Gabatarwar Sashe na 4
Wannan sashen ya yi magana game da Yusufu da Ayuba da Musa da kuma Isra’ilawa. Dukansu sun jimre da jarraba daga Shaiɗan. An yi wa wasu daga cikinsu rashin adalci, an tura wasu kurkuku, wasu an mai da su bayi, wasu kuma sun yi rashin ʼyan’uwansu babu zato. Amma Jehobah ya cece su a hanyoyi da yawa. Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci yadda waɗannan bayin Allah suka ci gaba da bauta wa Jehobah duk da wahalar da suka sha.
Jehobah ya yi amfani da Annoba Goma don ya nuna cewa ya fi dukan allolin Masar ƙarfi. Ka nuna yadda Jehobah ya kāre bayinsa a dā da kuma yadda yake yin hakan a yau.
A WANNAN SASHEN
DARASI NA 14
Wani Bawa da Ya Yi Biyayya ga Allah
Yusufu ya yi abin da ya dace amma duk da haka, ya sha wahala sosai. Me ya sa?
DARASI NA 15
Jehobah Bai Manta da Yusufu Ba
Duk da cewa Yusufu ya yi nesa da danginsa, Allah ya ci gaba da kasancewa tare da shi.
DARASI NA 16
Wane Irin Mutum Ne Ayuba?
Ya yi wa Jehobah biyayya duk da cewa hakan bai yi masa sauki ba.
DARASI NA 17
Musa Ya Bauta wa Jehobah
Sa’ad da Musa yake jariri, mahaifiyarsa ta cece shi don basirar da ta yi.
DARASI NA 19
Annoba ta Daya Zuwa Uku
Fir’auna janyo annoba wa mutanensa saboda da fahariyarsa bai kyale shi ya yi abin da ya kamata ya yi ba.
DARASI NA 20
Annoba ta Hudu Zuwa Tara
Mene ne bambancin da ke tsakanin annobar nan da sauran guda ukun?
DARASI NA 21
Annoba ta Goma
Wannan annobar ta yi muni sosai, har ta sa Fir’auna da kansa ya yi biyayya.
DARASI NA 22
Abu Mai Ban Mamaki a Jar Teku
Annoba guda goma ba su kashe Fir’auna ba, amma wannan mu’ujizar da Allah ya yi ya kashe shi.