Gabatarwar Sashe na 8
Jehobah ya albarkaci Sulemanu kuma ya ba shi hikima da kuma damar gina haikalin. Amma daga baya ya daina bauta wa Jehobah. Idan kana da yara, ka bayyana musu yadda bauta ta ƙarya ta sa Sulemanu ya daina bauta wa Allah. An raba mulkin kuma wasu sarakuna su sa mutanen suka soma bautar gumaka. A wannan lokacin, an kashe annabawan Jehobah masu aminci da yawa. Sarauniya Jezebel ta sa mutanen da ke arewacin ƙasar bautar gumaka. A lokacin, Isra’ilawa ba sa bauta wa Jehobah. Amma da akwai wasu amintattun bayin Jehobah kamar su Sarki Jehoshaphat da kuma annabi Iliya.
A WANNAN SASHEN
DARASI NA 44
Haikalin Jehobah
Allah ya amince da addu’ar Sarki Sulemanu kuma ya albarkace shi sosai.
DARASI NA 49
An Hukunta Wata Muguwar Sarauniya
Jezebel ta yi shiri a kashe wani dan Isra’ila mai suna Naboth don ta kwace gonarsa! Amma Jehobah ya ga kulle-kullen da ta yi kuma ya hukunta ta.
DARASI NA 50
Jehobah Ya Kāre Jehoshaphat
Sa’ad da makiya suke so su kai wa Yahuda hari, sarki Jehoshaphat ya roki taimakon Allah.