Wasika Daga Hukumar Da Ke Kula Da Ayyukan Shaidun Jehobah
’Yan’uwanmu:
An soma wallafa wani talifi mai jigo “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” a Hasumiyar Tsaro na wa’azi ta Janairu-Maris 2008. Tun daga lokacin ana wallafa wannan sabon talifin a kai a kai don mu amfana!
Mene ne waɗanda suka karanta wannan talifin suka ce? Bayan wata ’yar’uwa ta karance talifin da ya yi magana game da Martha, sai ta ce: “Na yi dariya sa’ad da nake karatun domin da ni da ita duk kanwar ja ce. A duk lokacin da nake da baƙi, ina yawan shagala da aiki kuma in mance cewa ya kamata in ɗan shaƙata da su.” Sa’ad da wata matashiya ta karance labarin Esther, sai ta ce: “Muna iya damun kanmu da tufafi da kuma adon da ke tashe. Ko da yake ya kamata mu riƙa yin shiga mai kyau, amma bai kamata mu wuce gona da iri ba.” Ta daɗa cewa: “Jehobah ya fi yin la’akari da halayenmu.” Bayan wata ’yar’uwa kuma ta karance talifin da ya yi magana game da manzo Bitrus, ta ce: “Na ji daɗin karanta talifin nan sosai. Sa’ad da nake karanta labarin, na ji kamar ina wurin sa’ad da abubuwan suke faruwa.”
Waɗannan ’yan’uwan da muka ambata da kuma wasu da suka rubuta wasiƙa don su nuna cewa sun amfana daga talifin, sun tabbatar da abin da manzo Bulus ya ce: “Gama iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu.” (Rom. 15:4) Hakika, Jehobah ya sa an rubuta waɗannan labaran cikin Littafi Mai Tsarki don su koya mana muhimman darussa. Za mu iya koyon darussa daga misalansu, ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah.
Muna ƙarfafa ku ku karanta wannan littafin da zarar kun karɓe shi. Yaranku za su ji daɗin littafin idan kun yi amfani da shi a Bautarku ta Iyali. Kada ka fasa zuwa taro sa’ad da ake tattauna shi a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Kada ka karanta shi a garaje, amma ka yi tunani da kuma bimbini a kansa. Ka ga abubuwan da maza da mata da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suka gani kuma ka ji ƙarar da suka ji. Ka yi tunani a kan abin da suka yi sa’ad da suke cikin wani yanayi kuma ka yi tunani a kan abin da za ka yi da a ce kai ne.
Muna farin cikin aika muku wannan littafin. Muna fatan cewa zai zama albarka a gare ku da kuma iyalinku. Muna aika muku da ƙaunarmu da kuma fatan alheri,
Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah