kuma ’yan’uwanmu a ikilisiya. Duk da haka, idan muka yi aure, kula da maigidanmu ko matarmu ne zai fi muhimmanci. Jehobah ya ce maigida ya “manne wa matarsa.” (Farawa 2:24) Ya kamata miji ya ɗauki ra’ayin matarsa da muhimmanci kuma matar ma ta yi hakan. Don haka, za ka iya tambayar kanka: ‘Ina ƙaunar matata ko mijina kuma ina ba shi ko ba ta lokacin da take bukata?’

15. Me ya sa ya kamata ma’aurata su guji kusantar wani ko wata da ba matarsu ko mijinsu ba?

15 Idan muna yawan kusantar wani da ba matarmu ko mijinmu ba, hakan zai iya ɓata aurenmu. Kuma a sannu a hankali, za mu soma son mutumin. (Matiyu 5:28) Wannan sha’awar za ta iya yin ƙarfi har ta sa mu yi wani abin da zai ɓata aurenmu.

“KADA GADON AURENKU YA ƘAZANTU”

16. Wace doka ce Littafi Mai Tsarki ya bayar game da aure?

16 Bayan Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zaman aure ya zama abin daraja a gare ku duka,” ya ƙara da cewa “kada gadon aurenku ya ƙazantu, gama Allah zai hukunta masu yin zina da masu yin lalata.” (Ibraniyawa 13:4) “Gadon” da aka ambata a ayar nan yana nufin jima’i tsakanin mata da miji. (Karin Magana 5:18) Ta yaya ma’aurata za su daraja wannan tanadin kuma kada su ƙazantar da shi?

17. (a) Yaya mutane da yawa suke ɗaukan zina? (b) Wane ra’ayi ne ya kamata Kiristoci su zama da shi game da zina?

17 Wasu mutane suna ganin cewa cin amanar aure ba laifi ba ne. Bai kamata mu bar wannan halin ya shafe mu ba. Jehobah ya gaya mana dalla-dalla cewa ba ya son lalata da zina. (Karanta Romawa 12:9; Ibraniyawa 10:31; 12:29) Idan muka yi jima’i da wani da ba mijinmu ko matarmu ba, mun ƙazantar da gadon aurenmu. Hakan zai nuna cewa ba ma daraja ƙa’idodin Jehobah kuma za mu ɓata dangantakarmu da shi. Don haka, zai dace mu guji yin wani abin da zai kai ga yin lalata. Hakan ya ƙunshi yin tunanin da bai dace ba game da wani ko wata.​—Ayuba 31:1.

18. (a) Me ya sa zina ta yi daidai da bautar gumaka? (b) Yaya Jehobah yake ɗaukan zina?

18 Bisa dokar da aka bayar ta hannun Musa ga Isra’ila ta dā, zina zunubi ce mai tsanani kamar bautar gumaka. Kuma akan kashe duk wanda ya yi zina ko bautar gumaka. (Littafin Firistoci 20:​2, 10) Ta yaya zina ta yi daidai da bautar gumaka? Idan Ba-isra’ile ya bauta ma wasu alloli, ya karya alkawarin da ya yi wa Jehobah cewa zai bauta masa shi kaɗai. Idan ya yi zina, har ila ya karya alkawarin da ya yi wa matarsa cewa zai ƙaunace ta ita kaɗai. (Fitowa 19:​5, 6; Maimaitawar Shari’a 5:9; karanta Malakai 2:14.) Hakan ya nuna cewa a dā, Jehobah yana ɗaukan zina a matsayin zunubi mai tsanani.

19. Me zai taimaka mana kar mu yi zina?

19 Wane darasi ne hakan ya koya mana? Ko da yake ba ma bin Dokar da aka bayar ta hannun Musa, har ila ra’ayin Jehobah game da zina bai canja ba. Kamar yadda ba ma bauta ma wasu allolin ƙarya, bai kamata mu ci amanar matarmu ko mijinmu ba. (Zabura 51:​1, 4; Kolosiyawa 3:5) Idan muka yi hakan, za mu ɓata aurenmu da kuma dangantakarmu da Jehobah.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 26.

YADDA ZA KU ƘARFAFA AURENKU

20. Ta yaya hikima za ta iya taimaka wa ma’aurata?

20 Ta yaya za ku ƙara ƙarfafa aurenku? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurin hikima ake ginin gida, ta wurin fahimta kuma ake kafa ta.” (Karin Magana 24:3) Gida zai iya zama da kyau da kuma ƙarfi ko kuma ya zama marar kyau da haɗari. Haka yake da aure. Mutum mai hikima zai tabbata cewa aurensa ko aurenta ya kasance mai daɗi.

21. Ta yaya sani zai ƙarfafa aure?

21 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da gidan nan ya ce: “Ta wurin sani ake ciccika ɗakuna da dukan kaya masu daraja da na arziki.” (Karin Magana 24:4) Abin da ka koya a Littafi Mai Tsarki zai iya gyara aurenka. (Romawa 12:2; Filibiyawa 1:9) Zai dace ma’aurata su karanta Littafi Mai Tsarki da littattafanmu tare don su ga darussan da za su koya. Ku nemi hanyoyin da za ku ƙaunaci juna da kuma daraja juna. Ban da haka ma, za ku iya neman hanyoyin da za ku yi wa juna alheri. Ku roƙi Jehobah ya taimaka muku ku kasance da halayen da za su ƙarfafa aurenku kuma su sa ku ƙaunaci juna.​—Karin Magana 15:​16, 17; 1 Bitrus 1:7.

Ku bi ja-gorancin Jehobah sa’ad da kuke ibada ta iyali

22. Me ya sa ya kamata ma’aurata su nuna ƙauna da ladabi da biyayya?

22 Zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ƙaunaci matarmu ko mijinmu kuma mu mutunta ko daraja juna. Hakan zai sa aurenmu ya kasance da ƙarfi kuma mu ji daɗinsa. Abu mafi muhimmanci kuma shi ne, zai sa Jehobah farin ciki.​—Zabura 147:11; Romawa 12:10.