Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 4

A Ina Kakanninmu Suke?

A Ina Kakanninmu Suke?

1, 2. Menene mutane da yawa suka yi imani da shi game da waɗanda suka mutu?

MILIYOYIN mutane a Afirka sun yi imani cewa mutuwa, ba ƙarshen rayuwa ba ce, amma ƙaura ce kawai, wucewa ce daga rai zuwa wata duniya. Da yawa suna tunanin cewa kakanninsu da suka mutu sun ƙetare ne daga duniya ta zahiri zuwa duniya da ba a gani, daga duniyar mutane zuwa duniya ta ruhohi.

2 Waɗannan kakannin, ko kuma ruhohin kakanni, an yi imanin cewa suna tabbatar da rayuwa da kuma arzuta iyalansu a duniya. Bisa wannan ra’ayin, ruhohin kakanni abokanai ne masu iko, suna iya kawo girbi mai kyau, su kawo lafiyar jiki, kuma su yi kāriya daga lahani. Idan aka yi banza da su ko kuma aka ɓata musu rai, an ce sukan kawo wahala​—ciwo, talauci, da kuma bala’i.

3. Ta yaya wasu mutane suke bauta wa kakanni?

3 Mutane da suke da rai suna yin abubuwa da kuma bukukuwa domin su daraja kuma su kyautata nasaba da take tsakaninsu da ruhohin kakanni. Irin waɗannan abubuwa musamman suna bayyana a jana’iza da kuma al’adun binne mutum, kamarsu kwanan zaune da kuma jana’iza ta biyu. Bauta wa kakanni ya bayyana a wasu hanyoyi ma. Alal misali, kafin wasu mutane su sha giya, suna zubar da kaɗan a ƙasa ga kakanni. Har ila, bayan an gama dafa abinci, ana barin abinci a cikin tukunya domin idan kakanni suka zo, su samu abin da za su ci.

4. Menene mutane da yawa suka yi imani da shi game da kurwa?

4 Wasu mutane sun yi imani cewa mutane rayayyu suna da kurwa da take tsira daga mutuwar jiki. Idan mutum ya yi rayuwa mai kyau, an ce kurwarsa tana tafiya sama, ko kuma aljanna, amma idan mutum ya yi rayuwa da ba ta da kyau, kurwarsa an ce za ta shiga cikin jahannama. Sau da yawa mutane suna haɗa wannan ra’ayin da imani na al’ada. Alal misali, jaridar da take sanar da jana’iza wani lokaci tana cewa mutumin ya “ƙetare” ko kuma “ya je wurin kakanni.” Waɗannan imani suna bisa ra’ayi ne cewa kurwa, ko kuma ruhu, yana tsira daga mutuwa ta jiki. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan?

Kurwa da Kuma Ruhu

5, 6. In ji Littafi Mai Tsarki, mecece kurwa?

5 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kurwa ba wata aba ce da take cikin mutum ba; kurwar ita ce mutum kansa. Alal misali, sa’ad da Allah ya halicci Adamu, “mutum kuma ya zama rayayyen mai-rai.” (Farawa 2:7) Ba a ba Adamu kurwa ba; shi kansa ne kurwa, cikakken mutum.

6 Hakan, mun karanta cewa ana haifan kurwa. (Farawa 46:18) Suna iya ci kuma suna yin azumi. (Leviticus 7:20; Zabura 35:13) Suna baƙin ciki kuma suna suma. (Irmiya 13:17; Yunana 2:7) Ana iya sace kurwa, a bi ta, kuma ana iya saka ta a mari. (Kubawar Shari’a 24:7; Zabura 7:5; 105:18) Wasu Littafi Mai Tsarki sun fassara kalmar asali da “kurwa” ce a waɗannan ayoyin, yayin nan wasu suka yi amfani da kalmomi kamar su “rai,” “halitta,” da kuma “mutum.” Duka suna nufin abu ɗaya ne.

7. Waɗanne ayoyin Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa kurwa za ta iya mutuwa?

7 Tun da kurwa mutum ne, sa’ad da mutum ya mutu, kurwar ta mutu. Ezekiel 18:4 ta ce: “Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.” Haka, Ayyukan Manzanni 3:23 ta ce: “Kowane mai-rai wanda ba ya kasa kunne ga annabcin nan za a halaka shi sarai daga cikin jama’a.” Saboda da haka kurwa ba wata aba ba ce ba da take tsira daga mutuwar jiki.

8. Menene ruhu da yake cikin mutane?

8 Ruhu ba ɗaya yake da kurwa ba. A cikin mutane, ruhu shi ne ikon rai da yake taimakonsu suke yin ayyukan rayuwa. Ruhun, kamar lantarki yake. Lantarki zai iya sa fanka ko kuma firiji ya yi aiki amma ba zai iya fifita ba ko kuma ya sa abubuwa su yi sanyi ba. Hakazalika, ruhunmu yana taimakonmu mu gani, mu ji, kuma mu yi tunani. Amma ruhun ba zai iya yin waɗannan abubuwa ba, ba tare da idanu, kunnuwa ko kuma ƙwaƙwalwa ba. Abin da ya sa ke nan da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutum: “Numfashinsa ya kan fita, ya kan koma turɓayarsa kuma; a cikin wannan rana shawarwarinsa su kan lalace.”​—Zabura 146:4.

9. Menene kurwa da ruhu ba sa yi ba?

9 Saboda haka, in ji Littafi Mai Tsarki, ba abin da yake barin jiki a lokacin mutuwa, ba kurwa ko kuma ruhu, da zai ci gaba da rayuwa a duniya ta ruhu.

Yanayin Matattu

10. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da yanayin matattu?

10 To, menene yanayin matattu? Tun da Jehobah ne wanda ya halicci mutane, ya san abin da yake faruwa da mu bayan mun mutu. Kalmarsa ta koyar da cewa matattu ba su da rai, ba sa ji, ba sa gani, ba sa magana, ko kuma tunani. Littafi Mai Tsarki ya ce:

  • “Matattu ba su san kome ba.”​—Mai-Wa’azi 9:5.

  • “Ƙaunarsu duk da ƙiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun ƙare.”​—Mai-Wa’azi 9:6.

  • “Babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.”​—Mai-Wa’azi 9:10.

11. Bayan Adamu ya yi zunubi, menene Jehobah ya gaya masa?

11 Ka yi tunanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kakanmu na farko, Adamu. Jehobah ya sifanta Adamu “daga turɓayar ƙasa.” (Farawa 2:7) Da a ce Adamu ya yi biyayya da dokar Jehobah, zai rayu har abada cikin farin ciki a duniya. Amma, Adamu ya yi rashin biyayya ga dokar Jehobah, kuma sakamakon haka mutuwa ce. Ina Adamu ya tafi da ya mutu? Allah ya ce: “[Za] ka koma ƙasa; gama daga cikinta aka ciro ka: gama turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.”​—Farawa 3:19.

12. Me ya faru da Adamu a lokacin mutuwa?

12 A ina Adamu yake kafin Jehobah ya halicce shi daga turɓaya? Ba ya ko’ina. Bai wanzu ba. Saboda haka, sa’ad da Jehobah ya ce Adamu zai “koma ƙasa,” Yana nufi ne cewa Adamu zai sake zama marar rai, kamar turɓaya. Adamu bai rayu ba a duniya ta ruhu. Bai ‘ƙetare’ ba zuwa duniyar ruhohi na kakanni. Bai je sama ba ko kuma jahannama. Ya koma yanayin rashin rai; ba ya wanzuwa kuma.

13. A lokacin mutuwa, me yake faruwa da mutane da kuma dabbobi?

13 Abu ɗaya ne yake faruwa da mutane duka? Hakika kuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Mutane da dabbobi] wuri ɗaya za su; duk na turɓaya ne, turɓaya kuma za su koma.”​—Mai-Wa’azi 3:​19, 20.

14. Wane bege matattu suke da shi?

14 Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa Allah zai ta da matattu zuwa rai a aljanna a duniya. (Yohanna 5:​28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15) Amma wannan lokacin har yanzu yana zuwa a gaba. A yanzu, suna kwance cikin mutuwa. (Yohanna 11:​11-14) Bai kamata mu ji tsoron su ba ko kuma mu bauta musu, tun da ba za su iya taimakonmu ba ko kuma su yi mana lahani.

15, 16. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya sa mutane su yi imani da cewa matattu ba su mutu ba da gaske?

15 Ra’ayin wai ba ma mutuwa da gaske ƙarya ne da Shaiɗan Iblis yake yaɗawa. Domin ya huɗubantar da mutane game da wannan ƙaryar, shi da aljannunsa suna ƙoƙari su sa mutane su yi tunanin cewa ciwo da wasu matsaloli, ruhohin matattu ne suke haddasa su. Gaskiya ne cewa wasu matsalolin, aljannu ne suke haddasa su da kansu. Kuma gaskiya ne cewa wasu matsaloli babu hannun aljannu a ciki. Amma ba gaskiya ba ne cewa waɗanda suke kwance cikin mutuwa za su yi mana lahani.

16 Har ila, da akwai wasu hanyoyi da aljannu suke ƙoƙari su sa mutane su yi tunani cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da matattu ba daidai ba ne. Suna yaudarar mutane su yi tunanin cewa sun ga ko sun yi magana da wanda ya mutu. Aljannun suna yin haka ta wajen wahayi, mafarkai, da kuma bokaye, ko kuma wasu hanyoyi. Amma, ba matattun ba ne mutane suke gamuwa da su, da aljannu ne waɗanda suke nuna cewa su ne mutane da suka mutu. Dalili ke nan da Jehobah ya haramta duba da kuma magana da matattu.​—Kubawar Shari’a 18:​10-12; Zakariya 10:2.