Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 7

Su Waye Suke Yin Addini na Gaskiya?

Su Waye Suke Yin Addini na Gaskiya?

1. Menene dole mu yi don mu faranta wa Allah rai?

DOMIN mu more danganta ta ƙauna da Allah, dole ne mu guji saka hannu cikin addinin ƙarya. Dole ne mu yi addini na gaskiya. A yau miliyoyin mutane a dukan duniya suna yin haka.

2. A ina za a samu Shaidun Jehobah, kuma menene aikinsu?

2 Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta, masu bauta ta gaskiya “taro mai-girma” ne waɗanda suka fito “daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9) A ƙasashe 235, miliyoyin Shaidun Jehobah suna da ƙwazo wajen taimakon wasu su koyi game da hanyoyi na ƙauna na Jehobah da kuma farillansa.

Gane Masu Bauta ta Gaskiya

3. Ga wa Shaidu suke yin bauta, kuma wace irin bauta suke guje wa?

3 Shaidu sun fahimci cewa Jehobah ne kaɗai ya cancanci a bauta masa. Sun ƙi su yi sujjada wa gumaka ko kuma hotuna na addini. (1 Yohanna 5:21) Ba sa bauta wa matattu ta wajen saka hannu cikin kwanan zaune ko kuma wasu bukukuwa da suke ɗaukaka imani na addinan ƙarya da kuma “koyarwar aljannu.” (1 Timothawus 4:1) Amma, suna yi wa masu makoki ta’aziyya ta wajen bayyana alkawuran Allah cewa za a yi tashin matattu a aljanna a duniya.​—Yohanna 5:​28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.

4. Menene matsayin mutanen Allah game da sihiri?

4 Shaidu ba sa saka hannu cikin sihiri, bokanci, ko kuma maita, sun san cewa irin waɗannan abubuwa daga Iblis ne. Ba sa dogara ga sihiri ya kāre su​—dogararsu ga Jehobah ne.​—Misalai 18:10.

5. A wace hanya ce Shaidun Jehobah “ba na duniya ba”?

5 Yesu ya ce almajiransa za su kasance “ba na duniya ba.” (Yohanna 17:16) Yesu kansa ya ƙi ya saka hannu cikin siyasa na zamaninsa. (Yohanna 6:15) Hakazalika, Shaidun ba sa saka hannu cikin siyasa, ɗaukaka ƙasa, kokawar neman matsayi na wannan duniyar. Amma, suna biyan harajinsu kuma suna biyayya ga dokokin ƙasar da suke zaune.​—Yohanna 15:19; Romawa 13:​1, 7.

6. Waɗanne umurnai ne bayin Allah suke bi game da aure da kuma kisan aure?

6 Domin suna biyayya ga umurnin gwamnati, Shaidun suna tabbata cewa aurensu sun yi shi bisa doka. (Titus 3:1) Kuma suna yin biyayya ga umurnin Allah, kuma saboda haka suna guje wa auren mace fiye da ɗaya. (1 Timotawus 3:2) Bugu da ƙari, tun da suna amfani da mizanan Allah a rayuwarsu, bayin Allah aure-aurensu ba sa ƙarewa cikin kisan aure.

7. Ta yaya Shaidun suke nuna ƙauna ga juna?

7 Shaidu suna ƙaunar juna. Wannan ƙaunar, tare da ƙaunarsu ga Allah, tana haɗa kansu cikin ’yan’uwantaka, ko da yake suna daga ƙabilai dabam dabam da kuma al’ummai. Idan bala’i ta auku ko kuma a lokatai na bukata, Shaidun ba sa ɓata lokaci su taimaki juna. Shaidun suna nuna ƙauna ta hanyar da suke rayuwa.​—Yohanna 13:35.

Shaidun Jehobah suna da haɗin kai cikin ’yan’uwanci na dukan duniya

8. Waɗanne munanan abubuwa ne mutanen Allah suke guje wa?

8 Mutanen Jehobah suna aiki tuƙuru su yi rayuwa mai gaskiya, mai adalci kuma. Suna guje wa sata, ƙarya, fasikanci, maye, da kuma rashin gaskiya a kasuwanci. Maza ba sa dukān matansu. Kafin su zama Shaidu, wasu suna yin waɗannan abubuwa, amma da taimakon Jehobah sun daina. An ‘wanke su,’ a idanun Allah.​—1 Korintiyawa 6:​9-11.

Masu Yin Nufin Allah

9. Menene wani littafi ya ce game da cocin ruhaniya na Afirka?

9 Hakika, addinai da yawa suna da’awar cewa suna da gaskiya. Wataƙila su yi nuni da ayyuka masu kyau domin su tabbatar da da’awarsu. Alal misali, game da abin da ake kira cocin ruhaniya a Afirka, wani littafi ya ce: “[Sababbin rukunin Kiristoci] suna karɓan aikin boka. . . . Suna da’awar yin bokanci kuma suna cewa suna yin mu’ujizoji. Annabawa a tsakaninsu suna ba da wahayi kuma suna fassara mafarkai. Suna yin amfani da tsarkakken ruwa, tsarkakken mai, toka, kyandir da kuma turare su warkar kuma su yi rigakafi.”

10, 11. Me ya sa abin da wai mu’ujiza ne a yau ba sa nuna cewa addinin daga Allah ne?

10 Waɗanda suke cikin addinin suna da’awar cewa mu’ujiza tana tabbatar da cewa addininsu Allah ya albarkace shi. Amma aba da wai mu’ujiza ce ba ta tabbatar da cewa Allah ya albarkaci addini. Shaiɗan ya ba da iko ga wasu masu addinin ƙarya su yi ‘ayyuka masu girma.’ (2 Tasalonikawa 2:9) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce kyautar mu’ujiza daga Allah, kamarsu yin annabci, magana da wani harshe, da kuma sani na musamman, za “a kawarda shi.”​—1 Korintiyawa 13:8.

11 Yesu ya yi gargaɗi: “Ba dukan mai-ce mini, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aika nufin Ubana wanda ke cikin sama. A cikin wannan rana mutane dayawa za su ce mini, Ubangiji, Ubangiji, ba mu yi annabci da sunanka ba, da sunanka kuma muka fitarda aljanu, da sunanka kuma muka yi ayyuka dayawa masu-iko? Sa’annan zan furta musu Ban taɓa saninku ba daɗai: rabu da ni, ku masu-aika mugunta.”​—Matta 7:​21-23.

12. Su waye za su shiga Mulkin sama?

12 To, su waye za su shiga cikin Mulkin sama? Waɗanda suka yi nufin Jehobah ne.

Masu Wa’azin Mulkin Allah

13. Wane aiki ne Allah ya umurci mutanensa su yi a yau, kuma su waye ne suke yin sa?

13 Menene nufin Allah ga mutanensa a yau? Yesu ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.” (Matta 24:14) Wannan shi ne aikin da Shaidun Jehobah suke yi da ƙwazo.

14. Menene Mulkin Allah, kuma su waye za su yi sarauta a Mulkin?

14 A dukan ‘duniya,’ Shaidun Jehobah suna yin bisharar Mulkin Allah cewa gwamnati ce ta sama da za ta yi sarauta bisa dukan duniya cikin adalci. Sun koyar da cewa Jehobah ya naɗa Yesu Kristi ya zama Sarkin wannan Mulkin, tare da mutane 144,000 waɗannan abokanan sarautarsa ne da aka zaɓa a tsakanin ’yan Adam.​—Daniyel 7:​14, 18; Ru’ya ta Yohanna 14:​1, 4.

15. Menene Mulkin zai halaka?

15 Ta wajen amfani da Littafi Mai Tsarki, Shaidun sun nuna wa mutane cewa Mulkin Allah zai halaka sarautar Shaiɗan gabaki ɗaya. Addini na ƙarya zai shuɗe tare da koyarwarsa na rena Allah da kuma ɗaukaka Iblis. (Ru’ya ta Yohanna 18:8) Gwamnatin mutane ma za ta shuɗe, wadda take gāba da Allah!​—Daniyel 2:44.

16. Su waye za su zama talikan Yesu Kristi, kuma a ina za su zauna?

16 Bugu da ƙari, Shaidun Jehobah suna sanar da cewa Yesu Kristi zai kawo amfani ga dukan waɗanda suka yi abin da Allah yake bukata a gare su. Za su zama talakokinsa a duniya. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai.”​—Zabura 72:​12, 13.

17. Su waye ne kawai suke shelar Mulkin Allah?

17 Babu wani rukunin mutane da suke yin nufin Allah ta wajen wa’azin bisharar Mulkin. Sai Shaidun Jehobah kawai suke sanar da Mulkin Allah a dukan duniya.