BABI NA ƊAYA
‘Shi da Yake Matacce Ne, Yana Jawabi Har Yanzu’
1. Me ya hana ’ya’yan Adamu da Hawwa’u shiga gonar Adnin, kuma mene ne Habila yake sha’awa sosai?
HABILA ya kalli tumakinsa yayin da suke cin ciyawa a kan tudu. Bayan haka, wataƙila ya mai da hankalinsa ga wani ɗan haske da ya hanga daga nesa. Ya san cewa a inda hasken yake, akwai wani takobi mai harshen wuta da ke juyawa. Wannan takobin ya tare hanyar shiga cikin lambun Adnin. Iyayensa sun taɓa zama a lambun, amma yanzu babu wanda zai iya shiga wurin. Ka yi tunanin iska mai daɗi na maraice da ke hura sumar Habila, yayin da yake kallon sama kuma yake tunanin Mahaliccinsa. Shin zai yiwu mutum ya sake yin sulhu da Allah kuwa? Hakika, abin da Habila yake sha’awa ke nan.
2-4. A wace hanya ce Habila yake mana jawabi a yau?
2 Habila yana maka jawabi a yau. Ta yaya yake yin hakan? Za ka iya cewa hakan ba zai yiwu ba domin wannan ɗan Adamu ya mutu tun da daɗewa, kusan shekara dubu shida yanzu, kuma ya riga ya zama turɓaya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Matattu ba su san kome ba.” (M. Wa. 9:5, 10) Ƙari ga haka, ba a rubuta wani furucin da Habila ya yi cikin Littafi Mai Tsarki ba. Shin ta yaya yake mana jawabi a yau?
3 Allah ya hure manzo Bulus ya yi wannan furucin game da Habila: “Ta wurin wannan fa shi da yake matacce yana jawabi har yanzu.” (Karanta Ibraniyawa 11:4.) “Wannan” da aka ambata a ayar nan yana nufin bangaskiyarsa. Habila ne mutumi na farko da ya taɓa kasancewa da bangaskiya. Ya kamata mu yi koyi da bangaskiyarsa. Yin hakan zai nuna cewa muna sauraron jawabinsa.
4 Tun da Littafi Mai Tsarki bai yi magana sosai game da Habila ba, mene ne za mu iya koya game da shi da kuma bangaskiyarsa? Bari mu gani.
Rayuwa Jim Kaɗan Bayan An Halicci Mutum
5. Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce Habila ya rayu a “farkon duniya”? (Ka duba hasiya.)
5 Ba a daɗe da halittar mutum ba sa’ad da aka haifi Habila. Luka 11:50, 51.) Hakika, Yesu yana magana ne game da mutanen da suke da begen samun ceto. Ko da yake Habila ne mutumi na huɗu da ya taɓa rayuwa, mai yiwuwa shi ne na farko da Allah ya ga cewa ya cancanci samun ceto. * A bayyane yake cewa Habila bai yi girma cikin mutane masu halin kirki ba.
Shekaru da yawa bayan haka, Yesu ya ce Habila ya rayu a “farkon duniya.” (Karanta6. Wane irin hali ne iyayen Habila suke da shi?
6 Ko da yake mutane ba su daɗe da rayuwa a duniya ba a lokacin, amma sun riga sun faɗa cikin mummunan yanayi. Wataƙila Adamu da Hawwa’u, iyayen Habila kyawawan mutane ne masu kuzari sosai. Amma, sun riga sun yi wani kuskure mai tsanani kuma sun san da hakan. A dā su kamilai ne kuma suna da begen yin rayuwa har abada. Amma, sa’ad da suka yi tawaye da Jehobah, sai ya kore su daga cikin Aljannar da ke lambun Adnin. Adamu da Hawwa’u ba su damu da bukatun kowa ba har da na ’ya’yansu. Sun fi mai da hankali ga nasu bukatun, shi ya sa suka zama ajizai kuma suka rasa rai na har abada.—Far. 2:15–3:24.
7, 8. Wane furuci ne Hawwa’u ta yi sa’ad da ta haifi Kayinu, kuma wataƙila me take tunani?
7 Sa’ad da aka fid da Adamu da Hawwa’u daga lambun Adnin, sai suka sami kansu a tsaka mai wuya. Duk da haka, sa’ad da suka haifi ɗansu na fari, wato Kayinu, sai Hawwa’u ta ce: “Na sami namiji da taimakon Ubangiji.” Wataƙila ta yi tunanin alkawarin da Far. 3:15; 4:1) Shin Hawwa’u ta ɗauka cewa ita ce wannan macen, kuma Kayinu ne “zuriyar” da Allah ya yi alkawarinta?
Jehobah ya yi a cikin lambun game da wata mace da za ta sami “zuriya.” Wannan zuriyar ce za ta halaka wannan mugun mala’ika da ya yaudari Adamu da Hawwa’u. (8 Idan har ta yi wannan tunanin, to ta yi kuskure. Kuma idan sun tarbiyyar da Kayinu da wannan ra’ayin, to sun sa shi girman kai. Sa’ad da Hawwa’u ta haifi ɗanta na biyu, ba ta yi wani furucin yabo game da shi ba. Maimakon haka, sun sa masa suna Habila, wanda mai yiwuwa yana nufin “Wofi.” (Far. 4:2) Wataƙila sun sa masa wannan sunan domin sun ɗauka cewa Kayinu zai fi shi hankali.
9. Mene ne iyaye za su iya koya daga Adamu da Hawwa’u?
9 A yau, iyaye za su iya koyan darasi daga Adamu da Hawwa’u. Idan ba ku lura ba, kalamanku da ayyukanku za su iya sa yaranku su zama masu fahariya da mugun buri da kuma son kai. A wani ɓangare kuma, za ku iya tarbiyyar da yaranku su ƙaunaci Jehobah kuma su ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Abin baƙin ciki, Adamu da Hawwa’u ba su cika aikinsu na tarbiyyar da yaransu da kyau ba. Duk da haka, zuriyarsu ta kasance da bege.
Me Ya Sa Habila Ya Kasance da Bangaskiya?
10, 11. Wace irin sana’a ce Kayinu da Habila suka koya, kuma wane irin hali ne Habila yake da shi?
10 Da alama cewa sa’ad da Kayinu da Habila suke girma, Adamu ya koya musu sana’ar da za su yi don su taimaka wajen biyan bukatun iyalin. Kayinu ya zama manomi kuma Habila ya zama makiyayi.
11 Amma da shigewar lokaci, Habila ya yi abin da ya fi kiwon tumaki muhimmanci, wato ya koyi kasancewa da bangaskiya. Daga baya Bulus ya yi magana game da wannan halin. Ka tuna cewa babu mutumin da ya kafa wa Habila misali mai kyau. Mene ne ya taimaka masa ya yi imani da Jehobah? Bari mu tattauna abubuwa uku da wataƙila suka taimaka masa ya yi hakan.
12, 13. Ta yaya halittun Allah suka ƙarfafa bangaskiyar Habila?
12 Halittun Jehobah. Hakika, Jehobah ya la’anta ƙasa shi ya sa ƙaya da sarƙaƙƙiya suka tsiro kuma ƙasa ta daina ba da amfani sosai. Duk da haka, iyalin sun sami abincin da suke bukata don su rayu. Ƙari ga haka, Allah bai la’anta dabbobi da tsuntsaye da kifaye da tsaunuka da ruwaye da kuma abubuwan da ke sararin sama ba. Duk inda Habila ya juya, sai ya ga halittu da suke nuna cewa Jehobah wanda ya halicci dukan abubuwa, Allah ne mai ƙauna da hikima da kuma nagarta. (Karanta Romawa 1:20.) Tabbas, yin bimbini a kan waɗannan abubuwan sun taimaki Habila ya ƙara kasancewa da bangaskiya.
13 Babu shakka, Habila ya keɓe lokaci don yin tunani game da Jehobah. Ka yi la’akari da lokacin da yake kiwon tumakinsa. Aikin makiyayi ya ƙunshi yin yawo sosai. Saboda haka, yakan kai dabbobinsa kiwo a kan tuddai, a cikin kwari da kuma a hayin kogi, wato a duk inda akwai ciyawa da ruwa da kuma laima. Tumaki suna bukatar kulawa sosai, kamar dai Allah ya halicce su ne don ’yan Adam su ja-gorance su kuma su kāre su daga haɗarurruka. Shin Habila ya fahimci cewa shi ma yana bukatar ja-gora da kāriya da kuma kula daga Allah, wanda yake da hikima da kuma iko fiye da ’yan Adam? A bayyane yake cewa ya nemi ja-gora daga Allah sa’ad da yake addu’a kuma hakan ya sa ya ƙara kasancewa da bangaskiya.
14, 15. Ta yaya alkawuran Jehobah suka ba Habila abubuwa da dama da zai yi bimbini a kai?
14 Alkawuran Jehobah. Babu shakka, Adamu da Hawwa’u sun gaya wa ’ya’yansu dalilin da ya sa Jehobah ya kore su daga lambun Adnin. Saboda haka, Habila yana da abubuwa da dama da zai yi bimbini a kai.
15 Jehobah ya ce zai la’anta ƙasa. Habila ya ga cikar wannan annabcin da yake ƙaya da sarƙaƙƙiya sun tsira. Jehobah ya ce Hawwa’u za ta sha wahala sa’ad da take da juna biyu kuma za ta yi naƙuda. Habila ya shaida cikar waɗannan kalmomin sa’ad da ake haifan ƙannensa. Jehobah ya san cewa rashin biyayya da suka yi zai sa Hawwa’u ta bukaci Adamu ya ƙaunace ta fiye da kima, shi kuma zai mallake ta. Habila ya ga yadda hakan ya faru tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa. Yadda waɗannan annabce-annabcen suka cika, sun nuna wa Habila cewa maganar Jehobah tabbatacciya ce. Saboda haka, Habila ya ba da gaskiya cewa alkawarin da Allah ya yi game da “zuriyar” zai cika. Wannan zuriyar ce za ta magance matsalolin ’yan Adam da suka soma a lambun Adnin.—Far. 3:15-19.
16, 17. Mene ne mai yiwuwa Habila ya koya daga cherubim da Jehobah ya sanya a lambun Adnin?
Farawa 3:24.
16 Bayin Jehobah. Ko da yake a lokacin, babu mutum mai bangaskiya da Habila zai yi koyi da shi, amma akwai mala’iku a duniya da suka kafa wa Habila misali mai kyau. Sa’ad da Jehobah ya kori Adamu da Hawwa’u daga lambun Adnin, ya ɗauki mataki don ya tabbata cewa su da yaransu ba za su sake shiga wannan lambun ba. Jehobah ya sanya cherubim da kuma takobi mai harshen wuta da ke juyawa babu fashi a hanyar shigan lambun, domin kada wani ya shiga. Waɗannan cherubim mala’iku ne masu matsayi sosai.—Karanta17 Ka yi tunanin yadda Habila ya ji sa’ad da yake kallon waɗannan cherubim a lokacin da yake yaro. Da ganin siffarsu, Habila ya fahimci cewa suna da iko sosai. Kuma ‘takobin’ nan mai harshen wuta da ke juyawa babu fashi ma abu ne mai ban al’ajabi. Shin sa’ad da Habila yake girma, ya taɓa ganin lokacin da cherubim ɗin suka gaji kuma suka bar aikinsu? A’a. Dare da rana, shekara da shekaru, waɗannan halittu masu iko da basira sun ci gaba da kasancewa a wurin. Ta hakan, Habila ya gane cewa Jehobah yana da bayi masu adalci da suke bauta masa babu fashi. Akasin iyalinsa da ba su yi biyayya ga Jehobah ba, Habila ya lura cewa waɗannan cherubim suna da aminci kuma suna biyayya ga Jehobah sosai. Babu shakka, misalin waɗannan mala’ikun ya ƙarfafa bangaskiyarsa.
18. Mene ne zai iya sa mu kasance da bangaskiya a yau?
18 Habila ya daɗa ƙarfafa bangaskiyarsa ta wajen yin bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya bayyana game da kansa, ta halittunsa da alkawuransa da kuma misalan bayinsa. Idan muka yi la’akari da misalinsa, za mu ji kamar yana mana jawabi, ko ba haka
ba? Matasa musamman za su iya kasancewa da gaba gaɗi cewa zai yiwu su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah ko da mene ne danginsu suka yi. Littafi Mai Tsarki da halittun Allah da kuma misalan amintattun bayinsa na zamaninmu, za su iya taimaka mana mu kasance da bangaskiya.Me Ya Sa Allah Ya Karɓi Hadayar Habila?
19. Mene ne Habila ya koya da shigewar lokaci?
19 Yayin da Habila yake daɗa samun dalilan kasancewa da bangaskiya, ya nemi hanyar da zai bayyana hakan. Amma, mene ne ɗan Adam zai iya ba Mahaliccin sama da ƙasa? Hakika, Allah ba ya bukatar kyauta ko kuma taimako daga wajen ’yan Adam. Da shigewar lokaci, Habila ya fahimci cewa idan yana da kyakkyawar aniya kuma ya miƙa hadaya da dukan zuciyarsa, zai iya faranta wa Jehobah rai.
20, 21. Wace irin hadaya ce Kayinu da Habila suka miƙa wa Jehobah, kuma mene ne Jehobah ya yi?
20 Habila ya shirya ya miƙa hadaya da tumakinsa. Ya zaɓi tumaki mafi kyau, wato ’ya’yan fari a cikin tumakinsa kuma ya yi hadaya da gaɓoɓi mafi kyau na naman. Kayinu ma ya so Allah ya albarkace shi, sai ya shirya amfanin gonarsa don ya miƙa hadaya da shi. Amma, muradinsa ba kamar na Habila ba. Yayin da waɗannan ’yan’uwa biyu suke ba da hadayunsu, aniyar kowannensu ta bayyana a fili.
21 Wataƙila Kayinu da Habila sun ƙona hadayun a kan bagadai da suka gina kusa da inda cherubim ɗin suke. A lokacin, waɗannan cherubim ne kaɗai wakilan Jehobah a duniya. Me ya faru? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji ya kula da Habila da baikonsa.” (Far. 4:4) Ayar ba ta ambata yadda Jehobah ya bayyana ra’ayinsa ba.
22, 23. Me ya sa Jehobah ya karɓi hadayar Habila?
22 Me ya sa ya karɓi hadayar Habila? Shin irin hadayar da Habila ya miƙa ce ta sa hakan? Habila ya miƙa hadaya da abu mai rai, wato abu mai jini kuma a gaban Allah jini yana wakiltan rai. Wataƙila Habila ya fahimci muhimmancin hakan, shi ya sa ya yi hadayar da abu mai rai. Ƙarnuka da yawa bayan haka, Allah ya bukaci a yi masa hadaya da rago marar tabo. Wannan yana wakiltar hadayar Ɗansa marar aibi, wato “Ɗan Rago na Allah,” wanda daga baya ya zub da jininsa a madadin ’yan Adam. (Yoh. 1:29; Fit. 12:5-7) Amma da alama cewa Habila bai san da wannan shirin ba.
23 Duk da haka, Habila ya yi hadaya da tumaki mafi kyau daga cikin garkensa. Jehobah ya karɓi hadayar Habila kuma ya amince da shi. Habila ya yi hakan ne domin yana ƙaunar Jehobah kuma yana da bangaskiya sosai.
24. (a) Me ya sa Allah ya ƙi karɓan hadayar Kayinu? (b) Ta yaya mutane da yawa a yau suke da irin ra’ayin Kayinu?
Far. 4:5) Shin amfanin gona da Kayinu ya miƙa ne ya sa Allah ya ƙi karɓar hadayarsa? A’a, domin daga baya, Jehobah ya bar mutanensa su yi hadaya da amfanin gona. (Lev. 6:14, 15) Amma, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa ayyukan Kayinu “miyagu ne.” (Karanta 1 Yohanna 3:12.) Kayinu yana ganin Allah zai amince da ibadar da ba a yi da zuciya ɗaya ba. A yau ma, mutane da yawa suna da irin wannan ra’ayin. Ba da daɗewa ba, abin da Kayinu ya yi ya nuna cewa bai yi imani da Jehobah ba kuma ba ya ƙaunarsa.
24 Ba hakan yake da Kayinu ba. Jehobah bai “kula da Kayinu da baikonsa ba.” (25, 26. Wane gargaɗi ne Jehobah ya ba Kayinu, amma mene ne Kayinu ya yi?
25 Sa’ad da Kayinu ya ga cewa Allah bai amince da hadayarsa ba, sai ya fara gāba da Habila maimakon ya yi koyi da shi. Jehobah ya ga cewa Kayinu ya fara kasancewa da baƙar aniya a zuciyarsa, sai ya yi masa gargaɗi. Jehobah ya gaya masa cewa mugun tunani da yake yi zai kai shi ga yin zunubi. Ya kuma ce idan ya canja halinsa, zai “amsa” roƙonsa.—Far. 4:6, 7.
26 Kayinu ya yi watsi da gargaɗin da Allah ya yi masa. Sai ya gaya wa ƙanensa su fita yawo a cikin gona. Sa’ad da suka isa wurin, sai Kayinu ya kashe shi. (Far. 4:8) Ta hakan ne Habila ya zama mutum na farko da aka kashe saboda imaninsa. Ya mutu, amma da sauran rina a kaba.
27. (a) Me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa za a ta da Habila daga matattu? (b) Me ya kamata mu yi don mu ga Habila a nan gaba?
27 Allah yana bukatar ya saka wa Habila, kuma ya yi hakan ta wajen hukunta Kayinu. (Far. 4:9-12) Za mu iya koyan darasi daga bangaskiyar Habila. Habila bai daɗe a duniya kamar tsararsa ba, mai yiwuwa wajen shekara ɗari ne kawai ya yi. Duk da haka, ya yi rayuwar da ta faranta wa Allah rai. Ya mutu da sanin cewa Jehobah, Ubansa na sama yana ƙaunarsa kuma ya amince da shi. (Ibran. 11:4) Saboda haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ba zai manta da shi ba, kuma zai ta da shi daga matattu sa’ad da ya mai da duniya aljanna. (Yoh. 5:28, 29) Za ka so ka gan shi a aljanna? Idan amsarka e ce, to ka ƙudura cewa za ka saurari jawabinsa kuma ka yi koyi da mafificiyar bangaskiyarsa.
^ sakin layi na 5 Wannan furucin “farkon duniya” yana nufin watsa iri, kuma hakan yana da alaƙa da haihuwa. Saboda haka, ya shafi zuriyar ’yan Adam da aka fara haifa. Amma, me ya sa Yesu ya ce Habila ya rayu a “farkon duniya,” maimakon Kayinu wanda shi ne ɗan fari? Domin tunanin Kayinu da ayyukansa sun nuna cewa da gangan ne ya yi tawaye da Jehobah. Da alama cewa hukuncin da aka yanke wa Kayinu ɗaya ne da na iyayensa, wato ba za a ta da shi daga matattu ba kuma ba za a gafarce shi ba.