Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 6

Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?

Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?

1. In ji Kalmar Allah, waɗanne addinai iri biyu kawai ake da su?

“KU SHIGA ta wurin ƙunƙuntar ƙofa,” in ji Yesu, “gama ƙofa da fāɗi ta ke, hanya kuwa da fāɗi, wadda ta nufa wajen halaka, mutane dayawa fa suna shiga ta wurinta. Gama ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:​13, 14) Akwai addinai iri biyu ne kawai in ji Kalmar Allah: ɗaya na gaskiya; ɗayan kuma na ƙarya, ɗaya daidai, ɗayan kuma ba daidai ba; ɗaya yana kai wa ga rai, ɗayan kuma yana kai wa ga halaka.

2. Ta yaya Nassosi suka nuna cewa ba dukan addinai ba ne suke faranta wa Allah rai?

2 Wasu mutane suna tunanin cewa dukan addinai suna faranta wa Allah rai. Ayoyin Littafi Mai Tsarki na gaba sun nuna cewa hakan ba gaskiya ba ne:

  • “ ’Ya’yan Isra’ila suka sake yin aikin mugunta a idanun Ubangiji, suka bauta ma ba’alim, da Ashtaroth, da allolin [Siriya], da allolin Sidon, da allolin Moab, da allolin ’ya’yan Ammon, da allolin Filistiyawa: suka bar bin Ubangiji, ba su bauta masa ba. Fushin Ubangiji fa ya yi ƙuna a kan Isra’ila.” (Alƙalawa 10:​6, 7) Idan muka bauta wa gumaka ko kuma wani allah ban da Allah na gaskiya, ba za mu samu yardar Jehobah ba.

  • “Wannan Al’umma tana girmama ni da leɓunansu, amma zuciyarsu tana nesa da ni. Amma banza su ke yi mini sujjada, koyarwa da su ke yi dokokin mutane ne.” (Markus 7:​6, 7) Idan mutane da suke da’awar suna bauta wa Allah suna koyar da nasu ra’ayi maimakon abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar, bautar su banza ce. Allah ba ya karɓa.

  • “Allah ruhu ne; waɗanda su ke yi masa sujjada kuma, sai su yi sujjada cikin ruhu da cikin gaskiya kuma.” (Yohanna 4:24) Bautar mu dole ta jitu da gaskiyar Kalmar Allah.

‘Ya’yan Addini na Ƙarya

3. Waccece hanya ɗaya na sansance addini na gaskiya daga na ƙarya?

3 Ta yaya za mu sani ko addini yana faranta wa Allah rai ko a’a? Yesu ya ce: “Kowane itacen kirki ya kan fitarda ’ya’yan kirki; amma ɓātacen itace ya kan fitarda munanan ’ya’ya . . . Bisa ga ’ya’yansu fa za ku sansance su.” Wato, idan addini daga Allah ne, zai ba da ’ya’ya masu kyau; amma idan addini daga Shaiɗan ne, zai ba da munanan ’ya’ya.​—Matta 7:​15-20.

4. Wane hali ne masu bauta wa Jehobah suke nunawa?

4 Addini na gaskiya yana yin mutane waɗanda suke ƙaunar juna kuma suna ƙaunar wasu. Wannan ma domin Jehobah kansa Allah ne mai ƙauna. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” Ta yaya addini zai kai ga wannan mizani na bauta ta gaskiya?​—Yohanna 13:35; Luka 10:27; 1 Yohanna 4:8.

5. Yaya encyclopedia ya kwatanta sayar da bayi na Afirka?

5 Ka yi la’akari da sayar da bayi na Afirka. The New Encyclopædia Britannica ya ce: Aƙalla mutanen Afirka 18,000,000 aka kai ga ƙetaren hamada na Musulunci da kuma sayar da bayi na Tekun Indiya tsakanin shekara ta 650 da 1905. A cikin rabin ƙarni na 15, Turawa suka fara kasuwanci a bakin tekun Afirka ta yamma, kuma a shekara ta 1867 an tura mutanen Afirka misalin 7,000,000 zuwa 10,000,000 zuwa bauta a Sabuwar Duniya.”

6. Ta yaya addini ya saka hannu a sayar da bayi?

6 Menene matsayin addini a lokacin wannan bala’i na Afirka sa’ad da maza, mata, da yara an raba su da gidajensu da iyalansu, an ɗaure su da sarƙa, an yi musu lamba da ƙarfe mai ƙuna, an saya an kuma sayar kamar shanu? Bethwell Ogot ya rubuta a Daily Nation na Nairobi, Kenya: “Kiristanci da Musulunci duka suna koyar da imanin haɗin kai na ’yan Adam, duk da haka su suka soma sayar da bayi da wariyar launin fata. . . . Ya kamata mu fahimci zunubi da yake tsakanin Musulmai da Kiristoci, tsakanin Yamma da Gabas ta Tsakiya, da kuma makantar ɗabi’a da ya kai ga ƙarnuka na wahala marar iyaka ga mutanen Afirka.”

Addini da Kuma Yaƙi

7. Wane aiki shugabannan addinai suka yi a yaƙe-yaƙe?

7 Addinan ƙarya sun nuna munanan ’ya’yansu a wasu hanyoyi. Alal misali, ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce “ka yi ƙaunar maƙwabcinka,” shugabannan addinai a dukan duniya sun ba wa yaƙi goyon baya da ƙwazo.​—Matta 22:39.

Addinan ƙarya suna saka hannu cikin yaƙe-yaƙe da kuma sayar da bayi

8. (a) Ta yaya shugabannan addinai suka ɗaukaka kisa a yaƙe-yaƙe na Afirka? (b) Menene wani fasto ya ce game da shugabannan addinai a lokacin yaƙin basasa na Nijeriya?

8 A sane yake sosai cewa a shekara ta 1994, wasu mata masu zaman zuhudu da kuma firistoci sun saka hannu ciki kashe mutane a Rwanda. Addini shi ne babban dalili na wasu yaƙe-yaƙe a Afirka. Alal misali, a lokacin yaƙin basasa na Nijeriya, addinan biyu sun ƙarfafa mutane su yi yaƙi. Da yaƙin ya ci gaba, wani fasto ya ce shugabannan coci sun “ture gefe guda aikin da Allah ya ba su.” Ya kuma ce: “Mu da muke kiran kanmu bayin Allah mun zama bayin Shaiɗan.”

9. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da masu hidimar Shaiɗan?

9 Littafi Mai Tsarki ma ya faɗi haka: “Shaiɗan da kansa ya kan mayarda kansa kamar mala’ika na haske. Ba wani abu ne fa masu-hidimansa kuma su mayarda kansu masu-hidiman adalci.” (2 Korintiyawa 11:​14, 15) Kamar yadda miyagun mutane da yawa suna nuna cewa suna da nagarta, Shaiɗan yana ruɗan mutane da mutane masu hidima waɗanda suke bayyana suna da adalci amma waɗanda ayyukansu mugunta ne da kuma ’ya’yansu ruɓaɓɓu.

10. A wace hanya ce shugabannan addinai suke musun Allah?

10 A dukan duniya, shugabannan addinai sun yi wa’azin a yi ƙauna, zaman lafiya, da kuma nagarta, amma sun yi ƙiyayya, yaƙi, da kuma rashin ibada. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su da kyau. Ya ce: “Suna shaida, cewa, sun san Allah; amma ta wurin ayyukansu sun yi musunsa.”​—Titus 1:16.

Ka Fita Daga “Babila Babba”

11. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta addinin ƙarya?

11 Za mu ga abin da Jehobah yake tunani game da addinin ƙarya ta wajen karatun littafin Ru’ya ta Yohanna na Littafi Mai Tsarki. A nan an kwatanta addinin ƙarya da mace ta alama, “Babila Babba.” (Ru’ya ta Yohanna 17:5) Ka lura da yadda Allah ya kwatanta ta:

  • “Babbar karuwa . . . wadda sarakunan duniya suka yi fasikanci da ita.” (Ru’ya ta Yohanna 17:2) Maimakon kasancewa da aminci ga Allah, addinan ƙarya sun saka hannu cikin siyasa, sau da yawa suna gaya wa gwamnati abin da za ta yi.

  • “A cikinta aka samu jinin annabawa da na tsarkaka, da na dukan waɗanda aka kashe a duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 18:24) Addinan ƙarya sun tsananta kuma sun kashe bayin Allah masu aminci kuma su suke da alhakin mutuwar miliyoyi a yaƙe-yaƙe.

  • “Ta ɗaukaka kanta duka, ta yi annashuwa kuma.” (Ru’ya ta Yohanna 18:7) Addinan ƙarya suna da arziki ƙwarai, wanda shugabannansu suke amfani da shi su yi annashuwa.

  • “Dukan al’ummai suka ruɗe da sihirin[ta].” (Ru’ya ta Yohanna 18:23) Ta wajen koyarwarta ta ƙarya cewa kurwa ba ta mutuwa, addinan ƙarya suka buɗe ƙofar sihiri iri-iri da kuma bokanci kuma suka ɗaukaka tsoron matattu da bautar kakanni.

12. Wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya bayar game da addinan ƙarya?

12 Wajen yin gargaɗi mai ƙarfi ga mutane su bar addinan ƙarya, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata, domin kada ku yi tarayya da zunubanta, kada ku sha rabon annobanta.”​—Ru’ya ta Yohanna 18:​4, 5.

13. Menene zai faru da addinan ƙarya da kuma waɗanda suke yinsu?

13 A nan gaba kaɗan, Babila Babba, daular addinin ƙarya na duniya, za a halaka ta gabaki ɗaya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Rana ɗaya annobanta za su zo, mutuwa, da kewa, da yunwa; za a ƙone ta sarai da wuta; gama Ubangiji Allah mai-ƙarfi ne wanda ya shar’anta mata.” (Ru’ya ta Yohanna 18:8) Don mu guje wa karɓan ‘ɓangaren annobanta,’ dole ne mu ware daga addinan ƙarya, kada mu saka hannu cikin ayyukanta, bukukuwanta, da kuma imani da suke baƙanta wa Allah rai. Batun gaggawa ne. Ya shafi rai!​—2 Korintiyawa 6:​14-18.