SASHE NA 4
Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace
“Kowane ƙuduri a bisa shawara ya kan kafu.”
Dukanmu muna bukatar kuɗi don mu biya wa iyalanmu bukatunsu. (Misalai 30:8) Littafi Mai Tsarki ma ya ce, “dukiya, kāriya ce.” (Mai-Wa’azi 7:12) Tattauna batun kuɗi a matsayin ma’aurata yana iya zama abu mai wuya, amma kada ku bar kuɗi ya jawo matsala a tsakaninku. (Afisawa 4:32) Ma’aurata suna bukatar su amince da juna kuma su yanke shawara tare a kan yadda za su kashe kuɗi.
1 KU YI SHIRI DA KYAU
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “In wani daga cikinku na son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin?” (Luka 14:28, Littafi Mai Tsarki) Yana da muhimmanci ku tsara yadda za ku kashe kuɗinku. (Amos 3:3) Ku tsai da shawara a kan abubuwan da kuke bukatar ku saya da kuma yawan kuɗin da kuke so ku kashe wajen sayensu. (Misalai 31:16) Ko da kuna da kuɗin sayan wani abu, ba lallai sai kun saye shi ba. Ku ƙoƙari ku guji karɓan bashi. Kada ku sayi abin da ba ku da kuɗinsa.—Misalai 21:5; 22:7.
SHAWARA:
-
Idan kuɗin da kuka keɓe don yin sayayya a wata ya yi saura, ku zauna ku tattauna abin da za ku yi da shi
-
Idan kun lura cewa kuɗin da kuka kashe ya fi wanda kuka samu, ku tsara yadda za ku rage sayayyar da kuke yi. Alal misali, ku riƙa dafa naku abincin maimakon sayan abinci a waje
2 KU FAƊI GASKIYA KUMA KU ƊAUKI KUƊI YADDA YA DACE
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Mu yi abubuwan da ke daidai, ba wai a gaban Ubangiji kaɗai ba, har ma a gaban mutane.” (2 Korintiyawa 8:21, LMT) Ku gaya wa junanku gaskiya game da yawan kuɗin da kuke samu da kuma wanda kuke kashewa.
Ku riƙa tattaunawa tare sa’ad da kuke so ku tsai da shawara a kan batun da ya shafi kuɗi. (Misalai 13:10) Tattauna batun kuɗi zai taimaka muku ku zauna lafiya a aurenku. Kada kowannenku ya ɗauka cewa kuɗin da yake samu nasa ne shi kaɗai, domin kuɗin na iyalin ne. —1 Timotawus 5:8.
SHAWARA:
-
Ku yanke shawara a kan yawan kuɗin da kowannenku zai iya kashewa ba tare da neman izini ba
-
Kada ku jira sai matsalar kuɗi ta taso kafin ku tattauna batun kuɗi