Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 2

Mu Bauta wa Allah da Zuciya Mai Tsabta

Mu Bauta wa Allah da Zuciya Mai Tsabta

“Ku tabbata kun kasance da tunaninku babu laifi.” ​—1 BITRUS 3:16.

1, 2. Me ya sa muke bukatar ja-goranci idan muka sami kanmu a wurin da ba mu sani ba? Mene ne Jehobah ya ba mu da zai taimaka mana?

A CE kana so ka je wani wuri da dare. Mene ne za ka ɗauka don kada ka yi tuntuɓe ka faɗi? Idan ka ɗauki toci, zai taimaka wajen haska maka hanya. Neman ja-goranci ko taimako yana da muhimmanci domin idan ka san inda za ka, ba za ka shiga damuwa ba.

2 Dukanmu muna fuskantar matsaloli sosai a rayuwa kuma a wasu lokuta, za mu iya rasa abin da za mu yi. Amma Jehobah ya ba wa kowannenmu zuciya don ta riƙa mana ja-goranci. (Yaƙub 1:17) Bari mu bincika ma’anar zuciya kuma mu san yadda take aiki. Bayan haka, za mu bincika yadda za mu shirya zuciyarmu da kuma yadda za mu riƙa yin la’akari da mutane. A ƙarshe, za mu koyi yadda zuciya mai kyau za ta sa mu yi rayuwa mai kyau.

MECE CE ZUCIYA KUMA TA YAYA TAKE AIKI?

3. Mece ce zuciya?

3 Zuciyarmu babbar kyauta ce daga Jehobah. Tana taimaka mana mu san abin da yake da kyau da wanda babu kyau. Kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “tunanin zukatansu” a Littafi Mai Tsarki tana nufin “sanin kanka.” Idan zuciyarmu tana aiki da kyau, za ta sa mu bincika kanmu kuma mu san ainihin yadda muke. Ban da haka ma, za ta sa mu san ainihin tunaninmu da yadda muke ji. Za ta taimaka mana mu riƙa yin abu mai kyau kuma mu ƙi marar kyau. Ƙari ga haka, za ta sa mu riƙa farin ciki a duk lokacin da muka tsai da shawara mai kyau kuma mu yi baƙin ciki a lokacin da muka tsai da shawarar da ba da dace ba.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 5.

4, 5.  (a) Me ya faru a lokacin da Adamu da Hauwa’u suka ƙi bin abin da zuciyarsu ta gaya musu? (b) Waɗanne labaran Littafi Mai Tsarki ne suka nuna yadda zuciya take aiki?

4 Dukanmu muna da zaɓi, ko mu bi abin da zuciyarmu take gaya mana ko mu ƙi yin hakan. Adamu da Hauwa’u sun ƙi su bi abin da zuciyarsu ta gaya musu, shi ya sa suka yi zunubi. Ko da yake sun yi baƙin ciki daga baya, amma ba abin da za su iya yi don sun riga sun yi wa Allah rashin biyayya. (Farawa 3:​7, 8) Ko da yake su ba masu zunubi ba ne a lokacin kuma sun san cewa ba shi da kyau a yi wa Allah rashin biyayya, sun ƙi su yi abu mai kyau da zuciyarsu ta gaya musu.

5 Amma akwai wasu mutane ajizai da suka bi abu mai kyau da zuciyarsu ta gaya musu. Ayuba yana cikin waɗannan mutanen. Ya tsai da shawarwari masu kyau, shi ya sa ya ce: “A dukan kwanakin raina, zuciyata ba ta taɓa kunyatar da ni ba.” (Ayuba 27:6) Sa’ad da Ayuba ya ambaci ‘zuciyarsa,’ yana nufin abin da yake taimaka masa ya san abin da yake da kyau da wanda bai da kyau. Dauda kuma fa? Akwai wasu lokutan da Dauda ya ƙi ya bi abu mai kyau da zuciyarsa ta gaya masa kuma ya yi zunubi ga Jehobah. Daga baya “ya damu” sosai saboda hakan. (1 Sama’ila 24:5) Hakan ya nuna cewa zuciyar Dauda ce take gaya masa cewa ya yi zunubi. Amma idan yana bin abu mai kyau da zuciyarsa take gaya masa, ba zai sake yin zunubin ba.

6. Me ya sa za mu ce zuciya kyauta ce daga Allah?

6 Mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ma a wasu lokuta suna sanin abubuwan da suke da kyau da waɗanda ba su da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama tunaninsu yakan same su da laifi a wani lokaci, a wani lokaci kuma ba ya samunsu da laifi.” (Romawa 2:​14, 15) Alal misali, yawancin mutane sun san cewa kisa da kuma yin sata bai da kyau. Waɗannan mutanen ba tare da saninsu ba suna bin abin da zuciyarsu take gaya musu, wato abin da Jehobah ya halicce su da shi da yake taimaka musu su san nagarta da mugunta. Ban da haka ma, suna bin ƙa’idodin da Allah ya tsara da suke taimaka mana mu tsai da shawara mai kyau.

7. Me ya sa a wasu lokuta zuciyarmu za ta iya yaudarar mu?

7 Amma a wasu lokuta, zuciyarmu za ta iya yaudarar mu. Alal misali, tunaninmu da ra’ayinmu na ajizanci za su iya lalata zuciyarmu, kuma hakan zai sa mu bi shawarar da ba ta dace ba. Amma mutum ba zai iya kasancewa da zuciya mai kyau haka kawai ba. (Farawa 39:​1, 2, 7-12) Sai ya shirya ta. Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su taimaka mana mu yi hakan. (Romawa 9:1) Bari mu bincika yadda za mu iya shirya zuciyarmu.

TA YAYA ZA MU SHIRYA ZUCIYARMU?

8. (a) Ta yaya tunaninmu zai iya shafan zuciyarmu? (b) Me ya kamata mu tambayi kanmu kafin mu yanke shawara?

8 Wasu mutane suna ganin cewa bin ra’ayinsu ɗaya yake da bin zuciyarsu. Suna ganin cewa za su iya yin duk wani abin da suka ga dama. Amma da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta tunaninmu zai iya yaudarar mu. Tunanin da muke yi yana da iko sosai har zai iya ɓata zuciyarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyar mutum ta fi kome ruɗu, cike take kuma da mugunta ƙwarai. Wa zai iya saninta?” (Irmiya 17:9) Don haka, a wasu lokuta za mu iya ganin cewa tunaninmu ya dace alhali bai dace ba. Alal misali, kafin Bulus ya zama Kirista, ya tsananta wa mutanen Allah sosai kuma ya ɗauka cewa abin da yake yi daidai ne. A ganinsa, zuciyarsa mai kyau ce. Amma da ya fahimci cewa Jehobah ba ya son abin da yake yi, sai ya tuba. Daga baya ya ce: “Ubangiji ne zai gwada ni.” (1 Korintiyawa 4:4; Ayyukan Manzanni 23:1; 2 Timoti 1:3) Babu shakka, kafin mu yanke shawara, zai dace mu yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Shin Jehobah zai so in yi wannan abin?’

9. Mene ne tsoron Allah yake nufi?

9 Idan kana ƙaunar wani ko wata, ba za ka yi abin da zai ɓata masa ko mata rai ba. Don haka, da yake muna ƙaunar Jehobah, muna tsoron yin wani abin da zai ɓata masa rai. Kuma ya kamata mu ɗauki yin hakan da muhimmanci sosai. Mun ga hakan daga labarin Nehemiya. Bai yi amfani da matsayinsa na gwamna don ya zama mai arziki ba. Me ya sa? Ya ce domin yana “tsoron Allah.” (Nehemiya 5:15) Nehemiya bai yarda ya yi wani abin da zai ɓata wa Jehobah rai ba. Mu ma muna bin misalin Nehemiya, shi ya sa muke tsoron yin abin da zai ɓata wa Jehobah rai. Za mu iya sanin abubuwan da Jehobah yake so idan muna karanta Littafi Mai Tsarki.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 6.

10, 11. Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka mana mu san ko ya dace mu sha giya ko a’a?

10 Alal misali, Kirista yana iya tsai da shawara ko zai sha giya ko a’a. Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka masa ya yanke shawara mai kyau? Ga wasu misalai: Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya ba. A maimakon haka, ya ce giya kyauta ce daga wurin Allah. (Zabura 104:​14, 15) Amma Yesu ya gaya wa mabiyansa su guji ‘yawan shaye-shayen’ giya. (Luka 21:​34, Littafi Mai Tsarki) Manzo Bulus ma ya gaya wa Kiristoci su guji “shaye-shaye, da buguwa.” (Romawa 13:13) Ya ƙara da cewa, masu maye “ba za su shiga mulkin Allah” ba.​—1 Korintiyawa 6:​9, 10.

11 Don haka, Kirista zai iya tambayar kansa: ‘Shin dole ne in sha giya? Shin ina shan giya a duk lokacin da nake son in huta? Sai na sha giya kafin in kasance da ƙarfin zuciya? Zan iya rage yawan giyar da nake sha? * Shin zan iya jin daɗin liyafa da abokaina ko ba giya a wurin?’ Za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu iya tsai da shawarar da ta dace. (Karanta Zabura 139:​23, 24.) Ta haka ne muke shirya zuciyarmu ta riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Amma akwai wani abu da muke bukata mu yi da za mu tattauna a gaba.

DALILIN DA YA SA MUKE LA’AKARI DA MUTANE

12, 13. Me ya sa tunanin zuciyarmu ya bambanta da na wasu? Ta yaya za mu bi da wannan bambancin?

12 Tunanin zuciyarmu ba ɗaya yake da na sauran mutane ba. Abin da zuciyarka ta yarda ka yi, zuciyar wani ba za ta yarda masa ya yi ba. Alal misali, za ka iya tsai da shawarar shan giya, wani kuma ya ƙi yin hakan. Me ya sa ra’ayinku ya bambanta?

Idan ka shirya zuciyarka, za ta taimaka maka ka zaɓa ko za ka sha giya ko ba za ka sha ba

13 Wurin da mutum ya girma da ra’ayin iyalinsu da abubuwan da ya faru da shi a rayuwa da dai wasu abubuwa za su iya shafan tunaninsa. Idan ya zo ga batun shan giya, wani da yake yawan shan giya zai iya yanke shawarar daina sha gaba ɗaya. (1 Sarakuna 8:​38, 39) Don haka, idan ka ba ma wani giya kuma ya ƙi sha, yaya za ka ji? Za ka yi fushi ne? Shin za ka nace lallai sai ya sha? Ko kuma za ka so ya gaya maka dalilin da ya sa ya ƙi? A’a. Me ya sa? Domin kana yin la’akari da shi.

14, 15. Wane abu ne ya faru a zamanin manzo Bulus? Wace shawara ce Bulus ya bayar?

14 A zamanin manzo Bulus, akwai wani abin da ya faru da ya nuna yadda tunanin zuciyar mutane zai iya bambanta. Wasu naman da ake sayarwa a kasuwa an riga an yi amfani da su a bautar ƙarya ko kuma an yi hadaya da su ga gumaka. (1 Korintiyawa 10:25) Amma a wurin Bulus, ba laifi ba ne a ci irin wannan naman. A ganinsa, duk abincin da muke da shi Jehobah ne ya ba mu. Amma wasu ’yan’uwa da suka yi bautar gumaka a dā suna ganin cewa yin hakan bai dace ba sam. Shin Bulus ya yi tunanin cewa: ‘Ai zuciyata ba ta damu na kuma ina da ’yancin cin duk abin da nake so’?

15 Bulus bai yi irin wannan tunanin ba. Ya yi la’akari da ra’ayin ’yan’uwansa, shi ya sa ya daina wasu abubuwa ko da yake yana son yin su. Bulus ya ce bai kamata mu riƙa ‘nuna halin son kai’ ba. Ya ƙara da cewa: ‘Gama ko Almasihu bai yi son kai ba.’ (Romawa 15:​1, 3) Kamar yadda Yesu ya yi, Bulus ma ya yi la’akari da wasu, shi ya sa bai so kansa ba.​—Karanta 1 Korintiyawa 8:13; 10:​23, 24, 31-33.

16. Me ya sa bai kamata mu shar’anta ɗan’uwanmu don zuciyarsa ta yarda ya yi wani abu ba?

16 To, me zai faru idan zuciyar wani ta yarda masa ya yi wani abu da muke gani bai dace ba fa? Bai kamata mu nace a kan ra’ayinmu, muna ganin cewa mu muke da gaskiya, ba shi ba. (Karanta Romawa 14:10.) Allah ya ba mu zuciya don ta riƙa shar’anta mu ne ba don ta shar’anta mutane ba. (Matiyu 7:1) Don haka, ba ma son mu riƙa nacewa a kan ra’ayinmu domin zai iya kawo rashin haɗin kai a ikilisiya. Amma zai dace mu riƙa yin abubuwan da za su sa mu kasance da haɗin kai da juna.​—Romawa 14:19.

ZA MU AMFANA IDAN MUNA DA ZUCIYA MAI KYAU

17. Me ya faru da tunanin zuciyar wasu?

17 Manzo Bitrus ya ce: ‘Mu kasance da tunaninmu babu laifi.’ (1 Bitrus 3:16) Amma abin baƙin ciki shi ne, idan mutane suka ƙi bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma suka ci gaba da hakan, zuciyarsu za ta daina damunsu. Manzo Bulus ya ce irin waɗannan mutanen ‘tunanin zuciyarsu ya mutu, kamar an ƙona shi da ƙarfe mai wuta.’ (1 Timoti 4:2) Shin wuta ta taɓa ƙona ka? Idan aka taɓa ka a wurin, ba za ka ji kome ba. Haka ma yake, idan mutum ya ci gaba da yin zunubi, zuciyarsa za ta lalace.

Zuciya mai tsabta za ta taimaka mana a rayuwa kuma ta sa mu yi farin ciki kuma mu kasance da kwanciyar hankali

18, 19. (a) Idan hankalinmu ya ƙi kwantawa, me wataƙila hakan yake nufi? (b) Me za mu yi idan zuciyarmu tana damin mu don zunubin da Allah ya riga ya gafarta mana?

18 Idan hankalinmu ya ƙi kwantawa, mai yiwuwa zuciyarmu tana gaya mana cewa mun yi zunubi. Hakan zai sa mu bincika kanmu don mu san abin da muka yi kuma mu daina yin abin. Muna son mu riƙa koyan darussa daga kuskuren da muka yi don kada mu sake yi. Alal misali, ko da yake Sarki Dauda ya yi zunubi, amma zuciyarsa ta dame shi sosai shi ya sa ya tuba. Ya yi baƙin ciki don abin da ya yi kuma ya tsai da shawara cewa ba zai sake yi wa Jehobah rashin biyayya ba. Shi ya sa ya yi wannan furucin cewa Jehobah “mai-hanzarin gafartawa” ne.​—Zabura 51:​1-19; 86:​5, LMT; ka duba Ƙarin Bayani na 7.

19 Amma wasu suna iya yin baƙin ciki bayan sun tuba daga zunubin da suka yi da daɗewa. Irin wannan tunanin yana sa sanyin gwiwa kuma ya sa mutum ya ji kamar bai da wani amfani. Idan kana jin hakan a wasu lokuta, zai dace ka tuna cewa ba zai yiwu ka canja abin da ya riga ya faru ba. Ko da ka san abin da ke da kyau da abin da ba shi da kyau a lokacin da ka yi zunubin, Jehobah ya riga ya gafarta maka gaba ɗaya, ba ya ganinka da alhakin zunubin kuma. Yanzu kana da tsabta a gaban Jehobah kuma ka san cewa yanzu kana yin abin da ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ya fi zuciyarmu.” (Karanta 1 Yohanna 3:​19, 20.) Zai dace ka tabbata cewa Jehobah ya riga ya gafarta maka zunubinka. Hakan yana nufin cewa ƙaunar da yake mana da yadda yake gafarta wa mutane za su taimaka mana mu rage baƙin ciki da kuma kunyar da muke ji. Idan mutum ya amince cewa Jehobah ya gafarta masa, zuciyarsa ba za ta riƙa damunsa ba kuma zai riƙa bauta wa Allah da farin ciki.​—1 Korintiyawa 6:11; Ibraniyawa 10:22.

20, 21. (a) Mene ne wannan littafin zai taimaka maka ka yi? (b) Wane ’yanci ne Jehobah ya ba mu? Kuma ta yaya za mu yi amfani da shi?

20 An tsara wannan littafin ne don ya taimaka maka ka shirya zuciyarka don ta riƙa gargaɗe ka da kuma kāre ka a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Za ta taimaka maka ka yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a hanyoyi dabam-dabam na rayuwa. Hakika, wannan littafin bai ba mu jerin dokokin da za mu riƙa bi a kowane yanayi ba. Muna yin rayuwa ne bisa “koyarwar Almasihu.” (Galatiyawa 6:2) Kuma ba ma yin duk wani abin da muka ga dama don ba a kafa mana doka a kan kowane batu ba. (2 Korintiyawa 4:​1, 2; Ibraniyawa 4:13; 1 Bitrus 2:16) A maimakon hakan, muna amfani da ’yancinmu don mu nuna ma Jehobah cewa muna ƙaunarsa.

21 Idan muka yi bimbini a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi amfani da su, muna amfani da ‘hankalinmu’ domin mu kasance da ra’ayin Jehobah. (Ibraniyawa 5:14) Yin hakan zai shirya zuciyarmu don ta ja-gorance mu kuma ta taimaka mana mu ci gaba da ƙaunar Allah.

^ sakin layi na 11 Likitoci da yawa sun ce bai da sauƙi masu maye da giya su rage yawan shan giya. Shi ya sa likitoci suka shawarce su cewa zai dace su daina sha gabaki ɗaya.