Gabatarwar Sashe na 10
Jehobah shi ne Sarkin duniya gabaki ɗaya. Shi ne yake iko kuma zai ci gaba da kasancewa da iko. Alal misali, ya ceci Irmiya daga wata rijiyar da aka jefa shi ciki don ya mutu. Ya ceci Shadrach da Meshach da kuma Abednego daga wuta mai zafi. Ya kuma ceci Daniyel daga hannun zakuna. Jehobah ya kāre Esther don ta iya ceton mutanenta. Ba zai bar mutane su ci gaba da yin mugunta har abada ba. Annabcin da aka yi game da babban gunki da kuma bishiya sun nuna cewa Mulkin Jehobah zai mulki duniyar nan kuma zai cire mugunta gabaki ɗaya.
A WANNAN SASHEN
DARASI NA 57
Jehobah Ya Aiki Irmiya Ya Yi Wa’azi
Abin da wannan annabin ya ce ya ba wa dattawan Yahuda haushi sosai.
DARASI NA 58
An Halaka Urushalima
Mutanen Yahuda sun ci gaba da bauta wa allolin karya, don haka Jehobah ya rabu da su.
DARASI NA 59
Matasa Hudu da Suka Yi wa Jehobah Biyayya
Wadannan matasa Yahudawan sun kudurta za su rike amincinsu ga Jehobah ko a Babila.
DARASI NA 60
Gwamnatin da Za ta Yi Sarauta Har Abada
Daniyel ya bayyana ma’anar mafarkin Nebuchadnezzar.
DARASI NA 61
Sun Ki Bauta wa Gunki
Shadrach da Meshach da kuma Abednego su ki bauta wa gunki zinariya da sarkin Babila ya yi.
DARASI NA 64
An Saka Daniyel a Cikin Ramin Zakuna
Kamar yadda Daniyel ya yi, ka rika yi wa Jehobah addu’a a koyaushe!
DARASI NA 65
Esther Ta Ceci Mutanenta
Ta zama sarauniya duk da cewa ita ba ’yar kasar Fasiya ba ce kuma ba ta da iyaye.
DARASI NA 66
Ezra ya koyar da Dokar Allah
Bayan mutanen sun saurari abin Ezra ya gaya musu, sai suka yi alkawari na musamman wa Allah.
DARASI NA 67
Ganuwar Urushalima
Me ya sa Nehemiya bai ji tsoro ba sa’ad da ya ji cewa makiyansa suna sun su kawo masa hari?