SASHE NA 3
Su Waye Suke Zama a Duniya ta Ruhu?
1. Ta yaya aka kwatanta addinin al’ada da mashahurin kabarin sarakuna a Masar?
IMANI na addinin al’ada na Afirka an kwatanta shi da mashahurin kabarin sarakuna a Masar (pyramid). A saman, Allah ne mafi girma a iko na ruhaniya. A gefe-gefen ƙananan alloli ne, ko kuma iskoki, waɗanda bayin Allah ne. Tare da su kuma kakanni ne, waɗanda suke tunawa da iyalansu a duniya suke damuwa da yanayinsu. A ƙarƙashi kuma akwai masu ɗan iko na ruhaniya: masu sihiri, masu duba, da kuma mayu.
2. Ta yaya magana ta Afirka ta nuna cewa imani na al’ada yana rinjayar addinai?
2 Wannan imani na al’ada ya rinjayi wasu addinai a Afirka. Wata magana ta Afirka ta ce: “Imani (Kiristanci ko Musulunci) ba zai hana mu bauta wa allolin ƙasarmu ba.”
3. A ina za mu koyi gaskiya game da waɗanda suke zama a duniya ta ruhu?
3 Yaya gaskiyar imani na al’adar Afirka take? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana gaskiya game da waɗanda suke zama a duniya ta ruhu.
Jehobah, Allah na Gaskiya
4. Me manyan addinai na Afirka suka yi imani da shi?
4 Manyan addinai uku na Afirka sun yi imani da cewa da akwai Allah kuma shi ne mafi girma. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi da, “Allahn alloli, da Ubangiji[n] iyayengiji, Allah ne mai-girma, mai-iko mai-ban tsoro.” (Kubawar Shari’a 10:17) Musulmai ma sun yi imani da Allah ɗaya mafi girma. Game da addinin al’ada a Afirka, Farfesa Geoffrey Parrinder ya ce: “Yawancin mutanen Afirka sun yi imani da Allah mafi girma, uban alloli da mutane, mahaliccin dukan halitta.”
5. Waɗanne sunaye ne ake amfani da su wajen kiran Allah?
5 Amma, duk da yaɗuwar imani da Allah, yawancin mutane ba su da cikakken sani game da Allah. Mataki na farko na sanin wani shi ne sanin sunansa. Game da sunan Allah, da akwai ɗimaucewa tsakanin addinai. A Kiristendam, an fi kiransa Ubangiji, laƙabi da yake nufin “Mai girma.” Ga Musulmai, Allah ne. Tsakanin waɗanda suke yin addinin al’ada, sunan da suke yin amfani da shi su nuna Mai Girma ya bambanta daga yare zuwa yare. A littafinsa Concepts of God in Africa, John S. Mbiti ya jera sunayen Afirka dabam dabam da laƙabi fiye da 500 na Allah. Alal misali, da Yarbanci (Nijeriya), ana kiran Allah Olodumare; ga Kikuyawa (Kenya), shi Ngai ne; a tsakanin mutanen Zulu (Afirka ta Kudu), shi Unkulunkulu.
6, 7. Menene sunan Allah, kuma ta yaya muka sani?
Fitowa 3:13.
6 Menene Allah kansa ya ce game da sunansa? Sa’ad da Allah ya umurci Musa ya ja-goranci Isra’ilawa ya fito da su daga ƙasar Masar, Musa ya yi tambaya: “Ga shi, sa’anda na zo wurin ’ya’yan Isra’ila, na ce musu, Allah na ubanninku ya aike ni gareku, su kuma sun ce mini, Wane sunansa? me zan ce musu?”—7 Allah ya amsa: “Hakanan za ka ce ma ’ya’yan Isra’ila, [Jehobah], Allah na ubanninku, . . . ya aike ni gareku: wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.” (Fitowa 3:15) Wannan sunan Allah ya bayyana fiye da sau 7,000 a cikin Littafi Mai Tsarki, ko da yake wasu masu fassarar Littafi Mai Tsarki sun sake shi da laƙabi kamar su, “Allah” ko kuma “Ubangiji.”
8. Yaya Jehobah yake, kuma menene ne dole mu yi idan muna son mu samu tagomashinsa?
8 Menene ainihi kamanin Jehobah? Shi ruhu ne, mai girma, mai ɗaukaka. Shi ne mafi girma, ba shi da na biyu, babu wanda ya yi daidai da shi. (Kubawar Shari’a 6:4; Ishaya 44:6) Jehobah ya ce wa Musa: “Ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.” (Fitowa 20:3-5) Wato, domin mu samu tagomashin Jehobah, dole ne mu bauta masa shi kaɗai. Ba ya so mu bauta wa wani abu ko kuma wani.—Fitowa 20:3-5.
Yesu Kristi, Sarkin Mulkin Allah
9. Me ya sa za mu ce Yesu ba daidai yake da Jehobah ba?
9 A yau da akwai ɗimaucewa sosai game da ko wanene Yesu. Mutane da yawa a cikin Kiristendam sun yi imani cewa Yesu ɓangare ne na Allah Uku Cikin Ɗaya “Mai Tsarki.” Amma Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa Allah uku ne cikin ɗaya ba. Kuma bai koyar da cewa Yesu daidai yake da Jehobah ba. Yesu da kansa ya ce: “Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.
10. A ina Yesu yake kafin ya zo duniya?
10 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa kafin Yesu ya rayu a duniya, ya rayu a sama, halitta ce ta ruhu mai girma. Kamar yadda Jehobah ya halicci Adamu da Hauwa’u a duniya, haka ya halicci ruhohi a sama. Yesu shi ne ruhu na farko da Jehobah ya halitta.—Yohanna 17:5; Kolosiyawa 1:15.
11. Ta yaya aka zo ga haifar Yesu ya zama mutum?
11 Kusan shekara 2,000 da ta shige, Jehobah ya ƙaurar da ran wannan halittar ta ruhu zuwa cikin budurwa Maryamu. Mala’ika Jibra’ilu ya ce mata: “Za ki yi ciki, za ki haifi ɗa, za ki ba shi suna Yesu. Za shi yi mulki kuma . . . mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”—Luka 1:31, 33. *
12. Menene dalili ɗaya da ya sa Yesu ya zo duniya?
12 Aka haifi Yesu, ya yi girma ya zama mutum, kuma ya koyar da mutane game da manufar Jehobah da nufinsa. Ya gaya wa gwamna daga Roma: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37) Ta wajen bincika abin da Yesu ya koyar, za mu iya koyon gaskiya game da manufar Allah da kuma nufinsa. Za mu koyi yadda za mu samu yardar Allah.
13. Menene dalili na biyu da ya sa Yesu ya zo duniya?
13 Dalili na biyu na zuwan Yesu cikin duniya shi ne domin ya ba da ransa fansa ga ’yan Adam. (Matta 20:28) Ya yi hakan ne domin mu samu ’yanci daga zunubi da muka gāda daga kakanmu Adamu. Wannan, kuma zai sa ya yiwu mu rayu har abada. Manzo Yohanna ya rubuta: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”—Yohanna 3:16.
14. (a) Me ya faru da Yesu bayan mutuwarsa na mutum? (b) Menene matsayin Yesu yanzu a sama?
14 Bayan mutuwarsa ta mutum, an ta da Yesu daga matattu zuwa sama, inda ya soma rayuwar halittar ruhu mai girma. (Ayyukan Manzanni 2:32, 33) Daga baya, Jehobah ya ba shi “sarauta da daraja, da mulki, domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa.” (Daniyel 7:13, 14) Yesu ya zama babban Sarki: Sarkin gwamnatin Jehobah ta samaniya. Ba da jimawa ba zai nuna ikonsa bisa dukan duniya.
Mala’iku, Manzannin Allah
15. Yaushe kuma a ina aka halicci mala’iku?
15 Ba Jehobah da Yesu ba ne kawai suke zama a duniya ta ruhu. Jehobah ya halicci wasu halittun ruhu, mala’iku. Jibra’ilu da ya yi magana da Maryamu, yana ɗaya daga cikinsu. Mala’ikun ba su fara rayuwa a duniya ba kamar mutane. An halicce su da daɗewa a sama kafin aka halicci mutane a duniya. (Ayuba 38:4-7) Akwai miliyoyin mala’iku.—Daniyel 7:10.
16. Me ya sa bai kamata mutane su bauta wa mala’iku ba?
16 Mala’iku masu aminci ba sa so mu bauta musu. Sau biyu, da manzo Yohanna ya so ya bauta wa mala’iku, suka yi masa gargaɗi, suna cewa: “Kada ka yarda ka yi: . . . Ka yi sujjada ga Allah.”—Ru’ya ta Yohanna 19:10; 22:8, 9.
17. Me ya nuna cewa mala’iku za su iya kāre bayin Allah kuma me ya sa hakan abin ban ƙarfafa ne?
17 Mala’iku ba sa bayyana kuma ga mutanen Allah a duniya, kamar yadda suka yi sa’ad da suka ceci manzannin Yesu daga fursuna. (Ayyukan Manzanni 5:18, 19) Amma, idan muka bauta wa Jehobah bisa ga Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, za mu tabbata cewa mala’ikun Allah waɗanda ba a ganinsu, za su kāre mu. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tsare su kuma.’ (Zabura 34:7; 91:11) Me ya sa wannan zai ƙarfafa mu? Domin da akwai miyagun abokan gāba a duniya ta ruhu da suke so su halaka mu!
Shaiɗan, Abokin Gāban Allah
18. (a) Me ya sa wani mala’ika ya yi wa Allah tawaye? (b) Waɗanne sunaye aka ba wa wannan mala’ika ɗan tawaye?
18 Ba dukan mala’ikun Allah ba ne suka kasance da aminci a gare shi. Wasu sun yi masa tawaye. Sun mai da kansu abokan gāban Allah da kuma abokan gāban mutane a duniya. Ta yaya wannan ya faru? Dukan
halittun ruhu da Jehobah ya halitta suna da adalci kuma da nagarta. Amma dai, ɗaya daga cikin waɗannan kamiltattun ’ya’ya, ya so mutane su bauta masa kuma ya yi aiki bisa wannan mugun muradi nasa. Wannan halittar ruhu aka ba ta suna Shaiɗan, wanda yake nufin “Ɗan hamayya [da Allah].” Kuma an kira shi Iblis, wanda yake nufin “Maƙaryaci,” tun da ya yi baƙar ƙarya game da Jehobah.19. Me ya sa kuma ta yaya Shaiɗan ya azabtar da Ayuba?
19 Shaiɗan yana matsa wa mutane su bi shi wajen tawaye ga Allah. Ka ga abin da ya yi wa amintaccen bawan Allah Ayuba. Ayuba attajiri ne. Yana da tumaki 7,000, raƙuma 3,000, shanu 1,000 da kuma jakai 500. Yana da kuma yara 10 da barori da yawa. Da farko, Shaiɗan ya kashe dabbobin Ayuba da kuma barorinsa. Sai kuma, ya sa “guguwa mai-girma” ta rushe gida, ta kashe dukan ’ya’yan Ayuba. Bayan haka, Shaiɗan ya azabtar da Ayuba da “gyambuna masu-ciwo, tun daga tafin sawunsa har kan kansa.”—Ayuba 1:3-19; 2:7.
20. (a) Ta yaya aka saka wa Ayuba domin amincinsa? (b) Ko da yake Ayuba ya riƙe aminci ga Allah, menene Shaiɗan ya yi wa wasu mutane da yawa?
20 Duk da wannan bala’in jarraba, Ayuba ya kasance da aminci ga Allah. Jehobah ya warkar da shi kuma ‘ya ba Ayuba ninki biyu na abubuwa da yake da su dā.’ (Ayuba 42:10) Shaiɗan ya kasa karya amincin Ayuba, amma ya yi nasara wajen yaudarar mutane da yawa daga Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.”—1 Yohanna 5:19.
21. (a) Ta yaya Shaiɗan ya nuna muradinsa cewa a bauta masa? (b) Me ya sa Yesu ya ƙi ya bauta wa Shaiɗan?
21 Shaiɗan yana so mu bauta masa. Wannan ya bayyana sarai a jarraba Yesu da ya yi kusan shekara 2,000 da ta shige. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shaiɗan ya tafi da [Yesu] cikin wani dutse mai-tsawo ƙwarai, ya gwada masa dukan mulkokin duniya, da ɗaukakarsu; ya ce masa, Dukan waɗannan ni ba ka, idan ka fāɗi, ka yi mini sujjada.” Yesu ya ƙi yana cewa: “Rabu da nan, ya Shaiɗan: gama an rubuta, Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.” (Matta 4:8-10) Yesu ya san dokar Jehobah sarai, kuma ba ya son ya yi abin da Shaiɗan yake so.
Aljannu, Miyagun Ruhohi
22. Menene aljannu suka yi wa mutane?
22 Wasu mala’iku sun bi Shaiɗan wajen yi wa Allah tawaye. Waɗannan aljannun mala’iku, abokan gāban mutane ne a duniya. Miyagu ne masu ƙeta. A dā, sun kurmantar kuma sun makantar da mutane. (Matta 9:32, 33; 12:22) Sun sa wasu rashin lafiya, sun kuma haukatar da wasu. (Matta 17:15, 18; Markus 5:2-5) Har yara ma sun azabtar.—Luka 9:42.
23. (a) Menene miyagun ruhohi suke so daga wajen mutane? (b) Menene Shaiɗan da aljannunsa suka yaudari mutane suke yi?
23 Kamar Shaiɗan, waɗannan miyagun ruhohi suna so a bauta musu. Maimakon su ƙi bauta daga mutane—da fahimtar cewa bauta ta Jehobah ce—suna da muradinta, suna biɗan ta, suna ɗaukaka ta kuma. Ta wajen yaudara, ƙarya, da tsoro, Shaiɗan da kuma aljannu sun sa mutane suna bauta musu. Hakika, ba mutane da yawa ba ne suka sani cewa suna bauta wa Shaiɗan da aljannunsa. Yawancin mutane za su yi mamaki su sani cewa addininsu yana daraja Shaiɗan. Domin haka Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Abin da Al’ummai ke yanka, suna yanka ma aljanu ba Allah ba ne.”—1 Korintiyawa 10:20.
24. Menene abu ɗaya da Shaiɗan yake amfani da shi ya ruɗi mutane?
24 Hanya ɗaya da Shaiɗan da aljannunsa suka ruɗi mutane suna bauta musu shi ne ta wajen yaɗa ƙarya game da waɗanda suka mutu. Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da wannan.
^ sakin layi na 11 Alkur’ani ya yi maganar haihuwar Yesu na mu’ujiza a Sura ta 19 (Maryam). Ya ce: “Sai Muka aika ruhinMu zuwa gare ta [Maryam]. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaici. Ta ce, ‘Lalle ni, ina neman tsari ga Mai rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!’ Ya ce ‘Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne domin in bayar da wani yaro tsarkakke gare ki.’ Ta ce, ‘A ina yaro zai kasance a gare ni alhali kuwa wani mutum bai shafe ni ba, kuma ban kasance karuwa ba?’ Ya ce, ‘Kamar haka Ubangijinki ya ce, Shi a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma domin Mu sanya shi wata alama ga mutane, kuma wata rahama ce daga gare Mu. Kuma abin ya kasance wani al’amari hukuntacce.’ ”