Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?

Addinai biyu ne akwai a duniya: daya na kai mutum ga hallaka. Wannan littafin zai taimaka maka ka sami rai na har abada.

Gabatarwa

Rayuwarmu, yanzu da kuma nan gaba, ka dogara ga Allah Mai Iko Duka. Saboda haka, ya kamata Allah ya amince da ibadarmu!

SASHE NA 1

Dukan Addinai ne Suke Koyar da Gaskiya?

Addinai suna da’awar bauta wa Allah, amma dokoki da abin da suka yi imani da su sun bambanta. Shin, dukansu gaskiya ce?

SASHE NA 2

Ta Yaya Za Ka Koyi Gaskiya Game da Allah?

Mutane za su iya samun wani tushen gaskiya kuwa?

SASHE NA 3

Su Waye Suke Zama a Duniya ta Ruhu?

Al’adun gargajiya na da karfi sosai a Afrika. Amma al’adun suna da amfani kuwa? An ba da amsar a cikin Littafi Mai Tsarki.

SASHE NA 4

A Ina Kakanninmu Suke?

Mutane da yawa sun yi imani cewa idan mutum ya mutu bai daina rayuwa ba, amma ya tafi ne daga duniya zuwa wani wuri. Mene ne littafi mai tsarki ya ce game da hakan?

SASHE NA 5

Gaskiya Game da Sihiri, Bokanci, da Kuma Maita

Ruhohi suna da iko kuma suna so su yi mana illa, amma kada mu dauka kamar karfinsu babu iyaka.

SASHE NA 6

Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?

Wasu suna ganin kamar Allah ya amince da dukan addinai. Shin Littafi Mai Tsarki ya koyar da hakan?

SASHE NA 7

Su Waye Suke Yin Addini na Gaskiya?

Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka san wadanda suke yin nufin Allah.

SASHE NA 8

Ka Ki Addinin Karya; Ka Yi Addini na Gaskiya

Yesu ya ce: “Wanda ba shi wajena gāba da ni yake.” Ta yaya za ka nuna wanda kake goyon bayansa?

SASHE NA 9

Addini na Gaskiya Zai Amfane Ka Har Abada!

In ka bauta wa Jehobah, zai yi maka albarka yanzu da kuma a nan gaba.