Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

’Yan’uwa:

Muna son Littafi Mai Tsarki domin mu bayin Jehobah ne. Mun tabbata cewa labaran da ke cikin Kalmarsa gaskiya ne kuma suna taimaka mana a rayuwa. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana irin ƙaunar da Jehobah yake wa dukan ’yan Adam. (Zabura 119:105; Luka 1:3; 1 Yohanna 4:19) Muna so mu taimaka wa mutane su san gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah. Shi ya sa muke farin cikin fitar da wannan littafi mai jigo, “Darussa Daga Littafi Mai Tsarki.” Bari mu gaya muku wasu abubuwan da ke cikin littafin.

An shirya wannan littafin musamman don yara. Amma za a iya yin amfani da shi wajen yin nazari da manyan mutanen da suke so su san saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Tun da Littafi Mai Tsarki na kowa ne, dukanmu za mu amfana daga wannan littafin don zai taimaka mana mu yi farin ciki a rayuwa.

Wannan littafin yana ɗauke da labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki daga littafin Farawa har zuwa Ru’ya ta Yohanna. Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu sa labaran su kasance da sauƙin fahimta kuma an rubuta labaran bi da bi.

Amma ba labari kawai aka bayar a wannan littafin ba. An shirya labaran da kuma hotunan a yadda za su iya ratsa zuciyarmu da kuma sa mu ga kamar abubuwan suna faruwa ne a gabanmu.

A cikin wannan littafin, an ba da labaran mutanen da suke ƙaunar Jehobah da waɗanda ba sa ƙaunar sa. Kuma hakan na motsa mu mu koyi darussa daga labaransu. (Romawa 15:4; 1 Korintiyawa 10:⁠6) An raba wannan littafin zuwa sassa guda 14. A kowane sashe, an ba da gajeren bayani a kan darasin da za mu iya koya.

Idan kuna da yara, kuna iya karanta darussan tare da su kuma ku tattauna hotunan. Bayan haka, sai ku karanta nassosin da aka ɗauko labarin daga ciki. Ku taimaka wa yaranku su ga alaƙar da ke tsakanin nassosin da kuma labarin da suka karanta. Za a iya yin hakan da manyan mutanen da suke so su san saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Muna fatan wannan littafin zai taimaka wa kowa, manya da ƙanana su san Kalmar Allah kuma su bi ƙa’idodinsa a rayuwarsu. Ta hakan, su ma za su soma bauta masa tare da mutanensa.

’Yan’uwanku,

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah