Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 74

Yesu Ya Zama Almasihu

Yesu Ya Zama Almasihu

Yohanna ya daɗe yana gaya wa mutane cewa: ‘Wani da ya fi ni iko yana nan zuwa.’ Da Yesu ya kusan kai shekara 30, sai ya bar Galili kuma ya zo Kogin Urdun, inda Yohanna yake yi wa mutane baftisma. Yesu yana so Yohanna ya yi masa baftisma amma sai Yohanna ya ce masa: ‘Kai ne ya kamata ka yi mini baftisma.’ Yesu ya ce: ‘Jehobah yana so ka yi mini baftisma.’ Sai suka shiga cikin Kogin Urdun kuma Yohanna ya nitsar da shi cikin ruwan.

Da Yohanna ya gama masa baftisma, sai Yesu ya yi addu’a. Nan da nan sama ta buɗe kuma ruhun Allah ya sauko kamar tsuntsu a kansa. Sai Jehobah ya yi magana daga sama cewa: “Wannan Ɗana ne, ƙaunataccena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.”

Da ruhun Jehobah ya sauko a kan Yesu, sai ya zama Kristi ko kuma Almasihu. Yanzu ne zai soma aikin da Jehobah ya aiko shi ya yi a duniya.

Bayan Yesu ya yi baftisma, sai ya tafi jeji kuma ya yi kwana 40 a wajen. Da ya dawo sai ya je wurin Yohanna. Da Yohanna ya ga Yesu yana zuwa, sai ya ce: ‘Wannan shi ne Ɗan ragon Allah, wanda zai cire zunubi daga duniya.’ Yohanna ya faɗi hakan ne don ya nuna wa mutane cewa Yesu shi ne Almasihu. Ka san abin da ya faru da Yesu sa’ad da yake cikin jeji? Bari mu gani.

“Murya kuwa ta fito daga sammai, ‘Kai ne Ɗana ƙaunatacce, raina yana jin daɗin ka sosai.’”​—Markus 1:11